Monday, July 30, 2018

TARIHIN FACEBOOK

KADAN DAGA TARIHIN YADDA AKA QIRQIRI
FACEBOOKA ranar hudu ga watan
February 2004 Mark Zuckerberg, wani bayahude
dan garin Newyork mazaunin garin Palo Alto,
California da ya karyata akwai Allah ya fara
watsa shafin Facebook a duniya daga dakinsa
na makaranta. Duk da dai ance kwana shida da
watsa shafin wasu dalibai uku suka zarge shi
da cewa yayi masu alkawarin zai bude masu
website amma ya sace fasaharsu ya bude nasa,
maganar da tafi inganci ita ce ya saci fasahar
wani website din makarantarsu ne mai suna
uConnect. Can kuma sai abokansa su hudu
'yan dakinsu a Jami'ar Harvard din da ya kasa
gamawa amma yake ikirarin cewa ya gama suka
maka shi kotu a kan cewa ya zagaya ta bayen
fage ya bude website din da su biyar suka
hana idanunsu barci wajen kirkira. Kotu dai ta
sa ya biya uConnect din da kuma abokansa da
wani kaso. sannan an tabbatar cewa ciwon
rashin ganin kalolin ja da kuma kore ne ya
sanya shi sanyawa shafin launi fari da ruwan
bula wanda sune yafi gani sosai Kada kuyi
mamakin ganin yadda 'yan matan mu ke saka
hotunansu kamar suna gasar kyau domin
asalin saboda dandalin ya bude shi ne don
daliban hostels din makarantar su wai saboda
su san juna ta hanyar zaban hoton mace ko
namijin da yafi kyau. Ya taba samun tangarda a
awani lokacin don an rufe shi na sati daya
saboda makarantar tayi zargin cewa yana dauke
hankalin dalibai sai dai an barshi ya cigaba da
aikin bayan an lura da irin makudan kudin da
shafin yake samu ta hanyar yiwa wasu
kamfanoni tallace tallace Facebook ya kusa kai
shekara goma sha hudu da watsuwa a duniya,

No comments:

Post a Comment