Wednesday, May 13, 2020

KETA SARARIN SAMANIYA

KETA SARARIN SUBHANA

Tsawon miliyoyin shekaru babban abinda ya fi jan hankali da burge Dan Adam shine yadda Tsuntsaye da kwari ke iya tashi sama. Wannan burgewa ta zama kishi domin mutane, duk da cewa Allah bai hore musu wata halitta a jikinsu da za su iya tashi ba, amma an yi ta kokarin kirkirar fuka-fukai don kwaikwayon halittu masu tashi. Mutane daban-daban daga al'ummomi da dama sun gwada tashi sama ta hanyar kwaikwayo, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma rasa gabobi. Duk da cikas da aka fuskanta maimaikon kokarin ya ragu sai ya ringa habaka. Cikin suratul Rahman sai Allah ya ce mana
Q55:33" Ya ku (gungun) aljanu da mutane, idan zaku iya ketasararin sammai da kasa, to ku keta. Amma sai da izinin Allah zaku iya ketawa"
Wannan aya ta zama daya daga cikin ayoyin mu'ujizar Qur'ani domin ta fadi wani abu da zai faru a gaba.
Abbas Ibn Firnas, mutumin Kasar Andalusia wanda ya rayu a garin Cordoba, shine masanin kimiyya na farko a tarihi wanda ya fara kera jirgin sama mai fuka-fuki kuma ya tashi sama ya yi zagaye har na kimanin mintuna goma a gaban bainar jama’a a shekarar 875 AD, wato kusan karni biyu da rabi bayan wafatin manzon Allah. Amma kamar yadda turawa su ka saba sace wa musulmi darajar farko ta kirkirar abubuwa da dama, ya sa ba’a jin sunan wannan dan taliki a hurumin mutum na farko da ya fara kera jirgin sama. Wannan bincike na sa bai sami ci gaba ba har daular musulunci ta Andalus ta rushe, amma ina zaton aikinsa ne ya janyo mashahurin masanin kimiyya na kasar Rum, wato Leonardo Da Vinci (1452), bayan kimanin shekaru 600, ya ba shi karsashin nazari a wannan fage inda har ya yi wasu zane-zane da ke nuna za'a iya kirkirar na'ura da za ta iya tashi ba tare da an kwaikwayi yin fuffuke irin na dabbobi ba. Duk da haka wannan zane bai yi tasiri ba har bayan kimanin shekaru 400 da mutuwar sa. A farkon karnin da ya gabata ne cikin shekarar 1903 wasu yan uwa guda biyu (Wilbur Brothers) na kasar Amurka su ka cimma nasarar yin inji na farko da ya bar doron kasa kuma yayi tafiya a cikin sararin samaniya. Wannan nasara ta samu ne sakamakon gane amfani da hanyoyin nan guda hudu dake ba kowane abu mai tashi damar iyo a cikin iska (4 forces of Aerodynamics) wato Ingiza (Thrust), Tirjiya (Drag), nauyi (Weight) da kuma karfin dagawa sama (Lift). Samun daidaiton wadanna abubuwa ke bada damar iyo a iska domin ingiza na samuwa ne daga karfin na'ura da kuma iska, haka nan tirjiya na samuwa ita ma daga na'ura da iska sai kuma karfin dagawa wadda ta ta'allaka ga nauyi dake dogaro ga maganadisun dake jan komai kasa (Gravity) wadda karfin inji ke iya gujewa. Ko daga wadannan abubuwa da ke baiwa jirgi ikon tashi sama, mai lura na iya gane cewa babu wani abu da zai iya tashi sama sai da izinin Allah domin da zarar Allah ya zuke iskarsa kuma ya dankare maganadisu (Gravity) to babu wani abu da zai iya dagawa sama ko da kuwa bai kai auduga nauyi ba.
Bayan wadancan abubuwa hudu da dole sai sun hadu ake iya tashi sama, akwai kuma wasu abubuwa dake da tasirin gaske wajen sauka da tashin jiragen sama:
--Yanayin Dumi (Temperature): da ke haifar da yadda iska zata kasance wajen nauyinta (Density) na daya daga ciki. Idan iska bata da nauyi jirgi ba zai iya tashi ba amma idan tayi nauyi sai ya iya tashi
--Iska: har ila yau, iska da ke kadawa ita ce ke bada saitin bangaren da jirgi zai tashi ko kuma ya sauka domin baya tashi sai ta daura da nahiyar da take kadawa haka wajen sauka sai ta daura da nahiyar da iskar ke kadawa (wato idan iska na kadawa yamma sai jirgi ya sauka ta gabas), shi yasa ake ganin wani jan kyalle mai kama da bututu a gefen titin da jiragen sama ke tashi, ya na nuna inda iska ke kadawa
--Layukan tsaye da na kwance a doron duniya (Longitudes da lattitude): na taimakawa matuka jirgi wajen gane nahiyoyi
--Mahadar wadancan layuka (Co-ordinates): Dukkan garuruwan dake doron kasa na da mahadar wadannan layuka da ke kusa da su kuma na kano daban yake da na kaduna ko Abuja. Shine yasa duk da cewa babu tituna a sama kuma matukan jirgin sama ba sa iya hangen doron kasa amma amfani da wannan mahada ya na sa su gane sun zo inda za su je ba tare da hakikanin ganin wajen ba
--Doron maganadisun duniya na arewa (North magnetic pole): Wanda duk ya san compass da ake sawa a dardumar sallah don nuna al-qibla yana ganin wata allura da ke kwance ta na nuna nahiya. To ita allurar a koda yaushe ta na fuskantar inda wannan maganadisu na arewa yake don haka a duk inda ka ke da zarar ka gane arewa dole ne ka gane ina sauran jihohin gabas, kudu da yamma su ke.
--Zangon rediyo (frequency) Tukin jirgi ba zai yiwu ba sai da zangon rediyo domin kusan mafi mahimmancin na'urorin da ake amfani da su ta hanyar zangon rediyo ake amfanin da su, misalin na'urarorin da ke amfani da zangon rediyo wajen jagorancin jirgi a wajen sauka (ELS), da na'urar gane nisa (DME), da na'urar gane nahiya nan take (Automatic direction finder) da kuma naurar tangaraho da rada dukkanninsu ta zangon rediyo ake amfani dasu.
Wadannan abubuwan da na lissafa sai da su jirgin sama zai iya tashi kuma dukkansu babu wani abu da bai dogara da wani abu halittacce daga ubangiji ba. Hatta shi kansa injin jirgi da mutum ne ya kirkire shi ba zai yi aiki ba sai da iska da Allah ya halitta. Domin ga yadda injin jirgi ke aiki: wato da zarar an kunna shi sai wasu manyan farfeloli da ke ciki su fara juyawa a guje kuma an kera su yadda idan suna juyawa sai su dinga zukar iska daga waje da karfin gaske (da mutum zai tsaya saitin su sai iskar ta fizgo shi cikin injin). Da zarar iskar ta shiga cikin injin sai ta dunkule saboda karfinta da kuma rashin sarari, sai a watsa mata fetur wanda zai sa ta fara konewa cikin gaggawa (idan ka leka cikin injin sai kaga wuta ce ta ke ci gagga-gagga) wannan konewa sai ta dada kumburawa da fadada wannan iskar yadda dole sararin wajen zai mata kunci dole ta nemi hanyar ficewa cikin gaggawa. Fitar wannan iska da karfi ke baiwa jirgin kuzarin zabura (misali shine idan ka cika balan-balan kuma sai ka saki bakinta za ka ga ta fice a guje tana zarya). A takaice haka ne yadda injin jirgi ke aiki, ka ga lallai shi kansa idan babu iskar da Allah ya halitta ba zai yi tasiri ba. Wannan shine manufar waccan aya da Allah ke cewa sai fa da izininsa za a iya keta sararin sama.
A yau Dan Adam ya kai tsaikon ba jiragen sama wadanda ke kara-kaina a doron duniya ba, har wadanda ba su da matuka an kirkira su na tafiye-tafiye zuwa wasu duniyoyi da ke cikin rukunin tauraron mu, wato Rana. Cikin irin wadannan jirage wanda ya fi shahara sune yan tagwayen jiragen da kasar Amurka ta harba daf da juna a shekarar 1977 wandanda aka yi wa lakabi da Voyager I da Voyager II. A yanzu haka shi wannan jirgi na Voyager 1 da ke gudun kilomita dubu 61,200 a awa guda, a ranar yau ta 20 ga watan Mayu na 2019, ya yi tafiyar shekaru 41 da wata 8 da kwana 15, tun a shekarara 2012 ya fice daga rukunin tauraronmu. Ya kasance jirgi na farko da ya iya dauko hoton jerin rukunin duniyoyi da ke kewaya rana. Wannan jirgi zai ci gaba da lulukawa sama’u har zuwa shekarar 2025 lokacin da na’urorinsa za su daina aiki. Tsarki ya tabbata ga ubangiji wanda ya baiwa Dan Adam irin wannan basira ta kera jirgi wanda ake sarrafawa daga doron duniya, ya yi tsawon shekaru ya na tafiya tare da bada bayanai na hotuna ga abubuwan da ya ke karo da su. A wannan jirgi ne Carl Sagan ya sa aka dauki sautin gaisuwa da yaruka daban daban na duniya ko da Allah ya sa watarana wannan jirgi zai karo da wasu halittu a hanyarsa.

No comments:

Post a Comment