Monday, May 18, 2020

SIFFOFIN MUNAFUNCI






SIFFOFIN MUNAFUNCI
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ، وَإِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ، متفق عليه؛
An karɓo daga Abdullahi dan Amru (R.A) daga Annabi (SAW) yace:
Abubuwa guda hudu wanda suka kasance tare dasu ya kasance munafiki, wanda siffa daya ta kasance tare da shi daga hufun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da shi, har sai ya bar ta.
1. Idan yayi magana, ya zamanto sai yayi karya.
2. Idan yayi alkwari, sai yasaba.
3. Idan an yi rigima dashi, sai ya ketare dokar Allah.
4. Idan kuma aka Qulla alƙawari, to zai yaudare ka.
Bukhari (34) da Muslim(58) suka rawaito shi.
SHARHI
--------------
Wadannan siffofi guda hudu idan suka taru ga mutum, to ya zama munafiki, in kuwa daya ce, to wanan ya zama yanada siffa ta munafunci.
To amma abin da ake nufi da munafunci a nan gurin, munafuncin aiki.
Don munafunci iri biyu ne kamar haka:
1. Akwai Annifaqul Amali, munafunci a cikin aiki.
Da Kuma
2. Annifaƙul I’itiqadi, munafunci na zuci, wanda yake nufin mutum ya bayyana musulunci a zahiri, amma a zuciyarsa yana nan kan addininsa na kafirci.
To duk mai wannan ba musulmi ba ne, ko da ya rantse.
Don munafukai masu irin wannan, sai da suka zo wajen Annabi (SAW) suka rantse suka ce sun yarda da shi amma Allah ya qaryata su Allah madaukakin sarki yace:
اذا جاء ك المنفقون قالو انك لر سو ل الله و الله يعلم انك لر سو له و
الله ان المنفقين لكذ بون ( المنا فقون:
(Idan Munafukai suka zo wajenka, suka ce, "Mun shaida kai Manzon Allah ne!” Allah ya san kai manzonsa ne, Allah ya shaida hakika Munafukai karya suke ) (Al-munafuƙun 1)
و من الناس من يقول ءامنا با الله وباليوم الا وم هم ب مو منين: البقرة.
(A cikin mutane akwai wadanda za su ce, "Mun yi imani da Allah da ranar ƙarshe"alhali su ba Muminai ba ne) [Al-Baƙara: aya ta 8].
To wannan shi ne munfuncin zuci, kudure kafirci a zuciya, amma mutum yana bayyana musulunci a harshensa, wannan ba musulmi ba ne, kuma irin wadannan su ne Allah yace akansu,
ان المنفقون فى الدرك الاسفل من النار ولن تجد لهم نص) النساء:
(Hakika munafukai suna kasan wuta, kuma ba zaka sami wani mataimaki a tare da su ba.) [Annisa’i]
ان المنفقون بخد عو ن الله وهو خد عهم و اذ قا مو الى الصوة قامو كسالى يراءون الناس ولا يذ كرو ن الله الا قليلا) النساء:
(Haqiqa munafukai suna yaudarar Allah, Amma Allah yana mayar musu da yaudararsu akansu, idan suka tashi yin sallah, sai su tashi suna kasala, suna yi (Sallar) don mutane su gani, ba sa ambaton Allah, sai zan kadan) [Annisa’i:142]
Duk ayar da tazo ta nuna dawwama a cikin wuta ga munafukai, to da irin wadannan munafukai take.
2. Kashi na biyu shi ne, munafunci a aikace.
Zuciyarka da imani, amma kana da wani aiki wanda bai kamata a ce kai musulmi ne kake yi ba, aikin irin aikin munafukai ne.
To irin wannan, idan mutum ya yi, sai ace ya yi aikin munafunci, amma ba ma cewa shi munafuki ne, sboda faɗin Allah a kansa, "Haƙiƙa munafukai suna qasan wuta...." wannan ba ta shafe shi ba.
Saboda kar mutum ya yi amfani da wannan hadisin, ya kafirta ‘yan uwansa, batare da ya fahimta ba, dole sai ya ware, Annifaƙul I’itiqadi, wanda yayi shi ya zama kafiri.
Amma Annifakul Amali, duk wanda ya yi shi yana nan a matsayinsa na musulmi, amma fasiƙin musulmi ne.
Allah (S.W.T) ya kiyaye imaninmu.

No comments:

Post a Comment