Friday, December 21, 2018

TARIHIN IMAM FAKHRUDDIN AL RAZI

TARIHIN IMAM FAKHRUDDIN AL RAZI
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Cikakken sunansa shine Abu Abdullahi Muhammad Ibn Umar al Husayn al Taymi al Bakri al Tabari'at fakhraddin al Razi. Amma anfi masa lakabi da 'shaikul Islam' ko kuma ace 'Al fakhrur Razi', ko 'Sultan Al Mutakallimina', ko kuma ace masa 'Shaykul Mushakkiqina'.
Shi Gangaran ne a fannin Ilimi. Gwanin tafsirin Al-kur'ani, Jagaba a ilimin falsafa, Shugaba neshi a ilimin Balaga, zakaqaquri ne kuma a ilimin lissafi..
An haife shi a a shekara ta 1149 miladiyya, a wani gari mai suna Rey wanda yake a cikin kasar Iraqi. A hannun mahaifinsa ya soma ɗaukar darasu sannan daga bisani ya soma zagayawa wajen malumma domin ɗaukar ilimi daga garesu, harma an bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen nan da ake yiwa lakabi da 'Al Majd al Jilil' masu bin falsafa da koyarwa ta Imamuna Ghazali.
Kusan ana iya cewa a neman ilimi da karantarwa Imam Ar Razi ya k'arar da kwanukan rayuwarsa, domin kuwa ance ya rinka bin garu-ruwa na nesa dana makwabta akan haka, har daga bisani Allah ya karɓi ransa a wani gari mai suna Herar dake kasar Afghanistan.
Ance Imam Ar Razi yayi muhawara da masana daban daban na zamaninsa, sannan ya rubuta littattafai na ilimi kimanin guda ɗari, ya kuma tara ɗumbin dukiya da ɗalibai masu yawa a rayuwarsa, har saida takai akwai lokacin da idan zaiyi tafiya izuwa wani gari ɗalibai 300 keyi masa rakiya, sannan mutane dubu ɗaya keyi masa dakon dukiyarsa wadda ta kunshi zinare da azurfa da kayayyakin alatu.
Imam Razi, ya rayu a wani lokaci mawuyaci, lokacin da ake ganiyar rikici tsakanin mabiya shi'a da Sunni a Iran, a lokacin da rikicin mulki ya mamaye daular farisa, a lokacin da kuma sa-in-sa ta dabaibaye malumma akan falsafar wanda ya kamata ayi biyayya dashi tsakanin Imam Ibn Sina da kuma Imam Al Ghazali.
Saboda haka a wancan lokaci Imam Ar Razi sai ya zama mabiyin Sunni, kuma ya nesanta kansa da neman mulki, tare da ɗosanuwa bisa tafarkin falsafar Imam Ghazali.
Kasancewar sa gwani a fannin tsara zance da iya muhawara, yasa duk wani malami na zamanin ke shakkar ya kalubalanceshi akan inda yasa gaba, domin matsawar za'a zubeta, to shine zaiyi nasara. Amma kuma hakan, sai ya jaza masa hasada da bakin jini a wurin malamai 'yan uwansa. Har ana tsammanin silar mutuwarsa yazo ne a bisa guba da mabiya ɗarikar Karramiyawa suka sanya masa a abinci.
A fannin Ilimin Alkurani mai girma, Imam Razi ne marubucin littafin tafsirin nan mai mujalladi takwas mai suna 'Mafatihul Ghaib', da kuma wani littafin daya rubuta mai suna 'Aja ibul Quran' wanda ya tattaro abubuwan mamaki da al'ajabi da suka zo a cikin alkurani mai girma. Don haka ka tsaye ana iya cewa yayiwa Al-kur'ani hidima.
Dangane da falsafar sa a ilimin sararun samaniya kuwa, Ar Razi ya taɓa faɗa cewa "Khalala la nihayata laha" (watau ita sama an halicce ta ba tare da tana da iyaka ba).
Sannan kuma yayi tsokaci a game da falsafar cewa duniyar mu kaɗaice ke ɗauke da bil'adama a duk faɗin maɗaukakiyar duniya, inda ya tafi akan cewa hakika Sarkin daya halicce ta, yana da ikon ya halicci dubunnai misalinta tare da wanzar da halittu acikinta.
A karshe ya rasu a hekarar 1209 a garin Herat na kasar Afghanistan bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ga kaɗan daga ƙlittattafan daya rubuta kuma:-
-Al Mutakallim fi ilmul Kalam
-Ilm Alkhalq
- Kitab al firasa
- Kitab al nafs wal ruh
- Kitab al manɗiq
- Sharh quwa-huma
-Risala al Huduth
- Sharh almaa lahil Husna
- Nihayat al iqul fi Dirayal al usul
-Mabahith al Mashriqiyy fi ilm al Ilahiyya wal tabiiyyat
Da wasunsu.
Da fatan Allah yajiqansa ya kuma kyauta namu zuwan amin.

ZUWAN TURAWA 3

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
Kashi na Uku
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Can da Yammaci, sai suka aika manzonsu zuwa ga Mai unguwa Mallam Na-marwa, da cewar "Mu turawa da muka zo wannan birni ayau, muna son ka sanar da dukkan larabawa mazauna birnin nan naku cewa muna son su hallara a gabanmu manyansu da k'ananunsu har da bayinsu baki ɗaya suna masu biyayya ga umarnin mu".
Ai kuwa koda mai unguwa ya labarta musu umarnin turawa, sai suka ce "munji kuma munyi biyayya." Nan take kuwa suka fara taruwa a kofar fadar kano.
Da larabawan nan suka gama hallara, sai turawa suka fito a garesu, suka zauna reras akan kujeru suna fuskantar larabawan da suma suke a zaune.
Shugaban turawa ya kira tafintansa wanda bamu san sunan saba, sannan yace ya tsaya a tsakiya domin soma aikinsa. Daga nan sai akace masa ya tambayi larabawan nan cewa iya su kaɗai kenan mazauna wannan birni?
Tafinta ya sauya harshe gami da tambayar larabawa kamar yadda aka umarceshi. Take sai larabawa auka amsa da cewar "Iya mu kaɗai kenan, in banda matayenmu da kananun yara da muka bari a gida."
Nan ma tafinta ya fassarawa turawa abinda suka faɗa.
Sai kuma turawa suka kara cewa ku faɗawa waɗannan mutanen cewa "Yaku bak'i mazauna wannan kasa, babu damuwa da zata riske ku. Ba muzo domin kuba, ko kuma domin wanin kuba. Ba kuma kusan dalilin zuwan muba, ko kuna da masaniya game da haka?"
Da larabawa suka ji haka sai suka amsa da cewa "Ya shugaba, mu fatake ne kurum waɗanda kaduwanci ya kawo mu wannan kasa don haka Ɓbamusan komai game da harkar (sarauta) gwamnati ba"
Sai shugaban Turawa ya sake cewa "kuyi sani yaku larabawa, zuwan mu wannan kasa yana da sila da kuma dalili. Mu mutanen yammaci ne, kuma muna da wani ɗan uwa da ake kira Bature mai Launi. Shi ya kasance shugaban mune wanda ya zauna a wani gari mai suna 'Kafin-Yamusa'.. Ko kuna da masaniyar haka?"
Sai larabawa suka amsa da cewar "kwarrai munji labarin haka".
Sai shugaban turawa ya cigaba da cewar "Hakika, ɗanuwanmu yazo wannan kasa ya samu sarkin kasar Mai suna Magaji ɗan Yamusa wanda ya karɓeshi cikin girmamawa da kulawa tare da martabawa. Ya zauna tare dashi da alkawarin zasu taimaki junansu. Watarana, marigayi ɗanuwanmu yana zaune, shi bai san cewa magauta sun shiga tsakaninsu da magaji ɗan Yamusa ba, sai kurum Magaji ɗan Yamusa ya shigo gareshi tare dayi masa kisan gilla ba tare da ɗanuwanmu ya aikata masa wani kuskure ba.
Bayan haka, sai Magaji ɗan yamusa ya rugo izuwa ga sarkin kano Ali alokacin da yaji muna nan tafe domin neman mafaka. Shikuma Sarkin kano Ali sai ya bashi mafaka tare da ɗaukaka darajarsa, har ya bashi muhalli mai kyau, da kuɗi, da bayi da dawakai na hawa.
Munji wannan labari ne daga mutane dangane da abinda Sarki Ali ya yiwa wanda yayi mana laifi, kuma mun kamu da matsanancin ɓacin rai dangane da haka.
Don haka muka zo nan da fatan mu kama Sarki Ali da abokinsa Magaji ɗan Yamusa. Gashi munzi kuma bamu tarar dasu ba".
Shugaban Turawa yaci gaba da cewa " yaku larabawa ku sani cewar bani da labarin Sarki Ali yayi tafiya izuwa sokoto. Kuma ina rantsuwa gareku da cewar idan da mun san haka, kuma mun tabbatar da hakan, da babu abinda zai kawo mu wannan gari. Ina muku rantsuwa guda uku abisa haka (wallahi, Tallahi, Billahi kamar yadda yake a al'adar su larabawan wajen tabbatar da abu na gaskiya).
Kuma Tabbas mun samu labarin sirri akan hanyarmu ta zowa nan cewar Sarki Ali ya tafi sokoto amma ban baiwa labarin amanna ba. Amma da ace na gamsu dashi, da sokoto na nufa ba nan ba.
Munzo nan ne kurum ta dalilin Sarkin Ali da abokinsa Magaji, don haka ku kwantar da hankalinku a game damu. Kada kuji tsoro, tabbas ba zaku tozar taba, ba kuma zamu firgita kuba."
Daga nan sai turawa suka sake cewa "A yanzu zamu tafi neman Inda Ali da Magaji suke. Idan kuna da saye da siyarwa kuna iya cigaba dayi da abokanan hurɗarku. Amma a tare damu da akwai hatsi da zamu so ku nik'a mana shi a matsayin abincin mu bisa son ranku ba bisa tilastawa ba".
Larabawan nan suka ɗauka baki ɗayan su cewar "Munji kuma munyi biyayya da hakan, muna muku marhaban lale tare da duk abinda kuka zo dashi"
Shikenan, abinda akayi kenan. Daga nan sai turawa suka fito da buhuna saba'in na hatsi, suka umarci masu yi musu dakon kaya su ɗauka subi larabawa dashi izuwa gidajensu.
Sukuwa larabawa, sai suka rarraba hatsin ga iyalansu, suka umarcesu da su nika tsabar hatsin nan da gaggawa.
Ai kuwa da yammacin wannan rana suka soma aikin, kuma gari baiyi duhu sosai ba suka kammala, a inda larabawan suka harhaɗa garin tare da aikawa ga turawa suna sanar nusu da cewa an kammala aiki.
Kwana biyu bayan haka, sai turawa suka sake aikowa larabawa da buhunan hatsi guda dari biyu, suna masu neman a nika musu su.
A wannan karon ma, iyalan larabawan sun kammala aikin a yini guda.
Ai kuwa turawa sunyi matukar murna gami da farin ciki da hakan, sun kuma yi godiya sosai ga larabawan.
Bayan haka, sai turawa suka yanke shawarar fita domin neman Sarkin Kano Ali da abokinsa Magaji ɗan Yamusa.
Bayan sun gama shiri sai suka fita daga kano, amma sun bar wasunsu waɗanda zasu tsare gari. Su kuwa sai suka nufi sokoto.
Akan hanyar sune sukayi kiciɓus da wasu dakarun Kano waɗanda suke dawowa daga sokoto (Ainihinsu tare suke da Sarki Ali, amma saboda yaji labarin turawa sai ya sulale ya barsu. Zakuji labarin su a gaba).
Waziri Amadu ne ke jagorancin wannan tawaga, anyi wannan haɗuwa ne kuma a wani daji da ake kira 'Dajin Rubin' (Tana kuma iya yiwuwa turawa ne suka sanyawa dajin wannan suna saboda mutuwar ɗanuwansu Reuben a dajin)
Da gamuwar su sai faɗa ya kaure a tsakani. Aka soma fafatawa, dakarun waziri Amadu suna afkawa turawa da sara da suka, yayin da suma turawa suka mayarwa da dakarun martani da harbi.
Sai dai cikin abinda baifi awa ɗaya ba, turawa suka karya lagon wanna tawaga suka kuma watsa ta. Ya zamana an kashe wasu, wasu kuma suna zube a kakkarye harsashi yayi misu lahani, yayin da saura suka shige daji da gudu suna masu neman tsira da rayukansu..

ZUWAN TURAWA 4

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
Kashi na Huɗu
Sadiq Tukur Gwarzo
Bayan yaki ya kare, sai Turawa suka mika da tafiyarsu izuwa Sokoto.
Ragowar dakarun can kuwa da suka tsere, sai suka nufo kano da gudu don neman mafaka.
Sai dai tun kafin su iso, tuni har labari yazo ga turawan da suka rage a kano, waɗanda aka barsu a gari da zimmar su tsare garin tunda sun karɓe iko dashi.
Ai kuwa tun kafin dakarun su iso, sai turawan suka haɗa tawaga suka nufi wajen ganuwa, suka jejjeru suna sauraren su.
Bayan misalin awa guda suna jira, sai ga dakarun sun karaso. Wanda ya karɓi shugabancin tawagar shine Wamban Kano Abbas, tunda idan ba'a manta ba, da fari Sarki Alu ne ke shugabancin dakarun, amma bayan ya sulale sai Waziri Amadu ya maye gurbinsa, yanzu kuwa da waziri Amadu baya nan, shine Wambai Abbas ya zama jagora.
Turawan nan suka tsaida waɗannan dakaru, sannan suka karɓe dukkanin makaman dake jikkunan su.
Daga nan aka basu damar shiga garin kano bisa sharaɗin kowa gidansa kurum zai nufa, banda kuma yinkurin tada tarzoma.
Anyi haka a lokacin tsakiyar sanyi na wannan shekarar.
Daga nan kuma, sai Turawa bayan sun koma gida suka shiga neman shawarwari daga gurin Larabawa mazauna kano akan wanda ya kamata a naɗa sarki a kano musamman wanda ya fito daga zuriyar Abdullahi.
Sai larabawan nan sukace ai kuwa Wambai Abbas ne yafi dacewa, tunda babban su waziri Amadu ya rasu.
Sai turawa suka amsa da cewar haka nan ne.
Sai dai fa duk da haka, turawa sun shiga tambayar Manyan kano na wancan lokacin dake zaune a birni, cewar wa ya dace ayiwa sarki, sai suma ɗin kuwa suka ce abaiwa Wambai Abbas sarauta.
To kunji yadda sarki Abbas ya zama sarki na farko a kano a zamanin turawa.
Yanzu kuwa, bari mubi sawun turawa izuwa sokoto, karkashin jagorancin Bature mai kwagiri domin muji yadda ta kasance.
Koda turawa suka shiga kasar sokoto, sai suka game da wasu dakarun turawa dake zaune a wani gari mai suna Argungu, suka nufi sokoto baki ɗayansu.
A yammacin ranar wata lahadi Turawa suka isa garin sokoto, a wannan yammacin kuma yaki ya kaure a tsakanin Dakarun sarkin musulmi kuma sarkin sakkwato Attahiru da turawa.
Ance a wannan rana sai da aka shafe dare babu bacci ana gwabza yaki, ba tare da wani ya samu galaba akan ɗanuwansa ba.
Da garin Allah ya waye, sai aka sake komawa fagen fama. Aka shiga gwabzawa.
Amma a wannan karon, cikin kankanin lokaci aka soma rinjayar dakarun sakkwato da yaki, saboda salon faɗa da turawa suka sauya.
Da sakkwatawa suka ga ba dama, sai runduna ta yage..
Sarkinsu Attahiru Abdu yaja tawaga yayi gabas da gudu.
Wazirinsa mai suna Muhammadul Bhukari kuma yaja tasa tawagar yayi arewa da gudu.
Shikenan, sai turawa suka shiga cikin garin sokoto cikin salama.
Suka shiga tara mutane wuri ɗaya, sannan sukayi musu jawabi cikin girma da arziki.
Sukace "kada wanda ya tsorata, domin mu ba zamu cutar da kowa ba."
Harma sun kasance suna cewa mutane "Ku zauna a gidardajinku, yakin ya kare, a yanzu kuna cikin kariya da tsaro, don haka kada wani abu ya firgita ku "
Sai dai kuma wani abin haushi ga turawa shine, har yanzu basu kama Sarkin Kano Ali da Abokinsa Magaji ɗan Yamusa ba, don haka. Wannan karon ma, ba tare da jimawa ba sai suka sake yin shiri suka fita daga sokoto izuwa neman ababen harinsu..

ZUWAN TURAWA 5

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Kashi na Biyar

Sadiq Tukur Gwarzo

Amma dangane da Sarkin Kano Ali ɗan Abdullahi (maje karofi) Alfallati, munji cewar a zamanin da yake mulkinsa, sai watarana wani manzo yazo masa wanda ake kira Baban Kano.
Wannan Manzo ya zone daga Lokoja, a haɓnunsa kuma akwai wasika daga wani Attajiri Ba'agale mai hurɗa da turawa, mai suna Adamu Jakada.
Koda manzo yazo fada, sai akai masa iso ga sarki ya shiga gareshi ana fadanci, yayi gaisuwa tare da mika masa wannan wasika dake tare dashi.
Nan take sarki ya karɓi wasikar, ya shiga karantawa a zuci ba a bayyane ba.
Ance ga abinda ke cikin rubutun:
Daga Adamu Jakadan Kiristoci. Aminci ga sarkin kano Ali ɗan Abdullahi.
Bayan gaisuwa, wannan manzo Baba Kano na aiko shine domin ya shaida maka da baki cewar Turawa na zuwa gareka.
Hakika, kayi sanin cewa babu makawa sai sunzo. Babu kuma abinda zai tunkuɗe zuwan nasu. Don haka sai kayi taka tsan-tsan, ka kuma lura da sha'anoninka.
Idan kanaganin ba zaka iya yakar suba, to zaifi kyau ka mika wuya a garesu. Kayi musu kyawawan zantuka, gami da kyaututtuka, ni kuma nasan da sannu zaka tsira daga garesu dakai da mutanenka.
Ina mai maka nasiha a bisa haka, don Allah indai ka aminta da nasihata to godiya ga Allah domin babu abinda zai faru.
Amma idan baka ɗauketaba, to ina kara jan hankalinka abisa abinda zai auku mummuna.

Koda sarki Ali ya kammala karantawa, sai bai cewa fadawansa komi ba, amma ya mayarda martani da baki ga Baba kano, yana maicewa
"Kayi sani yakai Baba Kano, bazan mika wuya ga kiristoci ba, ba kuma zan nemi tsira daga wurin suba.
A maimakon haka, zan yakesu matsawar suka zo kasata."
Ya faɗi haka a gaban fadawansa, amma fa a zuciyarsa ba haka abin yake ba domin ya tsorata har ma yayi shirin tserewa.
Daga wannan rana ne kuwa ya soma shirin tafiya sokoto domin neman mafaka.
To kuma bayan lokacin tashi yayi ga Sarki Ali har ma ya fita daga garinsa, ya riski sokoto, kwanaki kaɗan yayi a garin sai ya baroshi da niyyar komowa Kano.
Koda suka riski kasar zamfara, suka shiga wani gari mai suna Gidan Goga (Ko Birnin Goga) sai suka sauka anan da niyyar hutawa. Aka baiwa sarki Ali wani gida ya shige.
Ance Sarki Ali yana zaune a kofar ɗaki sai kwatsam yaga matarsa mai suna kubura ta shigo gidan a fusace tare da jama'arta.
Koda sarki ya kaleta ya ganeta, sai yace mata "yake kubura, menene damuwarki?"
Sai kubura tace "Ya kai wannan sarki, kiristoci sun shiga turakar ka, sun kuma karɓe iko da birninka, sun ruguza daular ka."
Sarki Ali yace "Babu sarki sai Allah, yaushe haka ta faru?"
Kubura ta amsa masa da cewa "kwanaki talatin kenan bayan barowarka birni."
Sarki Ali yayi jim cikin takaici sannan yace mata "yanzu menene abinyi?"
Kubura tace "masa idan dai kana son tsira, dole ka gudu. Komawa kano ba naka bane. Domin bayan fitowar mu daga kano, munji ance suma sun fito nemanka.
Don haka tun barowar mu kano muke ta azama ba dare ba rana domin mu riskeka mu sanar maka da wannan labari. Kayi sani, wanda duk ya tsere, to ya kuɓuta."
Da sarki Ali yaji wannan jawabi nata, sai kuma ya nemi shawararta game da tserewar. Ta kuwa ce masa lallai ya tsere a wannan dare domin hakan shine kaɗai mafita.
Ai kuwa da tsakar dare Sarki Ali tare da iyalinsa da wasu zaɓaɓɓu a tawagarsa suka tsere suka nufi kusurwar birnin Gobir.
Koda gari ya waye, sai ragowar mutanen sa suka nemeshi sama ko kasa basu ganshiba, sai daga baya suka gane cewa da dare ya tsere.
Da aka sanar da ɗan uwansa kuma mai taimaka masa Waziri Amadu cewar Yayansa ya tsere, sai yace ina hujjar haka? Sai aka ce masa ai jiya kubura matarsa ta riskeshi da yammaci.
Waziri Amadu yace "daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma, lallai wannan mutum ya ja mana abin kunya, yanzu ina ya shiga, kuma menene dalilin gudunsa?"
Daga nan sai waziri Amadu ya tara sauran mutane ya sanar musu da abinda ɗan uwansa yayi. Dajin haka Sai kuwa sukace yanzu suna karkashin sane, don haka sai ya jagorancesu izuwa duk inda yaso.
Waziri Amadu kuwa sai yace to indai haka ne, kowa yahau dokinsa mu nufi kano (domin bashi da labarin turawa)
Kunji yadda ta faru har waziri Amadu da tawagarsa sukayi kichiɓus da turawa a dajin Rubin, wanda akace yana nan kusa da garin kwatarkwashi ta kasar zamfara, inda har kuma waziri Amadun ya rasa ransa a fafatawar, yayinda kaninsa ya tsere da wasu mutanen, yaje ya mika wuya ga turawa dake kano daga baya kuma suka naɗa shi sarkin kano.
Ance a yammacin wata ranar jumua aka naɗa sarki Abbas (maje Nasarawa) sarkin kano. Kuma sai da kanawa suka shafe sati guda cur suna kaɗe-kaɗen tambura da ganguna da wasanni don murna.
Daga bisani Gwamna Lugga ya aika suje Dungurum ta zungeru don su haɗu dashi.
Ai kuwa haka sarki Abbas yayi hawa da tawagarsa ya tafi Zungeru.
Gwamna Lugga kuwa ya tarbeshi, yayi masa godiya gami da kara masa matsayi. Daga bisani Sarki Abbas ya komo kano lafiyaaaa.
Anan labarin Abdullahi Alghadamasi yazo karshe.
Sai dai daga bisani, an jiyo cewar watanni huɗu zuwa biyar da tserewar Sarki Alu, sai turawan faransa suka kameshi, suka kuma mika shi ga turawan Burtaniya dake nemansa. Kuma a hannunsu ya rasu yana tsare a garin Lokoja.

YAKIN BASASA NA KANO

TARIHI: TUNAWA DA YAK'IN BASASAR KANO
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN
Galadima Yusufu mutane keso ba Alu ba. A garin Garko ya kamu da cuta mai tsanani kuma acan ya mutu. Kafin rasuwar sa, kowa yayi amannar cewa shine zai zamo Sarkin kano, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko.
Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da 'ya'yansu sukace yanzu menene abinyi? Sai wasu sukace abu d'aya ya kamata muyi, mutum d'aya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano. Shine Mallam Babba, Alu kenan. Daga nan suka aika masa, sannan suka dora shi a gadon Mulkin Yusufu.
Bayan sunyi haka, da dare suka binne Yusufu da hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar dashi akan karagar mulki. Sukayi masa nad'i. Sai kuma akace fadawa kowa yazo yayi mubaya'a. Kaji yadda Alu ya zamo Sarki. Kuma shine dalilin da yasa dayaji turawa na tafe ya tafi sokoto domin ziyartar hubbalen Shehu tayadda Sarkin Musulmi zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya masa baya.
Jama'ar gari, mafarauta da maharba ne sukayi bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin Basasa ya barke.
Basasa anan na nufin yakin da akayi don dora Alu akan karagar mulki. Anyi shine a Ramli shekarar 'Ba-Sa-Sha'. 'Sha' a ilimin Hisabi na nufin 1000, 'Sa' na nufin 300, 'a' na nufin 1, yayin da 'ba' ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai baka shekara ta 1303 kenan bayan Hijira. (Dai-dai da 1894 miladiyya).
Ana kiran Alu da suna 'Mallam Babba' (Ma'ana babban malami), domin a wurin mu duk wani dan Sarki Mallam ne koda bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya bashi wata sarauta sai a daina cewa Mallam, a koma kiransa da wannan sarauta.
Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano izuwa Kamri wajen Tukur, domin shi akafi so.
An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum wasu kauyuka ne dake kusa da juna a kasar katsina). Naji labarin cewa anji masa raunika sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. Ance Sarki Alu yayi fushi sosai akan cewa don me zasu yiwa d'an uwansa na jini haka? Sarki Alu yace "kuyi maza ku kawo masa ruwa yasha". Amma sai Sarki Tukur yace "kada a kawo min ruwa, azumi nakeyi, bazan sha ruwa ba". A haka kuwa Allah ya amshi ransa. Allahu Akbar!!!
A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shiyasa ake Kiran sa da 'Maje-Gurum' kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu 'Maje-Garko', ake kiran Sarki Abbas kuma 'Maje Nasarawa'.
Marigayi Alhaji Mahmud Koki tafinta ne na turawa, shine kuma ya bamu wannan labari. An rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka wallafa a shekarar 1977.
ASALIN YAKIN BASASA
Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shine d'a na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari mai suna Kauran-Namoda. Sai k'aninsa Muhammad Bello (shima dan Marigayi Ibrahim Dabo ne) ya hau karagar mulki.
Ance Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin karbe muk'amai daga hannun 'ya'yan 'yanuwansa yana dasa 'ya'yansa na cikin sa. Sannan ya kara yawan jakadu masu tattara Haraji, abinda yayi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi kenan, tare da janyo masa bakin jini a gurinsu. Ance tun alokacin ya fara sharewa dansa Muhammad Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu. Ya rinka aikawa da Kyaututtuka izuwa Sokoto domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.
Shikuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, sarkin musulmi Abdurrahman (danyen kasko) ne ya nada shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sunce bai kai shekaru arba'in ba aka nad'ashi mulki, Wasu kuma sunce bashi da karsashin Rike mulki.
A wannan lokacin, sai dan uwansa Galadima Yusuf, wanda yake d'a ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi tare da jama'ar sa suka gudu izuwa garin Takai wadda ke kudu maso gabashin Kano.
Mutuwar Galadima Yusuf ce sanadin dora Sarkin kano Alu a mazauninsa. Sannan a hankali suka rinka cinye garuruwan kano da yaki. A haka har sai da rundunar su tayi karfi, suka shigo kano a ranar wata Laraba, 19 ga watan agusta na shekarar 1894 miladiyya ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano bayan rundunar yak'insa ta raunana.
Dafatan zamu amfanu da darussan wannan labari.

TARIHIN SARAUNIYA AMINA

TARIHIN SARAUNIYA AMINA TA BIRNIN ZAZZAU: MACE MAI KAMAR MAZA..
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Amina Sarauniyar Zazzau, ko kuma ace sadaukiyar zazzau wadda akace ta rayu a wajajen shekara ta 1433 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya uku da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Watau ita Amina ɗin da ƙanwarta mai suna Zariya, sai namijin kaninsu da ake kira Karama.
Ance Amina tayi sarautar Zazzau bayan rasuwar ɗan uwanta Karama wanda ya soma gadar mahaifinsu, a wajajen shekara ta 1509 zuwa 1522, ance kuma shekarunta 13 kacal akan karagar mulki ta rasu. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, shugaba ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.
Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta-yi-ta kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Mulkin Amina ya faɗaɗa tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja, da kuma can yankin kwararrafawa dake kasar bauchi sai kuma ƙananan garuruwa na kabilun Nufawa da jukun da dama da sarauniya Amina ta karɓe ikonsu waɗanda akace ba masu girma bane, amma ta kafasu a matsayin makarai, watau kamar dai ace wurare ne data ya-da zango kuma suka faɗa karkashin ikonta. Shine har akace tana sanyawa ayi ganuwa don samar da tsaro, ganuwar da ake sanyawa suna 'Ganuwar Amina' (har yanzu akwai wuraren a jihohin kano da katsina).
Da yake Kasar hausa na cikin yamutsin yake-yake tun daga wajajen shekara ta 1200 har zuwa 1700, Kasar zazzau ta zamo cikin halin rashin zama lafiya da makwabtanta a wannan lokaci. Daular Songhai ta kawo mamaya kasar hausa a wannan tsakani, sannan garuruwan kano, katsina da Borno sun zamo manyan abokan gaba ga zazzau. Don haka akace kasar zazzau ta zamo tana matukar bukatar jarumin shugaba a koda wanne lokaci.
Akace akan haka ne Amina ta gaji sarauta. Kuma duk da kasancewar ta mace, ta zamo jaruma abar tsoro ga sadaukai.
Tun tana karama ake ganin alamomin sadaukantaka a tare da ita har girman ta. Don haka lokacin da tahau kan mulki bata samu turjiya daga Sadaukan fadar zazzau ba.
Ance watan Amina ukku akan gadon sarauta ta fara fita yake-yake, inda tarinka cinye garuruwa da yaki tana faɗaɗa masarrautar ta.
A wata fadar ma ance kafin tabar mulki, saida ta tursasa sarakunan Kano da katsina su rinka biyanta Haraji na bayi da goro domin su zauna lafiya. Koda yake wani zancen ya ruwaito cewa Amina ta fuskanci matsananciyar turjiyar yaki daga wani Sarki mai suna Muhammadu Kanejeji, sarkin da Littafin Tarihin kano mai taken 'Kano chronicle' ya ruwaito a matsayin Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan haɓe. Amma wasu na ganin ta taɓa samun nasarar da har saida ta kori kowa daga birnin kano.
Sai dai bisa wannan, wasu masanan tarihi Mr. J.F Ajayi da Michael Crowder sun sanya rayuwar Amina baya da yadda ake ɗauka duba da yadda littafin tarihin kano ya zayyana cewar tayi sharafi a zamanin sarki Kanajeji, wanda lissafi ya auna cewar ya rayu ne a wuraren shekara ta 1420-1438.
Shi kuma wani masanin tarihin afirka mai suna P.J.M. McEwan ya ruwaito cewa Sarauniya Amina tacinye garuruwan Nufawa dana Kwararrafawa dake yankin ta duka da yaki a lokacin rayuwarta.
Wasu kuma sunce ga dukkan alamu, sai da Amina tafi karfin sarakunan hausa dake mulkin garuruwan kano, Rano, katsina, Daura da Gobir kafin rasuwar ta.
A takaice dai, Babu wani daya taɓa ruwaito cewa Sarauniya Amina ta taɓa aure na din-din-din a rayuwarta, balle ace tabar zuriya bayan rasuwarta. Abinda akace tanayi shine, tana zaɓar sadauki ne idan ta cinye gari da yaki ta (aureshi) kwana dashi, kashegari ta hallaka shi, har wasu sukace a irin haka ta haɗu da wani wanda ya hallaka ta.
Sarauniya Amina tana da jarumta sosai, don haka duk inda zatake yaki itace ke jagorantar rundunar yakin. Kuma zaiyi wahala tayi yaki bataci nasara ba. Wannan ne silar dayasa sunanta ya ɗaukaka a lokacin har wasu ke cewa Amina batayi sarautar zazzau ba, kurum dai Shugabar mayakan zazzau ce wadda sunanta ya kasance maɗaukaki.
Wasu turawa kuwa sun rubuta tarihinta ɗaruruwan shekaru da suka gabata. Har ma ance Shirin fim din Hollywood mai suna 'Xena: The warrior queen' anyi shi akan tane domin ya nuna tarihin ta.
Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu.
Wasu kuma sukace sam nemar ta akayi aka rasa bayan wani attajiri dayaji labarinta, sai yazo ya nemi kwana da ita, kafin gari ya waye ya sirare yabarta. Ance dagari ya waye sai itama tabar gari, kuma ba'a kara jin duriyar taba. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarinta ya ke ba.
Har ila yau, Wasu sunce kabarinta nacan kasar Bidda, kusa da wani gari nai suna Atagara, wai taje yaki ne ajali ya kamata har aka binneta acan..
Ana mata kirari da 'amina 'yar bakwa ta san rana, mace mai kamar maza kwari ne babu'.
Sai dai har yanzu da akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, musamman wajen tabbatar da cewar tayi sarautar zazzau ko kuwa gimbiyar yaki kurum ta zamo ga zazzau ɗin, ba illa yadda wani littafin masarautar zazzau na baya-bayan nan ya rubuta sunayen sarakunan Zazzau tun daga farkon madarautar har zuwa yau ba tare da sanya sunan taba, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce, Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa, a matsayin jaruma a daular masarautar Zazzau.

YAKIN SANTOLO



TUNAWA DA YAKIN SANTOLO
(YAKI DON TABBATAR DA MUSULUNCI A KASAR HAUSA)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
Hakika, idan har Tarihin kasar hausa bazai cika ba sai an kalli tarihin kano, to haka ma tarihin kano da zuwan musulunci kano bazai taɓa kammaluwa ba har sai an sanya wani yanki na Santolo.
Santolo tsohuwar daular hausawa ce, tsohuwar masarauta ce wadda salsalar ta take tukewa da salsalar asalin hausawa.
A cikin zantuka masu yawa na maruwaitan tarihin kano, an gamsu cewar wani mai suna 'Dala' shine wanda ya soma zama akan dutsen da ayau ake kira dutsen Dala, a wajajen shekara ta 700 miladiyya, tun a wancan lokacin kuma wasu na ganin akwai mutane dake rayuwa a gefa da kuma kan wani dutse mai suna 'santolo', wanda kuma da alama, sunan ya samo asali ne daga mutumin daya soma rayuwa a saman dutsen.
Zuwa yanzu, babu takamaimen tarihin asalin kafuwar santolo, sannan kuma yana da wuya a iya lissafa tsawon zamanin da mutane suka soma rayuwa akan dutsen santolo, to amma tarihi ya auna cewar mazauna Santolo dana Dala dake kano suna da alaka kodai ta jinsi, ko ta addini ko kuma ta duka gaba ɗaya, tunda har ma an samu cewa acan baya alakar kasuwanci na shiga tsakanin mazauna waɗannan duwatsu biyu. Wasu kuma na ganin Santolo tayi shaharar da har daga Borno ake zuwa yin fatauci a koma, to amma daga baya sai Allah ya fifita Dala sama da ita Santolon.
Babban abin tunawa dangane da Santolo shine 'Yakin Santolo' wanda aka gwabza tsakanin Sarkin Kano Ali Yaji ɗan Tsamiya da kuma shugaban Santolo mai lak'abin 'Magajin Santolo' wanda ya karɓi bakuncin takwaransa 'magajin Dala' bayan sarki Ali ya karya tsumburbura dake saman dutsen dala ya kuma kori Magajin Dala da mutanensa.
Tarihi ya nuna cewa asalin garin Kano ya faro ne daga dutsen dala, inda ake bautar gunkin wata aljanna mai suna 'tsumburbura' dake saman dutsen, amma daga baya maɗatai ta kafu, har Bagauda yazo ya soma sarautar ɗaukacin yankunan maɗatai dana yankin dala, waɗanda suka haɗe da sunan kano.
Haka kuma, tsawon zamani a kano babu addinin musulunci, daga masu bautar tsunburbura karkashin ikon magajin dala (wanda yayi gadon Barbushe) sai kuma maguzawa waɗanda basa bautar komai irinsu Bagauda da salsalarsa dake sarautar kano.
A haka kano ta taho har akazo kan mulkin Sarki Ali yaji ɗan Tsamiya a wuraren shekara ta 1300-1380 miladiyya, wanda ya karɓi bakuncin kabilar fulani Wangarawa daga Kasar Mali, waɗanda suka kawo musulunci garin kamar yadda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya faɗa a littafinsa na tarihin kano da tarihin zuwan wangarawa birnin.
To, bayan sarki Ali Yaji ya karɓi addinin musulunci, sai kuma ya jagoranci karya gunkin tsunburbura tare da umartar masu bauta masa su dawo musulunci, amma sai sukace sam-sam ba zasu bar addinin kaka-da-kakan-nin suba suyi addinin dungure, don haka sai suka gudu izuwa Santolo domin cigaba da bautar da suka saba.
Wannan ne yasa sarki Ali Yaji ya shirya dakaru kimanin dubu bisa dawakai, ɗauke da takubba da kuma garkuwa ta bakin karfe, tare da gudunmiwar wangarawa suma kimanin ɗari biyu, suka dirarwa Santolo da yaki.
Watakila, Sarki Ali ya shirya wannan yakin ne domin ya samu labarin cewa Magajin Dala da Mutanen santolo zasu zo su yakeshi, ko kuma tana iya yiwuwa yayi ne kurum da niyyar hana bautar gumaka tare da tabbatar da addinin musulunci a sassan kano.
Amma dai ance a lokacin, sai mutanen santolo suka ɗare bisa dutsen na Santolo, suka rinka sakarwa dakarun Sarki Ali Yaji kibbau, har takai sun hana su kusantar dutsen.
To amma daga bksani, Sarki Yaji da dajarunsa sun samu galabar hawa kan dutsen tare da karkashe dakarun Santolo, ciki kuwa harda shugabansu Magajin Santolo.
Babu takamaimen bayanin ko magajin dala ya mutu a yakin ko kuma guduwa yayi daga baya ya mutu, to amma dai an samu cewar tun daga lokacin ya zamo musulunci ya samu karɓuwa a yankin, kuma tun daga nan ba a k'ara samun wasu mutane da suka yi bautar wani abu ba Allah ba akan wannan dutsen.
Dutsen Santolo gagarumi ne, faffaɗa da doro, tsayinsa ya tafi kamar hawan bene daga baya, daga gabansa kuwa goshi yayi mai faɗi da santsi, tsakiyarsa nada faɗi harma akwai koguna da akace dabbonin daji misalin su kyarkeci, dila da macizai ke rayuwa.
Koda yake, bamuji sunan gunki da aljanar dake saman dutsen santolo ba, amma har yanzu mutanen dake zagaye da wurin sun kiyaye cewar kakanninsu sun basu labarin cewar a zamanin da, ana taruwa ahau kan wannan dutse don neman wata biyan bukata.
Sannan kuma akwai wata rijiya zuzzurfa dake saman dutsen mai suna 'Rijiyar Giɗaɗo', wadda akan hana mutane zuwa kusa da ita saboda kuɓuta daga k'wank'waman dake wurin masu halaka mutane.
Zuwa yanzu garin santolo ya kasu biyu, akwai sabon garin santolo wanda kanawa (kabilar hausawa) ke ciki, sai kuma santolon fulani, amma dukkan su suna karkashin ikon dagaci mai suna Santolo Da'u.
Haka kuma dutsen yana nan a tskiyar kauyukan sabon garin santolo, santolon fulani, Madawa, Koɗe, kyarmawa, da Tsakuwa waɗanda dukkanin su suke cikin gundumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.