Saturday, April 28, 2018

HIKAYAR ANNABI HUDU

Hikayar Annabi Hudu
  Annabi Hudu {a.s} ne da ya
kasance daga cikin Annabawan Allah
Madaukaki da aka aiko domin shiryar da
al’umma zuwa ga kadaita Allah da gudanar da
bauta a gare shi, kuma Annabi Hudu {a.s} ya
zo ne bayan da al'umma suka sake komawa
kan tafarkin shirka bayan tsawon shekaru
masu yawa da barin Annabi Nuhu {a.s}
duniya, kuma an aiko Annabi Hudu {a.s} ne ga
mutanensa da ake kira da Adawa. Sai a biyo
mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
A cikin suratu-Hudu an ambaci hikayoyin
Annabawa mafi girman daukaka guda biyar da
irin matsalolin da suka fuskanta wajen isar da
sakon shiriyar da aka aiko su da shi zuwa ga
al’umma, gami da irin azabar da aka saukar
ga wadanda suka kafirta daga mutanensu,
kuma aka ambaci surar da suratu-Hudu, to a
cikin surar zamu saurari hikayar Annabi Hudu
{a.s} ne kan irin matakin da ya dauka wajen
kiran mutanensa zuwa ga bautan Allah
Madaukaki tare da kokarin shiryar da su zuwa
ga yin amfani da hankulansu wajen tantance
tsakanin gaskiya da bata, musamman sanin
cewa; gumakan da suke bauta musu, ba su
amfanarwa kuma ba su cutarwa, don haka
wace ƙarya ce suke ƙirƙirowa a tsakaninsu ta
hanyar danganta faruwan ayyuka daga
wadannan gumaka?.
Alkur’ani mai girma a cikin Suratu –Hudu
daga aya ta 50 zuwa 53 yana fayyace mana
hakikanin hikayar da cewa:-
"Kuma zuwa ga Ãdãwa {Mun aiko} ɗan'uwansu
Hũdu. Ya ce: Yã kũ mutãnena, Ku bauta wa
Allah, ba ku da wani abin bautãwa {da gaskiya}
sai Shi, babu abin da kuka kasance kuna
aikatawa sai ƙirƙirãr {ƙarya} kawai".
"Yã ku mutãnena, bã na tambayarku wata lada
a kansa {shi wannan saƙo}, lalle lada ta ba ta
zama ba fãce a wajen wannan da Ya halicce ni,
shin bã zaku hankalta ba?"
"Kuma ya mutãnena, Ku nẽmi gãfarar
Ubangijinku, sannan ku tũba zuwa gare Shi,
zai sakar muku sama ta kwararo muku da
ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi a kan
ƙarfinku, Kuma kada ku jũya baya kunã mãsu
laifi".
Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi
Hudu {a.s} ce kamar yadda ta zo cikin
littattafan tarihi kamar haka;-
Bayan da ruwan dufana ya halakar da
mutanen da suka kafircewa sakon Annabi
Nuhu {a.s}, sannan mutane 'yan kadan da
suka tsira daga wadanda suka yi imani suka
dauki matakin sake gina kasa, a wannan
lokaci dukkanin mutanen da suke kan bayan
kasa muminai ne da suke kadaita Allah
Madaukaki. Sannan bayan shudewar shekaru
masu yawa, inda har mutanen da suka rayu
da Annabi Nuhu {a.s} suka bar duniya, sai ya
zame jikokinsu ne suke ci gaba da rayuwa a
duniya, sai kuma aka sake samun bullar
gurbatar tunani bayan mutane sun mance da
wasiyar Annabi Nuhu {a.s} tare da komawa
kan mummunar dabi'ar bautar gumaka.
Hakaki bautar gumaka ta samo asali ne a
tsakanin mutane sakamakon matakin da
wasu daga cikin jikokin mutanen Nuhu {a.s}
suka dauka na sassaka gumakan mahaifansu
da suka tsira daga ruwan dufana da nufin
kada a mance da su, inda mutane suke
girmama gumakan fiye da kima, kuma hakan
ya ci gaba da gudana har ya kai ga matakin
da girmamawar ta rikide zuwa bautar gumaka.
Hakika makircin shaidan ya yi galaba a kan
hankulan mutane inda suke riya cewa
wadannan gumakan da suke girmamawa sune
tsaninsu zuwa ga Allah Madaukaki, kuma
suna matsayin Ubangiji ne, don haka suka
koma suna shirka wa Allah wajen bauta, inda
duhun bata da rudun rayuwa suka sake
dawowa kan doron kasa, sakamakon haka
Allah cikin jin kansa da rahamarsa ga talikai
ya aiko musu Annabi Hudu {a.s} domin shiryar
da su hanya madaidaiciya.
Annabi Hudu {a.s} ya kasance daga kabilar da
ake kira A'da, kuma wannan kabilar tana
zaune ne a wani waje da ake kira da Ahqa'f,
kuma waje ne mai sahara da yawan yashi
kusa da bakin teku. Kabilar Adawa tana
rayuwa ce cikin haimomi masu girma da suke
da ginshikai masu karfi da tsayi, kuma Adawa
sun kasance sun fi sauran mutanen da suke
rayuwa da su a bayan kasa girman jiki da
karfi gami da tsayi kamar yadda suka
kasance suna alfahari da karfinsu, saboda
babu wani jinsin bil-Adama da ya kai su karfi
a wannan zamani, kuma duk da tarin
ni'imomin da Allah ya yi a gare su, amma suna
rayuwa ce cikin duhun bata da rudun rayuwa
ta hanyar bautar gumaka, sannan suna kare
wadannan gumaka da dukkanin karfinsu tare
da yaki dominsu.
Hakika Adawa sun kasance suna cutar da
Annabinsu tare da gudanar da izgili a gare shi
da cewa; "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka
a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa,
Munã zaton ka daga maƙaryata. Kuma
kasancewar Adawa mutane ne masu alfahari
da irin karfin jikin da aka ba su, maimakon su
yi tunanin cewa; lalle Allah da ya halicce su
shi ne mafi karfi da girman iko a kansu, kuma
tabbas zasu koma zuwa gare shi, amma sai
suka zabi yin riko da gumaka a matsayin abin
bautansu. Annabi Hudu {a.s} ya dauki
matakin fadakar da su tare da kokarin mai da
su kan fidirarsu ta dan Adamtaka da cewa:
"Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da
wani abin bautã wa, koma bayansa . Shin bã
zã ku ji tsoron Allah ba?".
Haka nan Adawa sun dauki matakin gabatar
da zargi da kokarin muzantawa ga Annabi
Hudu {a.s} da cewa: Shin kana son zama
shugaba ne a kanmu ta wannan kira naka?
Shin kana son wata lada ce daga gare mu,
inda zamu dinga tattara maka dukiya? Amma
sai Annabi Hudu {a.s} yana mayar musu da
martanin cewa: Baya neman wata lada daga
gare su, sai a wajen Allah Madaukaki, iyakan
abin da ke bukatar gani shi ne su 'yantar da
tunaninsu tare da sanya hankalinsu a gaba
domin ganin hakikanin hasken rayuwa, inda
ya ambata musu tarin ni'imomin da Allah ya yi
musu a rayuwa tare da sanya su a matsayin
magada ga mutanen Annabi Nuhu {a.s}, kuma
ga tsananin karfin jiki da Allah ya huwace
musu tare da zaunar da su a waje mai tarin
arziki da wadatar amfanin gona ta hanyar
saukar musu da ruwan sama da ke rayar da
kasa, amma mutanen Hudu {a.s} suka
butulce tare da yaudaruwa da karfin jikin da
aka ba su, suna jin cewa babu wani abin da
zai fuskance su, ba tare da sun kare kansu da
karfi ba, don haka suka kara girman kai da
dagawa a bayan kasa.
A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu
ne daga cikin taskar iyalan gidan manzon
Allah tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta
Annabi Hudu {a.s} kamar haka:-
Allamah Muhammad Husain Tabataba'i
ma'abucin tafsirin Al-Mizan ya nakalto
ruwayar iyalan gidan manzon Allah tsarkaka
{a.s} cewa: Hakika Adawa sun kasance suna
rayuwa ce a wata kauye mai dauke da
amfanin gona da yawan dabino, kuma sun
kawata kauyen da tarin gine-gine ga kuma
karfin jiki da aka huwace musu, amma sai
suka wofantar da hankulansu wajen gudanar
da bautar gumaka, don haka Allah Madaukaki
ya aiko musu Annabi Hudu {a.s} domin ya kira
su zuwa ga addinin Musulunci tare da
kauracewa gumakan da suke bauta musu,
amma sai suka kafirce tare da daukan
matakin cutar da Annabi Hudu {a.s}, don haka
aka aiko musu da fari na tsawon shekaru
bakwai.

No comments:

Post a Comment