MATHEMATICS KASHIN BAYAN KIMIYYA DA FASAHA
1. Sau da yawa za ka ga mutane su na kokawa da wahalar
lissafi da kuma yawan faduwa jarrabawar sa. Kuma za ka ji Dalibai su na
tambayar wai mai ya sa a ke tilasta su sai sunyi lissafi? Kuma a ina ne za su
yi amfani da shi? Ko kuma mene amfanin sa?. Wadannan tambayoyi sun biyo bayan
rashin sanin gudun-mawar da lissafi ya ke bayarwa a duk wata harka da ta shafi
kimiyya da fasaha. A yanzu babu wani ilimin kimiyya da fasaha mai zurfi wanda
ba ya bukatar ilmin lissafi. Hatta ilmin kasuwanci, banki, da sauransu, babu
wanda mutum zai iya yi da kyau ba tare da lissafi ba. Duba tun daga haluntun
ubangiji: sammai, da kassai, rana da wata, dare da rana, safiya da
maraice. Duk wadannan abubuwane da mutane ma su tunani suke shan mamaki wajen
yadda su ke gudana bisa tsari. Haka, idan mutum ya duba irin baiwar da Allah Ta’ala
ya yi wa dan Adam ta kere-kere: Radio, Talabijin, Mota, Jirgin ruwa da na sama,
Inji mai kwakwalwa, da dai sauransu. Mutum ya kan sha mamaki yadda wadannan
abubuwa duka su ke aiki bisa tsari. To duk wadannan abubuwa su na gudanane bisa
tsarin ilimin lissafi. Wannan shi ya sa, mutum ba ya iya samun shiga kowace
jama’i a duniya domin karantun kimiyya ko fasaha sai da shaidar lissafi mai
kwari. Haka kuma, ba ka iya samun aiki mai kyau da ya shafi kimiyya da fasaha,
sai ka na da shaidar lissafi mai kwari. Wannan shi ne ya sa wasu sukan yiwa
lissafi kirari: Rariya matatar dalibai. AHA MUJE ZUWA.
2. Mutane sun sha banban
Malaman sanin
yanayin dan Adam tuni su ka gano cewa mutane sun sha banban wajen yadda su ke
fahimta da zartar da abubuwa. Kuma ita fasaha iri-iri ce. Wasu mutane akwai su
da saurin gane abubuwa da su ka shafi lissafi, wasu kuma sun fi saurin gane
abubuwa da su ka shafi yare. Wasu sun fi so su yi abu da hannunsu, wasu kuma
sun fi so su karanta, haka kuma wasu sun fi son sauraro. Dangane da lissafi,
ina ganin mutane sun kasu kashi uku: Kashin farko su ne mutanen da Allah Ta’ala
ya yi mu su baiwa mai yawa ta fahimtar lissafi. Wadannan mutane, da zaran an
dan yi musu bayani nan take sai ka ga sun gane abin da a ke nufi. Wani lokacin
su kan gane abu fiye da wanda ya yi mu su bayanin, ko da kuwa malamin su ne.
Kai wasu ma suna da basirar gane abubuwa ba tare da an koyar da su ba. To
wadannan mutane ba su da yawa a cikin jama’a. Kashi na biyu su ne kishiyar na
farko. Su kuma mutanene da ke shan wuya kwarai wajen gane duk wani abu da ya
hada da lissafi. Kuma a kan sha wuya wajen koya musu lissafi. Ko da kuwa an yi
bayani sosai sun yi kamar sun gane, da zaran an yi musu tambaya, sai ka ga ashe
sanin Damisar Bunu su ka yi. To su ma wannan kashin ba su da yawa sosai cikin
jama’a. Kashi na uku su ne wadanda su na gane lissafi idan an yi musu cikakken
bayani, amma sukan sha wuya kafin su gano wasu abubuwa masu zurfi. Amma da
zaran sun tara hankali gu daya sun dage, sai ka ga sun gane abin da ake nufi. Wadannan
mutane su ne su ka fi yawa a alumma.
Manyan
matsaloli guda biyu da ke damun dukkan dalibai sune: Na daya mafiya yawa
dalibai tun tuni an cusa musu ra’ayin cewar lissafi abune mai wahalar gaske kuma
sun amince; to wadannan mutanen, da wuya su koyi lissafin koda kuwa suna da
basirar yin lissafin. Matsala ta biyu itce, mafiya yawan malamai masu koyar da
lissafi su kan su basu iya lissafin ba, musamman a primary da secondary; lalle
kuwa idan dalibi bai sami tushen lissafi mai kyau ba, to fa da wuya dalibin nan
yayi wani katabus a gaba. Hmmm.
3. Yadda ya kamata
dalibi ya koyi lissafi
Ga dukkanin
dalilbi mai sha’awar karatun kimiyya da fasaha kamar su: Mathematics,
Chemistry, Physics, Geology and Mining, Computer Science, ko Engineering,
kamar: Chemeical, Electirical, Mechanical, Civil, Computer da dai sauransu. Ko
kuma karatun zane-zane, kamar su Archintecture, Planning, Survey, Construction
da dai sauran su. Ko karatun Likitanci, ko karatun harkar kasuwanci, kamar su:
Accounting, Finance, Economics, Banking da dai sauran su. To babu shakka
ba zai iya yin fice a wadannnan fagagen ba sai ya na da kyakkyawar fahimtar
lisafi.
Kamar yadda mu
ka sani, mutane da yawa su kan samu matsala wajen koyon lissafi, ba don komai
ba sai dai kawai don ba su san yadda ya kamata su koyeshi ba, ko kuma basu sami
malamai da su ka san yadda ya kamata a koyar da shi ba. Tambaya
itace, yaya dalibi zai yi domin ya dinga samun lissafi da dan sauki. Ga wasu
‘yan shawarwari da za su iya taimakawa in Allah ya so. Sune:
- Lallene ya kamata dalibi ya fahimci cewa ba’a koyon kowane irin karatu da sauki. Kaji abin da Annabi Musa AS yace: Lalle mun sha bakar wuya wajen wannan tafiya ta mu ta neman karatu. Dubi Suratul Kahfi ka sha karin bayani.
- Ya kamata kuma dalibi ya fahimci a wane ajin mutane uku ya ke da mu ka yi bayani baya. Wannan zai taimakawa kowa yasan matsayin sa. Domin idan mutanen ajin farko su na bukatar karatun awa daya, to mutanen aji na biyu zasu bukaci awa biyar ko fiye. Su kuma ‘yan aji na uku zasu bukaci awa biyu zuwa uku. Sabo da haka ka da kowa ya hada kan sa da wani.
- Sannan ya dace dalibi ya zamanto ya na shaawar lissafi. Duk da cewa akan samu masu basirar abu amma basa sonsa, bincike ya nuna cewa Idan mutum yana sha’awar abu, ya kan bashi lokaci. Hausawa suna ce wai So yafi bauta ciwo. Haka kuma wanda bai son abu, to, babu shakka da wuya ya bada hankali akan abun sosai balle ma ya fahimce shi.
- Kuma ya zama yana halartar aji akan kari ba latti. Sannan a aji ya zama mai tara hankali gu daya yayin duk da malami ke koyarwa. Shi lissafi abu ne mai bukatar natsuwa da tunani. Yayin duk da malami ke bayani idan hankalin ka ya na wani abu da ban, to da wuya ka gane abin da ya koyar.
- Lalle ne mutum kuma ya zanto mai naci. Da zaran an gama karatu a aji to mutum nan take ya je ya yi tishi a gida ko dakin karatu (library). Idan za ka fara karatu, to ka fara karanta misalai da malami ya bayar a aji, idan ka gane su, sai kaje gaba. Wato daga mai sauki zuwa mai wuya.
- Duk tambayoyin da malami ya bayar a yi a gida, to lalle ka dunga yi a kan kari. Idan da sauran lokaci, ka kwatanta yin sauran da malami bai ce a yi ba. Yin haka, zai tabbatar ma ka cewa ka gane ko ba ka gane ba. Abin da ba ka gane, sai ka kara dagewa da tunani har sai ka gano shi. Amma idan abin ya faskara, to sai ka nemi taimako wajan malamin ka ko abokin ka da kasan ya fi gane karatu. Lissafi bai yiwuwa sai da tunani da naci.
- Kafin aji na gaba, ka tabbatar da cewa ka gane karatun baya. Sannan idan da hali ka yi kokari kasan karatun da za ku yi nan gaba, kuma ka dan duba kadan kafin malami ya zo aji. Amma kar ka kuskura ka bar karatu ya taru sai lokacin jarrabwa ta kusa. Wannan baban kuskure ne, domin ita kwakwalwa ta na da iyaka. Ba ta son a takura ta da yawa cikin kankanin lokaci. Nan ta ke za ka ga mutum ya rikice.
- Zai kyau kuma mutum ya zanto ya hada kai da mutane ma su basirar lissafi domin su dinga yin karatu tare. Wannan ya kan taimakawa kwarai ga mutanen duka. Shi wanda ya yi bayani ya kan kan kara ganewa, shi kuma da akayi wa bayani, ya kan samu karuwa so sai.
- Banda Hadda: Shi lissafi ya na bukatar fahimta ne kawai. Kar ka kuskura ka yi haddar abin da baka fahimta ba. Lalle ka yi iyakacin kokarin ka ka ga cewa ka gane sakon da kyau. Da zaran wani abu ya sha ma kai, to ka je ka tamabaya. Allah ya ce ku tambayi masana idan ba ku sani ba. Su kuma Hasusawa su kance tsugunawa Wada ba gajiyawa ba ne.
- Sannan ka natsu ka gano hanyoyin da idan ka bi su to ka fi saurin gane karatu. To sai ka dage akan su.
- Haka kuma ka yi kokari ka gane lokutan da kafi jin dadin yin karatu a cikin su. Sai ka lizimce su da kyau, banda hira a wadannan lokutan.
- Bayan kuma ka gama duk abin da ya kamata ka yi to sai ka mikawa Allah sauran. A yi ta addu’a Allah ya buda ma ka basira ka dinga gane karatun da sauri. Saboda haka dalibi ya dage da addu’a Allah ya buda ma sa basira ya kara gane karatu.
4. Karkarewa da fatan
alheri
To kamar yadda Na nuna a baya, duk wani ci gaba da a ka samu na
kimiyya da fasaha, to lallai sirrin abin ya na cikin lissafi ne. Wannan shi ne
ya sa babu Jami’a a duniya da za ta dauki wani dalibi domin karatun
kimiyya ko fasaha sai ya na da shahadar lissafi mai kwari. Haka kuma ko da
mutum ya gama karatu, samun aiki na da wuya idan ba ka da kwarewa wajen
lissafi. Saboda haka na ke baiwa dalibai shawara, cewa su dage so sai
wajen karatunsu, su kuma tara hanlinsu gu daya. Allah Ya yi alkawarin cewa duk
mutumin da ya dage kan al’amari, to zai samu gudammawa daga gurin ubangiji.
Allah ya yi ma na jagora baki daya, amin.
DAGA ADAMU MAHADI ADAM GAYA
No comments:
Post a Comment