Thursday, April 19, 2018

MALICIOUS SOFTWARE


MALICICIOUS SOFTWARE
Wannan suna ne da ake bayar wa ga duk wani
irin manhaja (software) wanda ba'a buƙatar
kasancewar sa a cikin Na'urar komfiwta ko wayar
salula ko makamantan su, sannan kuma irin
waɗannan manajojin sun kasance sun kasance
suna da ikon da zasu lalata Na'urar tare da
dakatar da gudanar Na'urar ko kuma dai ya
samar da wani yanayi mara ɗaɗi ga Na'urar.
Irin Manhajojin akan iya sanya su cikin Na'urar
ka ta hanyar yardarka ko kuma ba da yardarka
ba, (wato ta hanyar yi ma ka Basaja), sannan
kuma irin waɗannan manhajojin zasu iya yaɗa
kansu daga wata Na'urar zuwa wata Na'ura
daban ko kuwa dai a'a. Hmm kuci gaba da sauraro dai
kuna tare da Adamu Mahadi adam Gaya
MALWARE: wannan kuwa suna ne wanda ake
faɗawa kowacce irin manhajar da ba'a buƙatar
kasancewar su a Na'ura. Wannan kuwa ya shafi
irinsu; Virus, spyware, worms, Trojan da dai
sauransu.
AHA
IRE-IREN MALICICIOUS SOFTWARE.
:::VIRUS:
wasu nau'in rubutu ne iri-iri wadda
suke yaɗa kansu daga wata Na'urar zuwa wata
ta hanyar sajewa da wata fail (file) domin ya
samu damar shiga Na'urar ka a ɓoye.
Su waɗannan nau'ikan rubutun da suke a
matsayin VIRUS sukan lalata fail ne (file) da yake
Na'urar komfiwtar duk wanda aka turawa, ko
kuma su hargitsa waɗannan fail (file) ɗin domin
amfanin wanda ya tura.
MENE NE AMFANIN SU IRIN WAƊANNAN VIRUS
ƊIN GA MASU ƘIRƘỊRANSU, MA'ANA WANI AMFANI
MAƘIRƘIRIN YAKE SAMU IDAN YA KIRKIRE SU ?

A Duk lokacin da mai kirkirar irin waɗannan
VIRUS ɗin ya ƙirƙire su to sai ya watsa su a kan
iska wato NETWORK (WIRELESS MEDIUMS), idan
wani ya buɗe Bluetooth nashi ko kuma ya sauƙe
(DOWNLOADING) wani fail (file) to sai su irin
waɗannan VIRUS ɗin su saje da waɗannan fail
ɗin domin su samu damar shiga Na'urar
komfiwta ko wayar ka don lalata ta.
To su kuwa waɗanda suke ƙirƙiro su sai su kirkiri
wata Manhaja wadda zata iya goge wannan
VIRUS ɗin sannan su kai shi kasuwa domin
sayarwa (COMPUTER WAREHOUSE) to a lokacin
mutane su rinƙa zuwa suna sayo wa.
To kaga wannan shine ribar da suke samu. Daga Adam Mohd Adam Gaya.

No comments:

Post a Comment