Monday, April 30, 2018

TARIHIN WASU UNGUWANNI A KATSINA

TARIHIN WASU UNGUWANNI DA KE CIKIN BIRNIN
KATSINA
1. Makudawa asalin unguwar daga Buzaye ne
naAgalawa wadanda suka zo don fatauci. Cikin
wadanda suka zauna har da wani hamshakin
Attajiri mai suna Alhaji Basari, wanda a zamanin
Sarki Dikko ba mai kudinsa.
2. Darma an kafa ta shekarun 1452 ko
1475.Unguwa ce ta attajirai da Malamai wadanda
sukashahara a zamanin baya, kuma zuriyarsu har
yanzu na tashe.
3. Gafai unguwar Gafai, ana jin cewa, asalinta
daga Larabawan kasar Spain ne (watau
Andalusia kenan), wanda wani Malami mai suna
Malam Buhari da dansa MalamYahaya suka baro
Andalus lokacin tana daular Musulunci, ba su yi
zangon dindindin a ko’ina ba sai Gafai. Wata
ruwayar kuma ta ce a’a mutanenkasar Maroko ne
suka kafa ta.
4. Tsohuwar Kasuwa. Asalinta daga kaya ne da
mutanen Tunisiya, Moroko kan kawo , a rika
musaya ta ba ni gishiri in ba ka manda. Amma
wurin ya zama birni da gari a lokacin Sarkin
Katsina Ummarun Dallaje, lokacin da wani Malami
daga kasar Barno mai suna Malam Usman ya zo
da almajiransa ya zauna a wajen. Rafindadi.
Unguwar ta samo asali ne daga waniAttajiri da
ya gina rijiyoyi guda 12, don a rikadibar ruwa
kyauta. Daga mutanen da suka rayasunan
unguwar shi ne zuriyar Waziri Zayyana, wadanda
su kuma asalinsu Larabawan Madinane. Unguwar
kuma tana da Sharifai. Daga cikinsu akwai zuriyar
Abba Abu (Allah ya kara masarahama).
5. Unguwar Alkali, unguwa ce da mafi yawansu
Alkalai ne. Asalinsu zuriyar Malam Muhammadu
Chomo ne, wanda are hasashen ya Frito daga
Futo-jallon ta kasar Mali. Suna da zuriyarsu
yanzu wadda suke kira zuriyar gidan Hambali.
6. Masanawa. Tsohuwar unguwa ce, wadda
asalin tadaga Waliyyai ne guda biyu - Wali Dan
Masani dakuma Wali Dan Marina. Wali Dan
Marina asalinsa Balarabe, shi kuma Wali Dan
masani asalinsa daga kasar Barno ya fito.
Unguwar tana da fitattun Malamai, da Attajirai.
Wani marubuci maisuna Malam Abdullahi Kasim,
ma’aikaci a dakin karatu na Katsina ya rubuta
littafi cikakke a kan tarihin unguwar. An kuma
buga littafin Bambadawa, asalinsu daga Sarki
Bambadawan Sarkin Katsina Umarun Dallaje,
wanda ake kira da Ummaru Kilaga. Wasu kuma
sun ce asalin su mutanen Sakkwato ne. Unguwar
kuma akwai wanzamai.
7. Gambarawa. Unguwa ce da ake kaulanin yadda
aka kafa ta. Wasu sun ce mutanen Barno ne,
wasu kuma sun ce mutanen Mali ne. Unguwa ce
wadda akwai shahararrun Malamai a cikinta,
irinsu Malam Babangida Abbas.
8. Albaba. Zuriyar wani Malami ne mai suna Abul
Gaisu, suka kafa Albaba. Sai kuma wasu
Larabawa da ake jin Sharifai ne. Daga cikin su ne
aka samu su Abba Jaye da Abba Dayyabu.
9. Kofar Sauri da makwabtanta. Asalin su nan
daga wani Sarkin samari ne. Asalin wadanda
suka zauna wajen kuma zuriyarsu ita tkea wajen
haryanzu Bare-bari ne daga kasar
Barno.Babarbaren da ya fara zama har yau akwai
zuriyarsa shi ne Malam Yunusa. Ya zo a 1754.
Sai kuma kakan Attajirin nan Abu Kyahi, wanda
ake kira Malam Umaru, wanda shi ma daga kasar
Kukawa ya zo ta kasar Barno.
10. Unguwannin Rafukka, Nasarawa da
Makera.Wadannan unguwanni sun dade. Rafukka
tananan tun zamanin Sarkin Katsina
MuhammaduBello. Wuri ne mai dausayi da
albarkar noma.Sarkin Katsina Dikko shi ne ya
kara raya wajen.Nasarawa, ita kusan tarihinta da
tasirinta dayada na Rafukka.
11. Yammawa. Yammawa, asalinta unguwa ce ta
mazauna aikin lambu da noma a Rafukka. Ta rika
canza mazauni kafin ta tsaya inda take, kuma
takafu. An kafa unguwar tun karni na 15. A shafi
na 164 Farfesa Munnir ya fara bayanin Kofofin
Katsina, inda ya fara da Kofar Guga, wanda a
tarihi sunan matar Sarkin Gobir ce Bawa Jan
Gwarzo, wanda ya hana Katsina sakat. Sai
matarsa mai suna Guga ta gudo, ta tona asirin
mijinta na sihirce-sihirce ga Sarkin Katsina. Da
wannan asirin ne da aka samu aka ci Gobirawa
dayaki. Wannan ya sa Sarkin Katsina,
Muhammadu Jan Hazo ya sanya ma Kofar suna
kofar Guga,domin ta nan Guga ta shigo Katsina.
12. Sararin Tsako. Sunan unguwar ya samo asali
ne daga kalmar Buzayen Agadas, wanda a lokacin
fili ne fayau Buzaye kadai a wurin in sun zo
fatauci ke zama. Sullubawa. Asalin, wanda ya
kafa unguwar, wani Malami ne mai suna Malam
Umaru Dunyana daga Zamdam ta kasar Maradi
jamhuriyar Nijar. Da shi aka yi jihadin Shehu
Usman Danfodiyo a Katsina.
13. Filin masallacin Idi da unguwar Tudun
’yanLihidda. Masallacin Idi a nan ake sallar Idi
tunkarni na 16 kafin jihadin Shehu Usman
Danfodiyo.
14. Tudun ’yan Lihidda kuwa, asalinsa mayakan
da ke raka Sarki ne masallaci ke tsayawa suna
kare masallata daga yiwuwar kawo masu hari.
Wani lokaci kuma a nan dakaru kan yi hawa don
tsare garin Katsina daga harin mahaya a
tabarayin.
15. Kofar Durbi. Sunan kofar ya samo asali ne
daga Hakimin Mani. Shi kuma daga Durbi ta
Kusheyi, wadanda sune gidan sarautar Durbawa.
16. Filin Samji. Asalin wajen daji ne mai namun
daji kala-kala. Sai wani Baturen Ingila D.O mai
suna Samuel J. ya mai da wajen wurin sukuwar
dawaki. Daga nan ne, sai wurin ya koma Filin
Samuel J. A hankali, a hankali sai kiran sunan
wajen ya canza zuwa Filin Samji.
17. Rimin Badawa. Asalin wajen wasu mutanen
Barno ne daga wani yanki da yanzu yake jihar
Yobe mai suna Bedde. Sune bayan sun dawo
daga Sakkwato sun amso tuta suka yadda zango
suka kafa unguwar, daga Bedde aka koma kiran
su Badawa.
18. Kofar Marusa. Sunan ya samo asali ne daga
wani Basaraken Habe mai suna Marusa Umaru.
19. Kofar Kaura ta samo asali ne daga wani
mayaki daya mai suna Kaura Gumari. Daga nan
ta cigaba da jan sunan duk wani Kaura da ya
shahara a Katsina. Kaura Gumari daga baya ya yi
hijira, ya koma Tasawa ta kasar Maradi a can ya
rasu.
20. Dan Dagoro. Sunan da kafuwar garin ya
samoasali ne daga wani Malami mai suna
Abubakar da ya zo daga kasar Damagaram. Sai
ya samu wata itaciya ya yi bukkarsa a sama. Sai
jama’a suna zuwa kallon wannan abin mamaki. A
dokar daji kuma mutum ya yi daki saman itace?!
Sai aka rika kiran abin Dan Dagwam. Daga nan
sai takoma Dan Dagoro.
21. Kofar Kwaya. Sunan ya samo asali daga wani
Sarkin Habe mai suna Sarkin Kwaya. Wali Jodoma
ya taba tsine ma kofar ya ce, ba za ta cigaba ba,
sai bayan shekaru dari biyar. Kuma bata fara
bunkasa ba, sai da aka yi shekaru dari biyar da
doriya da waccan tsinuwar.
22. Kofar ’Yan Daka. Ita ma asalinta daga
Basaraken Habe ne na garin ’Yan Daka. Kofar
tana hade daunguwar ’Yan taba. Wanda a nan ne
gidan ’Yan Daka yake. Akwai kuma Marinar
Kadabo wadda masu sana’ar Rini suka kafa
wajen. A unguwar akwai rijiyoyin Rini.
23. Babbar Ruga, Fulani makiyaya suka kafa
wajen,amma Turawan Mishan su suka bunkasa
wajenda gina asibitinsu na maganin cututtukan
da ake dauka ko ake kyama.
24. Filin Polo, wanda asalinsa filin wasan Polo ne,
shine na farko da aka kafa a Najeriya.
SarkinKatsina Muhammadu Dikko ne ya kawo
wasan akasar nan bayan dawowarsa daga Ingila.
Anshata filin a 1921. Yanzu wajen yananan.

DAGA ADAM MOHD ADAM GAYA.

1 comment:

  1. Assalamu alaikumni i will like to talk to you concerning the history you wrote abubakarsayyadi50@yahoo.com

    ReplyDelete