KALAMAN SOYAYYA 02
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki
tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na
ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya
daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya
raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar
da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana
a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne
dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma
idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa
soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki
kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar
ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya
canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a
koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna
raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau
babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya
adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu
da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a
rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance
cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan
lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata
da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke
domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar
‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu,
domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato
“INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin
soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya
yi sanadiyar raba ni da ke har abada. NA
TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda
zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani
babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada
dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da
kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
DAGA ADAMU MAHADI ADAM.
No comments:
Post a Comment