KARANTA KAJI YADDA ZAKA TSARA BUDURWARKA
Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama
biro in rubata miki shafin kauna !
Kizama kofa na zamao
makulli, mu hadu mu bude kofar soyyar lambun zuciyata!
Na kasa tsaye na kasa
zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban
kaman wata a daren sha biyar!
Ya madarar zuciyata,
ki zamo ciminti in zamo bulo mu gina gidan quana a filin soyayya.
Watau yau da na tashi, sai
na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar
da haske zuciyata,domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk
hasken raina
Ki zama petur na zama inji
mu hadu mu taa da lantarkin qauna
ya shiba ta na baki filin
zuciya ta ki shuka a duk wani lungun da sako bushiyar so a kauna don mu sami
inuwar da zamu zauna muyi soyayya.
Kece madubi abar dubawata
duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwat ba ke lami ce ya rabin
raina.
Ke ce makwarariyar madarar
zuciyata, wadda da na sha za ta haska ka zuciyata ta yi fari.
Rayuwata babu ke tamkar
wayar da ba wayar shaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.
Kunne ya kurmance saboda
rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai dai saboda
rashin begen zumar rayuwata kullum.
Ta tsagwaron zallar tsabar
kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum
Ya gangariyar madarar zumar
da bata da gauraye, ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar
masoyinta.
Idona ya bude ya ga haske
irin na walkiya don ya gan ki. Ziciyata na shan lawgadar zuma da madarar kauna
Idon basira lafazin
rayuwata
Alfijir na quana ya keto,
tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a sararin samaniyar zuciyata
Ya fankar da ke juya
zuciyata, zan zamo kwale kwale ki shigo bu hau kan kogin so, in zamo katifa ki
zamo gado a cikin dakin kauna.
Hadarin begen ki ya hado,
guguwar sonki ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki a filin zuciyata.
Gaisuwa daga kamfanin so,
harabar kauna, gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwa ga rabin rayuwata.
ya zare da allurar da ta
dinken zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a
nijeriya.
ya majaujawar zuciya ta,
zan zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin rijiyar soyayya
Ya tsokar zuciya ta, zan so
ace ki zama fura in zama nono mu hadu a kwaryar soyayya
Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya.
Ya masoyiyata, ki zamo
bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar
da ke.
Ya masoyiyata, ki zamo
hanta in zamo jini, muga mai raba mu.
Ludayin kaunar ki ya mamaye
min kokon zuciyata.
Ya masoyiyata, ki zamo mai
in zamo alabasa mu hadu mu soye juna.'.
a masoyiyata, ki zama
candir in zamo ashana, ku zamo itace in zamo makamaci mu hadu mu hura wutar so,
domin mu mu tafasa tukunyar kauna.
HMM, DAGA ADAM M. ADAM GAYA
No comments:
Post a Comment