YADDA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) SUKE FUSKANTAR WATAN RAMADAN
An tambayi Ibn Mas'ud (RA)
Yaya ku Sahabai (RA) kuke fuskantar watan Ramadan? Yaya kuke shiga watan Ramadan??
Sai ya amsa da cewa:
"Babu wani daga cikin mu da zaya fuskanci watan Ramadana ko zai shiga watan Ramadana, face babu daidai kwayar zarrah na hakkin dan uwansa ko jin haushin dan uwansa a cikin zuciyarsa." [Shehun Malami Ibn Rajab Al Hambali ne ya ambaci wannan a littafin sa mai suna, LATA'IFIL MA'ARIF]
Don haka ya ku 'yan uwa, mu yafewa junan mu, mu nemi afuwa a tsakanin mu, domin dacewa da wannan watan mai albarka babu bakin ciki da damuwar wani acikin zukatan mu.
Ni dai dukkan wanda nayi man wani abu ko na sani ko ban sani ba wallahi na yafe masa, na yafe masa, na yafe masa.
Don Allah nima ku yafe mani, don Allah ku yafe mani, don Allah ku yafe mani.
DAGA A.M.A.G
No comments:
Post a Comment