Friday, May 11, 2018

TARIHIN BUHARI

TAKAITACCEN TARIHIN MUHAMMAD BUHARI


BUHARI


Takaitaccen tarihin janar Mohammadu Buhari
An haifi Janar Muhammadu Buhari
ranar 17 ga watan Disambar shekarar
1942, a garin Daura.
Tauraruwar janar Buhari ta fara
haskawa a lokacin da aka bashi
mukamin ministan man petur da
ma'adanai a shekarar 1975, a zamanin
mulkin sojin janar Olusegun Obasanjo.
Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan
sabuwar jahar Arewa maso Gabas da
janar Murtala Ramat Muhammed ya kirkiro.
Daga bisani kuma aka nada shi shugaban hukumar NNPC wadda aka fara kafawa
a shekarar 1977.
A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada shi shugaban hukumar PTF wadda
aka kafa da kudaden rarar man da kasar ta samu a wannan lokaci domin gudanar
da ayyukan ci gaban al'umma.
Kuma ayyukan da janar Buhari yayi wa Najeriya kama daga hanyoyi, asibitoci
zuwa makarantu yasa wasu 'yan Najeriya son ganin ya sake zama shugaban
kasar.
Sau biyu janar Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugaban kasar
karkashin tutar jam'iyyar ANPP wato 2003 da 2007, wadanda duka bai samu
nasara ba.
Rashin nasarar da ya yi karo biyu bai sauya masa ra'ayi ba game da siyasa a
Najeriya, kuma tuni ya kaddamar da tashi jam'iyyar da ya kira CPC wadda yake
takarar shugaban kasa a zaben da da'a kayi a shekarar 2011 KAro uku kenan baba Buhari na tsayawa takarar shugabancin kasar nan Allah baibashi NASARA bayan faruwar hakan ne baba GMB ya kaddamar da wata sabuwar jammiyyar sa mai suna APC.. daga bisani yai nasar lashe zaben da akai a shekarar 2015 Wanda akayi awatan mayu shekarar 2015.
DAGA ADAMU MAHADI ADAM GAYA



No comments:

Post a Comment