A
zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku suka zo masa suna rike da
wani saurayi suka ce:
Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.
Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.
Umar:
kai don me ka kashe musu uba?
Saurayi:
Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifinsu, sai mahaifinsu ya
bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na dauki dutsin na buge shi
ya mutu.
ya mutu.
Umar:
saboda haka zan tsaida haddi akan ka.
Saurayi:
ka saurara min kwana uku, mahaifina ya mutu ya bar ni da kanwata da
kuma dukiya, idan ka kashe ni, dukiyar da yar uwata za su tozarta.
kuma dukiya, idan ka kashe ni, dukiyar da yar uwata za su tozarta.
Umar:
wa zai lamunce ka?
Saurayi
ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".
Umar:
ka lamunce masa Ya Aba Dharr?
Abu
Dharri: na'am
Umar:
ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.
Abu
Dharr: na yarda.
Saurayi
ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na uku, saurayi bai zo ba,
Hankalin
kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.
Kafin
sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.
Saurayi:
na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi a kaina.
Cikin
mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai, bayan ka sami damar da za ka
iya gudu abinka?
iya gudu abinka?
Saurayi:
na ji tsoro, kar a ce cika alkawari ya kare cikin mutane.
Umar
ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce masa?
Abu
Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin mutane.
Wannan
jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, suka ce sun yafewa
saurayi.
saurayi.
Umar:
don me?
Suka
ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.
Ni
ma na isar muku da wannan kissa ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwa
ga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Da fatan za mu kasance
masu:
Cika alkawari, alkhairi da kuma Afuwa ga junanmu.
Cika alkawari, alkhairi da kuma Afuwa ga junanmu.
ADMIN: ADAM MOHD ADAM GAYA
ALLAH YASAKAMA DA ALKHAIRI
ReplyDelete