TITANIC
Yadda
Aka Kera Jirgin Ruwan "Titanic"
Shahara
Shahara
Cikin
shekarar 1997 ne kamfanin shirya fina-finai na 20th Century Fox da ke Amurka,
ta hadin kai da wasu kamfanoni ‘yan uwansa suka fitar da wani fim mai suna
“Titanic”, wanda ya samu shahara fiye da sauran fina-finan da aka fitar cikin
shekarar. Wannan fim na “Titanic”, wanda shahararrun ‘yan wasa irinsu Leonardo
DiCaprio, da Kate Winslet suka fito a ciki, yayi suna musamman a tsakanin
matasa masu sha’awar jigon soyayya a cikin fina-finai. Wannan a bayyane yake.
Ba ma a kasashen Turai da Amurka inda aka shirya fim fin kadai ba, hatta a nan
gida Nijeriya wannan fim ya samu shahara sanadiyyar wannan jigo na soyayya da
aka tsofa cikin fim din; inda jarumi Leonardo DiCaprio, da kuma jaruma Kate
Winslet suka narke cikin kogin soyayya. Bayan haka, editan fim din shi ma wani
sananne ne wajen sana’ar, watau David Cameron. A takaice dai, an sayar da
kwafen fim din na gundarin kudi da kimarsa ta kai dalar Amurka sama da biliyan
daya da dubu dari takwas. Kuma har zuwa yau, shi ne fim da aka kashe kudi wajen
yinsa fiye da kowane fim a duniya.
Sai
dai kuma, sabanin wannan jigo na soyayya da ke cikin wannan fim, wani abin da
ya fi kama hankalin wasu cikin masu kallo – musamman masana Kimiyyar Kere-kere
- shi ne tarihin da ke tattare da wannan jirgin da dukkan wannan lamari ya faru
a cikinsa. Da farko dai, wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1912, a cikin
wani tafkeken jirgin ruwa mai suna RMS Titanic da kamfanin White Star Line na
kasar Ailand (Ireland) ya kera tsakanin shekarar 1909 zuwa 1912. Sanadiyyar
girma da kayan alatun da ke cikin wannan jirgin ruwa, da kuma cewa babu wani
jirgin ruwan fasinja mafi girma kamarsa a lokacin, ta sa aka shirya wannan shiri,
daidai lokacin da wannan lamari na hadarin jirgin yake cika shekara 85 (1912 –
1997). A halin yanzu akwai buraguzan wannan jirgi na RMS Titanic a karkashin
teku, kuma masana kan ilimin karkashin kasa da teku sun yi hasashen cewa nan da
shekaru hamsin masu zuwa buraguzan za su dangana da gundarin kasan tekun baki
daya, watau Ocean Floor. A yau in Allah Ya so za mu dubi yadda aka kera wannan
jirgin ruwa, da wadanda suka zana shi, da kuma yadda aka yi wannan lamari ya
faru.
Kamfanin
kera jiragen ruwa mai suna White Star Line da Harland & Wolff da ke kasar
Ailand ne suka kera wannan tafkeken jirgin ruwan fasinja mai suna RMS Titanic.
Sun yi wannan aiki ne a filin kera jiragen ruwa da suke da shi a birnin Belfast
na kasar Ailand din. Kuma hakan ya faro ne cikin shekarar 1909. Kafin wannan
shekara, wannan kamfani na White Star Line ya fara kera wasu jirage masu girma
wadanda ya sanya wa suna Olympic, sannan ya yi kudurin kera wasu manya na
musamman, masu dauke da kayan alatu na kasaita, wadanda kuma babu kamarsu a
wancan zamani – wajen girma, da kayan alatu, da fasahar kere-kere da kuma
tsarin sadarwa. Asalin sunan da wannan kamfani yayi niyyar baiwa wannan jirgi
na Titanic dai shi ne “Gigantic”; ma’anarsu daya ne da “Titanic”. Wannan jirgi
na Titanic dai an kera shi ne da mafi kwarewar kwarewa na zamanin, ta amfani da
kwararrun injiniyoyin lokacin, da kuma mafi kwarewar fasahar kere-kere na
lokacin. Bayan dukkan wannan, shi ne jirgin da ya fi girma a lokacin; domin
bayan mutum dubu uku da dari biyar da arba’in da bakwai (3,547) da yake iya
dauka, har wa yau yana iya daukan jirgin sama nau’in Airbus 380 guda daya, da
manyan motoci nau’in bas, da kuma kanana. A takaice dai, wannan jirgi na iya
daukan kaya da mutanen da nauyinsu ya kai tan 46,328. Kamfanin J.P.Morgan da
International Mercantile Marine Company ne suka dauki nauyin kera jirgin. Su
suka bayar da kudade da kuma kayan aikin da ake bukata wajen kerawa.
ADAM M. ADAM GAYA
No comments:
Post a Comment