Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za
su taimaka wajen zama da mace lafiya.
Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a
cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu
don haka ka kiyaye su.
NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana
sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa
ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da
kauna.
NA UKU:
Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka
fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta
a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakanin ku.
NA HUDU:
Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar
daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu.
To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayin ka.
NA BIYAR:
Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a
cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada
ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace
ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka
tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a
Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkin sa.
NA SHIDA:
Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan
uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bata zabin ko kai ko
danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin
bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.
NA BAKWAI:
Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce,
wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan
hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaqo mata a lokacin da ta yi
wani kuskure kana kokarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta
kuwa shine sakinta.
To kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin
kuskuren, da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi
maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina baina.
NA TAKWAS:
To kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa
butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara
ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kadaa
wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan
dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata masu kyau.
NA TARA:
Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi,
saboda haka ne ma Allah mds ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya
wajabta mata a wadanban lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya
dauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama
azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka saukaka mata
umarnika da hane- hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya saukaka
mata farillansa.
NA GOMA:
Ka sani cewa ita mace ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka
tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka
kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.
Annabi (SAW) yace" Inai miku wasiyya da mata Ku rike su da alheri,
domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tankwararre kuma Mafi tankwarewar
kashi shi ne sama , idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan
kuma ka barshi haka to zai dawwama a tankware kuma a karkace, to don haka inai
muku wasiyya ta gari dangane da mata.
Kuma Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma
ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina" S . A. W
Allah ya bamu ikon zama da iyalan mu.
*(Daga: Malam Aminu Daurawa)*
1. Ciyarwa gwargwadon iko.
2. Tufatarwa daidai iko.
3. Shayarwa.
4. Kayan kwalliya.
5. Kayan tsafta.
6. Gurin kwana.
7. Kula da lafiya.
8. Hakkin saduwa.
9. Ilmantarwa.
10. Girmamawa.
11. Mutuntawa.
12. Tausasawa.
13. Yabawa abincinta ko kwalliya ko tsafta.
14. Nuna damuwa da ita.
15. Sakar mata fuska da murmushi.
16. Gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17. Zama hira da tattaunawa da ita.
18. Kiranta da wani suna mai dadi.
19. Yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20. Fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21. Taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22. Bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23. Bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24. Mutunta iyayenta da danginta.
25. A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26. A yaba mata idan tayi daidai.
27. Kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28. Banda duka.
29. Banda zagi.
30. Banda saurin fushi.
31. Ka zama miji mai tsafta.
32. Ka zama miji mai kula da goge baki.
33. Miji mai kwalliya.
34. Miji bamai almubazzaranci ba.
35. Miji bamai mai kwauro ba.
36. Miji bamai shan taba ba.
37. Miji bamai mai shan giya ba.
38. Miji bamai yawon dare ba.
39. Miji bamai neman mata ba.
40. Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalanka.
41. Miji mai yawan fada.
42. Kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyalinsa.
43. Kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalanka suke ciki.
44. Kada ka zama miji mai tsananin kishi.
45. Kada ka zama miji mai yawan zagi.
46. Ka nuna wa matarka cewa gamsu da
yanayinta.
47. Ka bata dama ta fadi raayinta.
48. Kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
49. Ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
50. Yin wanka tare a wasu lokuta.
51. Rera mata waka da kirari.
52. Yin wasa da guje-guje da iyalinka.
53. Kada ya zama miji mai zargi.
54. Kada miji ya zama mai mugunta.
55. Kada miji ya zama mai kushe.
56. Kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
57. Kada miji ya zama mai ragwanci.
58. Mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59. Miji ya zama mai kaunar 'ya'yansa.
60. Miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa na qware.