Showing posts with label ISLAMIC. Show all posts
Showing posts with label ISLAMIC. Show all posts

Monday, May 18, 2020

WASIYYA GA ANGO



Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.
Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su.
NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna.
NA UKU:
Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakanin ku.
NA HUDU:
Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayin ka.
NA BIYAR:
Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkin sa.
NA SHIDA:
Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bata zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.
NA BAKWAI:
Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaqo mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana kokarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta kuwa shine sakinta.
To kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin kuskuren, da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina baina.
NA TAKWAS:
To kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kadaa wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata masu kyau.
NA TARA:
Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah mds ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a wadanban lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya dauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka saukaka mata umarnika da hane- hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya saukaka mata farillansa.
NA GOMA:
Ka sani cewa ita mace ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.
Annabi (SAW) yace" Inai miku wasiyya da mata Ku rike su da alheri, domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tankwararre kuma Mafi tankwarewar kashi shi ne sama , idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan kuma ka barshi haka to zai dawwama a tankware kuma a karkace, to don haka inai muku wasiyya ta gari dangane da mata.
Kuma Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina" S . A. W
Allah ya bamu ikon zama da iyalan mu.

*SHAWARWARI (60) GA MAZA MASU AURE...*
*(Daga: Malam Aminu Daurawa)*
1. Ciyarwa gwargwadon iko.
2. Tufatarwa daidai iko.
3. Shayarwa.
4. Kayan kwalliya.
5. Kayan tsafta.
6. Gurin kwana.
7. Kula da lafiya.
8. Hakkin saduwa.
9. Ilmantarwa.
10. Girmamawa.
11. Mutuntawa.
12. Tausasawa.
13. Yabawa abincinta ko kwalliya ko tsafta.
14. Nuna damuwa da ita.
15. Sakar mata fuska da murmushi.
16. Gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17. Zama hira da tattaunawa da ita.
18. Kiranta da wani suna mai dadi.
19. Yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20. Fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21. Taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22. Bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23. Bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24. Mutunta iyayenta da danginta.
25. A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26. A yaba mata idan tayi daidai.
27. Kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28. Banda duka.
29. Banda zagi.
30. Banda saurin fushi.
31. Ka zama miji mai tsafta.
32. Ka zama miji mai kula da goge baki.
33. Miji mai kwalliya.
34. Miji bamai almubazzaranci ba.
35. Miji bamai mai kwauro ba.
36. Miji bamai shan taba ba.
37. Miji bamai mai shan giya ba.
38. Miji bamai yawon dare ba.
39. Miji bamai neman mata ba.
40. Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalanka.
41. Miji mai yawan fada.
42. Kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyalinsa.
43. Kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalanka suke ciki.
44. Kada ka zama miji mai tsananin kishi.
45. Kada ka zama miji mai yawan zagi.
46. Ka nuna wa matarka cewa gamsu da
yanayinta.
47. Ka bata dama ta fadi raayinta.
48. Kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
49. Ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
50. Yin wanka tare a wasu lokuta.
51. Rera mata waka da kirari.
52. Yin wasa da guje-guje da iyalinka.
53. Kada ya zama miji mai zargi.
54. Kada miji ya zama mai mugunta.
55. Kada miji ya zama mai kushe.
56. Kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
57. Kada miji ya zama mai ragwanci.
58. Mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59. Miji ya zama mai kaunar 'ya'yansa.
60. Miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa na qware.

ADDU’O’IN NEMAN FALALA DA NEMAN TSARI







ADDU’O’IN NEMAN
FALALA DA NEMAN
TSARI

1 -ADDU’AR TASHI DAGA BARCI Alhamdu lillahillazi ahayana ba’ada ma’amatana wa ilaihin Nushur.
2 – ADDU’AR SATUFAFI
♥ alhamdu lillahillazi kasani ma asturu bihi aurati wa atajammalu bihi.
3 – ADDU’AR CIRE
TUFAFI ♥ Ilbis jadidan wa ish hamidan wamuttu shahidan
4 – ADDU’AR
FITA DAGA GIDA ♥
bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala kuwatan illa billahi
5 – ADDU’AR SHIGA GIDA ♥
bismillahi walajna wa bismillahi kharajna wa alallahi rabbina ta wakkalna
6 – ADDU’AR SHIGA MASALLACI ♥
bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulillahi allahumma igfirli zunubi waftahli abwaba rahamatika
7 – ADDU’AR FITA DAGA MASALLACI ♥
bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulillahi allahumma igfirli zunubi waftahli abwaba fadhalika.
8 – ADDU’AR JUYAWA ACIKIN BACCI ♥ la ‘ilaha illallahu wahidulkahharu rabbussamawati wal’ardi wama baina wumal azizul gafar
9 – ADDU’AR IDAN MUTUN YARAZANA ACIKIN BACCI ♥ auzu bikalimatillahit tammati min gadabihi wa’ikadihi washarri ibadihi wamin hamazatisshayati wa anyahadurun
10 – ADDU’AR AKAN ABOKAN GABA DA NEMAN TSARI ALLAH YAYI MUNA TSARI DA SU AMEN ♥ Allahumma manzilal kitabisari’al hisabi ihzamil ahzaba Allahummah zamhum wazalzilhu
11 – ADDU’AR DA MUTUN ZAI KARANTA IDAN WANI ABU YAFARU A GARE SHI.
allahumma la sahla illa maja’altahu sahala fa anta taj’alul hazna izash’ita sahala
12 – ADDU’AR SHIGA MAKABARTA. Assalamu alaikum ya ahala darukaumin muminin wa inna in sha allahu bikum lahikuna
13 –
ADDU’A YAYIN DA ZA’A SA MAMACI A CIKIN KABARI. minha khalaknakum wafiha nui’ dukum wa minha nukhuri jukum taratan ukhura.
14 – ADDU’A A BAYAN ANBINNE MAMACI. Allahumma Igfirlahu Allahumma sabbithu
15 – ADDU’A GA
WANDA YAYI SABON AURE. Allahumma inni as’aluka khairaha wa kaira majabaltaha alaihi wa a ‘uzu bika min sharraha washarrima jabaltaha alaihi.
16 - ADDU’AR
DUBA MARAR LAFIYA:.
as’alullahi aima rabbal arshil azima an yashfiyaka.
16 - ADDU’AR SHIGA BANDAKI:.
Allahumma inni a’uzu bika minal khubusi wal khaba’is.
18. ADDU’AR
FITA DAGA BAN DAKI
gufranaka. Alhamdu lillahillazi azhaba annil aza wa afani.
19 - ADDU’A YAYINDA ANKA SAUKAR DA ANNOBA
ma sha allahu la kuwwata illa billahi.
20. ADDU’AR SAUKA AMASAUKI:. a’uzu bi kalimatilahi tamati min sharrin ma khalaka.

SUNAYEN SAHABBAN DA SUKA HALARCI YAKIN BADAR







JERIN SUNAYEN SAHABBAN DA SUKA HALARCI YAKIN BADAR TARE DA MANZON TSIRA (SAW)
1. Manzon Allah Muhammad (SAW).
2. Abu Bakar as-Shiddiq (RA)
3. Umar bin al-Khattab (RA)
4. Utsman bin Affan (RA)
5. Ali bin Abu Tholib (RA)
6. Talhah bin ‘Ubaidillah (RA)
7. Bilal bin Rabbah (RA)
8. Hamzah bin Abdul Muttolib (RA)
9. Abdullah bin Jahsyi (RA)
10. Al-Zubair bin al- Awwam (RA)
11. Mus’ab bin Umair bin Hasyim(RA)
12. Abdur Rahman bin ‘Auf (RA)
13. Abdullah bin Mas’ud (RA)
14. Sa’ad bin Abi Waqqas (RA)
15. Abu Kabsyah al- Faris (RA)
16. Anasah al-Habsyi (RA)
17. Zaid bin Harithah al-Kalbi (RA)
18. Marthad bin Abi Marthad al-Ghanawi (RA)
19. Abu Marthad al-Ghanawi (RA)
20. Al-Husain bin al-Harith bin Abdul Muttolib (RA)
21. ‘Ubaidah bin al-Harith bin Abdul Muttolib (RA)
22. Al-Tufail bin al-Harith bin Abdul Muttolib (RA)
23. Mistah bin Usasah bin ‘Ubbad bin Abdul Muttolib (RA)
24. Abu Huzaifah bin ‘Utbah bin Rabi’ah (RA)
25. Subaih (maula Abi ‘Asi bin Umaiyyah) (RA)
26. Salim (maula Abu Huzaifah) r.a.
27. Sinan bin Muhsin (RA)
28. ‘Ukasyah bin Muhsin (RA)
29. Sinan bin Abi Sinan (RA)
30. Abu Sinan bin Muhsin (RA)
31. Syuja’ bin Wahab (RA)
32. ‘Utbah bin Wahab (RA)
33. Yazid bin Ruqais (RA)
34. Muhriz bin Nadhlah (RA)
35. Rabi’ah bin Aksam (RA)
36. Thaqfu bin Amir (RA)
37. Malik bin Amir (RA)
38. Mudlij bin Amir (RA)
39. Abu Makhsyi Suwaid bin Makhsyi al-To’i (RA)
40. ‘Utbah bin Ghazwan (RA)
41. Khabbab (maula ‘Utbah bin Ghazwan) (RA)
42. Hathib bin Abi Balta’ah al-Lakhmi
(RA) 43. Sa’ad al-Kalbi (maula HathiB-) (RA)
44. Suwaibit bin Sa’ad bin Harmalah (RA)
45. Umair bin Abi Waqqas (RA)
46. Al-Miqdad bin ‘Amru (RA)
47. Mas’ud bin Rabi’ah (RA)
48. Zus Syimalain Amru bin Amru (RA)
49. Khabbab bin al-Arat al-Tamimi (RA)
50. Amir bin Fuhairah (RA)
51. Suhaib bin Sinan (RA)
52. Abu Salamah bin Abdul Asad (RA)
53. Syammas bin Uthman (RA)
54. Al-Arqam bin Abi al-Arqam (RA)
55. Ammar bin Yasir (RA)
56. Mu’attib bin ‘Auf al-Khuza’i (RA)
57. Zaid bin al-Khattab (RA)
58. Amru bin Suraqah (RA)
59. Abdullah bin Suraqah (RA)
60. Sa’id bin Zaid bin Amru (RA)
61. Mihja bin Akk (maula Umar bin al-KhattaB-) (RA)
62. Waqid bin Abdullah al-Tamimi (RA)
63. Khauli bin Abi Khauli al-Ijli (RA) 64. Malik bin Abi Khauli al-Ijli (RA)
65. Amir bin Rabi’ah (RA)
66. Amir bin al-Bukair (RA)
67. Aqil bin al-Bukair (RA)
68. Khalid bin al-Bukair (RA)
69. Iyas bin al-Bukair (RA)
70. Uthman bin Maz’un (RA)
71. Qudamah bin Maz’un (RA)
72. Abdullah bin Maz’un (RA)
73. Al-Saib bin Uthman bin Maz’un (RA)
74. Ma’mar bin al-Harith (RA)
75. Khunais bin Huzafah (RA)
76. Abu Sabrah bin Abi Ruhm (RA)
77. Abdullah bin Makhramah (RA)
78. Abdullah bin Suhail bin Amru (RA)
79. Wahab bin Sa’ad bin Abi Sarah (RA)
80. Hatib bin Amru (RA)
81. Umair bin Auf (RA)
82. Sa’ad bin Khaulah (RA)
83. Abu Ubaidah Amir al-Jarah (RA)
84. Amru bin al-Harith (RA)
85. Suhail bin Wahab bin Rabi’ah (RA)
86. Safwan bin Wahab (RA)
87. Amru bin Abi Sarah bin Rabi’ah
(RA)
88. Sa’ad bin Muaz (RA)
89. Amru bin Muaz (RA) 90. Al-Harith bin Aus (RA)
91. Al-Harith bin Anas (RA)
92. Sa’ad bin Zaid bin Malik (RA)
93. Salamah bin Salamah bin Waqsyi (RA)
94. ‘Ubbad bin Waqsyi (RA)
95. Salamah bin Thabit bin Waqsyi (RA)
96. Rafi’ bin Yazid bin Kurz (RA)
97. Al-Harith bin Khazamah bin ‘Adi
(RA)
98. Muhammad bin Maslamah al-Khazraj (RA)
99. Salamah bin Aslam bin Harisy
(RA)
100. Abul Haitham bin al-Tayyihan (RA)
101. ‘Ubaid bin Tayyihan (RA)
102. Abdullah bin Sahl (RA)
103. Qatadah bin Nu’man bin Zaid (RA)
104. Ubaid bin Aus r.a.
105. Nasr bin al-Harith bin ‘Abd r.a.
106. Mu’attib bin ‘Ubaid r.a.
107. Abdullah bin Tariq al-Ba’lawi r.a.
108. Mas’ud bin Sa’ad r.a.
109. Abu Absi Jabr bin Amru r.a.
110. Abu Burdah Hani’ bin Niyyar al-Ba’lawi r.a.
111. Asim bin Thabit bin Abi al-Aqlah r.a.
112. Mu’attib bin Qusyair bin Mulail r.a.
113. Abu Mulail bin al-Az’ar bin Zaid r.a.
114. Umair bin Mab’ad bin al-Az’ar r.a.
115. Sahl bin Hunaif bin Wahib r.a.
116. Abu Lubabah Basyir bin Abdul Munzir r.a.
117. Mubasyir bin Abdul Munzir r.a.
118. Rifa’ah bin Abdul Munzir r.a.
119. Sa’ad bin ‘Ubaid bin al-Nu’man r.a.
120. ‘Uwaim bin Sa’dah bin ‘Aisy r.a.
121. Rafi’ bin Anjadah r.a.
122. ‘Ubaidah bin Abi ‘Ubaid r.a.
123. Tha’labah bin Hatib r.a.
124. Unais bin Qatadah bin Rabi’ah r.a.
125. Ma’ni bin Adi al-Ba’lawi r.a.
126. Thabit bin Akhram al-Ba’lawi r.a.
127. Zaid bin Aslam bin Tha’labah al-Ba’lawi r.a.
128. Rib’ie bin Rafi’ al-Ba’lawi r.a.
129. Asim bin Adi al-Ba’lawi r.a.
130. Jubr bin ‘Atik r.a.
131. Malik bin Numailah al-Muzani r.a.
132. Al-Nu’man bin ‘Asr al-Ba’lawi
r.a.
133. Abdullah bin Jubair r.a.
134. Asim bin Qais bin Thabit r.a. 135. Abu Dhayyah bin Thabit bin al-Nu’man r.a.
136. Abu Hayyah bin Thabit bin al-
Nu’man r.a.
137. Salim bin Amir bin Thabit r.a.
138. Al-Harith bin al-Nu’man bin Umayyah r.a.
139. Khawwat bin Jubair bin al- Nu’man r.a.
140. Al-Munzir bin Muhammad bin ‘Uqbah r.a.
141. Abu ‘Uqail bin Abdullah bin Tha’labah r.a.
142. Sa’ad bin Khaithamah r.a.
143. Munzir bin Qudamah bin Arfajah r.a.
144. Tamim (maula Sa’ad bin
Khaithamah) r.a.
145. Al-Harith bin Arfajah r.a.
146. Kharijah bin Zaid bin Abi Zuhair r.a.
147. Sa’ad bin al-Rabi’ bin Amru r.a.
148. Abdullah bin Rawahah r.a.
149. Khallad bin Suwaid bin Tha’labah r.a.
150. Basyir bin Sa’ad bin Tha’labah r.a.
151. Sima’ bin Sa’ad bin Tha’labah r.a.
152. Subai bin Qais bin ‘Isyah r.a.
153. ‘Ubbad bin Qais bin ‘Isyah r.a.
154. Abdullah bin Abbas r.a.
155. Yazid bin al-Harith bin Qais r.a.
156. Khubaib bin Isaf bin ‘Atabah r.a.
157. Abdullah bin Zaid bin Tha’labah r.a.
158. Huraith bin Zaid bin Tha’labah r.a.
159. Sufyan bin Bisyr bin Amru r.a.
160. Tamim bin Ya’ar bin Qais r.a.
161. Abdullah bin Umair r.a.
162. Zaid bin al-Marini bin Qais r.a.
163. Abdullah bin ‘Urfutah r.a.
164. Abdullah bin Rabi’ bin Qais r.a.
165. Abdullah bin Abdullah bin Ubai
r.a.
166. Aus bin Khauli bin Abdullah r.a.
167. Zaid bin Wadi’ah bin Amru r.a.
168. ‘Uqbah bin Wahab bin Kaladah r.a.
169. Rifa’ah bin Amru bin Amru bin Zaid r.a.
170. Amir bin Salamah r.a.
171. Abu Khamishah Ma’bad bin Ubbad r.a.
172. Amir bin al-Bukair r.a.
173. Naufal bin Abdullah bin
Nadhlah r.a.
174. ‘Utban bin Malik bin Amru bin al-Ajlan r.a.
175. ‘Ubadah bin al-Somit r.a.
176. Aus bin al-Somit r.a.
177. Al-Nu’man bin Malik bin Tha’labah r.a.
178. Thabit bin Huzal bin Amru bin Qarbus r.a.
179. Malik bin Dukhsyum bin Mirdhakhah r.a.
180. Al-Rabi’ bin Iyas bin Amru bin Ghanam r.a.
181. Waraqah bin Iyas bin Ghanam r.a.
182. Amru bin Iyas r.a.
183. Al-Mujazzar bin Ziyad bin Amru r.a.
184. ‘Ubadah bin al-Khasykhasy r.a.
185. Nahhab bin Tha’labah bin Khazamah r.a.
186. Abdullah bin Tha’labah bin
Khazamah r.a.
187. Utbah bin Rabi’ah bin Khalid r.a.
188. Abu Dujanah Sima’ bin Kharasyah r.a.
189. Al-Munzir bin Amru bin
Khunais r.a.
190. Abu Usaid bin Malik bin Rabi’ah r.a.
191. Malik bin Mas’ud bin al-Badan r.a.
192. Abu Rabbihi bin Haqqi bin Aus r.a.
193. Ka’ab bin Humar al-Juhani r.a.
194. Dhamrah bin Amru r.a.
195. Ziyad bin Amru r.a.
196. Basbas bin Amru r.a.
197. Abdullah bin Amir al-Ba’lawi r.a.
198. Khirasy bin al-Shimmah bin Amru r.a.
199. Al-Hubab bin al-Munzir bin al-Jamuh r.a.
200. Umair bin al-Humam bin al- Jamuh r.a.
201. Tamim (maula Khirasy bin al- Shimmah) r.a.
202. Abdullah bin Amru bin Haram r.a.
203. Muaz bin Amru bin al-Jamuh r.a.
204. Mu’awwiz bin Amru bin al-Jamuh r.a.
205. Khallad bin Amru bin al-Jamuh r.a.
206. ‘Uqbah bin Amir bin Nabi bin Zaid r.a.
207. Hubaib bin Aswad r.a.
208. Thabit bin al-Jiz’i r.a.
209. Umair bin al-Harith bin Labdah r.a.
210. Basyir bin al-Barra’ bin Ma’mur r.a.
211. Al-Tufail bin al-Nu’man bin Khansa’ r.a.
212. Sinan bin Saifi bin Sakhr bin Khansa’ r.a.
213. Abdullah bin al-Jaddi bin Qais r.a.
214. Atabah bin Abdullah bin Sakhr r.a.
215. Jabbar bin Umaiyah bin Sakhr r.a.
216. Kharijah bin Humayyir al-Asyja’i r.a.
217. Abdullah bin Humayyir al-Asyja’i r.a.
218. Yazid bin al-Munzir bin Sahr r.a.
219. Ma’qil bin al-Munzir bin Sahr r.a.
220. Abdullah bin al-Nu’man bin Baldumah r.a.
221. Al-Dhahlak bin Harithah bin Zaid r.a.
222. Sawad bin Razni bin Zaid r.a.
223. Ma’bad bin Qais bin Sakhr bin Haram r.a.
224. Abdullah bin Qais bin Sakhr bin Haram r.a.
225. Abdullah bin AbuTausif di Manaf r.a.
226. Jabir bin Abdullah bin Riab r.a.
227. Khulaidah bin Qais bin al-Nu’man r.a.
228. An-Nu’man bin Yasar r.a.
229. Abu al-Munzir Yazid bin Amir r.a.
230. Qutbah bin Amir bin Hadidah r.a.
231. Sulaim bin Amru bin Hadidah r a.
232. Antarah (maula Qutbah bin Amir) r.a.
233. Abbas bin Amir bin Adi r.a.
234. Abul Yasar Ka’ab bin Amru bin Abbad r.a.
235. Sahl bin Qais bin Abi Ka’ab bin al- Qais r.a.
236. Amru bin Talqi bin Zaid bin Umaiyah r.a.
237. Muaz bin Jabal bin Amru bin Aus r.a.
238. Qais bin Mihshan bin Khalid r.a.
239. Abu Khalid al-Harith bin Qais
bin Khalid r.a.
240. Jubair bin Iyas bin Khalid r.a.
241. Abu Ubadah Sa’ad bin Uthman r.a.
242. ‘Uqbah bin Uthman bin Khaladah r.a.
243. Ubadah bin Qais bin Amir bin Khalid r.a.
244. As’ad bin Yazid bin al-Fakih r.a.
245. Al-Fakih bin Bisyr r.a.
246. Zakwan bin Abdu Qais bin Khaladah r.a.
247. Muaz bin Ma’ish bin Qais bin Khaladah r.a.
248. Aiz bin Ma’ish bin Qais bin Khaladah r.a.
249. Mas’ud bin Qais bin Khaladah r.a.
250. Rifa’ah bin Rafi’ bin al-Ajalan r.a.
251. Khallad bin Rafi’ bin al-Ajalan r.a.
252. Ubaid bin Yazid bin Amir bin al-Ajalan r.a.
253. Ziyad bin Lubaid bin Tha’labah r.a.
254. Khalid bin Qais bin al-Ajalan r.a.
255. Rujailah bin Tha’labah bin Khalid r.a.
256. Atiyyah bin Nuwairah bin Amir r.a.
257. Khalifah bin Adi bin Amru r.a.
258. Rafi’ bin al-Mu’alla bin Luzan r.a.
259. Abu Ayyub bin Khalid al-Ansari r.a.
260. Thabit bin Khalid bin al-Nu’man r.a.
261. ‘Umarah bin Hazmi bin Zaid r.a.
262. Suraqah bin Ka’ab bin Abdul Uzza r.a.
263. Suhail bin Rafi’ bin Abi Amru r.a.
264. Adi bin Abi al-Zaghba’ al-Juhani r.a.
265. Mas’ud bin Aus bin Zaid r.a.
266. Abu Khuzaimah bin Aus bin Zaid r.a.
267. Rafi’ bin al-Harith bin Sawad bin Zaid r.a.
268. Auf bin al-Harith bin Rifa’ah r.a.
269. Mu’awwaz bin al-Harith bin Rifa’ah r.a.
270. Muaz bin al-Harith bin Rifa’ah r.a.
271. An-Nu’man bin Amru bin Rifa’ah r.a.
272. Abdullah bin Qais bin Khalid
r.a.
273. Wadi’ah bin Amru al-Juhani r.a.
274. Ishmah al-Asyja’i r.a.
275. Thabit bin Amru bin Zaid bin Adi r.a.
276. Sahl bin ‘Atik bin al-Nu’man r.a.
277. Tha’labah bin Amru bin Mihshan r.a.
278. Al-Harith bin al-Shimmah bin Amru r.a.
279. Ubai bin Ka’ab bin Qais r.a.
280. Anas bin Muaz bin Anas bin Qais r.a.
281. Aus bin Thabit bin al-Munzir bin Haram r.a.
282. Abu Syeikh bin Ubai bin Thabit r.a.
283. Abu Tolhah bin Zaid bin Sahl r.a.
284. Abu Syeikh Ubai bin Thabit r.a.
285. Harithah bin Suraqah bin al-Harith r.a.
286. Amru bin Tha’labah bin Wahb bin Adi r.a.
287. Salit bin Qais bin Amru bin ‘Atik r.a.
288. Abu Salit bin Usairah bin Amru r.a.
289. Thabit bin Khansa’ bin Amru bin Malik r.a.
290. Amir bin Umaiyyah bin Zaid r a.
291. Muhriz bin Amir bin Malik r.a.
292. Sawad bin Ghaziyyah r.a.
293. Abu Zaid Qais bin Sakan r.a.
294. Abul A’war bin al-Harith bin Zalim r.a.
295. Sulaim bin Milhan r.a.
295. Sulaim bin Milhan r.a.
296. Haram bin Milhan r.a.
297. Qais bin Abi Sha’sha’ah r.a.
298. Abdullah bin Ka’ab bin Amru r.a.
299. ‘Ishmah al-Asadi r.a.
300. Abu Daud Umair bin Amir bin Malik r.a.
301. Suraqah bin Amru bin ‘Atiyyah r.a.
302. Qais bin Mukhallad bin Tha’labah r.a.
303. Al-Nu’man bin Abdi Amru bin Mas’ud r.a.
304. Al-Dhahhak bin Abdi Amru r.a.
305. Sulaim bin al-Harith bin Tha’labah r.a.
306. Jabir bin Khalid bin Mas’ud r.a.
307. Sa’ad bin Suhail bin Abdul Asyhal r.a.
308. Ka’ab bin Zaid bin Qais r.a.
309. Bujir bin Abi Bujir al-Abbasi r.a.
310. ‘Itban bin Malik bin Amru al-Ajalan (RA)
311. ‘Ismah bin al-Hushain bin
Wabarah (RA)
312. Hilal bin al-Mu’alla al-Khazraj (RA)
313. Oleh bin Syuqra. (RA)

SIFFOFIN MUNAFUNCI






SIFFOFIN MUNAFUNCI
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ، وَإِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ، متفق عليه؛
An karɓo daga Abdullahi dan Amru (R.A) daga Annabi (SAW) yace:
Abubuwa guda hudu wanda suka kasance tare dasu ya kasance munafiki, wanda siffa daya ta kasance tare da shi daga hufun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da shi, har sai ya bar ta.
1. Idan yayi magana, ya zamanto sai yayi karya.
2. Idan yayi alkwari, sai yasaba.
3. Idan an yi rigima dashi, sai ya ketare dokar Allah.
4. Idan kuma aka Qulla alƙawari, to zai yaudare ka.
Bukhari (34) da Muslim(58) suka rawaito shi.
SHARHI
--------------
Wadannan siffofi guda hudu idan suka taru ga mutum, to ya zama munafiki, in kuwa daya ce, to wanan ya zama yanada siffa ta munafunci.
To amma abin da ake nufi da munafunci a nan gurin, munafuncin aiki.
Don munafunci iri biyu ne kamar haka:
1. Akwai Annifaqul Amali, munafunci a cikin aiki.
Da Kuma
2. Annifaƙul I’itiqadi, munafunci na zuci, wanda yake nufin mutum ya bayyana musulunci a zahiri, amma a zuciyarsa yana nan kan addininsa na kafirci.
To duk mai wannan ba musulmi ba ne, ko da ya rantse.
Don munafukai masu irin wannan, sai da suka zo wajen Annabi (SAW) suka rantse suka ce sun yarda da shi amma Allah ya qaryata su Allah madaukakin sarki yace:
اذا جاء ك المنفقون قالو انك لر سو ل الله و الله يعلم انك لر سو له و
الله ان المنفقين لكذ بون ( المنا فقون:
(Idan Munafukai suka zo wajenka, suka ce, "Mun shaida kai Manzon Allah ne!” Allah ya san kai manzonsa ne, Allah ya shaida hakika Munafukai karya suke ) (Al-munafuƙun 1)
و من الناس من يقول ءامنا با الله وباليوم الا وم هم ب مو منين: البقرة.
(A cikin mutane akwai wadanda za su ce, "Mun yi imani da Allah da ranar ƙarshe"alhali su ba Muminai ba ne) [Al-Baƙara: aya ta 8].
To wannan shi ne munfuncin zuci, kudure kafirci a zuciya, amma mutum yana bayyana musulunci a harshensa, wannan ba musulmi ba ne, kuma irin wadannan su ne Allah yace akansu,
ان المنفقون فى الدرك الاسفل من النار ولن تجد لهم نص) النساء:
(Hakika munafukai suna kasan wuta, kuma ba zaka sami wani mataimaki a tare da su ba.) [Annisa’i]
ان المنفقون بخد عو ن الله وهو خد عهم و اذ قا مو الى الصوة قامو كسالى يراءون الناس ولا يذ كرو ن الله الا قليلا) النساء:
(Haqiqa munafukai suna yaudarar Allah, Amma Allah yana mayar musu da yaudararsu akansu, idan suka tashi yin sallah, sai su tashi suna kasala, suna yi (Sallar) don mutane su gani, ba sa ambaton Allah, sai zan kadan) [Annisa’i:142]
Duk ayar da tazo ta nuna dawwama a cikin wuta ga munafukai, to da irin wadannan munafukai take.
2. Kashi na biyu shi ne, munafunci a aikace.
Zuciyarka da imani, amma kana da wani aiki wanda bai kamata a ce kai musulmi ne kake yi ba, aikin irin aikin munafukai ne.
To irin wannan, idan mutum ya yi, sai ace ya yi aikin munafunci, amma ba ma cewa shi munafuki ne, sboda faɗin Allah a kansa, "Haƙiƙa munafukai suna qasan wuta...." wannan ba ta shafe shi ba.
Saboda kar mutum ya yi amfani da wannan hadisin, ya kafirta ‘yan uwansa, batare da ya fahimta ba, dole sai ya ware, Annifaƙul I’itiqadi, wanda yayi shi ya zama kafiri.
Amma Annifakul Amali, duk wanda ya yi shi yana nan a matsayinsa na musulmi, amma fasiƙin musulmi ne.
Allah (S.W.T) ya kiyaye imaninmu.