Showing posts with label SCIENCE. Show all posts
Showing posts with label SCIENCE. Show all posts

Wednesday, May 13, 2020

KETA SARARIN SAMANIYA

KETA SARARIN SUBHANA

Tsawon miliyoyin shekaru babban abinda ya fi jan hankali da burge Dan Adam shine yadda Tsuntsaye da kwari ke iya tashi sama. Wannan burgewa ta zama kishi domin mutane, duk da cewa Allah bai hore musu wata halitta a jikinsu da za su iya tashi ba, amma an yi ta kokarin kirkirar fuka-fukai don kwaikwayon halittu masu tashi. Mutane daban-daban daga al'ummomi da dama sun gwada tashi sama ta hanyar kwaikwayo, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma rasa gabobi. Duk da cikas da aka fuskanta maimaikon kokarin ya ragu sai ya ringa habaka. Cikin suratul Rahman sai Allah ya ce mana
Q55:33" Ya ku (gungun) aljanu da mutane, idan zaku iya ketasararin sammai da kasa, to ku keta. Amma sai da izinin Allah zaku iya ketawa"
Wannan aya ta zama daya daga cikin ayoyin mu'ujizar Qur'ani domin ta fadi wani abu da zai faru a gaba.
Abbas Ibn Firnas, mutumin Kasar Andalusia wanda ya rayu a garin Cordoba, shine masanin kimiyya na farko a tarihi wanda ya fara kera jirgin sama mai fuka-fuki kuma ya tashi sama ya yi zagaye har na kimanin mintuna goma a gaban bainar jama’a a shekarar 875 AD, wato kusan karni biyu da rabi bayan wafatin manzon Allah. Amma kamar yadda turawa su ka saba sace wa musulmi darajar farko ta kirkirar abubuwa da dama, ya sa ba’a jin sunan wannan dan taliki a hurumin mutum na farko da ya fara kera jirgin sama. Wannan bincike na sa bai sami ci gaba ba har daular musulunci ta Andalus ta rushe, amma ina zaton aikinsa ne ya janyo mashahurin masanin kimiyya na kasar Rum, wato Leonardo Da Vinci (1452), bayan kimanin shekaru 600, ya ba shi karsashin nazari a wannan fage inda har ya yi wasu zane-zane da ke nuna za'a iya kirkirar na'ura da za ta iya tashi ba tare da an kwaikwayi yin fuffuke irin na dabbobi ba. Duk da haka wannan zane bai yi tasiri ba har bayan kimanin shekaru 400 da mutuwar sa. A farkon karnin da ya gabata ne cikin shekarar 1903 wasu yan uwa guda biyu (Wilbur Brothers) na kasar Amurka su ka cimma nasarar yin inji na farko da ya bar doron kasa kuma yayi tafiya a cikin sararin samaniya. Wannan nasara ta samu ne sakamakon gane amfani da hanyoyin nan guda hudu dake ba kowane abu mai tashi damar iyo a cikin iska (4 forces of Aerodynamics) wato Ingiza (Thrust), Tirjiya (Drag), nauyi (Weight) da kuma karfin dagawa sama (Lift). Samun daidaiton wadanna abubuwa ke bada damar iyo a iska domin ingiza na samuwa ne daga karfin na'ura da kuma iska, haka nan tirjiya na samuwa ita ma daga na'ura da iska sai kuma karfin dagawa wadda ta ta'allaka ga nauyi dake dogaro ga maganadisun dake jan komai kasa (Gravity) wadda karfin inji ke iya gujewa. Ko daga wadannan abubuwa da ke baiwa jirgi ikon tashi sama, mai lura na iya gane cewa babu wani abu da zai iya tashi sama sai da izinin Allah domin da zarar Allah ya zuke iskarsa kuma ya dankare maganadisu (Gravity) to babu wani abu da zai iya dagawa sama ko da kuwa bai kai auduga nauyi ba.
Bayan wadancan abubuwa hudu da dole sai sun hadu ake iya tashi sama, akwai kuma wasu abubuwa dake da tasirin gaske wajen sauka da tashin jiragen sama:
--Yanayin Dumi (Temperature): da ke haifar da yadda iska zata kasance wajen nauyinta (Density) na daya daga ciki. Idan iska bata da nauyi jirgi ba zai iya tashi ba amma idan tayi nauyi sai ya iya tashi
--Iska: har ila yau, iska da ke kadawa ita ce ke bada saitin bangaren da jirgi zai tashi ko kuma ya sauka domin baya tashi sai ta daura da nahiyar da take kadawa haka wajen sauka sai ta daura da nahiyar da iskar ke kadawa (wato idan iska na kadawa yamma sai jirgi ya sauka ta gabas), shi yasa ake ganin wani jan kyalle mai kama da bututu a gefen titin da jiragen sama ke tashi, ya na nuna inda iska ke kadawa
--Layukan tsaye da na kwance a doron duniya (Longitudes da lattitude): na taimakawa matuka jirgi wajen gane nahiyoyi
--Mahadar wadancan layuka (Co-ordinates): Dukkan garuruwan dake doron kasa na da mahadar wadannan layuka da ke kusa da su kuma na kano daban yake da na kaduna ko Abuja. Shine yasa duk da cewa babu tituna a sama kuma matukan jirgin sama ba sa iya hangen doron kasa amma amfani da wannan mahada ya na sa su gane sun zo inda za su je ba tare da hakikanin ganin wajen ba
--Doron maganadisun duniya na arewa (North magnetic pole): Wanda duk ya san compass da ake sawa a dardumar sallah don nuna al-qibla yana ganin wata allura da ke kwance ta na nuna nahiya. To ita allurar a koda yaushe ta na fuskantar inda wannan maganadisu na arewa yake don haka a duk inda ka ke da zarar ka gane arewa dole ne ka gane ina sauran jihohin gabas, kudu da yamma su ke.
--Zangon rediyo (frequency) Tukin jirgi ba zai yiwu ba sai da zangon rediyo domin kusan mafi mahimmancin na'urorin da ake amfani da su ta hanyar zangon rediyo ake amfanin da su, misalin na'urarorin da ke amfani da zangon rediyo wajen jagorancin jirgi a wajen sauka (ELS), da na'urar gane nisa (DME), da na'urar gane nahiya nan take (Automatic direction finder) da kuma naurar tangaraho da rada dukkanninsu ta zangon rediyo ake amfani dasu.
Wadannan abubuwan da na lissafa sai da su jirgin sama zai iya tashi kuma dukkansu babu wani abu da bai dogara da wani abu halittacce daga ubangiji ba. Hatta shi kansa injin jirgi da mutum ne ya kirkire shi ba zai yi aiki ba sai da iska da Allah ya halitta. Domin ga yadda injin jirgi ke aiki: wato da zarar an kunna shi sai wasu manyan farfeloli da ke ciki su fara juyawa a guje kuma an kera su yadda idan suna juyawa sai su dinga zukar iska daga waje da karfin gaske (da mutum zai tsaya saitin su sai iskar ta fizgo shi cikin injin). Da zarar iskar ta shiga cikin injin sai ta dunkule saboda karfinta da kuma rashin sarari, sai a watsa mata fetur wanda zai sa ta fara konewa cikin gaggawa (idan ka leka cikin injin sai kaga wuta ce ta ke ci gagga-gagga) wannan konewa sai ta dada kumburawa da fadada wannan iskar yadda dole sararin wajen zai mata kunci dole ta nemi hanyar ficewa cikin gaggawa. Fitar wannan iska da karfi ke baiwa jirgin kuzarin zabura (misali shine idan ka cika balan-balan kuma sai ka saki bakinta za ka ga ta fice a guje tana zarya). A takaice haka ne yadda injin jirgi ke aiki, ka ga lallai shi kansa idan babu iskar da Allah ya halitta ba zai yi tasiri ba. Wannan shine manufar waccan aya da Allah ke cewa sai fa da izininsa za a iya keta sararin sama.
A yau Dan Adam ya kai tsaikon ba jiragen sama wadanda ke kara-kaina a doron duniya ba, har wadanda ba su da matuka an kirkira su na tafiye-tafiye zuwa wasu duniyoyi da ke cikin rukunin tauraron mu, wato Rana. Cikin irin wadannan jirage wanda ya fi shahara sune yan tagwayen jiragen da kasar Amurka ta harba daf da juna a shekarar 1977 wandanda aka yi wa lakabi da Voyager I da Voyager II. A yanzu haka shi wannan jirgi na Voyager 1 da ke gudun kilomita dubu 61,200 a awa guda, a ranar yau ta 20 ga watan Mayu na 2019, ya yi tafiyar shekaru 41 da wata 8 da kwana 15, tun a shekarara 2012 ya fice daga rukunin tauraronmu. Ya kasance jirgi na farko da ya iya dauko hoton jerin rukunin duniyoyi da ke kewaya rana. Wannan jirgi zai ci gaba da lulukawa sama’u har zuwa shekarar 2025 lokacin da na’urorinsa za su daina aiki. Tsarki ya tabbata ga ubangiji wanda ya baiwa Dan Adam irin wannan basira ta kera jirgi wanda ake sarrafawa daga doron duniya, ya yi tsawon shekaru ya na tafiya tare da bada bayanai na hotuna ga abubuwan da ya ke karo da su. A wannan jirgi ne Carl Sagan ya sa aka dauki sautin gaisuwa da yaruka daban daban na duniya ko da Allah ya sa watarana wannan jirgi zai karo da wasu halittu a hanyarsa.

Sunday, December 9, 2018

ABUBUWA GOMA DANGANE DA ZUCIYA

ALLAH GWANI | ABUBUWAN MAMAKI GOMA DANGANE DA ZUCIYA
1] Zuciya tana fara bugawa tun kwanaki 22—23 da halittar ɗan-tayi a mahaifa.
2] Girman zuciyar mutum ta kai girman dunƙulallen hannun mutum.
3] Zuciya tana bugawa sau 60—100 a minti ɗaya yayin hutu — yayin da ba'a aiki.
4] Zuciya tana bugawa kimanin sau dubu ɗari (100,000) a kowacce rana.
5] Zuciya tana buga ko harba jini da yakai yawan galan dubu biyu a rana.
6] Zuciya za ta iya cigaba da bugawa bayan an cire ta daga jiki.
7] Zuciya ta dogara ne da tsarin lantarki domin bugawa.
8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 —190 a minti ɗaya.
9] Zuciya tana harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu yakai mil dubu sittin (60,000 Miles) in da za'a warware su.
10] An fara yin tiyatar zuciya a shekarar 1893, wanda likitan zuciya Daniel Hale Williams baƙar fata ɗan ƙasar Amurka ya gudanar.

1] Ciwo
2] Kumburi
3] Ɗumi idan aka taɓa gaɓar
4] Kasa iya aiki da gaɓar
Abin da ya kamata a yi bayan targaɗe:
1] A kare gaɓar ta yadda ba za'a ƙara yin irin motsin da ya haddasa ciwon ba.
2] A hutar da gaɓar daga aikinta, saboda cigaba da aikinta ka iya ta'azzara raunin.
3] A sanya ƙanƙara a wurin ƙimanin minti ashirin: Za'a sami ƙanƙara sai a faffasata, sannan a ɗaureta a zani ko tawul mai tsabta sai a sanya ta a daidai raunin sai ta yi kimanin minti ashirin.
4] A naɗe ko a ɗaure da bandeji; wannan zai temaka wajen kare gaɓar da rage kumburi.
5] A ɗaga gaɓar da ta yi targaɗen sama; misali, ta hanyar ɗorata a kan fulo yayin da ake kwance.
6) Bayan wannan taimakon gaggawa, a gaggauta tuntuɓar likitan Fisiyo domin cigaba da jinyar gaɓar har ta warke ta dawo aiki yadda ya kamata.
Warkewa ta wannan hanya zai sa tantanan su warke, sannan a magance motsawar raunin ko tashinsa ta hanyoyi da dama kamar; amfani da na'urorin rage raɗaɗi da kuma na'urorin da ke haɓaka tohowar tantani ba tare da dogara akan shan magunguna ba.
Abubuwa da ba'a so a yi bayan targade:
1) Kada a lallanƙwasa ko mimmiƙar da gaɓar da zarar an yi targaɗe da zimmar dawo da aikin gaɓar ko rage raɗaɗin ciwo.
2) Kada a mulmula wurin targaɗen.
3) Kada a yiwa gaɓar ruwan ɗumin har sai bayan kwana uku.
4) Kada a shafa mai ko wani magani me zafin gaske a targaɗen.
#Sprain
#Sport #Injuries
#Athletics
#Ligaments
Copy from Physio Hausa
Posted by Adam m. Adam


ILLAR SHAN SIGARI (Physio Hausa)

Ko kasan illar da shan taba sigari ke da ita ga warkewar ƙashi bayan karaya?
Muggan sinadaren da suke cikin hayaƙin taba na hana ƙwayoyin halittar ƙashi hayayyafa ko tsatstsafowa da wuri bayan karaya domin a samu haɗewar gurbin karayar a ƙashin.
Wannan yasa masu shan taba sigari ke samun ƙarin tsawaitar lokacin da karaya ya kamata ta warke, ko kuma rashin haɗewar ƙashin ɗungurugum.
#QuitSmokingToday
Like the page 

Saturday, December 8, 2018

MEYE ABINYI BAYAN TARGADE (Physio Hausa)

ME YE ABIN YI BAYAN TARGADE?
Targaɗe na daga cikin raunikan da ke ci wa mutane tuwo a ƙwarya, musamman matasa 'yan wasannin ƙwallo, da sauran wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Har da ma tsofi ko waɗanda shekarunsu suka miƙa da ke da ƙarin haɗarin faɗuwa.
Targaɗe rauni ne ga tantani ko tantanai da ke riƙe da ƙashi da ƙashi a gaɓa. Wannan rauni kan kasance sakamakon faɗuwa, tintiɓe, tsalle, bugu, murɗewar ko ɗamewar gaɓa fiye da ƙima, da sauransu. Haka nan targaɗe yana faruwa ne a kan gaɓa kawai.
Matakan targaɗe: An kasa matakin targaɗe zuwa matakai uku kamar haka:
1] Matakin farko: Tantanin zai sami rauni saboda ɗamewa.
2] Mataki na biyu: Tantanin zai sami rauni saboda 'yar yagewa ko tsagewa.
3] Mataki na uku: Tantanin zai tsinke ne gaɓa daya.
Alamun targaɗe sun haɗa da faruwar waɗannan abubuwa a gaɓar:

DALILIN HAIFAR JARIRI DA SHANYAYYEN HANNU

DALILIN HAIFAR JARIRAI DA SHANYEYYEN HANNU
Daga cikin matsalolin da jarirai kan gamu da su yayin haihuwa da kan sa a haife su da shanyeyyen hannu akwai larurar da ake cewa "Obstetric Erb's Palsy" a turancin likita. Wannan matsalar tana faruwa ne sakamakon raunata turken sama (wanda ya ƙunshi tushen jijiyoyin laka ta biyar da ta shida) na dandazon jijiyoyin laka da suka taso daga wuya zuwa hannu.
Haɗarin raunata wannan jijiya yayin haihuwa yana da alaƙa da:
1) Tankarewar kai ko kafaɗar jariri yayin haihuwa; wannan zai sa a ɗame jijiyoyin tsakanin wuya da kafaɗa.
2) Rashin ƙwarewar ungozoma wajen janyo kan jariri yayin temakawa mai haihuwa.
Gwargwadon girman raunin da akai wa jijiyar gwargwadon girman naƙasun da hannu zai samu.
Saboda haka jijiyar za ta iya samun rauni ta hanyar:
a) Ɗamewa
b) Yagewa
c) Tsinkewa ko cisgewar daga jikin laka.
Alamomin wannan larura:

Kamar yadda aka sani duk lafiyayyen jariri kan kasance cikin motsa ƙafafuwa da hannaye a kowanne lokaci, sai dai duk jariri mai wannan matsala zai kasa iya lanƙwasa ko ɗaga hannun kamar yadda yake yi da ɗaya hannun. Wannan matsala za ta iya kasancewa a hannun hagu ko dama, wani lokacin ma duka hannaye biyun.
Ɓarin da yake da wannan matsala zai kasance:
1) Hannu a ɗamfare da jiki.
2) Hannu ya murɗe/ juye ciki.
3) Gwiwar hannu a miƙe.
4) 'Yan yatsun hannun a dunƙule.
Ga duk jijiyar da ta ɗame ko ta yage aikinta na kaiwa da komowar saƙonni zuwa tsokokin hannu zai yi rauni. Amma yayin da jijiyar ta tsinke to aikinta zai yanke ne gaba ɗaya, kuma har ta kan kai ga buƙatar yin tiyata domin haɗa ko sadar da tsokokin hannu da waɗansu jijiyoyin.
A dukkan yanayi biyun likitocin Physiotherapy ne ke da alhakin farfaɗo da ayyukan jijiyoyin da suka sami waɗannan matsaloli.
A tuntuɓi likitocin Physio da zarar an lura da jariri ba ya iya amfani da ɗaya daga cikin hannayensa yadda ya kamata bayan haihuwa.
Erb's Palsy Support Page
Erb's Palsy Group CIO
Copy From Physio Hausa
page
Posted by Adam Mohd Adam Gaya
adamm.gy@gmail.com

SHANYEWAR KAFA (Physio Hausa)

KA SAN DALILIN SHANYEWAR KAFA BAYAN ALLURA A DUWAWU?
"Injection Nerve Palsy" matsala ce da ke faruwa sakamakon raunata jijiyar laka ta 'sciatic nerve' dake kai saƙonni zuwa wasu gungun tsokokin ƙafa.
Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura akan jijiyar yayin yin allura a duwawu, ko idan ruwan allurar ya lalace, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar wanda hakan ka iya danne ko shaƙe jijiyar har aikinta ya kassare.
Waɗanda suke da haɗarin gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:
1) Wanda bai bada haɗin kai yadda ya kamata ba yayin yin allurar, musamman Ƙananan yara.
2) Mai rama sosai.
3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.
4) Da kuma wanda tsautsayi ya faɗawa.
Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukkan rassan jijiyar a ƙafar nan take ko bayan wani ɗan lokaci.
Alamomin sun haɗa da:
1) Matsanancin ciwo
2) Sagewa
3) Rauni ko rashin ƙarfin ƙarfa
4) Rashin ji a fata kamar taɓawa
5) Wahalar tafiya: dingishi, jan kafa, da sauransu.
Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, gaggauta ankarar da jami'in lafiyar da yai allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa kamar ba ayi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti ka iya kawo naƙasu ga ƙafar.
Saboda haka akwai matuƙar buƙatar ganin likitocin jijiya-ƙashi-da-tsoka (Physiotherapists) domin su ke da alhakin dawo da aikin ƙafar da ta sami wannan matsala.
Copy from Physio Hausa
Page
Posted By Adamu Mahadi Adam Gaya