DALILIN
HAIFAR JARIRAI DA SHANYEYYEN HANNU
Daga cikin matsalolin da jarirai kan gamu da su yayin haihuwa da kan sa a
haife su da shanyeyyen hannu akwai larurar da ake cewa "Obstetric Erb's
Palsy" a turancin likita. Wannan matsalar tana faruwa ne sakamakon raunata
turken sama (wanda ya ƙunshi tushen jijiyoyin laka ta biyar da ta shida) na
dandazon jijiyoyin laka da suka taso daga wuya zuwa hannu.
Haɗarin raunata wannan jijiya yayin haihuwa yana da alaƙa da:
1) Tankarewar kai ko kafaɗar jariri yayin haihuwa; wannan zai sa a ɗame
jijiyoyin tsakanin wuya da kafaɗa.
2) Rashin ƙwarewar ungozoma wajen janyo kan jariri yayin temakawa mai
haihuwa.
Gwargwadon girman raunin da akai wa jijiyar gwargwadon girman naƙasun da
hannu zai samu.
Saboda haka jijiyar za ta iya samun rauni ta hanyar:
a) Ɗamewa
b) Yagewa
c) Tsinkewa ko cisgewar daga jikin laka.
Alamomin wannan larura:
Kamar yadda aka sani duk lafiyayyen jariri kan kasance cikin motsa ƙafafuwa da
hannaye a kowanne lokaci, sai dai duk jariri mai wannan matsala zai kasa iya
lanƙwasa ko ɗaga hannun kamar yadda yake yi da ɗaya hannun. Wannan matsala za
ta iya kasancewa a hannun hagu ko dama, wani lokacin ma duka hannaye biyun.
Ɓarin da yake da wannan matsala zai kasance:
1) Hannu a ɗamfare da jiki.
2) Hannu ya murɗe/ juye ciki.
3) Gwiwar hannu a miƙe.
4) 'Yan yatsun hannun a dunƙule.
Ga duk jijiyar da ta ɗame ko ta yage aikinta na kaiwa da komowar saƙonni
zuwa tsokokin hannu zai yi rauni. Amma yayin da jijiyar ta tsinke to aikinta
zai yanke ne gaba ɗaya, kuma har ta kan kai ga buƙatar yin tiyata domin haɗa ko
sadar da tsokokin hannu da waɗansu jijiyoyin.
A dukkan yanayi biyun likitocin Physiotherapy ne ke da alhakin farfaɗo da
ayyukan jijiyoyin da suka sami waɗannan matsaloli.
A tuntuɓi likitocin Physio da zarar an lura da jariri ba ya iya amfani da
ɗaya daga cikin hannayensa yadda ya kamata bayan haihuwa.
Erb's
Palsy Support Page
Erb's
Palsy Group CIO
Copy From Physio Hausa
page
Posted by Adam Mohd Adam Gaya
adamm.gy@gmail.com
No comments:
Post a Comment