HIKAYAR SARKIN BIRNIN HUNAN DA ALJANNU
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Daga cikin tsoffin hikayoyin da suka shahara a birnin Sin daruruwan shekaru da suka gabata, wannan hikaya na sahun gaba.
Akace a wani zamani daya shude anyi wani babban birni mai suna Hunan. A
wani lokaci kuma, sai ya kasance anyi wani attajirin sarki a garin
wanda ya tara mamakon dukiya a baitul malinsa. Har ya kasance ya
taskance sunduk'ai na zinariya kimanin dubu d'ari shidda acikin wannan
taska. Wannan ne yasa yaga buk'atuwar samo mutum mai amana don dank'a
masa gadin wannan taska.
Akan haka, sai ya baiwa wani amintaccen
Bafadensa mukullin taskar. Ya shaida masa cewa ya dank'a tsaron dukiyar
duk dake ciki a hannunsa. Baya son ko allura ta b'ata.
A kullum,
wannan ma'aji yana baro gida da dare, yazo ya kwana da safe ya koma
gida. Kullum haka kullum haka. Rannaan ya baro gida kenan sai hadari ya
hadu a gari, kafin kace haka ruwa ya kece mai mamakon yawa. Tilas
ma'ajin taskar sarki ya nemi mafaka a wata rumfa tsohuwa, da niyyar da
zarar ruwa ya d'auke sai ya k'arasa wajen aikinsa.
Abu dai kamar
wasa, a wannan dare sai da aka kwana ana ruwa. Hakan na nufin ma'aji a
rumfar daya fake ya kwana sab'anin a taskar sarki. Aikuwa bayan
d'aukewar ruwa ya runtuma izuwa taska. Sai dai ga mamakinsa, yana zuwa
sai ya tarar da ita a washe. Babu ko allura.
Wannan abu yayi
matuk'ar sanya shi jimami. Ya rasa inda zaiyi da kansa. Yayi dube-duben
duk da zaiyi tare da tambayar makwabta, amma sam bai samu wani abu mai
dadi ba. A k'arshe dai ya yanke shawarar tafiya don sanar da sarki
wannan mummunan labari.
Da zuwan sa fada, ya fadi gaban sarki yayi
gaisuwa. Sannan ya kwashe labari ya fad'awa sarki. Sarki yace sam bai
gamsu ba, k'arewa ma sai yasa fadawa su tuhume shi, yace awurin sa
wannan ai barkwanci ne. Abu dai kamar wasa, fadawa suka rink'a nakad'awa
ma'aji azaba, amma bai canza maganar saba. Sarki yasa aka je taska aka
gano yadda ma'aji ya fada hakanan take.
Da sarki yaga ana neman
hallaka ma'aji ba tare da samun wata magana mai k'wari ba, sai yace a
dakata. Yacewa ma'aji ya bashi lokaci, da zimmar yaje duk inda wannan
dukiya take ya maido da ita, ko kuma a maimakon ransa.
Ma'aji ya
taso daga wurin sarki a gajiye, tinkis-tinkis. Yana tafiya kamar wani
mashayi sabida azabar da aka gana masa. Azuciyarsa kuwa yana ta sak'a
yadda zaiyi da rayuwarsa. Kwatsam sai ga wani makoho ya bangaje shi.
Ma'aji cikin fushi ya dubi makaho zai daka masa tsawa saboda bangajin da
yayi masa, amma dubawar dazaiyi sai ya fahimci ai makaho ne, don haka
baice uffan ba, ya cije baki kurum yayi gaba.
Makaho ya juyo yana
doddogarawa da sandarsa, yana kai hannu dazimmar kamo tufafin wanda ya
bangaza, yana cewa yi hakuri mallam, kune ke ganin mu ba mune ke ganin
kuba.
Ma'aji yace to babu laifi, amma dai zaifi kyau ka rink'a yawo
da d'an jagora, kasan halin mutanen yau da zafin zuciya, idan wani ka
bangaza haka yana iya kwabd'eka da mari.
Makaho yace kwarrai kam.
Mutanen yau sai hakuri. Sai dai na karanci wani abu a tattare dakai, don
haka idan kanaso matso kusa na taimakeka.
Ma'aji yace me ka karanta? Kuma wanne irin taimako zakayi mini? Yana mai matsawa kusa da makaho.
Makaho ya dafa kafad'ar ma'aji a dai-dai sa'ar dayazo daf dashi sannan
yace "ni daka ganni nan, makaho ne mai karantar abinda ke zukatan
mutane. Kuma a yanzu na fahimci cewa matsalar kud'i ce ta dugunzuma
ka.."
Ma'aji yace tabbas haka nan ne. Daga nan ya zayyana masa labarin sa duka.
Makaho yace to biyo ni idan kana Iyawa, da sannu zaka gani da idonka.
Daganan suka fara tafiya. Ma'aji na gaba makaho na biye, amma makaho ke
fadin inda za'abi. Shine ke cewa ayi gabas, yamma, kudu ko arewa. A
haka har suka bar gari, suka shiga kungurmin daji cikin manya-manyan
duwatsu. Suka hau kan wata hanya da take a tsakankanin duwarwatsu, basu
jima ba sai ga wani katafaren birni a gabansu.
Nan ma dai suka shiga
cikin garin, ga mutane nata harkokinsu babu mai tankawa wani, gidajen
garin kuwa na alfarma ne dogaye gwanin ban sha'awa.
Suna cikin
tafiya, sai makaho yace wa ma'aji ya tsaya. Sannan makaho yayi nuni da
sandarsa izuwa kofar wani babban gida na alfarma, yace "ka kwankwasa
wannan kofa, ka nemi taimakon mutanen gidan akan matsalar ka, da yardar
Mai sama zaka dace da buk'atar ka." Daga nan bai k'ara cewa uffan ga
ma'aji ba, ya wuce gaba yabar shi anan.
Ba tare da bata lokaci ba,
ma'aji ya matsa kusa da kofar gidan ya fara kwankwasa ta sannu a
hankali. Ba'ajima ba kuwa sai yaji ana kici-kicin bude kofa.
Wani
mutumi fari dogo ne yafito daga gidan, yana sanye da tufafi kalar
tufafin da fadawan sarkin Hunan ke Sanyawa. Ma'aji ya kwashe duk abinda
ke tafe dashi ya fadawa wannan mutumi. Mutumi kuwa yace kwarrai kazo
inda za'a taimakeka, amma sai idan zaka iya jira na wasu yan kwanaki a
cikin wannan gida.
Ma'aji yace to babu matsala. Shikenan kuwa sai suka dunguma izuwa cikin gidan....
Zamu cigaba gobe insha Allahu
No comments:
Post a Comment