Shanyewar tafin sawu wato "Foot Drop" na faruwa ne sakamakon shanyewar ko raunin jijiyar laka da ke kaiwa da komowar saƙonni zuwa ga gungun tsokokin da suke da alhakin ɗago tafin sawu sama.
Wannan matsala ta shanyewar tafin sawu na kawo matsala musamman a yayin tafiya da sauran matsalolin da suke faruwa tare.
Abubuwan da suke kawo shanyewar tafin sawu sun haɗa da:
1) Raunata jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon matsalolin da ke biyo bayan tiyata, yanka, sara, suka ko haɗarin abun hawa, da sauransu.
2) Shanyewar ɓarin jiki
3) Cutar shan-inna
4) Kuskurewar allura a ɗuwawu, musamman ga ƙananan yara.
5) Shaƙewa ko danne jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon:
a)ɗaurin karaya a ƙafa, musamman ɗorin karaya na gargajiya ko kuma idan ba'a sami kulawa daga likitocin Fisiyo tun da farko ba.
b) danne tushen jijiyar a gadon baya sakamakon ciwon baya.
c) doguwar naƙuda, musamman idan aka samu tsawaitar matakin naƙuda na biyu, da dai sauransu.
Alamomin shanyewar tafin sawu:
1) Kasa iya ɗago tafin sawu sama; wannan zai sa mutum ya ɗinga jan ƙafa ko tafin sawu. Saboda haka masu wannan matsala su kan yi tintiɓe, da kuma samun wahalar riƙe takalmi a ƙafar har sai an sa maɗaurin agara.
2) Ciwo a tsokokin sharaɓa, wato gaban sangalali ko ƙwauri zuwa tafin sawu.
3) Jin yanayi marar daɗi a sharaɓa, misali ka ji kamar tafiyar kiyashi a sharaɓa zuwa tafin sau.
Wannan matsala ana warkewa kamar ba'a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti ka iya kawo naƙasu a ƙafar. Saboda haka akwai matuƙar buƙatar ganin likitocin Fisiyo domin su ke da alhakin farfaɗo da aikin jijiyar tafin sawun da ta samu matsalar.
#Foot #Drop
#Dropped #Foot
#Injection #Palsy
#Obstetric #Palsy
#Low #Back #Pain
edited by Adam M adam
No comments:
Post a Comment