TARIHIN
DAURA
Sadiq Tukur Gwarzo
Tsohon Littafin tarihi na masarautar Daura da ake masa laƙabi da suna Girgam kamar dai
sauran littattafan tarihin yawa-yawan masarautu, ya ruwaito cewar tun a wajajen
shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isah A.S wasu mutane ƙarƙashin jagorancin shugabansu
mai suna Najib (Wasu sunce Nimroid ko Namarudu sunansa) suka yo hijira daga ƙasar su ta haihuwa Kan'ana
tare da riskar inda ƙasar Daura take a yanzu.
Babu takamaen dalilin tasowar su, amma dai ance akan hanyar su ta tafiya, sun
yada zango a tsohuwar Misira tsawon wani lokaci har kuma daga bisani wasu
Misirawan na dauri suka shigo cikinsu akayi hijirar tare dasu.
Ance kuma da suka baro Misira sai suka shigo cikin ƙasar Libya, inda suka sauka
a birnin Tarabulus, a zamanin da wani Sarki mai suna Abdurdaar ke mulkinta har
ya so ya mallake wannan runduna amma bai samu nasara ba, daga ƙarshe shi Najib ya cigaba da
tafiya da mutanensa har suka riski wani wuri da ake kira Tsohon birni, inda
suka fara kafin birnin Daura kafin su koma sabuwar Daura.
Akwai ƙarancin sani matuƙa game da kafuwar daura ko
kuma tsawon lokacin da tayi tana sharafi.
Marubuci Zakariyya Kabo ya kawo hujjojin cewa Daurawa misirawa ne da suka zo
daga ƙasar su ta misira a littafinsa mai Suna 'Gamsasshen
Tarihin Hausawa'. Ga kaɗan daga hujjojinsa akan
haka:-
1. Da akwai wani takobi mai rubutu ajikinsa irin na mazauna kasar misira ada
can wanda koda turawa suka zo sai da suka ce wannan takobin babu masu irinsa
sai misirawa. Kuma ko yanzu kaje Daura ana iya ɗauko
maka shi ka gani.
2. Yanayin tsarin gine-ginen fadar Daura ɗaya ne dana misirawan-da.
Zakaga anyi soro, sannan katangun gida masu kaurin Gaske. Akan kuma yi manyan
turaku da babban fili a matsayin tsakar gida da manyan zaurukan hutawar sarki.
3. Tamburan da ake zanawa a bangwayen gidan sarauta na Daura.
Haka shima Marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya tafi akan cewa tsoffin mazauna
Daura Mangawa ne waɗanda basa jin Hausa, don
haka koda Bagauda ya riski Kano sai daya shafe aƙalla shekaru biyu yana Koyon
harshen Hausa na mazauna Kano.
Akwai kuma masu ganin cewa hijira biyu ko uku akayi daga can kan'ana zuwa
Daura. Inda suka ce a hijira ta farko, Najib ne ya jagorance ta. Amma a hijira
ta biyu, wata jaruma da ake kira Daurama ce ta jagorance ta. Kuma daga sunan
tane aka laƙabawa birnin suna Daura, har kuma aka samu
cewa an shafe tsawon lokaci mata ne ke jagorantarsa.
Ga sunayen Sarakunan farko da aka samu sun mulki Daura tun tsawon lokaci da ya
gabata:-
1. Kufuru
2. Ginu
3. Yakumo
4. Yakunya
5. Wanzamu
6. Yanbamu
7. Gizir-gizir
8. Inna Gari
9. Daurama
10. Ga-wata
11. Shatu
12. Fatatuma
13. Sai Da mata
14. Ja Mata
15. Ha-Ma
16. Sha-wata
17. Daurama II (wadda alokacinta ake tsammanin Bayajidda yazo Daura)
An samu cewa kusan dukkan waɗannan sarakuna mataye ne,
ana kiransu da suna 'Kabaras ' fassararsa shine Magajiya da hausa. Watau wadda
tayi gadon mulki kenan.
Haka kuma, akwai maganganu na tarihi dake nuna cewar an samu ɓullar Shugabanni mataye masu laƙabin 'Kabara' a wasu
masarautu na ƙasar Mali, da Isra'ila. Amma dai babu wanda
ya tabbatar da wata alaƙa data kasance tsakaninsu da
waɗannan Kabarori na Daura duk da cewar akwai
hasashen yanayin bautar da akace Kabarorin sunyi yafi kamanceceniya shigen
wadda aka taɓa samu anyi a Isra'ila.
Zuwan Bayajidda akafi labartawa a matsayin tarihin Hausa da Hausawa, amma a
zahiri, labarai sun nuna cewar Bayajidda ya riski Daura ne a zamanin da
Sarauniya Daurama Shawarata ke mulki, ita kuwa ana ganin itace sarauniya ta
goma sha bakwai a tarihin mulkin Daura.
No comments:
Post a Comment