Thursday, December 20, 2018

ZUWAN LARABAWA KANO

Tarihin Zuwan Larabawa Kano
A shekara ta 1453 miladiyya, a zamanin sarkin kano Yakubu dan Abdullahi Barja, sarkin kano na goma sha shidda a mulkin kanawa, wadansu larabawa mutanen kasar Gadamus masu fatauci suka zo daga Tarabulus (Libya), suka sauka a kano. Sune larabawan farko da suka fara zuwa kano.
Da saukar wadannan fatake, sai sukaje wurin sarkin kano Mallam yakubu, a jujin ‘yan Labu, a lokacin ba’a gina gidan sarautar kano na yanzu ba, suka ce da sarki a cikin harshen larabci su fatake ne, suna so su zauna a kano domin suyi ciniki.
A wannan lokaci kuwa, limamin kano Mallam Muhammadu Hashimu ne yake fassarawa sarkin kano abinda wadannan fataken larabawa ke fada a matsayin tafinta. Daga nan sai sarikin kano yakubu yayi farin ciki kwarrai da gaske, sannan yace da shamakin kano ya kaisu sararin nan dake yamma da unguwar Garke watau Dandali, suyi gidaje su zauna acan.
Sabili da wadannan mutane suna da jar fata, sai mutanen kano suka sa musu suna Turawa. Don haka koda larabawan suka zauna a wannan wuri, sai mutane suka sanyawa wurin Dandalin Turawa. Dalilin sunan dandalin turawa kenan yau kusan shekaru 553 kenan.
Tun daga wancan lokaci ne larabawa suka cigaba da zuwa kano fatauci. Kamar misali akwai Yamalawa mutanen Yamen, da larabawan Tunis duk sun riski kano, amma kowadanne akwai nau’in kasuwancinsu.
Su Larabawan Libya mafi yawan abinda suke siyarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan kamshi da kayan zaki.
Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga lokacin da aka soma samar da kasuwanci a Kano. A zamanin da, mutanen kano sunfi riko da noma fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar da sana’o’i na gargajiya misalin rini, jima, kira da sak’a. Wadannan su suka haifar da ainihin kasuwanci, domin mutum zaiyi abu ya siyar ga jama’a.
Koda yake, a wancan lokacin, ba’a fara amfani da kudi ba a kano, ana yin cinikin furfure ne, watu ban gishiri in baka manda.
Daga baya ne lokacin da fatake larabawa ko Asbinawa da Agalawa suka zo kano, kasuwanci ya fara kankama a kano.
Haka ma, sauyawar akalar kasuwancin kasar hausa daga izuwa kano kamar yadda littafin ‘Kano cibil war and the British Ober Rule 1882-1940’ na Muhammad F.A ya ruwaito ya taimakawa kano matuka gaya, domin an samu cewar fatake sun yiwa katsina tawaye ne, suka koma kano ungurungum da kasuwancinsu.
Zuwan turawa kano kuwa, da kuma yadda suka samar da farin kudi a shekara ta 1930 don yin musanje ya hadaka kasuwanci sosai a kano. Domin a zamanin ne kanawa suka samu buewar ido ainun a harkar, har ya zamana suna yiwa kansu jagoranci, abinda ya sanya kano ta k’ara bunksa kuma kenan har ake mata kirari da Tumbin giwa ko dame kazo an fika.
Kai ba ma nan ba, har daga kasashen Kasabalanka ta Morocco da Yunana ta Girka fararen fata sunzo fatauci kano, bari kuma kuji yadda su ka zo.
A karni na goma sha biyar, zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammdu Rumfa, wasu turawa fatake sunzo kano daga girka. Kasarsu acan kusa da Istanbul take, ana kiranta Yunana, a yankin kasashen Turawa.
Su wadannan turawa sunzo kano ne domin fatauci, sun kai kimanin arbain, da rakuma kusan talatin da biyar, masu dauke da kayayyakin dukiyoyi masu yawa kamarsu alkyabbu, jabbobi, falmarori, kuftoci, jauhohi, hulunan dara, takalma, kilisai, takardu da kuma takubba.
Sai wadannan fatake suka iso kofar fadar sarki, suka nemi iso sannan sukayi gaisuwa gareshi da Larabci.
A cikin malaman da su ke zaune, sai wani Malami mai suna Abdurrahman ya rinka fassara maganarsu da hausa.
Daga nan sai wadannan fataken suka gayawa sarki Muhammadu Rumfa cewa su ba Larabawa ba ne, Turawa ne mutanen Giris. Sun iya larabci ne kurum kuma fatauci ne ya kawosu kano. Nan take sai suka fito da kayayyakin da suke siyarwa.
Da ya ke a wannan zamanin, ba’a soma ciniki da kudi ba, sai sarkin na kano ya tambaye su cewa ku kuma me kuke da bukatar saye a wurinmu? Sai sukace muna bukatar bayi, fatu, kiraga, albasa da tafarnuwa. Daga nan sai sarki yace yana bukatar dukkanin kayayyakin nasu, sannan yasa a shirya musu kayayyakin da suke da bukata.
An ce, an ba su masauki a inda asbitin unguwar Marmara yake a yanzu, akayi musu dakuna dogaye da tsangayu masu fadi da tsawo, aka yi musu hayin shirayi, sannan kowanensu aka bashi gado da tabarma.
Sarki ya tura musu bayi domin suyi musu hidima. A lokacin saida bayin suka haka musu tijiya domin samar musu da ruwa saboda rashinsa, shine har akace idan turawan suna bukatar ruwa sai suce Akwa, wai sunan ruwa kenan da yarensu, daga bisani sai aka sanyawa rijiyar suna ‘Yar Akwa.
Wadannan turawa da suka zo a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, sune suka fara kawo takardu da takobi. Suna kiran takardu “Yarta krata”, takobi kuma “Takopis”. Watakila daga nan sunayen suka samo asali domin da harshen hausa kansakali ake kiran takobi.
Da lokacin tashin fataken yayi, sai suka hada gagarumar kyauta suka baiwa sarki, sarki ya dauki nasa ya kuma rarrabawa hakimansa, sannan yasa aka basu bayi hamsin mata da maza, da dawaki masu yawa, gami da sauran kayayyakin da suka bukata tunda fari, sannan aka hada tawaga domin tayi musu rakiya.
Su ka fita daga kasar kano, suka bi ta wani gari mai suna Dingas zuwa Damagaran, suka kalli hanyar Tunis, suka shiga cikin sahara har zuwa Wani gari mai nisan gaske dake cikin sahara a yankin Libya, sunansa Murzuk, daga nan suka dangana da birnin Turawa a bakin babban tekun bahar Rum, suka shiga manyan jiragen ruwa, suka koma kasar su ta girka. Wadannan sune Turawan farko da suka soma zuwa Kano.

No comments:

Post a Comment