Friday, December 21, 2018

TARIHIN SARAUNIYA AMINA

TARIHIN SARAUNIYA AMINA TA BIRNIN ZAZZAU: MACE MAI KAMAR MAZA..
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Amina Sarauniyar Zazzau, ko kuma ace sadaukiyar zazzau wadda akace ta rayu a wajajen shekara ta 1433 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya uku da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Watau ita Amina ɗin da ƙanwarta mai suna Zariya, sai namijin kaninsu da ake kira Karama.
Ance Amina tayi sarautar Zazzau bayan rasuwar ɗan uwanta Karama wanda ya soma gadar mahaifinsu, a wajajen shekara ta 1509 zuwa 1522, ance kuma shekarunta 13 kacal akan karagar mulki ta rasu. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, shugaba ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.
Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka. Ta-yi-ta kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Mulkin Amina ya faɗaɗa tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja, da kuma can yankin kwararrafawa dake kasar bauchi sai kuma ƙananan garuruwa na kabilun Nufawa da jukun da dama da sarauniya Amina ta karɓe ikonsu waɗanda akace ba masu girma bane, amma ta kafasu a matsayin makarai, watau kamar dai ace wurare ne data ya-da zango kuma suka faɗa karkashin ikonta. Shine har akace tana sanyawa ayi ganuwa don samar da tsaro, ganuwar da ake sanyawa suna 'Ganuwar Amina' (har yanzu akwai wuraren a jihohin kano da katsina).
Da yake Kasar hausa na cikin yamutsin yake-yake tun daga wajajen shekara ta 1200 har zuwa 1700, Kasar zazzau ta zamo cikin halin rashin zama lafiya da makwabtanta a wannan lokaci. Daular Songhai ta kawo mamaya kasar hausa a wannan tsakani, sannan garuruwan kano, katsina da Borno sun zamo manyan abokan gaba ga zazzau. Don haka akace kasar zazzau ta zamo tana matukar bukatar jarumin shugaba a koda wanne lokaci.
Akace akan haka ne Amina ta gaji sarauta. Kuma duk da kasancewar ta mace, ta zamo jaruma abar tsoro ga sadaukai.
Tun tana karama ake ganin alamomin sadaukantaka a tare da ita har girman ta. Don haka lokacin da tahau kan mulki bata samu turjiya daga Sadaukan fadar zazzau ba.
Ance watan Amina ukku akan gadon sarauta ta fara fita yake-yake, inda tarinka cinye garuruwa da yaki tana faɗaɗa masarrautar ta.
A wata fadar ma ance kafin tabar mulki, saida ta tursasa sarakunan Kano da katsina su rinka biyanta Haraji na bayi da goro domin su zauna lafiya. Koda yake wani zancen ya ruwaito cewa Amina ta fuskanci matsananciyar turjiyar yaki daga wani Sarki mai suna Muhammadu Kanejeji, sarkin da Littafin Tarihin kano mai taken 'Kano chronicle' ya ruwaito a matsayin Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan haɓe. Amma wasu na ganin ta taɓa samun nasarar da har saida ta kori kowa daga birnin kano.
Sai dai bisa wannan, wasu masanan tarihi Mr. J.F Ajayi da Michael Crowder sun sanya rayuwar Amina baya da yadda ake ɗauka duba da yadda littafin tarihin kano ya zayyana cewar tayi sharafi a zamanin sarki Kanajeji, wanda lissafi ya auna cewar ya rayu ne a wuraren shekara ta 1420-1438.
Shi kuma wani masanin tarihin afirka mai suna P.J.M. McEwan ya ruwaito cewa Sarauniya Amina tacinye garuruwan Nufawa dana Kwararrafawa dake yankin ta duka da yaki a lokacin rayuwarta.
Wasu kuma sunce ga dukkan alamu, sai da Amina tafi karfin sarakunan hausa dake mulkin garuruwan kano, Rano, katsina, Daura da Gobir kafin rasuwar ta.
A takaice dai, Babu wani daya taɓa ruwaito cewa Sarauniya Amina ta taɓa aure na din-din-din a rayuwarta, balle ace tabar zuriya bayan rasuwarta. Abinda akace tanayi shine, tana zaɓar sadauki ne idan ta cinye gari da yaki ta (aureshi) kwana dashi, kashegari ta hallaka shi, har wasu sukace a irin haka ta haɗu da wani wanda ya hallaka ta.
Sarauniya Amina tana da jarumta sosai, don haka duk inda zatake yaki itace ke jagorantar rundunar yakin. Kuma zaiyi wahala tayi yaki bataci nasara ba. Wannan ne silar dayasa sunanta ya ɗaukaka a lokacin har wasu ke cewa Amina batayi sarautar zazzau ba, kurum dai Shugabar mayakan zazzau ce wadda sunanta ya kasance maɗaukaki.
Wasu turawa kuwa sun rubuta tarihinta ɗaruruwan shekaru da suka gabata. Har ma ance Shirin fim din Hollywood mai suna 'Xena: The warrior queen' anyi shi akan tane domin ya nuna tarihin ta.
Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu.
Wasu kuma sukace sam nemar ta akayi aka rasa bayan wani attajiri dayaji labarinta, sai yazo ya nemi kwana da ita, kafin gari ya waye ya sirare yabarta. Ance dagari ya waye sai itama tabar gari, kuma ba'a kara jin duriyar taba. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarinta ya ke ba.
Har ila yau, Wasu sunce kabarinta nacan kasar Bidda, kusa da wani gari nai suna Atagara, wai taje yaki ne ajali ya kamata har aka binneta acan..
Ana mata kirari da 'amina 'yar bakwa ta san rana, mace mai kamar maza kwari ne babu'.
Sai dai har yanzu da akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, musamman wajen tabbatar da cewar tayi sarautar zazzau ko kuwa gimbiyar yaki kurum ta zamo ga zazzau ɗin, ba illa yadda wani littafin masarautar zazzau na baya-bayan nan ya rubuta sunayen sarakunan Zazzau tun daga farkon madarautar har zuwa yau ba tare da sanya sunan taba, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce, Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa, a matsayin jaruma a daular masarautar Zazzau.

No comments:

Post a Comment