Friday, December 7, 2018
ILLAR SHAN TABA (Physio Hausa)
KADAN DAGA ILLOLIN SHAN TABA SIGARI
Shan taba sigari na daga cikin babbar matsalar da ta fi lashe rayukan masu shan tabar. Kuma a cikin duk masu shan taba biyu ɗaya daga cikinsu kan mutu ne sakamakon larurorin da shan taba ke jefa su.
Shan taba sigari na da gagarumar illa ga dukkanin jiki kamar haka:
Zagayawar jini: Kamar yadda aka sani ne cewa zagayawar jini shi ne zagayawar rayuwa. Sai dai yayin da gubar da ke ɗauke cikin hayakin taba sigari ya shiga cikin jini hakan zai sa:
a) Kaurin jini ya ƙaru, wannan zai ƙara haɗarin daskarewar jini.
b) Ƙaruwar wahalar hauhawar jini da ingiza bugawar zuciya fiye da ƙima; wannan zai ƙarawa zuciya wahalar harba jini zuwa sassan jiki.
c) Cunkushewar ko matsewar hanyoyin jini; wannan zai ragewa sassan jiki samun isashshen jini.
Huhu wanda a nan ne ake canjin iska tsakanin iskar "oxygen" da muke shaƙa da iskar "carbondioxide" da muke fitarwa waje.
Shan taba sigari na rage wannan aiki baya ga lalata tanadin kariya da Allah ya shiryawa huhun, wannan zai karya garkuwar huhun ta yadda cututtukan numfashi kamar tarin Tibi, sankarar ko dajin huhu za su kama mutum cikin sauƙi.
Waɗannan illoli na shafar dukkan sauran sassan jiki kamar zuciya, jijiyoyin jini, kayan ciki, fata, ƙashi da raguwar ƙwayoyin halittar haihuwa da dai sauransu.
A taƙaice dai bayan dumbum illolin shan taba sigari, dukkanin wata cuta ko larura shan taba sigari na ta'azzara ta.
Wannan hoto da ke ƙasa misali ne na huhun wanda ba ya shan taba da wanda yake sha.
#Lung #Cancer
#CigaretteSmoking
#RespiratoryDiseases
#StopSmoking
Copy From Physio Hausa
Posted by Adam M. Adam
08161595562
Labels:
SCIENCE
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment