Alqur'an









MUSAN AL,QUR'ANI
Qur'ani na da harrufa 323,015
.
Qur'ani na da Juzi'i 30
.
Qur'ani na da Hizbi 60
.
Qur'ani na da rubu'i 240
.
Qur'ani na da ushuri 480
.
Surorin Makkah 85
.
Surorin Madinah 29
.
Surarin da suka fara da 'Alhamdu' guda 5
.
Surorin da suka fara da Tasbihi guda 6
.
Surorin da suka fara da harrufa guda 19
.
Guraren Sujjada a Qur'ani guda 15
.
Farkon wanda ya fara bayyana karatun Qur'ani cikin
Sahabbai a Makkah shi ne Abdullahi bn Mas'ud
.
Kalma mafi tsayi a cikin Qur'ani ita ce 'Fa'asqainaakum
uhu' ta na da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.
.
Qira'ar da tafi shahara wajen karatun Qur'ani ita ce
ruwayar Hafs daga Aasim. Hafs ya bar duniya a shekara ta
180 H, Asim kuma 127H
.
Tsuntsaye da aka ambaci sunayen su a Qur'ani;
*Alba'ubh
*As Salwa
*Al Guraab
*Al Jarad
*An Nahl
*Al Hudhuda
*Az Zubab
.
Sahabin da aka ambaci sunan sa a Qur'ani Zaidu bn
Thabit a cikin Suratu Ahzab
.
Rabe-raben Qur'ani ; akwai Surori masu suna;
*As Saba'ud Diwaal- sune Bakara, Aali Imran, Nisa'i,
Ma'ida, A'araf, An'am, Yunus. Su 7 ne, su suka fi tsayi.
*Akwai Almi'aini; daga bayan Yunus zuwa Surorin da suka
kai ayoyi 100 ko kusa da haka
*Almathani
*Almufassal su ne kananan surori daga 'Qaaf' ko 'Hujrat'
.
Surah mafi girma ita ce Suratu Fatiha
.
Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu
.
Shugaban masu Tafsirin Qur'ani shi ne Imamud Dabariy
.
Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur'ani shi ne
Annabi Musa (s.a.w) sau 136
.
Sura ta karshen sauka cikin Qur'ani ita ce suratun Nasr
(Iza ja'a)
.
Aya ta karshen sauka a Qur'ani ita ce aya ta 281 a cikin
Bakara (Wattaquu yauman) a magana mafi inganci
.
Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi;
*Baqara-Saniya
*Namli-Qudan Zuma
*Ankabut-Gizo Gizo
*Nahli-Turuwa
*Fiyl-Giwa
.
Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa;
*Suratu Yusuf
*Suratu Hud
*Suratu Ibrahim
*Suratu Muhammad
*Suratu Nuh
*Suratu Yunus
.
Surorin da aka ambace su da sunayen su taurari;
*Suratut Najm
*Suratul Qamar
*Suratud Dariq
*Suratush Shams
*Suratul Buruj

adadin annabawan da al,qur ani ya
lissafo gasu kamar haka:
1 annabi adam (a.s)
2 annabi idris (a.s)
3 annabi hudu (a.s)
4 annabi lud (a.s)
5 annabi yusuf (a.s)
6 annabi yakub (a.s)
7 annabi shu,aibu(a.s)
8 annabi haruna(a.s)
9 annabi iliyasu(a.s)
10 annabi zakariya(a.s)
11 annabi sulaiman(a.s)
12 annabi nuhu(a.s)
13 annabi salihu(a.s)
14 annabi ibrahim(a.s)
15 annabi isma,il(a.s)
16 annabi ishaq(a.s)
17 annabi ayuba(a.s)
18 annabi yunus(a.s)
19 annabi yusha,u(a.s)
20 annabi yahaya(a.s)
21 annabi luqman(a.s)
22 annabi dawud(a.s)
23 annabi musa(a.s)
24 annabi isa(a.s)
25 annabi muhammad (s.a.w)
ya allah kabamu albarkacin annabi
muhammad (s.a.w)

Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta;
*Suratul Fajr
*Suratul Laili
*Suratud Dhuha
*Suratul Asr
.
Dabbobin da aka ambace su cikin Qur'ani;
*Baqara Saniya
*Ba'ubha Kwarkwata
*Zubaab Quda
*Namli Tururuwa
*Hudhuda tsuntsu
*Naaqah Raquma
*Khail Doki
*Bighaal Alfadari
*Himar Jaki
*Qusuurah Zaki
*Jaraad Fari
*Zi'b Kerkeci
*Kalb Kare
*Guraab Hankaka
*Fiyl Giwa
*Ankabuut Gizo Gizo
*Nahl Zuma
*Su'ban
*Ibil Rakumi
.
Sunayen Mala'iku da ya zo cikin Qur'ani;
*Jibril
*Miika'iil
*Maalik
*Haruut
*Maarut
.
Daular da aka ambace ta cikin Qur'ani ita ce daular
Rumawa-Ruum
.
Qabilar da aka ambace ta a cikin Qur'ani ita ce qabilar
Quraishawa-Quraish
.
Littattafan Tafsiri da suka fi shahara;
*Tafsirud Dabari
*Tafsiru Ibn Katheer
*Tafsiru Ruhul Ma'ani-Aluusiy
*Tafsirul Qurdabi
*Tafsiru Mafaatihul Gaib
.
Gurare 4 sunan Mai Gidan mu ANNABI SAW ya zo a cikin
Qur'ani;
*Aali Imran aya ta 144
*Ahzab aya ta 40
*Muhammad aya ta 2
*Fathi aya ta 29.

SURORIN QUR'ANI, GUDA SHIDA DAKE KARYA SIHIR KO ASIRI.
1.Suratul Taubaayata 14.
2. Suratul Yunus ayata 57.
3.Suratul Nahliayata 69.
4.Suratul Isra,iayata 82.
5.Suratul Shu,araayata 78~82.
6.Suratul Fuslilatayata 44





AYOYIN DA SUKE KUNSHI SUJJADAR TILAWA: SUNE KAMAR HAKA:
Suratu Al-a'araf aya ta 206.
Suratur Ra'ad aya ta 15
Suratun Nahli ayata 49.
Suratul Isra'i aya ta 107.
Suratu Maryama, aya ta 58.
Suratul Hajj, aya ta 18. Da aya ta 77.
Suratul Furkan aya ta 60.
Suratun Namli, aya ta 25.
Suratus Sajda, aya ta 15.
Suratu Saad aya ta 24.
Suratu Fussilat aya ta 37.
Suratun Najmi aya ta 62.
Suratul Inshikak aya ta 21.
Sai wannan ayar ta cikin Suratul Alak.
 

MUSAN AL,QUR'ANI
*Shin kokunsan mafi tsayin sura itace suratul Bakara?
*Shin kunsan cewa mafi gajartan sura itace Suratul Kausar?
*Shin kokunsan Aya mafi tsayi itace Ayatid-Daini Ayata 282 na cikin Bakara?
*Kokunsan Aya mafi gajarta itace حم، طه، يس، طس ؟
*Kokunsan Mafi tsayin Kalma itace فاسقيناكموه (hijir :22)?
*Kokunsan Babu Inda غ tabiyo غ sai guri guda ومن يبتغ غيرالايلام دينا.. (Al'Imran:85)?
*Kokunsan Cewa Babu Aya daya mai Harafin ك acikinta har 23 sai Ayatud-Daini?
*Kokunsan cewa Suratul Fatiha bata da harafin ف ko guda?



MUSAN ALQURANI
MUHIMMAN TAMBAYOYI DA AMSOSHINSU ACIKIN ALQURA'ANI MAI GIRMA.
❁✿❁═ FITOWA TA DAYA ═ ❁✿❁
═════════❁✿❁═════════
Tambaya 1:
Wace surah ce akasamu maimaituwar sunan Allah (اللّٰه) acikinta har sau saba'in da uku (73).
🔘Ams: Suratul Anfal.
Tambaya 2:
Wadamme surorine aka ambaci yin shawara da hadinkai acikin al'amurra?
🔘 Sune surorin Alu imrana ayata (152) da (159), da Namli daga aya ta (29 zuwa 35), shura aya ta (38).
Tambaya 3:
Akwai wata aya da ta maimaitu acikin wata sura har sau talatin da daya (31), wannan wace ayace?.
🔘Ams: itace ayar
( فَبِأَيِّ آَلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَان)
A suratur Rahman
Tambaya 4:
Akwai wata sura duk wanda yakaranta ta a ranar Jumu'ah za'a haskakamasa har izuwa wata jumu'ah, wannan wace surace ?
🔘Ams: Itace suratul kahf (الكهف) (صحيح الجامع الصغير وزيادته للألباني 6470- 6471).
Tambaya 5:
Wadamme surorine baza'a samu harafin kaaf (ك/ک) acikin suba?
🔘Amsa: Sune suratul: Asr, Quraysh, Falaq.( العصر، قريش، الفلق)
Tambaya 6:
Saunawa waqafi lazimi yazo acikin Qur'ani ?
🔘Ams: Yazo sau ashirin da biyu (22) , acikin surori goma sha ukku (13)
Tambaya: 7
Saunawa waqafi mamnu'i yazo acikin Qur'ani ?
🔘Ams: Yazo sau sittin da takwas (68) , acin surori ashirin da bitu (22)
Tambaya: 8
Wadamme surorine adadin waqafinda ke cikinsu yayi daidai da adadin ayoyinsu ?
🔘Ams: Sune surori kamar haka:
1.Anfal, adadin ayoyinta 75, adadin waqafinda ke cikinta 75.
2.Yusuf, adadin ayoyinta 111, adadin waqafinda ke cikinta 111.
3. Ibrahim, adadin ayoyinta 52, adadin waqafinda ke cikinta 52
Tambaya 9.
Wace surace dukkan ayoyinta suke karewa da harafin dal (د)?
🔘Ams:
Itace suratul ikhlas (قل هو الله أحد)
Tambaya 10.
Wace surace acikinta akwai umarni dubu, da hani dubu ,da hukunci dubu, da labari dubu?
🔘Ams: Itace sural baqara (!?) ( Walllahu a'alam).
 

HANYOYIN HADDAR ALQURANI
═════════❁✿❁═════════
Kafin yin bayani fillah filla gameda hanyoyin haddar Alqur'ani mai girma, ba makawa ayi bayani gameda abubuwa muhimmai kamar haka:
Miye ake nufi da haddar Alqurani ?
Minene sharuddan haddar Alqurani ?
Minene manufar haddar Alqurani ?
 Ma'anar haddar Alqurani 🔘
Haddar Alqurani aikine da yakunshi kiyaye ko haddace lafuzzan Alqurani tare da sauran abubuwanda suke da alaqa da su.
Kamar tafsirinsa, qira'o'insa, tajwidinsa, i'irabinsa, balagarsa, sarfunsa, da sauransu.
Amma matakin haddar Alqurani na farko shine haddace lafuzzansa.
🔘 sharuddan haddar Alqurani 🔘
Babban sharadin haddar Alqurani shi ikhlas !
Ma'ana dole wanda zaiyi haddar ya kyautace niyyarsa ya kuma gyara manufarsa ta hayanyar ya qudurta neman aljanna da kuma yardar Allah gameda karatunsa ko haddarsa ga Alqurani.
Koyon karatunsa daga malami, da daisauransu.
┈┈┈••••┈┈┈
🔘 Yadda ake haddar Qur'ani a zamanance🔘
┈┈┈••••┈┈┈
Akwai hanyoyin haddar Qur'ani guda biyu a zamanance
1:Hadda ta hanyar yin afani da mushafi.
2: Haddar saurare (Hadda ta hanyar yin amfani da na'ura mai kwakwalwa (Computer) ko recorder tape)..
Yanada kyau kafin kafara haddar Alqurani ka iyakance yawan abinda kake iya haddacewa duk rana, kamar rabin shafi, shafi daya koma fiye da haka.
Bayan ka iyakance adadin abinda kakeson ka haddata, misali shafi daya, sai kafara.
Alokacinda zakayi hadda da mus'hafi kana huskoki guda uku (3)
1. Haddar aya bayan aya,
Ma'ana zakayita mai maita ayar (misali sau 50) , sannan kacigaba zuwa ayar da ke gabanta itama kayita maimaita ta (misali sau 50)
Sannnan sai ka hadesu subiyun kayita mai mai tasu, har sai kaji ba Matsala sai kacigaba a hakan,
2: Haddar Jam'i
Ma'ana zaka hade ayoyi 2 ko 3 kayi ta mai mai tasu aqalla sau 100 harsai kayi musu rabdi mai kyau, sai ka kara wasu.
3: Haddar Shafi daya a lokaci guda, ta yadda zaka mai maita shafin da Qur'ani har sai kaji yahaddatu bamatsala.
Sai dai wannan yanada wahala..
Haddar saurare :
Haddace muhimmiya wurin tabbatuwar haddarAlqur'ani, kuma anfi samunta ga makafi wadanda basa gani,
Haddace ta hanyar yin amfani da recorder ko computer, ta yadda zaka sauke software ( برنامج القراءة) a cikin cumputer ka (ko wani makamancinsa), a aciki zai nuna maka yadda zaka zabi ayoyinda kakeson yayi ta mai mai tamasu, sauran bayanai sai kabudeshi zaka ga.
👉🏻 A karshe, yanada kyau musan



YADDA AKE YIN MURAJA’AR ALQUR’ANI
Alqur’ani yana bukatar muraja’a kuma idan mutum ba ya yin muraja’a zai iya manta duk abin da ya haddace, saboda shi al-qur’ani kamar rakumi ne idan ka rike akalarsa sai ya bi ka, idan kuma ka sake shi sai ya gudu, don haka idan mutum ya haddace alqur’ani yana da babban aiki akansa na yawan maimaita abin da ya haddace, kamata ya yi ka dinga hada hadda da muraja’a a lokaci daya don kar kana haddace wani wuri na baya yana rushewa, daga cikin hanyoyin muraja’a akwai:
• Idan zai yiwu ka kasa al-qur-ani gida uku, kashin farko daga suratu Annas zuwa Ankabut, kashi na biyu daga suratul Kasas zuwa Yunus, kashi na uku daga suratu Attaubah zuwa Bakara.
• Idan ka haddace izu ashirin, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata kana maimaita shi, wannan zai taimaka wajan karfafa haddarka.
• Idan ka haddace izu arba’in, kar ka cigaba sai ka yi kamar wata biyu kana maimaita shi, wannan zai sa haddarka, ta yi kwari.
• Idan ka haddace al-qur’ani gaba daya ka yi kokari ka matsawa kanka, wajan yin bitar wani bangare na al-qur’ani kullum, kamar izu biyar ko goma kulum ko makamancin haka, duk kuma ranar da ba ka yi ba, ka yi kokari ka rama.

HANYA MAFI SAUKI WAJEN SAUKE ALQURANI A WATAN RAMADHAN.
#SAUKA DAYA.

Bayan Sallar -

Asubahi - Azahar - Laasar - Magriba - Isha
Shafi 4 - Shafi 4 - Shafi 4 - Shafi 4 - Shafi4

Izu 60 cikin kwana 30

#SAUKA BIYU

Asubahi - Azahar - laasar - Magriba - Isha
Shafi 8 - Shafi 8 - Shafi 8 - Shafi 8 - Shafi 8

Izu 120 cikin kwana 30

#SAUKA UKU

Asubahi - Azahar - Laasar - Magriba - Isha
Shafi 12 - Shafi 12 - Shafi 12 - Shafi 12 - Shafi 12

Izu 180 cikin kwana 30.
FALALA GUDA 10 GA WANDA YA HARDACE ALQURANI MAI GIRMA.
Hakika babu wani abu da zuciya zata hardace mafi falala da daukaka ta sami matsayi mafi girma kamar hardace maganar Allah ,alqurani shine yake raya zuciya ya sanya ta samu nitsuwa da rabauta anan duniya da lahira,hardace alqurani ba karamar falala bace da matsayi wanda babu wanda yashan iyakar falalar da matsayinsa sai Allah,amma ga kadan daga cikin falalar guda goma;-
1-Allah yayi yabo na musamman ga bayinsa masu hardace littafinsa alqur'ani,sai Allah yace:
( ﺑﻞ ﻫﻮ ﺁﻳﺎﺕ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻓﻲ ﺻﺪﻭﺭ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻭﺗﻮﺍ ﺍﻟﻌﻠﻢ ).
2-Ana daukaka daraja da matsayin wanda ya hardace alqurani acikin aljanna.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Za'ace ga ma'abucin alqurani karanta ka rera kamar yadda kake karantawa a duniya,domin matsayinka a aljanna yana tsayawa akan ayar karshe da ka karanta).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
3-Ana sanyawa Mahardacin alqurani kayan ado na karama da yardar Allah agareshi.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Alqur'ani zaizo a ranar alqiyama,sai yace: ya Ubangiji kayi masa ado wanda ya hardaceni, sai a sanya masa kambi na Karama,sannan sai Alqurani yace,ya Ubangiji ka kara yi masa ado,sai a sanya masa kayan ado na karama,sai Alqurani yace ya Ubangiji ka yarda da shi,sai ace da mahardacin alquranin karanta ka rera kana da kyakkyawan aiki ga kowace aya).
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.
4-Mahardacin Alqurani yana tare da tawaga ta Mala'iku ma'abuta karamci da daukaka.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Misalin wanda yake karanta alqurani yana mai hardacesa, yana tare da tawagar Mala'iku Ma'abuta karamci da daukaka awajan Allah).
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
5-Wadanda sukayi kowa hardar Alqurani su sukafi cancanta da limanci a cikin al'umma.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Wanda zai limanci mutane shine wanda yafi so karatun littafin Allah......).
@Muslim
6-Mahardata alqurani sune ma'abuta kwamitin Shura"wato masu tattawa abinda za'a zartar ga al'umma".
Daga Ibn Abbas R.A yana cewa:
"Mahardata alqurani sune yan majalissar sayyadina umar kuma sune masu bashi shawara....".
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
7-Mahardata alqurani su ake fara gabatarwa awajan binnewa a qabari.
Annabi s a.w ya kasance yana hada tsakanin mutum biyu a qabari ga wadanda sukayi shahada a yakin Uhudu,sai yace:
(Wa yafi yawan hardace surar alqurani?) Sai ya fara gabatar da shi acikin qabari".
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
8-Mahardata alqurani sune mutanan Allah kuma zababbun bayinsa.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Lallai Allah yana da mutanansa zababbu daga cikin mutane, ma'abuta alqurani sune mutanan Allah zababbansu).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
9-Ku riqa girmama Mahardata alqurani saboda girmamasu yana cikin girmama Allah.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Lallai yana cikin girmama Allah girmama wanda yayi furfura daga cikin musulinci,da mahardacin Alqur'ani,wanda baya karkacewa da alquranin...... da girmama shugaba mai adalci).
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.
10-Wuta bata qona mahardata alqurani a ranar alqiyama idan sun mutu da imani.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Da alqurani zai kasance acikin wani abu to da wuta bata kona saba).
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.
Abinda ake nufi da ace akwai wani abu da yake tare da alqurani da wuta bata konasa ba saboda albarkar alqurani,to ina ga mai imanin da yake jibintar alqurani??.
@ ﺍﻧﻈﺮ : ﻓﻴﺾ ﺍﻟﻘﺪﻳﺮ .
Wannan shine mafi fatan dukkan wanda ya hardace alqurani a zuciyarsa kuma ya mutu da imani wuta bazata konasaba.
@ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ - ﺍﻵﺩﺍﺏ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ .
Allah ne mafi sani.
Allah ka sanyamu cikin bayinki ma'abuta alqurani da hardarsa da aiki da shi,kuma ka sanya mu cikin wadanda alqurani zai cece su a gobe alqiyama.



HADDAR KUR'ANI
Haddar Kur'ani ta fi sauki a kan a rike haddar da yawaita muraja'a.
Yawancin yara a makarantun hadda sukan haddace 'sura' amma da sun shiga 'sura' ta gaba sai ta baya ta zube gaba daya, haka za a yi ta yi har a kai karshe.
A kan yi bikin yaye yara da suka yi hadda, amma da za ka ritsa wadanda aka yaye ka jarraba su sosai, da wuya ba a fadi ba nauyi ba.
'Yan mata sun fi samari ba da himma wajen halartar makarantun hadda, kuma sukan ba da himma sosai wajen kokarin haddace Kur'ani, amma da sun tafi gidan miji, bayan wani lokaci karami, sai ka nemi haddar ka rasa.
 


""ABIN NEMA A WAJEN BAYI DANGANE DA ALQUR'ANI MAI GIRMA""
Mu Kasance masu neman sanin ma'anonin Alqur'ani mai Girma da dabbaqa aiki dashi,yin haka shine mafi girman Abinda Allah Ya ke buqata a wajen BayinSa sama da haddaceshi tare da bijirewa karantarwan da yake cikinsa.
Ya Allah Ka sanyamu cikin wadanda Alqur'ani zai cecesu ranar Sakamako.

DUK ABINDA YA HADU DA AL-QUR'ANI YANA SAMUN DAUKAKA
Rubutawa Ummu Abdillah Gombe
Allah Ya turo Mala'ika JIBRILU da Alkur'ani zuwa ga Annabi (s.a.w) sai ya zama shugaba a cikin Mala'ikun Allah.
Annabi Muhammad (s.a.w) Ya karbi Alkur'ani sai ya zama shugaba a cikin Annabawa da duk ragowar halittun Allah.
An saukar da Alkur'ani a cikin watan Ramadan sai ya zama mafifici a cikin watanni.
Alkur'anin ya sauka a daren Lailatul Qadri sai ya zama mafificin dare a cikin darare.
An saukar da Alkur'ani zuwa ga al'ummar Annabi (s.a.w) sai al'ummar Annabi suka zama mafifita a cikin al'ummatai.
Duk zuciyar da Alkur'ani ya sauka a cikinta zata zama mafificiya a cikin ragowar zukata.
Don haka duk wanda ya wayi gari ya karanta Alkur'ani wannan ranar itace mafificiyar rana a cikin ranakun sa a rayuwa.
Annabi (s.a.w) yace; "TABBAS ALLAH YANA DAUKAKA DARAJAR MUTANE DA WANNAN LITTAFIN (AL-QUR'ANI) KUMA YANA SAUKE DARAJAR WASUN SU DA SHI (AL-QUR'ANI).
Allah Ka sanya mu a cikin wadanda Al-Qur'ani zai cece su
SHIN KO KASAN CEWA IDAN KADAUKI ALQURANI
Shin ko kasan cewa idan kadauki Alqurani a hannuka shaidan yana fushi. Idan kabudeshi shaidan yana kuka. Idan kayi bismilla kuma ya kan gudu. Idan kashiga karatu kuma yakan samu kunci a zuciyarsa.
*_KO KASAN ALQUR'ANI ZAIYI CETON MA'ABOTANSHI RANAR ALQIYAMA?_*
.
.
.
"An karbo daga Abu Umaamah Albaahiliy yace: Naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa: " Ku karanta Alqur'ani don zai zo ranar alqiyama yana mai ceton ma'abotanshi."
(Muslim)
Wanda ya ajiye tilawa yayi maza ya dawo ya cigaba da tilawarshi ba dare ba rana.
Wanda bashi da tsari na tilawa arana toh ya dage yayi kuma ya kiyayeshi.
Ka tashi cikin dare mutane na barci kayi ibada to lallai hakan akwoi riban gaske.
Cikin shagulgulanka ka warema Alqur'ani lokacinsa.
Kina nan kin duqufa karatun littafan hausa, da kallace kallacen finafinai, anyi magana kince wai ba abin yi kana zaune shiru! ki kiyayi kanki da bata lokaci a aikin banza!
Abin mamaki wani sai ya zauna yaita cewa wai duk ya gaji bashi da abunyi? Yana nan jin wake wake da kallace kallace, zantuka marasa amfani! shin a ina ka aje Qur'aninka? ka manta zikirine? ko har ka gama tanadin guzurinka ne?
Kar ka kuskura ka bar Qur'ani duk rintsi don cikin yawan tilawar qur'ani tare da tadabburin ma'anoninsa, kiyayeshi ba dare ba rana, aiki dashi, yanada wani dadi da natsuwa dake mantar dakai dukkan wahalhalun rayuwa, damuwa، dagulewan al'amura, baqin ciki da sauransu.
Ga kuma tarin Laada ko wane harafi daya lada goma. zaka iya qirga yawan ladan? Kaga yanda Ubangiji keso ma bayinsa rahamarsa sai wanda yaqi.
Shaikhul Islam bnTaimiyyah Allah ya masa rahama yace: Banga wani abu da yake gyara hankali da ruhi, kuma yake kiyaye jiki, sannan yake qunshe da farinciki fiye da lizimtar kallon littafin Allah.
'Yan uwa mu yi kokarin ribatan lokutanmu ga ababen da zasu amfanemu.

MUTANE 15 BASU TARE DA
MU, INJI MANZON ALLAH
S.A.W

1-Wanda baya kyautata
karatun alqurani.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 7527 )
2-Wanda yake ihu da
kururuwa alokacin masifa,da
wanda yake Aske gashin
kansa saboda wata masifa da
tasame shi,ko yake yaga
tutafunsa alokacin da wata
Masifa ta sameshi.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ( 1866 ) . ﻗﺎﻝ
ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ : ﺻﺤﻴﺢ
3-Wanda yake algush,baya
tare da mu.
@ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ : ﺻﺤﻴﺢ
4-Wanda yake dukan
kumcinsa alokacin
masifa,yake yaga tufafinsa
alokacin masifa,ko yake kira
ko kirari irin na jahiliyya.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 1297
5-Wanda baya jin tausayin
qananan cikinmu,kuma baya
girmama manyan cikin
mu.baya tare da mu
@ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : ﺣﺪﻳﺚ ﻏﺮﻳﺐ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ : ﺻﺤﻴﺢ .
6-Wanda yake koyi da
waninmu baya tare da mu
(Wanda yake koyi da
Yahudawa ko Masara baya
tare da mu).
@ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ( 2194 ).
7-Baya tare da mu, wanda
yayi Chamfi ko akayi masa
chamfi ya yarda,ko yayi
Bokanci ko akayi masa
Bokanci, ko yayi Sihiri ko ya
yiwa wani sihiri.
@ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ( 2195
8-Wanda ya Dauki takobi
akanmu(wanda ya dauki
takobi yakemu) baya tare da
mu.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 6874
9-Baya tare damu wanda yake
koyi da wani tafarki wanda ba
namuba.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ( 5439
10-Wanda baya rage gashin
bakinsa baya tare damu.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ( 6533 )
11-Wanda yayi da'awar
abinda banasaba yace
nasane,to baya tare damu.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ( 112
12-Wanda yayi Harbi cikin
dare baya tare damu.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
13-Baya tare damu, namijin
da yake kamanceniya da mata
daga cikin maza da wadanda
suke kamanceniya da maza
daga cikin mata.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ( 5433
14-Baya tare da mu,wanda ya
koyi harbi,kuma ya iya,sannan
yabari har koyansa ya lalace.
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ( 1919 )
15-Kada ku zauna tare da
mushrikai yabar yan uwansa
musulm.......... wanda yayi
hakan baya tare damu.
@ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ( 2330 )
ME AKE NUFI DA BAYA TARE
DA MU.
Ibn Hajar Al'asqalany acikin
Fathul Bari yana cewa:
(Baya tare damu;Yana nufin
baya kan sunnarmu ko
tafarkinmu ko hanyarmu,ba
yana nufin baya cikin
musulunci ko yazama
kafiriba.....har zuwa karshen
maganarsa).
@Duba Fathul Bari.
Allah ka rayamu akan tafarki
da Sunnar Annabi s.a.w kuma
ka amshi rayukanmu akan
haka.
KU KARANTA WASIYYOYIN DA
AKA UMURCI ANNABI S.A.W
YA KARANTASU GAREMU A
CIKIN SURATUL AN'AM
:
. 6:151 - Ka ce: "Ku zo, in
karanta abin da Ubangijinku
Ya haramta." wãjibi ne a
kanku kada ku yi shirkin kõme
da Shi, kuma ga mahaifa biyu
(ku kyautata) kyautatãwa,
kuma kada ku kashe ɗiyanku
sabõda talauci, Mũ ne Muke
azurta ku, kũ da su, kuma
kada ku kusanci abũbuwa
alfãsha, abin da ya bayyana
daga gare ta da abin da ya
ɓõyu, kada ku kashe rai
wanda Allah Ya haramta, fãce
da hakki. Wannan ne (Allah)
Ya yi muku wasiyya da Shi:
Tsammãninku, kunã hankalta.
6:152 - Kada ku kusanci
dũkiyar marãya fãce da wadda
take ita ce mafi kyau, har ya
kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika
mũdu da sikli da ãdalci, bã
Mu kallafã wa rai fãce
iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi
magana, to, ku yi ãdalci, kuma
ko dã yã kasance ma'abũcin
zumunta ne. Kuma da
alkawarin Allah ku cika.
wannan ne Ya yi muku
wasiyya da shi: Tsammãninku,
kunã tunãwa.
6:153 - Kuma lalle wannan ne
tafarkĩNa, yana madaidaici:
Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi
wasu hanyõyi, su rarrabu da
ku daga barin hanyãTa.
Wannan ne Allah Ya yi muku
wasiyya da shi tsammãninku,
kunã yin taƙawa.
LOKACIN DA ALLAH YA SAUKAR DA
WANNAN AYAR TA:
ﻭﺭﺣﻤﺘﻰ ﻭﺳﻌﺖ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ *
Ma'ana: Rahamata ta yalwaci
dukkan komi".
Sai Iblis yace:
ﺃﻧﺎ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ .
Ai nima ina daga dukkan komi.
Sai Allah ya saukar da:
ﻓﺴﺄﻛﺘﺒﻬﺎ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﻳﺘﻘﻮﻥ ﻭﻳﺆﺗﻮﻥ
ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﻳﺂﻳﺎﺗﻨﺎ ﻳﺆﻣﻨﻮﻥ *
Ai rahamata zan rubutata ne
kawai ga wadanda suke
kiyaye dokokina kuma suke
bada zakka, da wadanda kuma
suke yin imani da Ayoyina.
Sai Yahudu da Nasara suka
ce:
ﻧﺤﻦ ﻧﺘﻔﻲ ﻭﻧﺆﺗﻲ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ .
Indai hakane ai muma muna
kiyaye Dokokin Allah kuma
muna bada zakka.
Sai Allah ya saukar da Ayah ta
gaba kamar haka:
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺘﺒﻌﻮﻥ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻨﺒﻰ
ﺍﻷﻣﻲ *
Wadanda za a rubuta musu
wannan rahamar Sune
wadanda suke bin Manzon
nan Annabin nan Ummiyyi.
Ibnu Jurayj yace:
ﻓﻨﺰﻋﻬﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺇﺑﻠﻴﺲ ﻭﻋﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ
ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ، ﻭﺟﻌﻠﻬﺎ ﻷﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ .
Allah ya zare Ayar ga barin
Iblis da Yahudu da Nasara, sai
ya sanyata ga Al'ummar
Annabi mai tsira da Aminci.
ﺟﺎﻣﻊ ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ ﻟﻠﻄﺒﺮﻱ ( 9/97 ) .
ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻟﻠﻘﺮﻃﺒﻲ
‏( 9/38 ).


 

LITTAFAN TAFSEER MAFIYA SHAHARA ADUNIYAR MUSULUNCI.
1- Tafseer Ibn Jareer Attabariy.
2- Tafseer Abil-Laith Assamarqandiy.
3- Tafseeril Bugawiy.
4- Tafseer Baqiy Ibn Makhlad.
5-Tafseer Darul Manthur.
6- Tafseer Ibn Katheer.
7-Tafseer Ibn Abbas.
8-Tafseer Jalalainiy.
9- Tafseer Arraziy.
10- Tafseer Irshadil Aqal.
11- Tafseer Gara'ibul Qur'an.
12- Tafseeril Kishaf lil zamakhshariy.
13- Tafseeril Khazin.
14-Tafseerin Nusfiy.
15- Tafseer Assirajil Muneer.
16- Tafseeril Qurtubiy.
LAQABI DA ALKUNYA ACIKIN LITTAFIN ALLAHِ.
Dasunan Allah mai Rahama Mai Jin kai.
Tsira da amincinsa su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W da Ahlinsa da Sahabbansa dama wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har yazuwa ranar Sakamako.
.
Ayau wannan Shafi zaiyi dubane zuwa ga Laqubba da Alkunya na wadansu Bayin Allah da sukazo acikin Alqur'ani Mai girma.
1- ABU LAHAB = Sunansa na Asali Abdul'Uzza.
2- Almasihu ibn Maryam A.S = Wannan kai tsaye Annabi Isah A.S ake nufi.
.
3- Nuh A.S = Sunansa na Asali Abdul-Gaffar.
.
4- Zannun= Shikuma ana nufin Annabi Yunus A.S be.
.
5- Zulqifl A.S = Sunansa na Asali Bishir ibn Ayyub A.S.
.
6- Ruhul-Qudsi ko Ruhul Amin= Wannan Kumar Mala'ika Jibrilu A.s Kenan.
.
7- Zulqarnain A.s = Asalin sunasa shine Iskandar, Wasu kuma Sukace Sunansa Hurmus, ko Hardis ko Marziban ibn Mardibah, kokuma Yunaniy.
.
8- Uzairu = Asalin Sunansa Qidfir ko Idfir.
.
9- 'Dalutu = Ance sunansa Shawil ibn Anbar.
.
10- Fir'aun = Asalin Sunansa shine Walidu ibn Mus'ab ibn Rayyan.
.
Wadanda ba Wadannanba kuwa duk Sunayene kuma Zamuzo garesu da yardan Allah.
Allah ne Mafi Sani. (Aduba littafin التحبير في علم التفسير shafi na 152).
""WAJIBCIN TILAWAR ALQUR'ANI""
"عن أبى موسى الأشعري قال، قال رسول الله صلى الله عليه وسلم "تعاهدوا هذا القراءن، فوالذى نفسي بيده لهو أشد تفصيا من الإبل فى عقلها" متفق عليه.
An kar'bo daga Abuu Musa al'Ash'ariy yace, Manzon Allah (S) yace "Ku Alqwarci Wannan ALQUR'ANI, ina Rantsuwa da wanda Rayuta take HannunSa, Lallai Shine (ALQUR'ANI) yafi tsananin Ku'bucewa sama da Raqumi a Mad'aurinsa". (BUKHARIY DA MUSLIM NE. SUKA RAWAITO WANNAN HADISI).
**FA'IDODIN WANNAN HADISI**
1, Wajincin Riqo da Tilawar AlQur'ani mai Girma don Gudun mantashi.
2,Yawan Qaranta AlQur'ani da maimaitashi yana gadar da Ingantaccen Tilawarsa.
3,Saurin Kwacewar Tilawarsa a lokacinda aka K'aurace masa.
Mu Yawaita Salati ga fiyayyan Halitta a wannan Yini na Juma'a. اللهم صل وسلم على نبينا محمد.




ALQUR'ANI BABBAN KUNDI (2)
.
*Shin kokunsan mafi tsayin sura itace suratul Bakara?
*Shin kunsan cewa mafi gajartan sura itace Suratul Kausar?
*Shin kokunsan Aya mafi tsayi itace Ayatid-Daini Ayata 282 na cikin Bakara?
*Kokunsan Aya mafi gajarta itace حم، طه، يس، طس ؟
*Kokunsan Mafi tsayin Kalma itace فاسقيناكموه (hijir :22)?
*Kokunsan Babu Inda غ tabiyo غ sai guri guda ومن يبتغ غيرالايلام دينا.. (Al'Imran:85)?
*Kokunsan Cewa Babu Aya daya mai Harafin ك acikinta har 23 sai Ayatud-Daini?
*Kokunsan cewa Suratul Fatiha bata da harafin ف ko guda?
ALQUR'AN BABBAN KUNDI (1):
.
Acikinsa akwai labarin
nagartattun bayi kamar-
Annabawa, Manzanni, siddikai,
shahidai, waliyyai, da ma
tsaka-tsakin bayi a wajen
ayyukan alkhairi.
*Akwai labarin yadda ake
sanin Allah, da yadda za'a
bauta masa, da yadda mutum
zai zama na gari har ya taka
martaba ta waliyyan Allah
wadanda idan da zasu yi
rantsuwa da Allah akan wani
al'amari to zai barrantar dasu.
*Akwai labarin nagartattun
Sarakunan duniya wadanda
suka mulki duniya daga
mahudarta har zuwa
mafadarta, suka shimfida
adalci suka taimaki gaskiya da
ma'abotanta suka kuma
azabtar da azzalumai, suka
yada tauhidi suka rushe
bautar wanin Allah, irinsu Zul-
karnaini.
* Akwai labarin azzaluman
sarakuna wadanda suka rudu
da abinda Allah ya yaga musu
na mulki suka yi zalunci a ban
kasa suka danne gaskiya da
ma'abotanta suka kuma yada
karya suka taimaki makaryata
irinsu Fir'auna da
makamantansa.
*Akwai labarin matasa
wadanda suka bi Allah a
lokacin kuruciyarsu sai Allah
ya kara musu shiriya akan
shiriya, kamar Ashabul-kahfi.
*Akwai labarin makircin 'yan
uba da gunzugulu da kazafin
mata, da sharri duk sunzo a
sirar Yusuf Alayhis-Salam da
yan'uwasa da kuma Imra'atul
Aziz.
*Akwai mu'ujizozi masu
gallabar tunani kamar
Haihuwar Isa Alayhis-Salam
da fashewar teku ya zama
hanyoyi domin Musa Alayhis-
Salam da Mutanensa su wuce,
da baccin Ashabul da labarin
wanda Allah ya kashe shekara
dari kuma ya raya shi da dai
sauransu....
* Akwai ilimin gyaran zuciya
da likitancin cututtukan jiki, da
ilimin kimiyya da fasaha, da
ilimin sanin dabi'a da ilimin
sanin lissafi da Ilimin falaki da
sauransu....
Kai akwai ilimin komai ma,
babu abinda ba'a bayyana ba
acikin AlQurani, wanda ya sani
ya sani wanda bai sani ba
kuma bai sani ba.
Saboda haka al'ummar da
littafinta shine AlQurani,
Annabinta shine Muhammad
SAW ita tafi kowane al'umma
cancantar jagoranci a dukkan
komai, sai dai da dama daga
cikin Musulman kansu basu
san AlQuranin ba bare su kira
wasu zuwa ga haskensa.
ALQUR'AN BABBAN KUNDI:
Acikinsa akwai labarin
nagartattun bayi kamar-
Annabawa, Manzanni, siddikai,
shahidai, waliyyai, da ma
tsaka-tsakin bayi a wajen
ayyukan alkhairi.
*Akwai labarin yadda ake
sanin Allah, da yadda za'a
bauta masa, da yadda mutum
zai zama na gari har ya taka
martaba ta waliyyan Allah
wadanda idan da zasu yi
rantsuwa da Allah akan wani
al'amari to zai barrantar dasu.
*Akwai labarin nagartattun
Sarakunan duniya wadanda
suka mulki duniya daga
mahudarta har zuwa
mafadarta, suka shimfida
adalci suka taimaki gaskiya da
ma'abotanta suka kuma
azabtar da azzalumai, suka
yada tauhidi suka rushe
bautar wanin Allah, irinsu Zul-
karnaini.
* Akwai labarin azzaluman
sarakuna wadanda suka rudu
da abinda Allah ya yaga musu
na mulki suka yi zalunci a ban
kasa suka danne gaskiya da
ma'abotanta suka kuma yada
karya suka taimaki makaryata
irinsu Fir'auna da
makamantansa.
*Akwai labarin matasa
wadanda suka bi Allah a
lokacin kuruciyarsu sai Allah
ya kara musu shiriya akan
shiriya, kamar Ashabul-kahfi.
*Akwai labarin makircin 'yan
uba da gunzugulu da kazafin
mata, da sharri duk sunzo a
sirar Yusuf Alayhis-Salam da
yan'uwasa da kuma Imra'atul
Aziz.
*Akwai mu'ujizozi masu
gallabar tunani kamar
Haihuwar Isa Alayhis-Salam
da fashewar teku ya zama
hanyoyi domin Musa Alayhis-
Salam da Mutanensa su wuce,
da baccin Ashabul da labarin
wanda Allah ya kashe shekara
dari kuma ya raya shi da dai
sauransu....
* Akwai ilimin gyaran zuciya
da likitancin cututtukan jiki, da
ilimin kimiyya da fasaha, da
ilimin sanin dabi'a da ilimin
sanin lissafi da Ilimin falaki da
sauransu....
Kai akwai ilimin komai ma,
babu abinda ba'a bayyana ba
acikin AlQurani, wanda ya sani
ya sani wanda bai sani ba
kuma bai sani ba.
Saboda haka al'ummar da
littafinta shine AlQurani,
Annabinta shine Muhammad
SAW ita tafi kowane al'umma
cancantar jagoranci a dukkan
komai, sai dai da dama daga
cikin Musulman kansu basu
san AlQuranin ba bare su kira
wasu zuwa ga haskensa.
ALQUR'ANI BABBAN KUNDI (2)
*Shin kokunsan mafi tsayin sura itace suratul Bakara?
*Shin kunsan cewa mafi gajartan sura itace Suratul Kausar?
*Shin kokunsan Aya mafi tsayi itace Ayatid-Daini Ayata 282 na cikin Bakara?
*Kokunsan Aya mafi gajarta itace حم، طه، يس، طس ؟
*Kokunsan Mafi tsayin Kalma itace فاسقيناكموه (hijir :22)?
*Kokunsan Babu Inda غ tabiyo غ sai guri guda ومن يبتغ غيرالايلام دينا.. (Al'Imran:85)?
*Kokunsan Cewa Babu Aya daya mai Harafin ك acikinta har 23 sai Ayatud-Daini?
*Kokunsan cewa Suratul Fatiha bata da harafin ف ko guda?
.
Ya Allah ka sanar damu Alqur'ani kabamu ikon aiki dashi.
ALQUR'ANI BABBAB KUNDI (3)
.
*Shin kokasan cewa MUHAMMAD IBN MUSLIM IBN SHIHAB AZ-ZUHRIY Shine Wanda ya haddace Alqurani cikin Watanni 2 ?
.
*Shin kasan cewa Suratul MUJADALA Irace surar da akowace Aya saida Sunan Allah da Kalmar Allahu yazo?
.
*Kokasan ABU MUSA AL'ASH'ARIY yafi kowa dadin sautin karatun Alkur'ani?
.
*Kokasan Cewa sunan Allah da Kalmar الله yazo acikin Alqurani agurare 980?
.
*Kokasan cewa Sunan Annabi S.A.W da Kalmar محمد yazo cikin Alquranine agurare 4?
.
*Kokasan cewa sunan Annabi Musa shine akafi anbatawa a alqurani?
.
*sannan sunan Annabi Zulkifl shine aka ambata sau 1?
.
*kokasan cewa ABU AS'WAD ADDU'ALIY shine mutumin dayafara yiwa Alqur'ani Wasalu da digo ?
.
*shin kokasan cewa Sahabi gudane wato Zaidu sunansa yazo a alqur'ani.
.
Ya Allah ka kara mana sanin Wannan luttafi naka.



LAQABI DA ALKUNYA ACIKIN LITTAFIN ALLAHِ.
.
Dasunan Allah mai Rahama Mai Jin kai.
Tsira da amincinsa su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W da Ahlinsa da Sahabbansa dama wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har yazuwa ranar Sakamako.
.
Ayau wannan Shafi zaiyi dubane zuwa ga Laqubba da Alkunya na wadansu Bayin Allah da sukazo acikin Alqur'ani Mai girma.
.
1- ABU LAHAB = Sunansa na Asali Abdul'Uzza.
.
2- Almasihu ibn Maryam A.S = Wannan kai tsaye Annabi Isah A.S ake nufi.
.
3- Nuh A.S = Sunansa na Asali Abdul-Gaffar.
.
4- Zannun= Shikuma ana nufin Annabi Yunus A.S be.
.
5- Zulqifl A.S = Sunansa na Asali Bishir ibn Ayyub A.S.
.
6- Ruhul-Qudsi ko Ruhul Amin= Wannan Kumar Mala'ika Jibrilu A.s Kenan.
.
7- Zulqarnain A.s = Asalin sunasa shine Iskandar, Wasu kuma Sukace Sunansa Hurmus, ko Hardis ko Marziban ibn Mardibah, kokuma Yunaniy.
.
8- Uzairu = Asalin Sunansa Qidfir ko Idfir.
.
9- 'Dalutu = Ance sunansa Shawil ibn Anbar.
.
10- Fir'aun = Asalin Sunansa shine Walidu ibn Mus'ab ibn Rayyan.
.
Wadanda ba Wadannanba kuwa duk Sunayene kuma Zamuzo garesu da yardan Allah.
Allah ne Mafi Sani. (Aduba littafin التحبير في علم التفسير shafi na 152).


















1 comment:

  1. Maa Shaa Allaah ,Allaah yasaka da mafificin alkhairi.
    Amma malan inada Yar wata tambaya da Kuma Karin bayani wurin da akace sunan Allaah ya maimaitu say 73 Amma bayan nawa binciken ya nuna akasin haka..

    ReplyDelete