Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات
أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ
الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
1.wanda ya fi kowa tausayin al,ummata shi ne ABUBAKRIN ASSIDDEEQ
2.Wanda ya fi kowa karfi acikin addini (wanda ba ya bari ataba addinin ALLAH) shi ne UMAR
3.Wanda ya fi kowa jin kunya shi ne: USMAN
4.Wanda ya fi kowa sanin hukunce-hukunce
5.Wanda ya fi kowa iya karatun Qur,ani shi ne UBAYYU BIN KA,AB
6.Wanda ya fi kowa sanin halal da haram shi ne MU,AZU BIN JABAL
7.Kowace al,umma ta na da Amini, Aminin wannan al,umma shi ne ABU UBAIDA BIN JARRAH
8.Wanda ya fi kowa sanin ilimin rabon gado shi ne: ZAIDU BIN
SABIT
9.Kowanne Annabi ya na da mataimaki AZZUBAIR kaine mataimakina
10.Wanda ya ke son yayi karatun Qur,ani kamar yadda aka saukar da shi, to yayi salon karatu irin na ABDULLAHI BIN MAS,UD
11. HASAN da HUSAINI su ne shugabannin matasan gidan Aljannah
12.Shahidi wanda ya ke tafiya a ban qasa shi ne DALHATU BIN UBAIDULLAH
13.Na fansheka da iyayena SA,AD BIN ABI WAQQAS
14.Haqiqa ALLAH YA riqeni khalilinsa kamar yadda ya riqi Ibrahim khalil, gidana da na Ibrahin suna kallon juna a aljanna, ABBAS kuma ya na tsakaninmu, mumini atsakanin badadayai kenan
15.Maraba da tsarkakakke kuma abun tsarkakewa AMMAR BIN YASIR
16 ALLAH YA umarceni da inso mutum hudu kuma shi ma ya na sansu:ALI, DA ABU ZARRIN ALGIFARIYY, DA SALMANUL FARISIY, DA MIQDAD
17.Qasa ba ta taba daukar mutumin da, haka kuma sama bata taba rufe mutumin da yafi kowa gaskiyar magana kamar ABU ZARRIN ALGIFARIYY BA
18.Mayafinsa na gidan aljanna ya fi mayafin alhariri, haka kuma al,arshi yayi girgiza sabo da rasuwar SA,AD DAN MU,AZ
19.Ya ALLAH KA tabbatar da shi kuma ka sanya shi shiryayye mai shiryarwa: JARIR DAN ABDULLAH ALBAJALIY
20.Ya ALLAH KA sanar da shi hikima da fassarar Qur,ani ABDULLAHI DAN ABBAS
21.Wanda ya so MUTANEN MADINA Allah zai so shi wanda kuma ya qisu shima Allah zai qishi
22.Zababbun cikinmu kenan: WADANDA SU KA JE YAKIN BADAR
***************
( DUK WADANNAN BAYANAN
DUBA LITTAFIN IBN MAJA BABUN FI FADHA,ILI AS,HABI RASULULLAHI (SAW))
23. Ya BILAL bani labari da mafi fatanka a ayyukan da ka aikata a musulunci dan haqiqa ni na ji sautin takalminka a gabana a gidan aljannna,,,,,,,
*****(Bukhari 3679)******
24. Abubakr dan aljannane,
Umar dan aljannane,
Usman dan aljannane,
Ali dan aljannane,
Dalha dan aljannane,
Zubair dan aljannane,
Abdur-Rahman Bin Auf dan aljannane,
Sa,ad bin Abi waqqas dan aljannane,
Sa,id bin Zaid dan aljannane,
Abu Ubaidah bin Jarrah dan aljannane,
*******(Duba Tirmiziy 3748)****
25. Kada ku zagi sahabbaina wallahi da ace dayanku zai ciyar da misalin dutsen uhudu na zinare to da bazai kai mudun dayansuba, kai ba ma zai kai rabin nasuba (awajan girman lada)
*****(Bukhari da Muslim) ******
Muna rokon ALLAH wadannan sahabbai dama wadanda bamu ambataba ALLAH YA qara musu yarda,,,,,,,,,,
uwanka sugani sukaru wace hasara kayi?
ALLAH YASA muyi kyakkyawan karshe!
AMEEN
•
•
•
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Wabarakatuhu.
•
Ina Fatan Wannan Sakon zai isa gareki a duk
inda kike.
Yake 'Yar Uwa ta, Kada Ki yarda baqin ciki ko
tashin hankalin rayuwa su dagula miki
tunanin ki ko tsarin rayuwar ki.
•
Kada ki yarda Talauci ko rashin samun
abinda kike fatan samu yasa Imanin ki yayi
rauni.
•
Kada ganin Qawayen ki, ko Sa'o'in ki suna
saka kayan da ke bakya sakawa, ko suna
shafa man da ke bakya Shafawa, ko suna
Fesa turaren da ke bakya Fesa irin sa ko
kuma suna wani abu makamancin hakan
wanda ke ba kya yi yasa ki manta da irin
tarin baiwa da Ni'imar da Allaah Subhanahu
Wata'ala Yayi miki har kisa kanki a cikin
Damuwa.
•
Kada ki ga wata wai don tana da Farar Fata,
dogon gashi ko hanci, dogayen kafafu ko
kuma kayan dirin jiki hakan yasa ki dinga jin
kunya ko nauyin fita ko yin mu'amala a yayin
da kuke tare, kuma kada wadannan
abubuwan su ja hankalin ki har akai
matsayin da zaki dinga mata biyayya fiye da
qima.
•
KI sani cewa kema Kyakkyawa ce, kuma
kema abar so ce ga wasu (In ma ba ga
kowa ba), kuma kema mace ce don haka
kada wani abu na rayuwa yasa ki manta da
wannan.
•
Babu Mamaki idan na ce miki kema
Kyaykkyawa ce ki qi Amincewa da hakan,
amma ina so ki sani cewa; Kowane Mutum
yana da masoya, haka ma Makiya, kada ki
taba tunanin baki da Masoyi kuma kada ki
taba tunanin cewa ke Mummuna ce sannan
kuma kada ki taba tunanin baki da makiya.
Sannan ina so ki sani cewa "Kowane Mutun
Kyakkyawa Ne a idon Masoyan sa, Kuma
kowane Mutum Mummuna ne a idon
Makiyan sa." Lallai Kema Kyakkyawa ce
Domin Allaah baya taba halittar Mummunar
Halitta, Lallai Allaah Yana Da DALILIN SA na
Halittar ki a yadda kike, Matukar ba kin Raina
irin Ni'imar Da YA Yi miki bane, to Ki karbi
kanki a bisa irin matsayin da kika tsinci
kanki a ciki kuma ki nemi Dacewar sa. Lallai
SHI mai Amsa ADDU'AR bayinSa ne.
Amma fa lallai ne sai kinyi hakuri, kuma sai
kin jure. Lallai Allaah Yana Tare da masu
Hakuri.
•
¶ Dafatan zaki amfana da dan abunda na
rubuta ¶
*MAHAIFA SUNA SAMUN GAFARA TA HANYAR ADDUAR 'YA'YANSU ACIKIN QABARINSU.*
Yana daga cikin hakkin mahaifan mu akan mu, yawaita yi masu addua da nema masu gafara a wajan Allah, har ma wadan su malamai suna ganin Allah baya amsar adduar bawa har sai idan yana yi ma mahaifansa addua.
Daga Abi Hurairata رضي الله عنه yana cewa:
"Manzon Allah ﷺ yace:"
*(Lallai Allah yana daukaka matsayi da daraajar mutum a gidan Aljanna, Sai mutumin yayi tambaya,yace: "Ya Allah wannan karin matsayin daga ina??" Sai ace dashi,dalilin neman gafarar da 'ya yanka suke makane)*
@صححه الألباني-صحيح الجامع الصغير- (1617).
Awani Hadisin Manzon Allah ﷺ yace:
*(Idan dan Adam ya mutu, dukkan aiyukansa ladansu ya kare inbanda aiyuka guda ukku,Sadaka mai gudana,ilimin da ka koyar ake amfanuwa dashi,da kuma 'Da na kwarai wanda zai riqa yi maka addua)*
@الألباني-صحيح الجامع الصغير
Yana cikin alamar mutum shi mutumin kirkine idan yana yawaita yin addua ga mahaifansa kamar yadda hadisi ya tabbatar.
شيخ الإسلام ابن تيمية-رحمه الله-:
Yana cewa:
*"Bawa na kwarai bazai gushe ba yana nemawa mahaifansa gafara ba,har sai Allah yayi masu gafara, sannan Allah ya daukaka matsayinsu a cikin Aljanna"*
@شرح الوصية الصغرى(صـ131).
Yan uwa dan Allah mu yawaita addua ga mahaifan mu tare da nema masu gafara.
Wannan shine wasiyata agaremu baki daya.
*اللهم_إغفر_لنا_ولوالدينا_وللمسلمين والمسلمات_الأحياء_منهم والأموات🌺أمين*
🌺Namiji sinadarin rayuwar mace. Tauraro, mai qawata rayuwar mace. Namiji zuma, a ido kyawun kallo, a baki daďi mai daďaďawa. Namiji zaki, ga isa ga qasaita. Taka a hankali ďawisu, da kwalliyar ka aka halicce ka. Lu'u lu'u ne, abun son ko wacce mace. Katangar zinare, majinginin mace. Tsarin jikinka da hankalinka na shugaba, mai shugabantar masu rauni. Takawanka ďai-ďai yarima, girman ka ne, Allah Ya baka. Wa ya isa amsa? Balle har ya kwace? Na mu biyayya, don dole ce biyayyar.
🌺Ko wane saurayi matashi ya kamata ya tsoraci Allah a lokacin samartan sa, ya zama mutumin kirki na gari. Kuma ya tsare kansa daga gur'bata zuri'ar sa da wasu manyan zunubai. Ya san da cewa an haliccesa da shugabanci, sai ya ďauki hanyar zama shugaba na gari. Ana so ya zama mai mutuqar tunani da hankalin rayuwa. Mai nemo hanyoyin da zai bi na ganin ya zame wa matarsa ta duniya miji na gari, uba na gari kuma ga 'ya'yansa.
🌺Ka da kullum ka ce burin ka samun ta gari, kai kana son gangariya wacce ta haďa komai, ta iya komai, lafiyayyar budurwa. Wacce ta tsare kanta daga dukkan maza, take kokarin kiyaye dokokin Mahaliccin ta. Amma kai in aka ďauke ka da halin ka, aka sanya ka a makiroskof din rayuwa. Aka zankade ka, aka caje ka da kyau. Za a ga baka yi ko qanqanin cancanta da samun irin wannan macen ba.
🌺Ashe kenan kana ta cefanen rayuwa ne, amma ka manta da wani sinadari mafi muhimmanci. Dan'uwana mai albarka, ka cire son zuciya ka ajiye gefe. Ka cire rudin rayuwa ka yar da shi, ka ďebe karatuttukan da ka koyo, ko ka gani a wurin wasu. Waďanda basu dace da koyarwan musulunci ba. Ka riqi gaskiya, ka rungumi dai-dai, ka yi ďammara, ka kuma zage damtse. Ka binciko irin zamantakewar gidan Annabi (SAW), da koyo kissan zama miji na gari. Ka yi dubi cikin rayuwar magabata, ka karanta littafan su. Ka san menene rayuwar aure, da yanda ake yi a ji daďin sa. Ka karkaďe kanka, ka shirya fuskantar wata rayuwa mai cike da albarka, ni'imomi tare da jarabawowi. Kada ka shiga
ALBISHIRINKA MAI TASHI CIKIN DARE YANA ROKON ALLAH.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Babu wani bawa daga cikin bayin Allah,da zai kwanta da tsarki[ alwala]
Sannan ya tashi cikin dare, kuma ya roki Allah wani abu daga cikin
al'amuran duniya ko na lahira,face Allah ya biya masa buqatarsa.).
#SAHEEHU IBN MAJAH, KUMA ALBANY YA INGANTASHI.
FADAKARWA
Wannan Hadisi yana bayyanama abubuwa kamar haka;
~Muhimmancin kwanciya da alwala,kamar yadda ya tabbata acikin hadisi Annabi s.a.w ya umarci daya daga cikin sahabbansa idan yaje kwanciya barci yayi alwala irinta sallah.......
~Allah yana amsa adduar bayinsa acikin dare,kamar yadda Annabi s.a.w ya kara tabbatar da haaka awani hadisin.
Allah kabamu ikon kiyaye wannan ibada mai tsada acikin dare.
SADA
ZUMUNTA
3- Sada zumunta yana kara arziki, Bukari 5986
4- Sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7
5- Sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah, Bukari 5983
6- Sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.
7- Sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902
8- Sada zumunta wasiyyar da Annabi (SAW) yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669
9- Sada zumunta siffar muminai ce.
10 Sada zumunta yana sawa a karbi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674
11- Sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.
12- Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya dinka sada zumunta,. Bukari da Muslum.
13- Sada zumunta yana kare mutum daga la'antar Allah. Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25.
14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu, na Sadaka dana zumunta. Sahihu, Sunanil Tirmiziy. 1/202 .
15, Sada zumunta yana kara soyayya tsananin dangi da yan'uwa .
16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsananin yan'uwa.
17- Wanda baya sada zumunta bazai shiga Aljannah ba.
18- Allah taala ya yiwa mahaifa alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita, zai yankewa wanda ya yanketa.
19- Mai sada zumunta shine wanda ko ba'a zo masa ba, shi zai je.
20, Baya cikin sada zumunta sai wanda yazo maka kawai zaka je masa.
Allah Ya bamu ikon sauke wannan nauyi na sadar da Zumunta. Amin
Assalamu Alaikum
*YAHYA* *BIN* *UKSUM*
Yace Mai Gulma Yafi Mai Sihiri Sharri
*HASANUL* *BASARY*
Yace Duk Wanda Yakawo Maka Zancen Wani To Zai Kai Zancen Ka Wajen
Wani.
*SA'ID* *BIN* *ABI* *RUBAH*
Yace Angayama Cewa Azabar Kabari Kashi Uku Ce ?
1 Saboda Giba
2 Saboda Rashin Kiyaye Fitsari
3 Saboda Annamimanci.
.
*MUJAHID* *DAGA* *IBN* *ABBAS*
Yace Idan Kayi Nufin Ka Ambaci Aibun Abokinka To Ka Fara Ambaton Aibun Kanka.
.
*HAFS* *IBN* *USMAN*
Yace Umar Dan Khattab Yace:
Kada Ku Shagaltar Da Kanku Wajen Ambaton Aibun Mutane Domin
Yin Hakan Musiba Ce Ku Rika Ambaton Allah Domin Yin Hakan Rahama Ce.
.
*QAIS* *IBN* *HAZIM*
Yace Amr Ibn
Ass Ya Wuce Ta Gaban Wani
Mushen Alfadari Sai Yacewa
Abokansa: Wallahi Dayanku Ya Cika Cikinsa Da Naman Wannan Mushen Yafi Masa Alheri Akan Yaci Naman Wani Musulmi.
.
*AUN* *IBN* *ABDULLAHI*
Yace Ban Taba Son Mutumin Daya Bata
Lokacinsa Akan Binciken Aibun Mutane Ba Domin Bai Yi Haka Ba Sai Don Rafkana Da Take Cikin
Zuciyarsa Wadda Ta Hana Shi Shagaltuwa Da Aibun Kansa.
.
*BAKAR* *IBN* *ABDULLAHI*
Yace Idan Kuka Ga Mutum Ya Shagaltar Da Kansa Da Ambaton Aibun Mutane Alhali Ya Manta Da Nasa
Aibun To Lallai Ku Sani Cewa Anyi Masa Mummunan A
Lahira.
.
*AHNAF* *IBN* *QAIS*
Yace Ban
Taba Ambaton Aibun Wani Mutum Ba Bayan Ya Tashi Daga Wajena
```IDAN ZAMUYI FURUCI ALLAH YASA MU FADI ALKHAIRI
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
SIFFAR BACCIN MANZON ALLAH S.A.W
SIFFAR BARCIN MANZAN ALLAH SALLALLAHU WASALLALAM
Ya kasance yana Barci a Farkon dare, ya raya karshensa – wato yanayin Sallah a cikinsa kenan- Bukhari da Muslim.
Ø Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Kasance idan ya hau kan shinfidarsa zeyi Barci yana cewa : “ Bismikallahumma Amutu Wa’ahyaa” (Ma’ana Da sunanka Ubangiji, nake Mutuwa kuma nake Rayuwa. Mutuwa = Yin barci , Rayuwa = Farkawa daga barci) kuma idan ya farka daga barci yana cewa “ Alhamdu lil lahil ladhi Ahyaana ba’ada ma Amaatana Wa ilaihin nushur” ( Ma’ana Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya Rayamu bayan ya kashe mu, kuma gareshi tashi yake) Muslim.
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*SIFFOFIN MIJI NAGARI*
_*1.shine wanda yakeson matarsa bayan aurensu fiyeda yadda yake sonta a layi.*
_*2.Shine mai kishin* _*matarsa. Domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "duk* _*wanda baya kishin matarsa bazai shigaaljannah ba".*
*3.Shine wanda ya dauki aure a matsayin*_ _*Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba.*
_*4.Shine wanda ya* _*dauki matarsa a matsayin abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar shawararsa.*
*5.Shine wanda baya zagin*_ _*matarsa, baya cin mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha'intarta koda a bayan idon tane*
*6.Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin*_ *amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Shine wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake,"*_
_*hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta'ala.*
*7.Shine*_ *wanda idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu*_ *yaudara ko karya acikin zancensa. Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa:*_ *Iyayen matarsa, Iyayensa ne. 'Yan uwanta ma 'yan uwansa ne*_. _*Danginta ma danginsa ne Shine wanda yake daukar cewa farin cikin* _*matarsa shine farincikinsa. Kuma matsalar ta, itama tasa ce. Shine yake kokarin kiyaye sirrin* _*matarsa, kuma yake kokarin Kare mata mutuncinta koda a wajen 'yan uwansa ne, tare da hikima da fahimtarwa.*
_*8.Shine wanda baya fifita matarsa akan 'yan uwansa, kuma baya tauye mata darajarta.* _*Yana bawa kowanne gefe nasa hakkin kamar yadda shari'ah ta tanadar.*
*9.Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da*_
*hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.*_
_*10.Shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa* *akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara ba.*
*11.Shine wanda yake zaune da matarsa komai dadi komai*_ _*wuya ba zai dena*_ _*nuna mata soyayya ba wai*
*don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara*_
_*raguwa.*
_*12.Shine wanda*_ _*yake bawa matarsa yabo a duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin*_*dadinshi. Miji nagari baya raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko*_ _*gishiri yayi yawa. Sai dai yace: "uwargida abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi a ciki"*
_*Allah Yasa mazaje su gane,su sauke hakkinsu na kulawa,su daina yin* _*dare a layi, *kowurin mai shayi
Hakika Fitan rai yana da wani irin radadi
wanda babu mai saninsa sai dai Mamaci..
Mamaci yayin da ransa ya kusan fita,
Muryarsa takan karye, Qarfin jikinsa yakan
tafi.. Babu damar Eehu ko kururuwar zafin
da yake ji. Domin zafin mutuwa ya riga ya
ratsa dukkan sassan jikinsa..
Ba zai samu damar neman taimako ba,
ballantana adauke masa zafin radadin da
yake ji. Sai yayi fatan wannan nishin da
yakeyi ko zai zama dalilun samun
rangwame, amma inaa!!.
Idan har akwai ragowar wani Qarfi gareshi
shine za'a rika jin wani irin gurnani yana
fitowa daga chan cikin Qirjinsa da
Makogoronsa yayin da rai yazo fita.. Alhali
launin fuskarsa ya chanza saboda tsananin
halin da yake ciki.
Yayin da ranka yazo Makogoro, awannan
lokacin zaka manta da Makusantanka,
iyalanka ko 'Ya'yanka, balle Makobta.
Awannan lokacin ne 'Dan Adam yakan ji
wata irin Qishirwa mai tsanani wacce sai ya
gwammaci inama ya bayar da dukkan
abinda ya mallaka domin a bashi ruwan da
zai kurba koda kurbi guda ne!!.
A wannan lokacin duniya da dukkan abin
cikinta zasu zamanto ba komai ba...
Ballantana dukiya ko Mulki ko wani gata...
'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai
bane.. Kuma tun daga sannan zai fara
nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi
wajen sa'bon Allah!!
Tunda Shugaban Halitta (sallal Lahu alaihi wa
aalihi wa sallam) ya 'dan'dana zafin mutuwa,
Ka sani cewa kaima sai ka 'dan'dana!!
Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana
A'isha (rta) tana bayar da labarin jinyar da
Manzon Allah (saww) yayi adakinta, har
zuwa rasuwarsa. Tace :
"Hakika Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa
aalihi wa sallam) ya kasance a gabansa
akwai wata guga wacce akwai ruwa
acikinta, yana shigar da hannayensa acikin
ruwan sannan ya shafe fuskarsa dasu. Yana
cewa :
"LA ILAHA ILLAL LAAH!! HAKIKA MUTUWA
TANA DA RADADI!".
Sannan ya chira hannunsa sama yana cewa :
"ACIKIN TAWAGA MADAUKAKIYA!''.
an bashi za'bi ne tsakanin ci gaba da zaman
duniya, ko kuma komawa zuwa ga
Ubangijinsa).
Yana fa'dar haka har sai da aka karbi ransa
Yin Dha'a ko biyayya ko kyautatama mahaifa yana cikin mafi girman aikin alkhairi awajan Allah.
Bayan imani da Allah da Manzonsa da kadaita Allah acikin Ibada da kadaita Annabi s.a.w wajan koyin ibada,babu wani Hakki mai girma akan bawa wanda ya kai kyautatama mahaifa da yin Dha'a garesu.
Allah Ta'ala a gurare da dama acikin Alqurani mai girma yana kawo hakkin kyautatawa mahaifa a bayan kadaita shi da ibada.
Allah yana cewa:
{وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا * وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا}
Ma'ana:
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.
Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."
@ [الإسراء: 23 – 24]
Awani wajan Allah yayi umarni a godemasa sannan agodewa Mahaifa,sai Allah yace:
( وَوَصَّيْنَا الْإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَىٰ وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ )
Ma'ana:
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take."
@ لقمان (14)
●Wani daga cikin malamai magabata yana cewa:
"Godewa Allah shine bauta masa shikadai batare da hadashi da komaiba acikin bauta, godewa mahaifa kuwa shine,yin dha'a agaresu da kyautata masu da yi masu biyayya da yi masu addua Allah ne mafi sani".
WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH
(S.A.W).
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi amfani da su, ko ya sanar
da wanda zai yi amfani da su"
Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni zan karba ya Ma'aikin
Allah (S.A.W)
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike hannu na yace min:-
1. Ka guji aikata sabo, zaka zamo wanda yafi kowa bauta a cikin mutane.
2. Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zaka fi kowa
arziki cikin mutane.
3. Ka kyautata wa makobcin ka, zaka zamo (cikakken) Mumini.
4. Ka so wa mutane abinda kake so wa kanka, zaka kasance (cikakken) Musulmi.
5. Kada ka yawaita dariya, domin yawan Dariya na
kashe zuciya.
MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA RIKE SU KO KA SANAR DA WANDA ZAI YI AMFANI
DA SU.
IDAN KA TURA WA YAN UWA MUSULMAI BAKA SAN WA ZAI YI
AMFANI DA SU BA, KAGA KA SAMU LADAN
MUTANE MASU TARIN
YAWA.
Allah bamu iKon kiyayewa.
HAKKINA DAKE KANKU IDAN KUKA TAUYEMIN SHI TABBAS ALLAH BAZAI BARKUBA.
Tunatar dani azabar allah wacce yayi tattali domin azabtar da masu sa'ba masa. 😭
Tunatar dani radadin mutuwa wanda har mala'ikan mutuwar bai tsallakeshi ba.😭
Tunatar dani tambayoyin cikin kabari wadanda amsarsu sai wanda allah yaso da rahama😭
Tunatar dani tsayuwa afilin alkiyama wanda acikin zafin rana tare da qishirruwa alokacin da babu ruwan akusa.😭
Tunatar dani tsayuwa agaban ubangijina ayayin hisabi wanda tabbas ranar tananan zuwa. 😭
Tunatar dani da alkawarin da allah yayima wutar jahannama cewa sai yacikata da mutane masu laifi😭
******* ******** *******
******* ******** *******
******* ******** *******
Ku tunatar dani yawaita tuba tunda dai allah dakansa yace yanason mutum mai yawan tuba😌
Ku tunatar dani yawan karatun Qur'an domin annabi yace tabbas qur'an zai ceci masu karantashi aduniya😌
Ku tunatar dani sadar da zumunchi tunda har allah yace wanda ya sadar da zumunchi nikuma zan sadar dashi da rahamata😌
Ku tunatar dani biyayya ga iyayena tunda allah ne yace biyayya agaresu hanyar shiga aljanna ce😌
Ku tunatar dani tsayar da sallah akan lokaci tunda annabi yace sallah tana taya mutum kwanciyar kabari😌
Ku tunatar dani yawan sadaka tunda annabi yace duk wanda yayita allah ne zai biyasa aranar lahira😌
Mu zamo masu tunatar da juna tare dayin nasiha ga junanmu. Domin hakan shine zaisa mugudu tare kuma mutsira tare.🤝🏼🤝🏼🤝🏼 pls turawa 'yan uwanka da ahalinka domin sauke hakkinsu dake kanka
MUTUWA DOLE
😭😭 Yayin da ranka yazo Makogoro, awannan lokacin zaka manta da Makusantanka, iyalanka ko 'Ya'yanka, balle Makobta. Awannan lokacin ne 'Dan Adam yakan ji wata irin Qishirwa mai tsanani wacce sai ya gwammaci inama ya bayar da dukkan abinda ya mallaka domin a bashi ruwan da zai kurba koda kurbi guda ne!!.😭
ZAFIN DA BAWA YAKEJI YAYIN FITAR RAI 😭😭😭
Hakika Fitan rai yana da wani irin radadi wanda babu mai saninsa sai dai Mamaci..
Mamaci yayin da ransa ya kusan fita, Muryarsa takan karye, Qarfin jikinsa yakan tafi.. Babu damar Eehu ko kururuwar zafin da yake ji. Domin zafin mutuwa ya riga ya ratsa dukkan sassan jikinsa..😭
"Ba zai samu damar neman taimako ba, ballantana adauke masa zafin radadin da yake ji. Sai yayi fatan wannan nishin da yakeyi ko zai zama dalilun samun rangwame, amma inaa!!.😭
😭😭Idan har akwai ragowar wani Qarfi gareshi shine za'a rika jin wani irin gurnani yana fitowa daga chan cikin Qirjinsa da Makogoronsa yayin da rai yazo fita.. Alhali launin fuskarsa ya chanza saboda tsananin halin da yake ciki
😭
😭😭A wannan lokacin duniya da dukkan abin cikinta zasu zamanto ba komai ba... Ballantana dukiya ko Mulki ko wani gata... 'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane.. Kuma tun daga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi wajen sa'bon Allah😭😭
Zan mutu
Zaka mutu
Zaki mutu
Wlh wata rana za a wayi gari babu mu
Wannan duniyar da muke nema
Wannan duniyar da muke yiwa ado
Wannan duniyar da muke taqama da ita
Wlh ba matabbata ba ce
Wata rana zamu tattaru a gaban mahaliccin mu domin auna ayyukan mu.. Allah ka gafarta mana ba Dan halin mu ba
👇
Annabi SAW ya kasan ce yana zagayawa a cikin kashi daya na farkon dare (11-30pm) yana cewa: "Ga mutuwa nan tazo da bala'in dake bayan ta" Turmuzi ya rowaito. Kadan daga cikin bala'in bayan mutuwa sun hada da👉
👇
Kwanciya a cikin wani ziririn rami(KABARI) wanda mutum ko juyawa ba ya iya yi😭
👇
Zaman BARZAHU, Mutum bai san rana/lokaci da zai fita daga wannan yanayi ba😭
👇
Bayan wannan zaman,Za'a tashi a firgice, kowa zai dauki kayan laifin sa a kan shi kuma wallahi komin nauyin su sai ya dauka😭
👇
Masu korar mutane za suyi kora... za'a fara
Gudun fanfalaki😭
👇
Wani zufa ta rufe shi kamar wanda ya shiga swimming pool, a haka zai ta gudu baya gani😭
👇
Wani cikin shi yayi kato kamar yana dauke da 'yan adam duka, a haka zai ta gudu😭
👇
Wani zai tashi da jikin shi, half na jikin ya shanye a haka zai ta gudu😭
👇
A haka dai mutane zasu yi ta gudu cikin nau'uka daban-daban na wahala da azaba sakamakon zunubai😭
👇
Ana cikin wannan gudu sai haske ya dauke gaba daya. Ga firgici ga wahala, Masu kora kuma suna ci gaba da kora har dai a iso wani katon rami wanda karka shin sa wutan JAHANNAMA ce😭
👇
TSALLAKE SIRADI...
Ana nan cikin wannan tashin hankali, an tsaya cak sai ace a fara tsallakawa ga tsananin duhu😭
👇
Wasu da sun taka siradin zasu fada😭
👇
Wasu suna tsallakawa ana yago naman su😭
👇
Wasu su wuce da sauran jikin su da ya rage😭
👇
Wasu kuma jikin ya kare. Ya Allah kayi mana tsari da shiga wannan hali😭
👇
Allahu Akhbar! Wasu gabobin su da suke Alwala zasu haska masu hanya su wuce kamar keftawar Ido cikin jin dadi da nishadi.😊
👇
Wasu kuma duk hakan bazata faru gare su ba domin zababbun Allah ne, suna can karkashin inuwar Allah SWT,wato Al-Arshe👍😊
Ya Allah kasa mu cikin su.
👇
Bayan an gama wannan sai a kora mutane zuwa wani fili, a nan za'a tsaya cak kowa ba kaya a jikin sa, ba Uhm ba...😭
👇
Yinin wannan rana ya kai shekara 70 idan aka kwatanta shi da na duniya😭
👇
Rana a wannan yini.
Darasi na Daya-1
*Falalar Ra'atanul Fajir*
Hakika An ruwaito Hadisai Masu yawa da suke bayyan falalar,yin Sallar raka'a biyu bayan alfijir ya fito,daga bakin Annabi SAW ga kadan daga ciki:
1-Annabi SAW yafi san Raka'a biyu bayan fitowar alfijir,fiye da duniya gaba daya.
Aisha R.A ta ruwaito
@Muslim,Ahmad da Tirmizy.
2-Annabi SAW yana cewa:
"Kada kubar raka'a biyu bayan fitowar alfijir,ko da kuna tsammanin. Abokan gabanku".
Abi Hurairata R.A ya ruwaito shi.
@Ahmad da Abu Dauda
3-Babu wata Nafila da Manzon Allah SAW yake tsananin kiyayewa ba kamar yin. Raka'a biyu bayan alfijir Aisha R.A ta ruwaito
@Bukhari da Muslim da Ahmad da Abu Dauda
4-Annabi SAW yana cewa:Raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir,sunfi duniya da abinda yake cikinnta,alkhai ri.
Aisha R.A ta riwaito
@Muslim da Ahmad.
5-Daga Aisha R.A tana cewa: Banga wani aikin Alkhairi wanda Annabi SAW yake gaggawar aikatawaba,kamar yin. Raka'a biyu bayan fitowar alfijir.
@Muslim.
*ANA TAKAITA SU*
yana cikin Sunnar Annabi SAW game da dayin Nafilar fitowar alfijir,yana takaita karatu,amma yana cikasa Ruku'u da Sujada:
1-Daga Hafsa R.A tana cewa:Annnabi SAW ya kasance yanayin Sallah raka'a guda biyu kafin Sallar Assuba a dakinta kuma yana takaitasu Matuka.
@Bukhari da Muslim.
2-Daga Aisha R.A tana cewa:Manzon Allah SAW yana Sallamar raka'a biyu kafin Sallar safiya(tana nufin kafin Sallar Assuba) a dakinta,yana saukakasu har nakanyi tsammanin ya karanta Fatiha ma ko bai karantataba?
@Ahmad da Waninsa.
3-Daga gareta Aisha R.A tana cewa:tsawon tsayuwar Sallar Annabi. SAW na. raka'a biyu bayan fitowar alfijir, kamar tsawon karanta Suratul Fatiha ne.
@Malik da Ahmad
Wadannan Hadisai da ira-iransu suna nuna mana mustahabbanci gaggautawa da saukaka wadannan raka'o'i tare da cika sauran rukunnan sallah kamar ruku'u da Sujada
*WADANSU SURORINE ANNABI S.A.W YAKE KARANTAWA???*
Annabi SAW ya sannan ta mana karanta wadannan surori a wannan Nafila
MATAR SHEDAN
SHEDAN YANA DA WATA MATA GURGUWA:
Wata rana zai wuce sai yace mata ta matsa Don bata da wani amfani, sai tai dariya Tace: "Na fi ka illah don nice nake zuwa a karshen fitsari, idan mutum yana fitsari INA rike kadan daga ciki, da ya mi'ke sai in sakar masa, ya mike ba tare da ya wanke ba!"
Sai Shedan ya bushe da dariya yace "Kin ga kuwa duk Wanda bai da tsarki baida alwala, duk kuma Wanda bai da alwala bai da sallah!" Yace lallai kuwa kin cika sheidaniya!".
MAFITA:
Ya Muslim Ummah, a duk lokacin da muke fitsari bayan mun gama mu jira kadan muyi nishi, zamu ji wani fitsari kadan mai 'dumi ya biyo baya.... WANNAN shine fitsarin da Matar Shaidan take ri'kewa don ta 6ata mana ibadanmu!!
LA'ILAHA ILLALLAH, MUHAMMADUR RASULULLAH (SAW.W)
Don Allah in ka karanta ka aikawa wasu don suma Su amfana, mu kuma samu tsari gabadaya daga azabar Qabari.
Allah Ya tsare mu Ameeen.
WANDA YAKE SO KADA LADARSA TA TSAYA BAYAN MUTUWARSA TO YA KOYAR DA ILIMI KO YA YADA ILIMI
Hakika Annabi SAW ya kwadaita akan yada ilimi awaje da dama acikin Hadisan sa.
1-(Idan Dan Adam ya rasu dukkan aiyukansa sun tsaya,amma banda abubuwa guda ukku
-Sadaka mai gudana
-ilimin da ka karantar dashi
-Ko yaro na gari da zaiyi masa addua).
@Saheehul Jami'a.
Kuma ya kwadaita da isar da sakonsa da isar wa wanda baijiba abinda ya tabbata daga Annabi SAW
2-Annabi s.a.w yana cewa:
(....Ku isar da sakona ko da aya guda ce...).
@Saheehul Jami'i
3-Kuma mafi yawan lokutan Khudubar Annabi SAW yana fadar
(Wanda yake nan kuma yaji sai ya isar ga wanda baijiba...).
@ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( 230/6 )
Ibn Mubarak Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Ban san wani abu bayan Annabci mafi Falala da Matsayi da Daraja ga mutum ba,kamar Yada Ilimi"".
@ﺗﻬﺬﻳﺐ ﺍﻟﻜﻤﺎﻝ ( ٢٠ /١٦ ).
Ibn Qayyim Allah yayi masa Rahama yace:
"Yin kyauta da alkhairin yada ilimi shine mafi darajar matakin kyauta, kyàuta da yada Ilimi yafi alkhairi akan kyauta da yada dukiya,domin ilimi yafi dukiya daukaka).
@ﻣﺪﺍﺭﺝ ﺍﻟﺴﺎﻟﻜﻴﻦ ( ٢٨١ /٢ ).
Ibnul Jauzy Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Dukkan wanda yake son iliminsa ya amfane shi bayan mutuwarsa,to ya yada Ilimi da karantar dashi".
@ﺍﻟﺘﺬﻛﺮﺓ ( ٥٥ ).
Allama Abdurrahman Bn Ãli shiek Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Ka yi kokari wajan ýada ilimin Tauheedi,da Dalilai kebantattu da na gamammu,domin mafi yawan mutane sunyi asarar wannan ilimi".
@ﺍﻟﻤﻄﻠﺐ ﺍﻟﺤﻤﻴﺪ ( ٢٧٣ ).
Ibn Baz Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Wajibine mutum ya yi kokarin yada Ilimi da dukkan ikonSA da karfinSA......."
@ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( ٦٧/٦ ).
Imam Al'auzã'i Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Idan ma'abuta bidia suka bayyana bidiarsu, kuma kira zuwa ga bidia ya yawaita da amsama kiransu ga al'umma,to a wannan lokacin Yada ingantaccen Ilimi shi yake raya al'umma,kuma yin hakan isar da sakon Annabi s.a.w ne,kuma ràhamace da zata amfani dukkan al'umma".
@ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺪﻉ - ﻹﺑﻦ ﻭﺿّﺎﺡ ( 524 )
Ibn Usaimeen Allah yayi masa rahama.
SAYYADINA ALIYU (R.T.A) YANA CEWA:
.
ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺯﺍﺩ ﻓﺎﺍﻟﺘﻔﻮﻯ ﺗﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda ke son guzuri, to tsoron Allah ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﻋﺰﺍ ﻓﺎﻹﺳﻼﻡ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda ke son izza, to Muslunci ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﻋﺪﻻ ﻓﺤﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda ke son adalci, to hukuncin Allah ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺟﻠﻴﺴﺎ ﻓﺎﻟﻘﺮﺀﺍﻥ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Wanda yake son abokin zama, to Alkur'ani ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺯﻳﻨﺔ ﻓﺎﻟﻌﻠﻢ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son ado, to ilimi ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﻭﺍﻋﻈﺎ ﻓﺎﻟﻤﻮﺕ ﺗﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son wa'azi to mutuwa ta ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺃﻧﻴﺴﺎ ﻓﺬﻛﺮﺍﻟﻠﻪ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son debe kewa, to zikirin Allah ya ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﻏﻨﻰ ﻓﺎﺍﻟﻘﻨﺎﻋﺔ ﺗﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son wadata, to wadatar zuci ta ishe shi.
.
ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺟﻤﺎﻻ ﻓﺎﻷﺧﻼﻕ ﻳﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son kyau, to kyawawan dabi'u sun ishe
shi.
.
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺭﺍﺧﺔ ﻓﺎﻵﺧﺮﺓ ﺗﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda yake son hutu, to lahira ta ishe shi.
.
ﻭﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﻜﻔﻪ ﻛﻞ ﻫﺬﺍ ﻓﺎﻟﻨﺎﺭ ﺗﻜﻔﻴﻪ
Duk wanda wadannan Abubuwan basu ishe shi ba, to wuta
zata ishe shi.
.
Ya Allah ka bamu ikon kiyayewa Albarkal ANNABI S.A.W
Allah kabamu lafia da zama lafia k karemu sharrin masu sharri

Manzon Allah (saw) yanacewa mutanen dake kusa dani a ranar tashin Alkiyama sune masu yawan yi min salati! Allahumma salli Ala Muhd wa sallim! Ya Allah muna rokonka da sunayenka tsarkaka, don darajar Al'arshi, don girman mulkinka Allah, don soyayyar ka da Annabi Muhammadu (saw) duk wanda ya tura wannan sakon ga yan uwa musulmi koda mutum 5 ne ya Allah kaji kansa, ka gafar ta masa, ka daukakashi duniya da lahira, ka kareshi daga makiya, ka hadashi da manzon Allah (saw) ranar alkiyama sannan ka sakashi Aljanna Firdausi Ameen!
*(DUNIYA MAKARANTACE)*
_*👉 Kada ka tambayi maraya ina mahaifinka? Kada ka ce ma bazawara me ya kashe aurenki? Idan zaka taimaki talaka kada ka ce masa, ko kana da bukata? Wadannan tambayoyi ba su dace da halin mutanen kirki ba.*
*_👉 Duniya makaranta ce. Mutane su ne dalibanta. Rayuwa ita ce dakin karatu, lokaci shi ne babban malami a cikin ta. Muna haduwa a matsayin baki, sai kuma mu watse da dai daya.*
*_👉 Kada ka ce mutane ba su nema na sai idan suna da bukata. Fitila sai an shiga cikin duhu ake neman ta.*
*_👉 Duniya a tsakanin baka biyu take ( ). Baka ta farko ita ce haifuwa, ta biyu ita ce mutuwa. A tsakanin su kake rayuwa. Idan ka wuce sai a nade aikinka a aika maka shi ya zama abokin jin dadinka ko shan wahalarka*.
*_👉 Ruwan zafin da yake dafa kwai ya yi kwari shi yake dafa dankali ya yi laushi. Ba ruwan zafin ba ne, dabi'ar kowanensu ce. Haka mutane suke. Wani yau da gobe ke sa ya yi laushi, wani kuma sai ta sa shi ya sandare.*
*_👉 Duk wanda ya ji tsoro zai samu damuwa a zuciyarsa. Amma ban da wanda ya ji tsoron Allah. Shi kam wanda ya ji tsoron sa zai samu aminci da kwanciyar hankali a zuciyarsa*.
*_👉 Addu'a ba ta faduwa kasa. Ko a ba ka yau, ko a ba ka gobe, ko kuma a ba ka abinda ya fi wanda ka roka. Idan ba a ba ka ba sam, to akwai wani sharri da za a tunkude maka. Addu'a makamin mumini ce.*
*_👉 Wanda mutane suka fi so shi ne wanda yake kyautata masu. Allah ma yana son mai kyautata ma mutane.*
*_👉 Zabi aboki na kwarai, kada ka zabi mugu. Mugun aboki idan ya yi fushi zai zage ka, ya tona asirinka, ya musanta alherinka, ya yi maka kage da kazafi. Abokin kwarai idan ya yi fushi nan take ya tuna alherinka, sai ya tsare mutuncinka, ya hakurce ma laifinka.*
*_👉 Macce ita ce adon duniya. Babu mai kama da ita a cikin dangin tsuntsaye sai Dawusu. Mai kama da ita a cikin dabbobi ita ce Barewa. A duniyar mutane kuma ita ce aljannar duniya. Kai, duniyar da lahirar ma aljanna tana hannunta. Macce takan kai mahaifinta aljanna tun tana karama.
MUTANEN DA ALLAH ZAITONA MUSU ASIRI AFILIN HISABI SANNAN ALLAH YAKORASU WUTA
1-Daga ciki akwai masu dibar ganimar yaqi kamin araba. suyi Amfani da wani 6angare nata
2-sannan akwai mutumin da yake satar kudin hukuma (Gwamnati)
3- Kokuma duk wata dukiya da aka baka ajiya indai kacita to kana cikin mutananen da Allah zai fallasa a ranar Alqiyama
4- Akwai kafira da muna fukai da mushirikai da Azzalimai.
5-Malami dake Umarni a aikata abu mai kyau Amma shi baya aikatawa.
6- Dukkan wani mutumin banza. = Zakace ai kowa yana sa6on Allah Aa ba haka bane ba.:" Abunda ake nufi mutumin dayake sa6on Allah baya nadama baya sh٬awar yatuba yadaina wannan aikin wannan shi ake cema fajiri
7- Mutumin da yake aikata aiki don mutane suyaba baya neman yardar Allah
8- maciyi Amana domin galibi ita Amana a 6oye ake cinta to shikuwa Allah sai yatona Asirin bawa
9- Mutumin da yayi watsi da dan uwansa Musulmi yana jin yana neman dauki Amma yaqi bashi gudun mawa
Wadannan dukansu wallahi Allah bazai turasu wutar jahannama ba sai Allah yafallasa su a idon duniya afilin Hisabi
Tunatarwar Juma'a:
An Tambayi :
Wani Babban Malami Mai Suna Ibrahim Ibn Adhama. "Miyasa Muke Addu'a Ba a karba wa ?Saiyace Zuciyarku Ta Mutu Akan Abubuwa Guda 10.
《1》Kunsan ALLAH Amma Baku bashi Haqqinsa ba。
《2》Kunsan Aljannah Amma baku nemeta ba
《3》Kunsan Wuta Amma Baku Gujemata ba。
《4》Kunsan Mutuwa amma bakuyi mata tanadi ba。
《5》Kunsan Qur'ani amma kunqi aiki dashi。
《6》Kunce kuna gaba da shaidan amma kuna binsa。
《7》Kuna binne matattunku amma bakwa lura。
《8》Kuna cin arziqin ALLAH amma bakwa godiya。
《9》Kuna kallon aibin wasu kunbar naku。
《10》Kuna kurin son Maxon ALLAH amma kunbar sunnar sa。
YA UBANGIJI KABAMU IKON KYAUTATA AYUKAN MU DA RAYUWARMU YADDA KAKESO KODA RAYUWARMU BATASO.
*→01) HUKUNCE HUKUNCEN DA SUKA KEƁANCHI MATA MUMINAI*
_Wallafar Sheikh Salih Al-Fauzan_
_FITOWA TA FARKO_
_~FASALI NA ƊAYA~_
Hukunce-Hukunce da suka shafi abubuwa daban-
daban.
*1• MATSAYIN MACE KAFIN ZUWAN MUSULUNCI:*
Abinda ake nufi da kafin zuwan musulunci shine
zamanin jahiliyya wanda musamman larabawa
suka kasance suna rayuwa acikinta, dama sauran
mutane dake bayan ƙasa, wannan shine lokacin
da manzanci ya yanke, kuma hanyoyin shiriya
suka ɓace, kamar yadda yazo acikin hadith:
ALLAH ya dubi mutanen da ke bayan ƙasa a
wannan lokaci sai yaƙi su baki fayansu,
larabawan da waɗanda ba larabawa ba, sai
mutanen kirki daga cikin ma’abota littafi.
A wannan zamanin rayuwar mace ta kasance
rayuwa ce mai matsananciyar wahala musamnan
ma a cikin al’ummar larabawa waɗanda sun
kasance basa ma son haihuwar mace.
Akwai daga
cikinsu waɗanda suke binne ta da ranta acikin ƙasa har sai ta mutu, wasu kuma su ƙyaleta ta
rayu rayuwar ƙasƙanci da wulaƙanci kamar
yadda ALLAH (SWT) Yace:
۞ ﻭَﺇِﺫَﺍ ﺑُﺸِّﺮَ ﺃَﺣَﺪُﻫُﻢ ﺑِﺎﻟْﺄُﻧﺜَﻰٰ ﻇَﻞَّ ﻭَﺟْﻬُﻪُ ﻣُﺴْﻮَﺩًّﺍ ﻭَﻫُﻮَ ﻛَﻈِﻴﻢ۞
۞ﻳَﺘَﻮَﺍﺭَﻯٰ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡِ ﻣِﻦ ﺳُﻮﺀِ ﻣَﺎ ﺑُﺸِّﺮَ ﺑِﻪِ ﺃَﻳُﻤْﺴِﻜُﻪُ ﻋَﻠَﻰٰ ﻫُﻮﻥٍ ﺃَﻡْ ﻳَﺪُﺳُّﻪُ
ﻓِﻲ ﺍﻟﺘُّﺮَﺍﺏِ ﺃَﻟَﺎ ﺳَﺎﺀَ ﻣَﺎ ﻳَﺤْﻜُﻤُﻮﻥ ۞ َ
“Kuma idan aka yiwa ɗayansu albishir da ƴa
mace sai fuskarsa tayi baƙiƙirin yana cike da
tsananin baƙin ciki"
"Yana ɓuya daga (idon)
mutane saboda munin abunda akayi masa
albishir dashi, shin zai riƙe shine wulaƙance ko
kuwa zai binne shine acikin ƙasa? Kai! Wannan
hukunci nasu ya munana”
[Al-nahl: 58-59]
Kuma ALLAH (SWT) Yace:
۞ ﻭَﺇِﺫَﺍ ﺍﻟْﻤَﻮْﺀُﻭﺩَﺓُ ﺳُﺌِﻠَﺖ۞ ْ
۞ﺑِﺄَﻱِّ ﺫَﻧﺐٍ ﻗُﺘِﻠَﺖ ۞ ْ
.
“Idan kuma yarinyar da aka binneta da rai suka
tambayeta: da wane laifi aka kasheta?”
[Al-Takwir: 8-9]
Wato ƴar da aka binneta da ranta acikin ƙasa har
ta mutu. Macen da ta tsira daga binnewa da rai
kuwa, idan har ta rayu to zata rayu ne rayuwa ta
wulaƙanci, bata da rabo acikin gadon ƴan uwanta
komai yawan dukiyar da suka bari
SALLAH ITACE MAFI ALKHAIRI DAGA BACCI!!!
Me nene yasa Sallah tafi Alkhairi daga Bacci???
Amsa:
1.Bacci amsawa kiran Zuciyane
Sallakuwa amsawa kiran Ubangiji ne
2.Shi Bacci mutuwane
Sallakuwa Rayuwace
3.Shi Bacci hutune na Gangar jiki
Sallakuwa hutune na Ruhi
4.Shi Bacci da Mumini da Kafiri duk suna yinsa.
Sallakuwa Mumini ne kadai yake yinta
Masu tashi lokacin hudowar Alfijir sun rabauta, Fuskarsu kuma ta haskaka Goshinsu kuma shima yayi haske da kyalli, Lokacinsu kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu to kagodewa Allah.s.w.t. daya fifitaka idan kuma baka cikinsu to Karoqi Allah.s.w.t yasakaka acikinsu.
Menene yafi Alfijir kyaune?
Farillarsa(Sallar Asuba) zata sakaka acikin kulawar Ubangiji da kariyarsa,
Sunnarsa (Raka'ataylfajri) itace tafi Duniya da abinda yake cikinta
Sallarsa (kamar yadda Malaman tafsiri suka fassara wannan aya ta 78 Suratul - Isra'i وقرآن الفجر ana nufin Sallar Asubahi)
Ita Sallar Asubahi Mala'iku masu duty n safe da masu dutu n dare duka suna halartota.(Domin alokacin suke handing over na duty n su acikin wannan Duniya tamu)
Yakai Dan'uwa Mai girma kasani cewa : Duk wanda yarayu akan wani aiki to akansa zai mutu, Wanda kuma yamutu akan wani aiki to akansa za'a tashe shi
Idan kakaranta wannan Saqo kuma kayi aiki dashi to kasami Ladan aikin ka idan kuma katurawa wasu suma sukayi aiki dashi to Ladanka zai nunku awuri Allah.s.w.t In Allah.s.w.t yaso.
Kada kaboye Ilimi, Kabayyana shi zaka sami Kyakkyawan Sakamako
Kuyi Murna yaku masu Sallar Asubahi acikin Lokacin ta kuma acikin Jam'i.
*ILLAR FUSHI*
Fushi tamkar tabin hankali ne Karshen shi kuma Nadama ne, Inji *Aliyu Bin AbiTalib (R.A)* Ka lura Duk wanda fushi ya shafe shi yakan fidda shi daga dabi'a irin ta mutane,FUSHI shine tarkon abin da shaidan yafi amfani da ita wajen halaka dan adam. Inji Ibnul Qayyim.Ka lura in mutum yana cikin fushi to yakan iya aikata komai... a fusace Sannan Ba'a gane mutum me hakuri sai a lokacin FUSHI. Maganin fushi manzan Allah (s a w) yace idan kai fushi idan kana tsaye ne kazauna idan kana zaune ne ka kwanta ko kuma kabar wurin da aka saka kai fushin. Ya Allah kasa mu iya hadiye fushin mu, mu iya yafe ma "yan uwan mu dan mutsira ranar gobe kiyama.ALLAH ka jikan iyayenmu da yanuwanmu,da abokan mu,Ya ALLAH ka sa mu gama lfy
_*FALALAR RANAR JUMA'A*_
➖➖➖➖➖➖➖➖
_Kamar Yanda Muka Sani Ranar Juma'a Ranace da *Allah* Ya Fifitata Akan Sauran Ranaku, Wanda Hadisai da Dama Sunyi Bayani Game da Wannan Fifikon. Kadan Daga Cikin Falalar Ranar Juma'a Sun Hada da:_
_*1. Gafarar Zunubai:* Yana Daga Cikin Falalar Juma'a Shine Ana Gafarta Zunuban Bayi a Cikinta. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa:_
*ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ : ( ﺍﻟﺼَّﻼﺓُ ﺍﻟْﺨَﻤْﺲُ، ﻭَﺍﻟْﺠُﻤْﻌَﺔُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺠُﻤْﻌَﺔِ ، ﻛَﻔَّﺎﺭَﺓٌ ﻟِﻤَﺎ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻦَّ ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﺗُﻐْﺶَ ﺍﻟْﻜَﺒَﺎﺋِﺮُ} (مسلم:٢٣٣)*
_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Sallolin Farillai Biyar, da Juma'a Zuwa Juma'a, Suna Kankare Abinda Ke tsakaninsu, Idan Aka Nisanci Manyan Zubai}* (Muslim:233)._
_*2. A Cikinta Ne Mafi Falalar Sallah Take:* Hadisi Ya Tabbata Daga *Ibn-Umar* Yana Cewa:_
*ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ( ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ ) . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ " ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ " . ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ( ١١١٩ ) .*
_An Kar6o Daga *Ibn Umar (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Mafi Falalar Sallah a Wurin Allah Itace Sallar Asubah ta Ranar Juma'a a cikin Jam'i}* (Baihaqee). *Albany* Ya Ingantashi a Cikin Sahihil Jami'i (1119)._
_Yana Daga Cikin Banbancin Sallar Asubahin Ranar Juma'a da Sauran Ranakun Shine Anso a Karanta *Suratul Sajadah* a Raka'ar Farko; a Raka'a ta Biyu kuma a Karanta *Suratu Insan*._
_*3. Duk Wanda Ya Mutu Ranar Juma'a Za'a Kareshi Daga Fitinar Kabari:* An Kar6o Hadisi Daga
➡SAHABAI A SIKELIN MANZONALLAAH⬅
(1)---------Wandayafi kowa tausayin Al'ummah ta shine ABUBAKAR ASSADIQ.
(2)---------Wanda yafi kowa qarfi acikin addani shine. UMMAR.
(3)----------Wanda yafi kowa jinkunya shine USMAN.
(4)----------Wanda yafi kowa sanin hukunce hukuncen Alqalanci shine ALI.
(5)----------Wanda yafi kowa iya karatun Alqur'ani shine UBAYYU BIN KA'AB.
(6)-----------Wanda yafi kowa sanin Halal da haram shine MU'AZU BIN JABAL.
(7)-----------Kowacce Al'ummah tanada amini aminin wannan Al'ummah shine ABU UBAIDA BIN JARRAH.
(8)------------Wanda yafokowa sanin ilimin rabon gado shine ZAIDU BIN SABIT.
(9)------------Kowanne Annabi yanada mataimaki AZZUBAIRU Kaine mataimakina.
(10)-----------Wanda yake son yaji karatun Alqur"ani kamar yanda aka sauko dashi to yayi salon karatu irin na ABDULLAHI BIN MAS'UD.
(11)----------ALHASSAN sa ALHUSSAIN Sune shugaban matasan Aljannah.
(12)-----------Shahidi wanda yake tafiya adoron qasa shine DALHATU BIN UBAIDULLAH.
(13)------------Nafansheka da iyayena SA'AD BIN ABIWAQAS.
(14)------------Haqiqa ALLAAH Yariqeni khalili kamar yanda yariqi Ibrahim khalili gidana dana Ibrahim suna kallon junah a Aljannah ABBAS kums yana tsakanin mu mumini tsaqanin badadai kenan.
(15)-------------Maraba da tsarkakake kuma Abin tsarkakewa AMMAR BIN YASIR.
(16)-------------ALLAAH ya umurceni da inso mutun hudu kuma shima yana sonsu ALI da ABU ZARRIL GIFARI da SALMANUL FARISI da MIQDAD.
(17)--------------Qasa bata taba dauka sama bata taba rufe mutumin da yafi kowa gaskiyar magana kamar ABU ZARRIL GIFARI.
(18)--------------Mayafinsa nagidan Aljannah yafi mayafin Alhariri haka kuma al'arshi ya girgiza saboda rasuwarsa SA'AD BIN MU'AZ
(19)-------------Ya ALLAAH Kasanar da shi hikima da fassarar Alqur'ani ABDULLAHI BIN ABBAS (20)--------------Zabbabu cikin mu wanda suka halalci yaqin BADAR.**************Duba acikin Litafen IBN MAJAH Babin FIFADH ILIL AS'HABI RUSULLULLAHI (S.A.W
*```👉 KA TUNATAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANAN MUMINAI```*
👇 👇 👇 👇 👇
```👉Zauna da jama'a lafiya domin watarana sune zasuyi rakiyarka izuwa maqabarta.
👉Daure ka rike sallah akan lokaci domin watarana zata tayaka kwanciyar qabari.
👉Daure kayi biyayya ga iyayenka domin watarana kaima mahaifine.
👉Zamo mai yafiya a wajen mutane domin kaima a wajen Allah mai laifi ne.
👉Yi bautar Allah kamar kana ganinSa saboda Shi Yana ganinka.
👉Rike karatun qur'ani domin watarana zai Zama ceto a gareka
👉Daure ka turawa al-ummar musulmi domin yin aikin alkhai
KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE HANA MACE SHIGA ALJANNAH KODA KUWA TANA SALLAH:-
1) Duk Matar da take da aure tayi zina.
2)Duk Matar da ta Mallaki Mijinta ta hanyar asiri ko ta hanyar tsafi
3)Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna da Mijinta lafiya
4)Duk matar da ta raba mijinta da 'ya'yansa,ko ta Hanyar Asiri ko Yaudara
5)Duk matar data raba mijinta da Yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara
6)Duk matar da tayi asiri akan saukarwa kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai haila tazo mata
7)Duk matar da tasa aka daure mahaifar kishiyarta,don kar ta haihu
8)Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane
9)Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta don yayi mata kishiya.Ma'anar baka shine: Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya dawo dakin matsafiyar sai ya dawo namiji
10)Duk matar data nemi mijinta ya saketa,alhali baya cutar da ita.Kuma ba yadda ya iya
11)Duk matar da bata godewa mijinta bisa ga irin abubuwan da yake mata na Alkhairi
12)Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta
13)Duk matar da batayin wankan janaba, bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan haila ko biki
14)Duk matar da take tona asirin mijinta a cikin kawayenta
15)Duk matar da take annamimanci
16)Duk matar da take sa kayan da yake nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake fada akan irin shigar yahudawa da nasara
17)Duk matar data kara gashi akan nata
18)Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata wani abu wanda ba zai iya yi ba
19)Duk matar data dauki dan wani ta bashi Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba
20)Duk matar da zata cewa Mijinta tunda muke dakai meka taba yi mini.
Dukkan wadannan Laifuka guda 20, ko wani guda daya a ciki, idan Mata ta mutu tanayi bazata shiga Aljannah ba, Koda zata shiga sai an Babbaka ta.
*MU KOMA GA ALLAH😭😭😭.*
1 Dazaran katashi zaka bude Data don gani sakon duniya. Amma Sallar Asubah cikin Jam'i tagagareka. *Mu koma ga Allah.*
2 Kana iya minti 90 cikin kallon ball idan anyi rashin sa'a atafi extra-time. Amma Sallar farilla tagagareka cikin Jam'i don kallon ball. *Mu koma ga Allah.*
3 Kana iya haddace handout don ganin kaci jarrabawar duniya ta dan adam, Amma baka iya haddace surah daya ta Alqur'ani don guzurin lahira. *Mu koma ga Allah.*
4 Kanada halin kyautar mota don neman suna, Amma baka da hannun kyautatawa gajiyayyu da marayu don neman lahirarka. *Mu koma ga Allah.*
5 Kanada lokacin musu, Amma bakada lokacin yiwa Annabi salati. *Mu koma ga Allah.*
6 Kanada kudin sayan mota da sutura ta alfarma, Amma sayan Sinsiya ta sharar dakin Allah tagagareka. *Mu koma ga Allah.*
7 Kanada lokacin karanta jarida, Amma bakada lokacin karanta maganar mahaliccinka. *Mu koma ga Allah.*
8 Kana iya kuka don Asarar abun duniya, Amma tuna azabar kabari yagagareka. *Mu koma ga Allah.*
9 Kanada lokacin kallon season film, Amma sada zumunci tagagareka, don neman haye siradi. *Mu koma ga Allah.*
10 Kanada lokacin zuwa ko inane don neman abun duniya, Amma neman ilimin sanin mahaliccinka yagagareka. *Mu koma ga Allah.*
11 Kaine jagora wajen zalunci da cin dukiyar al'umma, Amma kiran sallah (Ladanci) Abun kunyane agareka. *Mu koma ga Allah.*
12 Ka zabi rayuwar duniya fiyeda ta lahira, bayan bakasan yaushe zaka mutu ba. *Mu koma ga Allah.*
*👉🏼NAZARI NA MUSAMMAN.*
1 Idan arziki ne yasanya kabijirewa mahaliccin ka, to yau ina *Qarunah?.*
2 Idan zallan sabon Allah kakeji dashi da shagaltuwa, to yau ina *Fir'aunah?.*
3 Idan zalunci kasa agaba to yau ina *Hamana?.*
*👉🏼YAKAI DAN'WA AMUSULUNCI KASAKE TUNANI.*
1 Talauci baya hana dautar Allah. Tuna da tarihin *Annabi muhammad (S.A.W).*
2 Idan hassada akema, Tuna da tarihin *Annabi yusuf. (A.S)*
3 Idan radadin ciwo zai sakamanta da Allah tuna da tarihin *Annabi Ayuba. (A.S)*
4 Idan
*Miji! Miji!! Miji!!!*
kusan ince kowace mace a duniya tasan wannan sunan koda kuwa karama ce
abin tambaya anan shin wanene *miji*🤔
*miji*
shine wanda ALLAH ya hadaku ya zama abokin rayuwarki a duniya wanda muke fatan har lahira ya sanya soyayya da tausayi a tsakaninku.
*miji*
shine wanda kika za6a ki kasance dashi har karshen rayuwarki
*miji*
shine wanda yake fita komai sanyi ko zafi,hunturu,ruwa domin ya nemo abinda zai rufa muku asiri dashi.
*miji*
shike ci dake ya baki abinsha ya miki sutura ya baki gun kwana inbaki da lafiya ya nema miki magani,ya dau dawainiyan makarantar ki dana ya'yan ki.
*miji*
shi kadai ne ALLAH ya yarjemiki ku kadaita tare har ku rufe kofa kuma bakwa tunanin faruwan wani abu Sai qarin nutsuwa.
*miji*
shine wanda inkina cikin damuwa baya gushewa sai yasaki farin ciki.
*miji*
shi kadai keda iko a kanki sama da iyayenki, shine sai da izininsa zaki fita
*miji*
shine wanda inya nemi saduwa da ke kika qi kike kwana cikin tsinuwan mala'iku
A'uzubillah
*miji*
shine Aljannarki shine wutanki kibishi kisamu aljanna kisaba kije wuta.
SubhanAllahi.
Mata mu kasance masu kyautatawa mazajen mu, mu nuna musu so da kauna mu tarairayesu mu tausaya musu mu kance dasu cikin halin farin ciki ko kunci dan samun Rahamar Ubangiji
*ALLAH yasa mudace*
*(ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺇِﻥْ ﺟَﺎﺀَﻛُﻢْ ﻓَﺎﺳِﻖٌ ﺑِﻨَﺒَﺈٍ ﻓَﺘَﺒَﻴَّﻨُﻮﺍ ﺃَﻥْ ﺗُﺼِﻴﺒُﻮﺍ ﻗَﻮْﻣًﺎ ﺑِﺠَﻬَﺎﻟَﺔٍ ﻓَﺘُﺼْﺒِﺤُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰٰ ﻣَﺎ ﻓَﻌَﻠْﺘُﻢْ ﻧَﺎﺩِﻣِﻴﻦَ)*
@Surat Al-Hujraat : 6]
*(ﻳَﺎ ﺑُﻨَﻲَّ ﺃَﻗِﻢِ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺃْﻣُﺮْ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﺍﻧْﻪَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨْﻜَﺮِ ﻭَﺍﺻْﺒِﺮْ ﻋَﻠَﻰٰ ﻣَﺎ ﺃَﺻَﺎﺑَﻚَ ۖ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻣِﻦْ ﻋَﺰْﻡِ ﺍﻟْﺄُﻣُﻮﺭِ)*
@Surat Luqman : 17]
@Muslim
*(ﻟَﻮْﻟَﺎ ﺇِﺫْ ﺳَﻤِﻌْﺘُﻤُﻮﻩُ ﻇَﻦَّ ﺍﻟْﻤُ
👏🏻Ya ke y'ar uwa musulma! ki sani cewa:-
1.🌷Aure ibada ne, tushensa soyayyace, ginshikin sa biyayyace sannan asalinsa amanace.
2.🌷Zaman lafiyar aure shine tushen samun dacewa da rahamar Allah wanda kuma ya ke samuwa ta hanyar kyakykyawar fahimtar juna.
3.🌷Kaunarki ga abinda miji ke so koda ba kyaso tare da mika wuya ga al'amarinshi muddin ba su saba wa Allah ba, kan karfafa dadin zamanta kewarku.
4.🍃Girmamawarki ga y'an uwan mijinki girmamawace agareki.
5.🍃Taimakawarki ga cigaban mijinki taimakawa kankine.
6.🍃Tsabta, kunya, girki, kawaici tare da tattausan lafazi kan karfafa alakarki ga mijinki.
7.🌸Ki tabbatar babu wani abu da mijinki zai ji daga gare ki sai mai dadi, babu abinda zai shaka sai mai kamshi kuma babu abinda zai gani sai kyakkyawa.
8.🌸Addu'aki agareshi babu hijabi, ki tabbatar da kyakkyawar addu'aki agareshi.
9.🌸Ki kiyayi bayyana farin cikinki yayin bakin cikinshi ko kuma bakin ciki ayayin farin cikinshi.
10.🐠Ki mayar da gidanki ya yi tamkar wajan debe kewa tare da gusar da bakin ciki agurin mijinki.
11.🐠Ki kasance mai hakuri tare da juriya akan halin da kuka tsinci kanku, ki zamo mai rufe sirrin mijinki.
12.🐠Ki zamo mai taimakawa mijinki awajan bautar Allah.
Ya Allah duk wanda ya dauki hannunsa mai albarka ya tura zuwaga y'an uwa ya Allah kabiya masa bukatarsa...⭐
*AURE IBADA NE! RASHIN SA TAWAYA NE:*
Hakika Allah ya aiko mazanni kafin Manzon Allah Annabin mu Muhammad (saw) kuma aka sanya su masu aure masu zuriya.., hakanan a tarihin rayuwar farin jakada Annabi (saw) shima an tabbatar yayi aure kuma yayi zuriya.
Yana daga cikin sunnnah mai girman lada yin aure.. An umarci matasa duk wanda ke da damar yin aure to yayi aure, haka nan an umarci iyaye in wanda suka amincewa halin sa da addinin sa yazo neman auren 'ya 'yansu su aurar masa.
Aure cikar kamala ne, karin daraja ne, akwai falala mai yawa da samun rayuwa mai dadi cikin zaman aure. Hatta nishadin zaman aure lada ne. Rashin yin aure ga mai iko gazawa ce da tawaya, maras aure na rayuwa cikin rauni da kaskanci da matsaloli.
Ga duk wanda ya girma tabbas dabi'ar nan ta halitta na son iyali zata bishi har zuci ta qawata masa son aure da burin samun zuriya. Allah ya sanya mana soyayya da tausayi tsakanin maza da matan mu.
Rayuwa dace ne, kuma rabo ne, wato ba kowa ne ke samun abinda yafi ba, ko samun abinda yake so a rayuwar sa. Allah sarki tausayin maras aure ya kamani.....
Hakika da so samu ne, ina ga duk al'ummar mu maza da mata ba mai za6awa kansa jinkirin aure. Ko ace namiji yana dama da iko da karfin ga66ai da lafiyar kwakwalwa ya zauna da mata daya. Ko mace yar gidan daraja, mai gata da lafiya ta daskare a gida har ta gama girmanta ba aure.
Na yarda da masu hasashen cewa jinkirin aure na jawo mana matsoli sun fi shurin masaki ga maza da matan mu a yau. Akwai masu cewa shike jawo yawan samun yasar da jarirai, fyade, fandarewa iyaye, shaye-shayen 'yan mata, yawon ta zubar da kallon fina-finan batsa da sauran irin su...
Muna rokon Allah ya bada ladan jarrabawa ga wadanda wani laruri ya jawo masu jinkirin aure.
Allah ya aurar dasu su rayu cikin aminci da natsuwa. Allah ya musanya masu damuwar da suka ji da farin ciki a duniya da lahira.
KANA SADA ZUMUNTA?
1-Allah ta'ala yayi Umarni da sada zumunta. Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38, Suratul bakara 210, Suratul Nisa'i 2 .
2- Sada zumunta yana kara tsawon rai, Bukari 5986, Muslum 2557.
3- Sada zumunta yana kara arziki, Bukari 5986
4- Sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7
5- Sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah, Bukari 5983
6- Sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.
7- Sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902
8- Sada zumunta wasiyyar da Annabi (SAW) yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669
9- Sada zumunta siffar muminai ce.
10 Sada zumunta yana sawa a karbi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674
11- Sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.
12- Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya dinka sada zumunta,. Bukari da Muslum.
13- Sada zumunta yana kare mutum daga la'antar Allah. Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25.
14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu, na Sadaka dana zumunta. Sahihu, Sunanil Tirmiziy. 1/202 .
15, Sada zumunta yana kara soyayya tsananin dangi da yan'uwa .
16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsananin yan'uwa.
17- Wanda baya sada zumunta bazai shiga Aljannah ba.
18- Allah taala ya yiwa mahaifa alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita, zai yankewa wanda ya yanketa.
19- Mai sada zumunta shine wanda ko ba'a zo masa ba, shi zai je.
20, Baya cikin sada zumunta sai wanda yazo maka kawai zaka je masa.
Allah Ya bamu ikon sauke wannan nauyi na sadar da Zumunta. Amin
*A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA'I GUDA UKKU*
*Na farko 1*
*Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.*
*Idan kudinsa ya ragu xai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.*
*Na biyu 2*
*kullum yana cin arxikin Allah in halal yaci xa'a tambaye shi in haram ne xa'ayi masa axaba akai bai san karshen hisabin mai xai kasanceba.*
*Na uku 3*
*kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda yadamu da duniya Bai san makomarsa ba shin aljannace ko wutace.*
*GASKIYA*
*Babu abunda xai amfaneka sai sallarka/ki*
*wanda yabar karatun Alqur,ani tsawon kwana uku ba tare da uxuriba sunansa MAQAURACI wanda ya qauracewa Alqur,ani kenan.*
*Duniya kwana 3 ce*
*Jiya: munganta baxata dawoba*
*Yau: muna cikinta baxata dauwama ba xata wuce*
*Gobe: bamusan ina xamu kasanceba.*
*ka gaisa da mutane, kayimusu afuwa kayi sadaka domin ni da kai dasu duk Matafiyane bissalam.*
,,ZINA BASHI CE!
'Yan uwana Maza da Mata akwai wata Qissa da zan Bamu, mai matu'kar amfani acikin wannan zamanin namu, ma'abocin Qissar, wanda abin yafaru dashi,shine yake bayar da Labarin yadda al'amarin ya kansace dashi.Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News
paper) ta 'kasashen Larabawa, kuma cikin harshen Larabcine, amma zanyi 'kokari wajen fassarawa gwargwadon yadda
na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a harshen Larabci.gata kamar haka.......
Mutumin yana cewa:
A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatunne sai na had'u da wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu muka 'kulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).Da iyayenta suka gane sai suka tambayeta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.Sai yayanta yataho nema na a fusace yana nufin
d'aukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima qanwata ciki ko ???Sai na amsa masa da cewa:
Wace ce, ni banma ta6a ganinta ba a Rayuwata,ban santah ba.Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita dole suka 'kyaleni.Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur'kushe tana tana
kuka.Saina dur Qusa na daga ta sai tasake yanke jiki tafad'i 'kasa har sau uku saina tambayeta a karo
na qarshe:"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?
Sai tace:Qanwarkace gata can wani yayi mata ciki!Yace sai naji kamar an sokeni da mashi, hankalina yatashi na tasa 'keyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.Da mukaje sai yafada min maganar data tayarmin da hankali.
Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.(Ban santa ba, banma ta6a ganinta ba)!Bayan zamani yaqara yin nisa sai nayi nufin yin
aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.
Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.Saita fadamin wata magana mai shiga rai."Don Allah karufa min asiri,
KAR KA BAR DUNIYA TA RUDEKA
***************
Wallahi duniya Mayaudariya ce, Makaryaciya ce, Kuma Tsohuwa ce Mai Makirci.
Babban dillalinta shine Shaitan. Mai Zakin baki, mai chusa Tunane-Tunane da Waswasia Zukatan Mutane!!
Yayin da Allah ya baka lafiya da dukiya da Mulki da 'Ya'ya, Sai shaitan La'ananne yazo ya rika Qawat maka zaman duniyar nan. Ba zai barka ka tuna da lahira ba, ballantana kayi tanadin tafiya, ko kuma guzuri domin gyaran lahira..
Kullum idan anyi zancen "LAHIRA" sai shaitan ya chusa ma Zuciyarka damuwa da kuma Baqin ciki.. Kai babu labarin da kafi son ji in banda labarin "DUNIYA" da abin cikinta wanda ba zai amfaneka ba.. Ko kuma labaran da zasu Qara maka sakankancewa acikin sa'bon Allah..!!
WALLAHI SHAITAN MAKIYINKA NE! BA ZAI YARDA KA SAMU JIN DADIN LAHIRA BA.. Kullum yana Qars shagaltar dakai yana nuna maka duniya, Zuciyarka tana qara Makancewa da lahira.. Da haka har ranar da Mala'ikan Mutuwa Zai kawo maka Ziyarar Qarshe!!
Babu wani mai rai fache kullum sai Mala'ikan Mutuwa ya kawo masa Ziyara sau Saba'in.. Yana zuwa yana duba agogon Zuciyarka, yana ganin sauran lokacin da ya rage maka!!
Duk ranar da ajalinka ya cika, Mala'ikan zai tarar dakai baka shirya ba, Baka kintsa ba, Baka tanadi Guzuri ba.. Kuma WALLAHI ba za'a jinkirta maka koda SECOND GUDA ba!!
Zai Fizgi ranka ya tafi dashi zuwa wajen Ubangijin nan naka wanda baka son haduwa dashi!!! LA ILAHA ILLLAL LAHU MUHAMMADUR RASULULLAHI!!!
Daga wannan ranar shikenan taka ta Qare.. Kodai ka huta kenan, Ko kuma an huta da sharrinka. WALLAHI KODA KA MALLAKI ZINARE (GOLD) DA LU'U-LU'U (💎) CIKIN DUNIYAR NAN, Ba zasu yi maka amfani ba.. Ba zasu tare maka azabar Allah ba!!! (Sai dai in ka ciyar dasu bisa tafarkin Taimakon Marayu, Miskinai, Masallatai, Makarantu, Zumunci, taimakon al'ummah da sauransu).
Amma idan ba haka ba, DUKIYA SHARRI CE GAREKA YA KAI DAN UWA!! Wallahi ba zaka matsa daga gaban Zatin Ubangiji ba, fache sai ka amsa tambaya akan kowanne KOBO DA SISI
*👿MATA SAI FA MUN GYARA!👿*
👿Wasu daga cikin dalilan da ke sanya jinnu shiga jikin mu fiye da maza. Duk wanda ya san matarsa ko 'yarsa na yi ku gyara musu:
👿1. Zama a bakin qofa, ko bakin windo da sauran hanyoyin wucewa.
👿2. Fesa turare mai qarfi yayin fita, ko kuma fesa turare lokacin kwanciya bacci mai qarfi kuma ba addu'a.
👿3. Yawan yin zanen lalle mai fulawa a madadin asalin na gargajiya. Wanda aljani da kanshi ya fad'i cewa kwalliyar su ne a jikin wata.
👿4. Zama babu ďankwali a cikin gida, da kwanciya babu shi. Ko bayyana gashin a fita waje.
👿5. Yawan zama ba tsarki, kamar in an yi an gama da dare kawai ta kwanta babu tsarki cikin qazanta. Kuma babu ko alwala har gari ya waye tangararan.
👿6. Rashin yin alwala a lokacin jinin al'ada da barin yin dukkan addu'o'i. Mafiya yawa in tana jini sai ta yanke dukka komai har sai ta yi tsarki. Wanda hatsari ne sosai.
👿7. Yawaita fushi da sanya damuwa a rai koda yaushe. Domin wata da aljanar ta shige ta cewa ta yi kullum in ta zo wuce wa zata ga tana bakin ciki da damuwa. To wai ita ma aljanar irin halin da take ciki kenan sai ta shigeta. Idan ta na magana ita kaďai na baqin ciki sai aljanar ta rinqa amsa mata tana rarrashinta. Daga karshe dai ta shigeta, in aljanar na baqin ciki sai ta rinqa yanka jikinta da wuka. Wanda matar ma haka ta koma yi.
👿8. Caba ado na gani na fada a fita musamman ga wacce bata yin azkar. Da gyara adon in an samu wuri a waje ko a cikin mota. Domin ita ma wata a nan jinnun ya shige ta. Yace ta tsaya a titi ta fito da powder ta qara shafawa ta gyaggyara. Shi ya zo wucewa sai ya ga gaskiya yana sonta.
👿9. Zama a wuraren da aka san suna zama. Kamar wuri da koda yaushe ke da danshi, zama tsakanin inuwa da rana (rabinki a rana rabi a inuwa). Qin shiga bandaki da addu'a ko dankwali. Ko yin waqe waqe a banďaki.
👿10. Shagala da duniya da yawa. Bana manta wani Ruqya da na kalla na wani bature ďan America. Aljanu ne a jikinsa sun kai 10 wanda a dalilin badala ya samo su
HUKUNCIN ZAKKAR FID- DA KAI
“ZAKKATUL FIDR”
“Zakkatul Fidir” ita ce ake kira a Hausance da “Zakkar Fid da kai”, ko “Zakkar kono”, ma’anarta kuma ita ce: zakkar da ta wajaba kowane Musulmi ya fitar da ita kafin gabatar da sallar Idi karama, kowa gwargwadon sa’i daya na abincin da aka fi amfani da shi a garin da yake, babu babba, babu yaro, ba namiji ba mace, babu d’a babu bawa; kowa sai ya fitar; Sayyiduna Abdullahi Ibn Umar (Allah ya kara yarda da su) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya farlanta wa mutane bayar da zakkar fid da kai a watan Ramadhan, sa’i ne na dabino, ko na alkama, da ta wajaba akan kowane Musulmi, d’a ko bawa, namiji ko mace.” [al-Bukhari, 2/130; Muslim, 2/677].. kowa zai fitar wa wanda ciyar da shi ta wajaba akansa..
Amma sharadin bayar da ita shi ne ya zamana mutum yana mallakar sama da abin da yake bukata a ranar idi, saboda haka talakan da ba ya mallakan sama da abin da zai ci, shi da iyalansa a daren idi, wato daren da aka ga watan Shawwal, da kuma ranar idi, to kuwa lallai wannan ibada ta zakkar fid da kai ba ta hau kansa ba, saboda ba zai iya ba, shi kuwa: ((Allah ba ya daura wa kowane rai wani abu sai abin da zai iya)) [al-Bakra: 286]..
Allah Madaukakin Sarki ya farlanta wannan zakka ne domin ta tsarkake mai Azumi daga kura-kuren da ya aikata a lokacin Azumi, irin su: alfasha a zance, da kuma ayyuka marasa fa’ida.. haka kuma Allah Madaukakin Sarki ya farlanta zakkar fid da kai ne; saboda a wadata mabukata, kada a bari har sai sun roki abin da za su ci a ranar idi, ranar da gaba dayan Musulmai suke cike da farin ciki da zuwansa, a dalilin haka ne ma Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yake cewa: ((Ku hutar da su yawon nema a wannan rana)) [Dar Kutniy 2/152; al-Baihakiy, 4/175].
Game da lokacin da ake fitar da zakkar fid da kai kuwa, malamai sun kara wa juna sani, inda bayanansu game da haka ya zo kaman haka:
* Mazhabar Imam Abu Hanifah (Allah ya kara yarda da shi): ta tafi akan cewa za a fitar zakkar fid da kai ne da zaran alfijir din ranar idin karamar sallah ya fito.
* Mazhabar Imam as-Shafi’iy, da Mazhabar Imam Ahmad (Allah ya kara yarda da su): sun tafi akan cewa zakkar fid da kai tana wajaba ne da zaran rana ta fada a ranar karshe na watan Ramadhan..
* Mazhabar Imam Malik (Allah ya kara yarda da shi): su kuwa Malikawa suna ganin cewa ya halatta a fitar da zakkar fid da kai kafin ranar idi da kwana daya ko biyu; domin an ruwaito cewa Sayyiduna Abdullah bn Umar da Al-Hassan (Allah ya kara yarda da su) cewa babu laifi a fitar da wannan zakkar kafin ranar idi da kwana daya ko biyu…
Saboda haka sam babu laifi idan aka gaggauta bayar da zakkar tun kafin ranar idin da kwana daya ko biyu..
Sai dai fa idan lokacin bayar da wannan zakka ya wuce, to zakkar ba ta saraya, dole ne a bayar da ita a matsayin biyan bashi “Qadha’i”.
Ana bayar da wannan zakka ne ga talakawa, haka ma mutane takwas din da ake ba su zakka –kaman yanda ya zo a ayar Suratut Tauba- suna cikin wadanda za a bai wa wannan zakkar ta fid da kai, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Ita zakka ana bayar da ita ne ga talakawa fakirai, da talakawa miskinai, da masu aikin tattara ta, da kuma wadanda ake tarairayar zukatansu domin shiga Musulunci, da wurin ‘yanta bayi, da biyan bashin wanda bashi ya yi masu kanta, da mayaka masu daukaka kalmar Allah, da matafiya, wannan kam wajibi ne da ya zo daga Allah, lallai Allah shi ne cikakken masani, mai kuma yawan hikima)) [at-Tauba: 60].
Sai dai duk da haka, za a iya bai wa mutum daya, kaman yanda za a iya rarrabawa mutane sama da daya, abin dai da za a lura da shi kawai shi ne: hutar da mabukata da wahalar nema a wannan rana..
Kaman yanda muka bayyana a baya, ana fitar da zakkar fid da kai ne daga abincin da aka fi amfani da shi a garin da mutum yake, kaman mu ce: shinkafa, da masara, da dawa da sauransu, kowane mutum za a fitar masa da sa’i daya ne irin sa’in Sayyiduna RasululLah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam), wanda ya yi daidai da (kilo giram 2.04); amma wanda ya bayar da abin da yafi haka, ya kyauta zai kuma sami lada akan hakan in Allah ya yarda.
Game da bayar da kudi a zakkar fid da kai kuwa, akwai sabani tsakanin malamai, inda jamhur din malamai suka tafi akan cewa ba a fitar da zakkar fid da kai sai daga abincin da yafi yalwata a cikin garin da za a fitar din, sai dai mazhabar Hanafiyya ta tafi akan cewa za a iya fitar da shi da kudi, daidai da kimar abincin da za a bayar, inda za a kiyasta kudin abincin da za a fitar din a bai wa mabukata, ta yiwu hakan ne zai fi masu akan a bas u tsabar abinci, musamman a wannan zamani..
Saboda haka, babu laifi a fitar da zakkar fid da kai da kudi, za a kiyasta kudin abincin da za a fitar din a bai wa mabukata, domin dauke masu damuwar rook da bukata..
Allah ya amshi ibadunmu, ya kuma dawwamar mana da darasin da muka dauka a cikin wannan mata, ta yanda za mu cigaba da gabatar da ayyukan alhairi na ibada da na mu’amala a tsakaninmu, mu cigaba da kyautata wa juna, da kuma hararo kwarjinin Allah Madaukakin Sarki a dukan rayuwarmu, amin.
INNALILLAHI WA INNAILAIHI RAJIUN!!!
Ko shekaru nawa zamuyi a wannan duniyar, dole watarana warhaka mun zamto tarihi.
Wanda ya mutu bazai gane cewa ae ya mutu ba. Zai dauka bacci yakeyi yake mafarkin mutuwa. Zai gani a mafarki gashinan yana kuka, anyimar wanka, anyimar sutura an sanyashi a makwancinshi (kabari)
Har sai yaji zaiyi juyi acikin kabarin kasa ta hanashi juyi sannan yayi kuru-ruwa, ammana babu wanda zai jishi.
Daga bisani kuma, bayan kowa ya watse daga kan kabarin nashi an barshi shi kadai a makwancinshi, sai Allah Ya dawo masa da ranshi. Sai ya bude idanunshi ya farka daga mummunar mafarkin daya keyi.
Daga farkawarshi, sai yaji dadi domin yaga mafarki yakeyi ba gaskiya ba, sai ya ta6a jikinshi wanda ke lullu6e da likkafani, daganan sai ya tambayi kanshi cewa:
"Ina riga ta, ina wando na, ina undies nida kuma suke?"
Sai Kuma yafara tunanin cewa:
"a ina nake anan?"
"inane nan kuma?"
"yaya nakejin kamshin kasa kuma?"
"Toh meye Kuma nakeyi anan?".
Ananne fa zai gane cewa ashe acikin kasa yake, Kuma abinda yake gani kamar mafarki ashe ba mafarki bane gaskiya ne. Sai yagane cewa lalle fa ashe mutuwa yayi dagaske ba mafarki ba.
Sai Kuma ya kara kurma ihu fiyeda na farko yana kiran makusantanshi domin yana tunanin zasu kowamar gudumawa.
Babu wanda zaijeshi balle ya amsamar. Daga nanne sai ya tuna ALLAHU JALLA WA AZZA Shi kadai Zai iya kawomar agaji. Sai yafara kuka yana kiran sunayen ALLAH yana cewa:
"Ya Ubangiji Ka gafarta mini, Ya Ubangiji Kayi mini rahama, Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!!
*Zaiyi kuka cikin tsoro irin wanda lokacin da yake raye bai ta6a yi ba*
Idan ya kasance mutumin kirkine, Mala'iku biyu masu sakakkun fuska suna murmushi zasu zo gareshi su zauna dashi suna rarrashin shi suna kulawa dashi.
Idan kuma mutumin banza ne, Mala'iku biyu zasu zo gareshi wadanda idan ya kallesu ma tsoro sai ya sake kamashi, zasu na azabtar dashi gwargwadon munanan ayyukanshi na banza daya gabatar a duniya.
Ya Allah Ka gafarta mana xunubanm
KYAWAWAN HALAYE SUNE MAFI NAUYI AIKI AKAN SIKELIN
Kyawawan hali da Dabi'u ya kunshi abubuwa guda shida;
*1-Kamewa daga cutar da mutane da hannunka da harshenka da matsayinka*
*2-Yin afuwa ya yafewa wanda ya cutar da kai*
*3-Yin alkhairi ga dukkan al'umma da abinda Allah ya hore maka,da yin alkhairi ga wanda baya maka alkhairi*
*4-Yada Alkhairin ga al'umma da janyo masu alkhairi*
*5-Sadar da Zuminci ga wanda ya yanke maka zuminci da wanda bai yanke maka ba*
*6-Yin mu'amala da mutane cikin sakin fuska da nishadi da walwala*
Manzon Allah ﷺ ya yafi kowa kyawun dabi'u kuma Allah ya bada shaidar haka yake cewa;
*{Lallai kai Manzon Allah ﷺ kana kan wadan su Dabi'u kyawawa masu girma}*
Kuma Manzon Allah ﷺ ya bayyana mana cewa;
*(Allah ya aiko shine dan ya cikasa kyawawan dabi'u da halaye)*
@صحيح الجامع
Babbar manufar manufar addinin musulinci da cikarsa da fahimtarsa shine al'umma su zama masu kyawawan halaye da dabi'u.
Manzon Allah ﷺ ya bayyanawa al'ummarsa cewa babu wani aiki mafi nauyi da yake nauyaya sikelin musulmi a ranar alqiyama kamar hali na kwarai da kyawawan dabi'u.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*A-(Babu wani aiki da ake dorawa akan mizani ya sanya mizani yayi nauyi kamar kyawawan halaye da Dabi'u,kuma lallai mai kyawun hali yana samu matsayin mai raya dare da ibada da rayq rana da Azumi)*
@صححه الألباني في صحيح الترمذي -رقم : (2003)
*B-Kyawawan halaye suna sanyawa bawa ya zama mafi soyuwar bayi a wajan Allah*
Manzon Allah ﷺ yace;
*(Mafi soyuwar bawa a wajan Allah,shine wanda yafi mutane kyawawan halaye)*
@صححه الألباني في صحيح الجامع - رقم : (179)
*C-Ana lumlumka sakamako da ladar masu kyawawan halaye*
Annabi ﷺ yana cewa;
*(Kuma lallai mai kyawun hali yana samu matsayin mai raya dare da ibada da raya rana da Azumi)*
@صححه الألباني في صحيح الجامع - رقم : (1620)
*D-Hali na kwarai hanyace ta shiga aljanna*
An tambayi Manzon Allah ﷺ akan minene yake shiga da mafi yawan mutane a aljanna,sai yace;
*(Kiyaye dokokin Allah da kyawan halaye)* Kuma an tambaye
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I
ma'anar ISTIMNA'I shine= fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba.
Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suke samu a jikunansu sakamakon Istimna'i wato Masturbation. An kawo hujjoji
gamsassu daga Al-Qur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saw) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I, Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba.
Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena, bubban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin
wannan bala'in shine :
1. Kallon Fina-finan batsa.
2. Shiga shafukan internet na batsa.
3. Yin zantukan batsa tsakanin
saurayi da budurwa.
4. Kusantar zina ta hanyar kallo da
shafa, ko zance da dai sauransu.
Wasu kuma suna aikata hakan ne
dan gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi d'inma ZINAR bane!!
Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!!
1. MUTUWAR IDANU.
2. MUTUWAR AL'AURA.
3. CIWON BAYA.
4. BUGAWAR QIRJI.
5. RIKICEWAR TUNANI.
6. YAWAN MANTUWA.
7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI.
8. SAURIN INZALI.
9. SHAFAR ALJANU, ETC.
Wad'annan 'yan kad'an ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu a haka zai je ya tarar da hisabi.
DAN GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta, ku Qaurace ma duk wani abinda zai rinQa motsa muku sha'awa, idan
da hali kuje kuyi aure, idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi.
ALLAH YA SAUWAQE.
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,
DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.
Manzon Allah (s.a.w) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA
DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"
Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.
1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka ji.
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*ZAUREN SHEIK JA'AFAR ISLAMIYYAH*
*FATAWA AKAN AZUMI*
Na Sheikh Abdulwahab Abdallah ibn Muhammad
Fitowa na 16
TAMBAYA :
WADANNE HALAYE YA KAMATA MAI AZUMI YA LAZUMTA?
AMSA:
*1. HAKURI:* Ya kamata mai Azumi ya lizimci hakuri, domin shine zai hana mutum bin soye soyen zuciyar sa, kuma shine zai bashi juriyar bin umarnin Allah. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Idan dayanku ya kasance yana Azumi, kada yayi maganganun fasikanci ko rafasu, kuma idan wani ya zageshi ko ya ya`keshi yace: Ni Azumi nake"(Bukhari ne da Muslim suka ruwaito).
*2. RIKON AMANA:* Ya kamata mai Azumi ya kasance mai rikon amana, domin rikon amana zai taimaka masa wajen bada hakkokin da Allah ya umarce shi ya bayar.
Anan ya zama wajibi mu jawo hankalin wadansu daga cikin yan kasuwa wadanda suke amfani da watan Ramadhan wajen cutar da al'umma wajen tsawwala farashin kayayyakin masarufi, da kuma yin algus ko yaudara a cikin ciniki, domin duk abinda aka samu ta hanyar haram shi zai sa cinsu da shansu da tufafinsu ya zama haram.
Kuma wannan shi zai sa Allah yaki karbar Addu'arsu.
Anan ma muna kara jawo hankalin shugabanni wadanda Allah ya danka dukiyar Al'umma a hannunsu da su ji tsoron Allah su rike Amana, kada su dinga diban dukiyar al'umma suna yin umrah ko kuma su biya wa wasu mutane, domin Allah baya karbar ibadar da akayi da dukiyar haram.
*3. RAHAMA:* Ana son mai Azumi ya zama mai jin kai, karimi, mai yalwar zuciya da hannu, kuma mai son biyan bukatar Al'ummah gwargwadon hali.
Domin Manzon Allah (S.A.W) yace: "Duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar din ba".
*4. NASIHA:* Ya kamata mai Azumi ya zama mai nasiha wajen hana munkari da umarni da kyakkyawan aiki.
*5. SULHU:* Ya kamata mai Azumi ya zama mai yin sulhu a tsakanin mutanen da basa ga maciji, musamman tsakanin dangi, domin ya tabbata cewa: kiyayya tana hana karbar ibada da addu'a, har sai masu adawar sunyi sulhu a tsakaninsu.
*6. RINTSE IDO DA KAME FARJI:* Ya kamata mai Azumi ya rintse idonsa ya kuma kame farjinsa daga dukkanin abinda Allah ya hana, musamman kallon matan mutane, da zina.
*7. KAME HARSHE:* Ya kamata mai Azumi ya kame harshensa daga giba (yi da mutane) da zagin mutane da cutar dasu da karya wacce ta zama ruwan dare a tsakanin al'ummah.
*8. IKHLASI:* Ya kamata duk mai azumi yayi domin neman yardar Allah, ba don mutane su yabe shi ba, kada kuma yayi don Allah da waninsa.
Anan muna jan hankalin yan uwa masu bada sadaka ko ciyar da masu Azumi da masu tafsirin Al'Kurani mai girma, da masu zuwa umrah, da limamai masu rera tilawa a sallar tarawihi, da masu sauran aiyuka na gari da su rinka yi domin neman yardar Allah.
*9. BIN SUNNAR MANZON ALLAH:* Ya kamata mai Azumi ya rinka koyi da sunnar Manzon Allah (S.A.W) sau da kafa a duk ibadar da zai yi.
Ya kuma nisanci dukkanin bidi'o'i, musamman bidi'o'in da ake yin su a cikin watan Ramadhan, kamar nafil fili da falaloli da ake bayarwa wadanda basu tabbata daga manzon Allah (S.A.W) ba, ko magabata nagari.
*10. TARBIYYAH:* Ya kamata mai Azumi ya kula da tarbiyar gidansa musamman kangararrun yara wadanda basa Azumi ko kuma masu shaye shaye.
Kuma ya kamata iyaye su yawaita yiwa ya yansu addu'a, a cikin watan Azumi, domin Allah ya shiryesu.
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*WA'AZI:*
*DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:*
*1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.*
*2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.*
*3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.*
*4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.*
*5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.*
*6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).*
*7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMANUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.*
*Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don hasken Alqur'aninka, don Rahamar nan taka wacce ta yalwace dukkan halittunka....*
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*ALHAMDULILLAH*
*WA'AZI:*
*DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:*
*1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.*
*2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.*
*3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.*
*4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.*
*5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.*
*6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).*
*7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMANUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.*
*Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don hasken Alqur'aninka, don Rahamar nan taka wacce ta yalwace dukkan halittunka....*
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
Wa'azi::::
WANI MALAMI YA TAMBAYI ĎALIBIN SA YAU SHEKARAR MU NAWA TARE DA KAI?
Dalibi : 33
Malami : me ka koya daga wuri na duk tsawon wannan lokacin?
Dalibi : na koyi abubuwa 8 .
Malami : inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ,yanxu duk tsawon shekarun da na bata tare da kai ace ba abun da ka koya sai abubuwa 8 kawai ??
Dalibi : mallam wallahi abun da na iya ke nan , kuma bana son in yi maka qarya .
Malami : fadamin su naji !!!
Dalibi :-
1- Na lura da rayuwar mutane gaba ďaya sai naga kowa yana da abun da yake so, amma idan ya tashi tafiya qabari sai abun nan da yake so ya rabu da shi , NI SAI NA DAUKI KYAWAWAN AYYUKA ABUN SO NA, SABODA IDAN NA TASHI TAFIYA QABARI SU SHIGA TARE DA NI.
2- na lura da fadin Allah ta'ala ( duk wanda yaji tsoron tsayuwa a gaban ubangijin sa , ya hana ran sa bin abin da take so, to aljannah ce makomar sa ) SAI NA RIQA YAQI DA RAINA AKAN DUK ABUN DA TAKE SO , SABODA INYI MATA GATA TA SAMU TA SHIGA ALJANNAH.
3- Na lura da halayyar mutane, sai na gane duk wanda yake da wani abu mai daraja yana tattalin sa ne ya kuma a dana shi don kar ya lalace, sai na tuna da fadin Allah ta'ala ( abun da ke hannun ku zai qare , amma na wurin Allah yana nan ) , TO DUK ABUN DA YAZO HANNUNA MAI DARAJA DA QIMA SAI INBAIWA ALLAH AJIYAR SA, DON NASAN BAZAI LALACE BA.
4- Na lura da rayuwar mutane,sai na gane kowa yana tunqaho ne da dukiyar sa, ko martabar sa , ko dangin sa, sai na tuna fadin Allah ta'ala ( mafi girma a wurin Allah acikin ku , shine wanda ya fiku tsoron sa ) SAI NA SANYA TSORON ALLAH ACIKIN AL'AMURA NA SABODA IN KASAN CE MAI GIRMA A WURIN SHI.
5- Na lura da rayuwar mutane,sai naga wannan na zagin wancan , wancan yana sukar wancan, kuma duk hassada ce ta jawo musu, sai na tuna fadin Allah ta'ala ( mune muka rabawa mutane abun da zasu rayu da shi a rayuwar su ta duniya ) , SAI NA DAI NA HASSADA NA NISANCI ABUN MUTANE, NA GANE CEWA DUK ABUN DA NA SAMU DAGA ALLAH NE , HASSADAR MA SAI TA TAFI TABAR NI.
6- Na lura da rayuwar mutane, sai naga sa shen su yana gaba da sa she, suna baqin ciki da junan su, suna kashe junan su, sai na tuna fadin Allah ta'ala ( lallai shaidan abokin gabar ku ne,ku riqe shi abokin gaba ) , SAI NA DAI NA GABA DA MUTANE , NA KAMA GABA DA SHAIDAN SHI KADAI.
7- Nayi nazari akan rayuwar mutane , sai naga da yawan su suna wahalar da kan su awurin neman arziqi , har yakai ga dayan su ya riqa neman abun da bai halatta a gare shi ba, sai na tuna fadin Allah ta'ala ( babu wata dabba akan qasa face arziqin sa yana wurin Allah ) , SAI NA SHAGALTA DA ARZIQINA NA WURIN ALLAH ,NA RABU DA ARZIQINA A WURIN SA .
8- Na lura da rayuwar mutane,sai naga mafi yawancin halittu sun dogara ne akan halittu irin su, wannan akan dukiyar wancan, wancan nauyin sa akan wancan , wannan akan wancan , sai na tuna da fadin Allah ta'ala ( Duk wanda ya dogara ga Allah , Allah ya ishe shi ) , SAI NA DAINA DOGARO DA MUTANE NA KAMA DOGARO DA ALLAH .
SAI MALAMIN YACE:ALLAH YAYI MAKA ALBARKA.
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
Daga Abdullahi bn Mas'ud Allah ya qara masa yadda, daga annabi (saw) yace:
((لا يدخل الجنة من كان في قلبه مثقال ذرة من كبر)) وقال رجل: إن الرجل يحب أن يكون ثوبه حسنا ونعله حسنة؟! وقال: ((إن الله جميل يحب الجمال، الكبر بطر الحق و غمط الناس)) أخرجه مسلم (٩١)
*Ma'ana:* ((Duk wanda ya kasance a cikin zuciyar sa akwai kwatankwacin alzarra na girman kai ba zai shiga aljanna ba)). Sai wani mutum yace: Lallai mutum zaiso tufafin sa da takalmin sa su kasance masu kyau?! Sai manzon Allah (saw) yace: ((Lallai Allah mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau, giman kai shine qin gaskiya da rena mutane)). Muslim ya fitar dashi (91).
Duba:
التحذير من الشيطان لحسين بن عودة العوايشة
Ta'aliqi:
• Girman kai shine qin gaskiya da rena mutane.
• Mai girman kai ba zai shiga aljanna ba.
• Girman kai dabi'ar shaidan ne don haka yi qoqari ka nisance shi.
• Girman kai yana daga cikin manyan zunubbai.
• Girman kai yana jefa mai yin sa cikin bata.
Allah ya kare mu daga girman kai.
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*LAYLATUL QADR*
*🔜 Aisha (R.A) ta ruwaito cewa: Annabi (S.A.W) yace: "Kunemi daren laylatul qadr a goma qarshe na watan ramadan*
*(Bukhari)*
*🔜 Aisha (R.A) Ta tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Idan na riski daren laylatul qadr wane addu'a zanke karantawa?*
*🔜 Sai Manzon Allah yace mata:* *(ALLAHUMMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFUWA FA'AFU ANNA)* *Ya Allah lalle kaine mai yin afuwa, Ina neman afuwanka, Kayi mana afuwa*
*(Tirmizi)*
*🔜 Anas (R.A) ya ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W) yace: "Lokacin da laylatul qadr zai kasance Mala'ika Jibrilu (A.S) zai sauqo da tawaga masu yawa na Mala'iku zuwa duniya suna neman rahama ga masuyin sallah.*
*Kuna ambaton Allah da wasu ayyuka na ibadah*
*(Shu'abul imaan)*
*🔜 Allah Ta'alah yana sauqowa daga sama zuwa qasa tare da wasu runduna na Mala'iku da kuma Mala'ika Jibrilu suna nema mana (Rahama, Gafara, Afuwa, Aminci) bazasu gushe ba har sai zuwa fitowar alfijir*
*(Suratul Qard)*
*Ana dacewa da wannan ranan acikin darare kamar haka*
*21st* *23rd* *25th* *27th* *29th*
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
▓•FALALAR YIN SALLAR ASHAM•▓
▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓
_______________
Ankarbo daga sayyadi Aliyu dan Abi Dalib
(RTA) yace
Na tambayi manzon Allah (SAW) acikin Falalar
yin sallar Asham Acikin wata Ramadan sai
Manzon Allah (SAW) yace
▓•Wanda yayi Asham adare na farko Awatan
Ramadan mumini yana fita daga cikin laifinsa
kamar yadda mahaifiyarsa ta haifeshi,
▓•Wanda yayi Asham Adarena 2 Allah zai
gafartawa iyayansa,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 3 Wani Mala'ika zaikira sunansa a karkashin Al'arshi yace
Anunka aiyukan Alkhairi kuma agafarta
laifukansa,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 4 za'a bashi ladan wanda yakaranta Attaura, Injila, zabura,
da Alqur'ani,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 5 Za'a bashi ladan yayi
sallah a makka da Madina,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 6 za'a bashi
ladan mala'ikun da suke kewaye da Baitul
ma'amuri kuma dukkan dutse da marmara
zasu nemi agafarta masa laifukansa
▓•Wanda yayi Asham Adare na 7 kamar yariski
Annabi musa ne yataimakeshi akashe Fir'auna
da Hamana,
▓•Wanda yayi adare na 8 Allah zaibashi ladan
daya bawa Annabi Ibrahim,
▓•Wanda yayi adare na 9 Kamar ya bautawa Allah ne irin wadda Annabi Muhd (SAW)
Yayiwa Allah,
▓•Wanda yayi adare na 10 Allah zai'azurtashi Da
Alkhairan duniya da lahira,
Wanda yayi adare na 11 zai fita daga duniya
kamar yadda aka haifeshi,
▓•Wanda yayi adare na 12 zaizo ranar Alkiya
yana Amintacce
▓•Wanda yayi adare na 13 Allah zaigina masa
birni Agidan Aljanna,
▓•Wanda yayi adare na 14 Mala'iku zasuzo suyi
masa shaidar yayi sallar Asham baza aimasa hisabiba,
▓•Wanda yayi adare na 15 Mala'iku zasuyi masa
salati da madauka Al'arshi da kursiyu
▓•Wanda yayi adare na 16 Allah zai rubuta
sunansa daga masu kubuta daga wuta,
▓•Wanda yayi adare na 17 za'a bashi lada kamarna dukkan Annabawa,
▓•Wanda yayi adare na 18 wani mala'ika zai
kiransa yace yakai bawan Allah
Allah ya yarda dakai da mahaifanka
▓•Wanda yayi adare na 19 Allah zaidaga
matsayinsa a Aljanna Firdausi,
▓•Wanda yayi adare na 20 Allah zaibashi ladan
shahidai da salihan bayi
▓•Wanda yayi adare na 21 Allah zaigina masa
daki a Aljanna da haske,
▓•Wanda yayi adare na 22 zaizo ranar Alkiyama
yana Amintacce daga bakin ciki
▓•Wanda yayi adare na 23 Allah zaigina masa
gida a Aljanna,
▓•Wanda yayi adare na 24 za'a amsa Addu'o
insa guda 24,
▓•Wanda yayi adare na 25 za'a dauke masa
azabar kabari,
▓•Wanda yayi adare na 26 za'a taramasa ladan
shekara Arba'in,
▓•Wanda yayi adare na 27 zaifice ranar
Alkiyama Akan siradi kamar walkiya
▓•Wanda yayi adare na
28 za'a daga martabarsa sau dubu
▓•Wanda yayi adare na 29 Allah zaibashi ladan
Aikin hajji dubu karbabbu,
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
Imam Bukhari
👳👳👳👳
Da
🌼🌼
Imam Muslim
👳👳👳👳
Sun rawauto
🌼🌼
Hadisi
🌼🌼🌼
Daga
Abdullahi Dan mas'ud
رضي الله عنه
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Yace:
Manzon Allah S.A.W
Yace:
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
عليكم بصدق فإن الصدق يهدي الي البر وإن البر يهدي الي الجنة ولا يزال الرجل يصدق ويتحر الصدق حتي يكتب عند الله صدي قا
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
(((Ma'ana)))
Ina yi muku umarni da yin gaskiya domin gaskiya tana sa mutum ya zama mai kyawawan hali shi kuma kyan hali yana kai mutum ga shiga
🏰ALJANNA🏰
mutum ba zai gushe ba yana fadar gaskiya da aiki da gaskiya har sai Allah ta'ala yasa an rubuta sunansa cikin masu gaskiya.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Manzon Allah yaci gaba da cewa:
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
واياكم والكذب فإن الكذب يهدي الي الفجور وإن الفجور يهدي الي النار ولا يزال الرجل يكذب ويتحر الكذب حتي يكتب عند الله كذابا.
(((صدق رسول الله)))
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
(((Ma'ana)))
Ina yi muku gargadi ku daina qarya domin qarya tana sa mutum ya zama mai sabon Allah shi kuma Sabon Allah yana kai mutum ga Shiga
🌋WUTA🌋
mutum ba zai gushe ba yana fadar qarya da aiki da qarya har sai Allah yasa an rubuta sunansa cikin jerin maqaryata.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Mazon Allah yayi gaskiya.
🌼🌼🌼🌼🌼 🌼🌼🌼
Allah ya bamu ikon fadar gaskiya da aiki da ita.
👏👏👏👏👏👏👏👏
Allah ya tsaremu da qarya ko wacce iri ce.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
اللهم آمين
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
YADDA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) SUKE FUSKANTAR WATAN RAMADAN
An tambayi Ibn Mas'ud (RA)
Yaya ku Sahabai (RA) kuke fuskantar watan Ramadan? Yaya kuke shiga watan Ramadan??
Sai ya amsa da cewa:
"Babu wani daga cikin mu da zaya fuskanci watan Ramadana ko zai shiga watan Ramadana, face babu daidai kwayar zarrah na hakkin dan uwansa ko jin haushin dan uwansa a cikin zuciyarsa." [Shehun Malami Ibn Rajab Al Hambali ne ya ambaci wannan a littafin sa mai suna, LATA'IFIL MA'ARIF]
Don haka ya ku 'yan uwa, mu yafewa junan mu, mu nemi afuwa a tsakanin mu, domin dacewa da wannan watan mai albarka babu bakin ciki da damuwar wani acikin zukatan mu.
Ni dai dukkan wanda nayi man wani abu ko na sani ko ban sani ba wallahi na yafe masa, na yafe masa, na yafe masa.
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba.
Dan haka ya sa muka ga cewa
yana da kyau mu ware wani lokaci na musamman, Domin fahimtar
da mu yadda ake yin sallar Jana'za.
'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata
ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya.
Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne
kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.
1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha}
2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.
3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji.
4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu.
DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama.
Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.
Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).
Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
*_FATAWOYIN AZUMIN RAMADAN, AKAN KOYARWAR ALQUR'ANI DA SUNNAH, BISA FAHIMTAR MAGABATA NA KWARAI._*
Mawallafi: Sheikh AbdulWahhab Abdallah (Imamu Ahlissunnah)
......... FITOWA TA 01
TAMBAYA TA 1:
WANE IRIN ALBISHIR MANZON ALLAH (S.A.W) YAKE YIWA SAHABBANSA KAFIN AZUMI?
AMSA:
Ya tabbata wajen Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yiwa sahabbanSa bushara zuwan Ramadan yana basu labarin cewar a cikin watan Ramadan ana bude kofofin rahama da kofofin Aljanna, kuma ana rufe Jahannama, sannan ana daure shaidanu, kamar yadda ya zo a hadisin Abi Huraira (Sahihul bukhari, hadisi na 1899).
Haka kuma an ruwaito daga Anas ibn Malik (RA) yace: Watan Ramadan ya shigo sai Manzon Allah (S.A.W) yace: “Hakika wannan wata (na Ramadan) ya halarto mu ku, a cikinsa akwai wani dare wanda ya fi watanni dubu alheri, duk wanda aka haramta ma sa (samun alherin da ke cikinsa) hakika an haramta ma sa alkhairi dukkansa. Kuma babu wanda ake haramtawa alherinsa sai wanda ba shi da rabo.”Sahihul Bukhari: kitabu bada'il khalki da Sunan Ibn Majah: Kitabus Siyam
TAMBAYA TA 2:
YAUSHE NE WATAN RAMADAN YAKE TABBATA?
AMSA:
Watan Ramadan yana tabbata ne da zarar an ga jinjirin wata ko cikar watan Sha'aban kwana talatin. Domin hadisi ya tabbata daga Abi Huraira yace, Manzon Allah (S.A.W) yace: “Ku yi Azumi domin ganin wata, kuma ku sha ruwa domin ganinsa. Idan kuma wata ya faku a gareku to ku cika Sha'aban kwana talatin.”
Bismillahir-rahmanir rahim
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد
Assalamu Alaikum
TUNATARWA
Alamomin Kyakkyawan Karshe
Alama ta farko: Bawa ya mutu jikinsa yana gumi, Manzon Allah (S.A.W) yace; mutuwar mumini ita ce mai gumi a jiki.
Alama ta biyu: Mutum ya mutu a daren Juma'a ko kuma a cikin yinin Juma'a. Manzon Allah (S.A.W) yace; Babu wani musulmi da zai mutu ranar Juma'a ko kuma cikin daren Juma'a har sai Allah ya kare shi daga fitinar kabari.
Alama ta uku: mutum ya furta kalmar shahada kafin ya mutu. Manzon Allah(S.A.W) yace: Duk wanda karshen maganarsa ta kasance "La'ilaha illallah" zai shiga aljanna.
Alama ta hudu: Mutum ya kasance shahidi, shahada ba kawai a kashe mutum a yaki don daukaka kalmar Allah ba, sai manzon Allah (S.A.W) ya ambata cewa mutum ya mutu ta hanyar konewa ko kuma nustewa a cikin ruwa, ko kuma sanadin annoba ko kuma ciwon ciki, ko kuma sanadiyar kare kansa, ko dukiyar sa, ko kuma mutuncinsa to wannan ma ya yi shahada.
Alama ta biyar: Mutum ya mutu yana yin bautar Allah, misali ya kasance yana yin sallah ne ko kuma yana yin azumi ko kuma akan hanyarsa ta don taron addini, Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: idan Allah yana nufin bawan sa da alkairi sai ya tsarkake shi kafin mutuwar sa, suka ce mene ake nufi da tsarkake bawa? Yace; aiki nagari wanda zai shagaltar da shi har mutuwa ta zo masa.
Allah ka kyautata karshen mu, ka sa mu cika da imani. Amin.
ALAMOMIN MACE 'YAR MADIGO (Lesbian)
Daga Ummul-Khairi Suleiman
KUYI HATTARA
* 'YAN MATA
* ZAWARAWA
* MATAN AURE
1- Ki Nisanci Duk Wata Kawa Da Zata Dinga Bayyana Miki Tsaraicinta.
2- Kada Ki Yarda Kawarki Ta Yabaki Ta Fuskar Sha'awa.
3- Ki Guji Kawar Da Zata Dinga Rungume Ki Da Nufin Wasa.
4- Ki Tsoraci Kawar Da Zata Dinga Kunna Miki Fina-Finan 'Yan Madigo (Lesbian).
5- Kada Ki Yarda Kawarki Ta Kama Hannunki Na Tsawon Lokaci Ta Jima Tana Shafa Miki Hannu, Da Sannu Zata Kai Ga Mabudin Sha'awa Shine Ta Fara Shafa Miki Kirjinki.
6- Ki Nisanci Kawar Da Zata Dinga Yawan Shafa Gashin Kanki.
7- Ki Kauracewa Kawar Da Za ta dinga Yawan Kwanciya Ajikinki Batare da Wani Dalili Ba.
8- Ki Kyamaci Kawar Da Akodayaushe Zata Dinga Son Ta dinga Ganin Jikin ki, Kamar Kirjin Ki Da Bayan Ki Zuwa Kasan Marar ki.
9- Ki Rabu Da Kawar Da Za Ta Dinga Yawan Yi Miki Kyaututtuka Masu Tsada Ba Bisa Dalili Ba.
10- Ki Bar Kawar Da Take Yawan Jan Ki Zuwa Gidan Kawayenta Wa'yanda Bakisan Su Ba Kuma Basu Da Mazaje Koma Suna Da Mazajen, Amma Wa'yanda Ki Ka Ga Suna Yawan Kulewa Cikin Uwar Daka Ko Suke Yawan Tafawa Suna Rungumar Juna, Ko Kwanciya Akan Cinyar Juna Ko Suke Yawan Cire Tufafinsu Agaban Juna Ko Wanka Tare.
11- Ki Kyamaci Kawar Da Bata Da Hira Sai Hirar Mace 'Yar Uwar ta.
12- Ki Guji Kawar Da Ba Ta Son Yawan Mu'amala Da Maza Amatsayin Samari Ko Masoya, Amma Ta fi Mu'amala Da Mace 'Yar Uwarta Matuka Ainun.
13- Ki Kauracewa Kawar Da Take Da Sha'awar Kallon Fina-Finan Batsa Musamman Irin Na Mace Da Mace (Lesbian).
14- Ki Fita Sha'anin Kawar Da Ake Yada Jita-Jitan Tana Madigo (Lesbian).
15- Ki Rabu Da Kawar Da Take Mu'amala Da Kawaye Masu Madigo (Lesbian) Koda Ita Ba ta Yi Domin Kallon Mai Yi Akeyi Mata Kema Haka Za'a Yi Miki Kallo.
16- Ki Yakice Kawar Da Take Zaman Kanta Agidan Da Ta Kama Take Haya Kuma Mata Ke Taruwa A Gidanta.
17- Ki Fita Sha'anin Kawar Da Ba Ta Jin Kunyar Cewa Aga-Aga, Na Kirji Ko Baya Ko Kasan Marar Juna.
18- Ki Hakura Da Kawar Da 'Yan Madigo Ke Burgeta
IYA ZAMA DA MIJI DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM.
1-Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAH kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda kika yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.
5- Kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki Dariya 😁.
11- Kada ki zama mai rainuwa acikin duk abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.
13- Ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayen mijinki da 'Yan Uwansa da kuma Abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita Unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki acikin abinda ya baki.
19- Ki kiyaye abinda mijinki yafi so.
20- Ki kiyaye abinda mijinki yafi sonci da safe, rana, da kuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.
29- Lallai kiyi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.
30- Kiyi shiru a du
*MINENE HASSADA, KUMA YA AKE HASSADA, KUMA SU WANENE MASU YIN HASSADA.*
1- Hassada wani mugun ciwo ne da ke Nukurkusar mai yinta a cikin zuciyarsa shi kadai.
Hassada shine Jin Zafi, Daci, ko Bacin Rai a yayin da kaga wani Dan'uwanka, Makwabci, Aboki ko ma wani kawai da ka sani a duniya ya samu daukaka, ko wani iri.
Hassada kala uku ce (3)
A- Akwai jin kyashi, shine mutum yaji a zuciyarsa don me wani zai fishi wani abu a rayuwa. Kudi, Mulki ko kuma Baiwa ko Mukami.
B- Mutum yaji shi bayason kowa ya samu wani abun alkhairi ko karuwa sai shi kadai.
C- Wannan shine yafi kowanne muni, wato mutum yaji cewa idan dai shi bazai samu abu ba to gara kar kowa ya samu. Irinsu sune suke yin a fasa kowa ya rasa
2- Mutane da yawa suna fadawa cikin aikata Hassada ba tare da sun ankara ba misali:
A- Yawan yin magana akan ci gaban wani ko wata e.g 1- oh su wane an haye, sai kace da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa basu wuce kala biyar ba.
2- Mutum ya rinka gamin wane an samu shiga, ji wai yanzu shine kaza, sai kace ba tare aka daukemu aiki ba.
3- Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iyayi wai shi a dole ga mai kwakwalwa
*YA ZA'AYI MUTUM YA GANE CIWON HASSADA YA FARA SHIGARSA*
Yanda mutum zai gane idan ya fara koyon Hassada shine:
A- Yawan damuwa da al'amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafeka ba ta ko wani hanya.
B- Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki, idan kaji mummunar labari game da wani kaji dadi a ranka ko ma kayi dariya ko shewa, idan kuma kaji labari mai dadi game da mutum sai kaji ranka ya baci, ka kasa yi masa fatan alkhairi, ka fara jin tsoron kar ya wuceka a level na rayuwa. Sai ka fara kokarin kai sukarsa a wajen abokan arzikinsa, ko kokarin fadin miyagun maganganu game dashi, ko kuma fadin kalamai na batanci game dashi. Musamman ma idan ba'a tambayeka labarinsa ba, shine Hassada
4- lllolin Hassada suna da yawa amma ga kadan daga ciki:-
1- Hassada tana cinye kyawawan ayyukan mai yinta kamar
*_NAMIJI:_*
Wata rana a makarantar manya malamin koyar da sanin halayyar dan Adam *(Psychology),*
Malam yace a cikinku wa zai fito gaban allo a fara da Shi?
Sai wata daliba Salma ta fito, Sai malam yace ta dauki alli *(chalk)* ta rubuta sunan mutane 30 masu muhimmanci a rayuwarta, Salma ta rubuta dangi, kawaye, abokan karatu da makwaftanta.
Sai malam yace ta goge 3 wadanda basu da muhimmanci sosai a wajenta, Salma ta goge suna 3 na abokan karatunta.
Sai malam yace ta kara goge 5 marasa muhimmanci, Salma ta goge makwaftanta, Malam yayi ta umartarta tana gogewa har sai da ya rage sunaye 4 ka dai sune:-
1. Babarta
2. Babanta
3. Mijinta
4. Ɗanta 1 data haifa.
Gaba dayan dalibai sai suka natsu sun gane cewa wannan ba wasa bane kamar yanda Malam ya fada da farko, yazo musu ne da wani darasi mai muhimmanci.
To! Sai malam ya kalli Salma yace ta kara goge 2 daga sunayen nan da suka rage, wannan zabin fa yana da wuya, Salma tayi jimmm! Hannunta yana rawa ba'a son ranta ba idonta ya cika da kwalla ta goge sunan Babarta da Babanta.
Sai malam yace ta kara goge 1, Sai Salma ta saka kuka ta goge sunan Ɗanta 1 Tilo Sai malam yace ta koma wajenta ta zauna.
Bayan wani ɗan lokaci sai malam yayi tambaya, yace:- " me yasa ta bar mijinta"?
Yace: Iyaye fa sune suka kawo ki duniya suka raine ki har kika girma, Ɗanki kuma ke kika yi cikinsa kika sha wahalar laulayin cikin kika haife shi, kika raine shi, kuma da Iyaye da Da ba zaki iya sake wadansu ba, amma miji ko yaushe zaki iya chanja wani.
Aji akayi shiru ana jiran amsar Salma, Salma cikin nutsuwa da sanyin murya tace:-
"Wata rana iyayena ina tare dasu suka dauke ni suka kaini gidan miji, idan na kawo musu ziyara sai su tambayeni, "lafiya"?
Idan yayi min laifi na taho gida sai su kira shi suyi ta bashi hakuri, suce na tashi na koma gidansa".
Ɗa na kuma wata rana zai barni idan ya girma zai mai da hankali kan sana'arsa da hidimar iyalinsa, Mut
🔷 YI MURMUSHI
Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji dadi. Yi murmushi idan ka ga mai kin ka, zai ji tsoro. Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi da-na-sani. Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Murmushi karfi ne ga namiji, kwarjini ne ga fuskar macce.
🔷 Makaho idan idonsa ya bude karya sandarsa yake yi. Haka dan Adam yake da saurin manta alheri da kin tuna baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa don Allah. Idan kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki.
🔷Wawa shi ke fadin abin da zai aikata, mai kuri shi ke bayyana abinda ya aikata. mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.
Gishiri da Sugar kalarsu daya ce. Banbancinsu yana bayyana ne idan aka dandana. Haka mutane su ke, sai an gwada akan san na kwarai.
🔷 Zama da mutanen kirki yana karar da kai ababe guda shida: Son Allah, da bin Allah, da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da barin girman kai.
🔷 Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su. Akwai kuma ma su kin ka duk yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da ya karbe shi.
🔷 Idan namiji bai ji dadin aure ba zai yi tunanin kara mata don ya samu jin dadi. Idan kuma ya ji dadi zai yi tunanin karawa don ya kara jin dadi. Mata ku yi hakuri karin aure dabi'a ce a cikin mazajenku.
*
*
♦ Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne duk inda zai zauna sai ya rinka kame-kame. Mai gaskiya a natse yake zamansa.
🔷
🔷
👌 Ana gane mumini ne a wurare uku: Idan ya samu ya gode ma Allah, idan ya rasa ya koka ma Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ma Allah
🔴 Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani.
🔴 Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah adukkan lamuransa.
🔴 Murna da annashuwa sun tabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun.
🔴 Wadatar zuciya ta tabbata ga mutumin da kullum yake gode
Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:
1. Tsayuwa abisa tafarkin Allah da Manzonsa (saww) da gaskiya.
2. Cikakken jin tsoron Allah afili da boye.
3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar.
4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe.
5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki. Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba’irar
6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA alahira.
7. Tunowa Shaitan da kuma kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam.
8. Gujewa kaɗaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba.
9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma rubuce-rubuce ko wakoki da hotunan batsa.
10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.
11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita:
‘diyar wani ce, Qanwar wani ce, Yayar wani ce. Watarana kuma zata zama Uwar wani. To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka, ko Qanwarka, ko yayarka, ko ‘yar da ka haifa.
12. Addu’ar neman tsari daga Miyagun ayyuka, da mummunan tunani.
اللهم إني أعوذ بك من منكرة الأخلاق والأفعال والأهواء
“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal Af’aali wal Ahwa’I.”
13. Daga karshe kuma ka tuna cewa zaka iya kamuwa da wata mummunar chutar da zata zamanto ajalinka.. Kuma koda baka kamu da Chutar zahiri ba, Wallahi in dai ka aikata zina sai chutar Munafurci ko Fasikanci ta shiga zuciyarka.
14. Tuno ranar da za’a tsayar da kai agaban Allah, a ranar taron Alqiyamah.. Ga iyayenka da Kakanninka har Jikokinka da jikokin-Jikokin
Fatanmu shine Allah shi kiyayemu baki daya daga wannan mummunan aiki. Wadanda kuma shaitan ya riga ya rudesu, to Allah yasa wannan rubutun ya zama dalilin tubansu.
1- shin kun san abubuwan da kuke kallo yana daga cikin manyan laifuka (kaba'ir ).
2- shin kun san abinda kuke kallo yana gadar da kaskanci da kuma rauni ta kowane bangare.
3- shin kun san abinda kuke kallo yana kawo raunin idanu da kwakwalwa, da yawan mantuwa, abu kankani sai kamanta.
4- shin kun san wannan kallon yana sa mutum ya fadi a idon Allah.
5- shin kun san wannan kallon yana hana mutum samun ilimi ko mantashi.
6- shin kun san wannan kallon yana hanaka /ki samun jin dadin rayuwar aure mai inganci da mijinki ko matarka, kuma duk da kuna son juna.
7- shin kun san cewa zaku iya mutuwa a cikin wannan yanayin ( mummunar cikawa).
8- shin kun san jikinku zai gaya muku ko badade ko bajima in baku tuba ba.
9- shin kun san duk abinda kuka yada kuna da zunubi, inma yai sanadiyyar lalacewar wani kuna da zunubin koda kuna kwance akabari har izuwa kiyama.
10- shin kun san cewa duk wanda yabar wani abu domin Allah, Allah zai musanya masa da abinda yafishi alkhairi.
11- shin kun san cewa Allah yana farin ciki sosai da tuban bawansa.
12- shin kun san cewa Allah zai wadataku da falalarsa idan kuka kame kawunanku gada haramun.
13- shin kun cewa sha'awar yan mintina ta haramun tana dai dai da azabar shekaru.
*YAN UWA MUSULMI KU TAIMAKI YAN UWAMMU WAJEN ISAR MUSU DA SAKON NAN KO ALLAH ZAI SHIRYASU TA DALILINKU KUSAMU LADANSU* .
There is high probability that you will block me immediately after reading my message
Pls extend my message to the group, thanks
🔜 ANNABI SAW YANA CEWA:-
"Mutum yana tafiya ne akan dabi'ar Abokin sa. Don haka kowa a cikinku ya duba yaga da wa ya kamata yayi abota".
🔜 Sayyadina Umar Allah ya kara masa yarda yana
cewa: "Babu wata ni'ima bayan ni'imar musulunci data wuce abaka aboki nagari. Don haka
duk wanda ya dace da aboki nagari a cikin ku yayi riko dashi Qaaam".
🔜 Imamul-shafi'I Allah ya jikan sa da rahama yana cewa:-
"In Allah ya azurta ka da aboki nagari to ka rike shi Gam da hannunka, Domin samun Aboki nagari abune me wahalar gaske, kuma rasashi abu ne mai saukin gaske".
🔜 Imam Hasanul Basari yana cewa:-
"Muna son Abokan mu nagari fiye da yanda muke son Iyalanmu da 'ya'yan mu. Domin
iyalan mu da 'ya'yan mu suna tuna mana Duniya.
Shi kuma Aboki Nagari yana tuna mana Lahira ne, Yace yana daga Siffar Aboki nagari ya fifita
bukatarka akan tasa bukatar".
🔜 Luqmanul Hakim yake
cewa da 'Dansa.Ya kai 'Dana, farkon Abunda zaka tsururuta arayuwar ka bayan imani da Allah
shi ne Aboki nagari. Domin Aboki na gari tamkar bishiya ce, in ka zauna akasanta, sai inuwarta ta lullubeka gabarin Rana. In ka tsinki Dan itacenta ta kosar dakai daga yunwa. In har bata anfanar da kai
ba kuma bazata taba cutar da kai ba. Allah ka bani Aboki nagari, kasa in zama nagari da kuma sauran al'ummar musulmai bakidaya.
🔜 Duk aboki nagari zai so wannan sako zuwa
ga abokinsa, don ya samu falalar abin da zai zama alkhairi agareshi. da sauran Musulmi...
GODIYA GA ABOKAINA NAGARI!
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta...
(Tahrim: 6).
Annabi (SAW) yana cewa a wani hadisi:
" Dukkanninku masu kiwone kuma ababan tambayane dangane da kiwon da aka baku, shugaba me kiwone (dangane ga talakawansa) kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi, mutum me kiwone dangane ga iyalinsa kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi."
Bukhari da Muslim.
Akwai wasu hanyoyi wadanda idan muka bisu zasu taimaka mana da yardar Allah wajen Tarbiyyar 'yayanmu, daga cikinsu akwai:
1. MU ZABAWA 'YA'YANMU UWA TA GARI.
Auren mace tagari muhimmin lamarine dake taimakawa wajen tarbiyyar 'ya'ya, domin uwa ita ce makaranta ta farko da yaro ke daukar darasi a cikinta, kuma halaye da dabi'un uwa suna tasiri matuka ga 'ya'yanta, sabida hakane shari'a ta kwadaitar damu wajen auren mace tagari ma'abociyar addini.
Annabi (SAW) yana cewa: " Ana auren mace sabida abubuwa guda 4; dukiyarta, da kyawunta, da daukakarta, da addininta. ka zabi ma'abociyar addini, sai hannunka yayi albarka."
Bukhari da Muslim.
Abu ne mai muhimmanci ga wanda yake da niyyar yin aure ya dage da addu'a akan Allah ya azurtashi da samun mace tagari, kuma yayi "istikhara" wato neman shawarar (zabin) Allah kafin auren, ya kuma nemi shawarar bayin Allah mutanen kirki, sannan yayi kokari wajen yin bincike akan nagartar yarinyar da kuma iyayenta, ya kuma fawwala al'amuransa zuwa ga Allah SWT.
Sannan kuma ya zama wajibi abi hanyoyin da Shari'a ta tsara wajen neman aure, kuma a nisanci sabawa Allah da sunan murna ko farinciki a yayin aure, wannan zai sa Allah Ta'ala ya sanya Albarka a cikin auren da kuma zuriyar da za a samu ta dalilin wannan auren.
2. ROKON ALLAH YA BAKA ZURRIYYA TA GARI.
Wannan dabi'ace ta Annabawa da Manzanni da bayin Allah salihai. Kamar yadda Allah ya bamu labari a kissar Annabi Zakariyya (AS), yake cewa: " A yayin nan Annabi Zakariyya ya roki Ubangijinsa, yace: ya Ubangiji ka bani kyauta daga gareka ta zuriyya tsarkakakkiya, hakika kai mai amsar addu'ane."
(Ali-Imran: 38)
A wata ayar kuma Allah ya bamu labarin salihan bayinsa, daga cikin siffofinsu suna addu'ar Allah ya basu mata da 'ya'ya nagari, yake cewa:
" Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu ka bamu kyauta daga matayenmu da zuriyyarmu abinda idanuwanmu za suyi sanyi dasu, kuma ka sanyamu mu zama shugabanni ga masu tsoron Allah."
(Al-furqan: 74)
Wannan ya nuna mana muhimmancin addu'a da rokon Allah wajen samun 'ya'ya nagari kasancewar har Annabawan Allah da Salihai sun yi irin wannan addu'ar.
Allah ya bamu ikon yiwa 'ya'yayenmu tarbiyya da ladabdar dasu bisa koyarwar Kur'ani da Sunnah, ameen.
Zamu cigaba InshaAllah.
TSUMA ZUCIYAR MASU IMANI
===============
Akwai Wata Budurwa da ALLAH Madaukakin
Sarki Ya 'Dauki Ranta, Aka Kaita Maqabarta
Aka Binneta.
.
Bayan An Dawo Daga Makabarta Sai Daya
daga Cikin Mutanen Da Suka Je Binnenta
Akwai Wani Mutum Ashe Yacire Zoben
Hannunsa Ya Sanya a Aljihun Gaban Rigarsa.
.
Sai Ya Je Yasami Limamin Unguwarsu Yace
Masa:
Mallam Ka Ji Abinda Yafaru Na Bar Zobe Na a
Gaban Aljihuna Kuma Ina Tunanin Yafada
Kabarin Nan, Kuma An Binne Dashi aciki.
.
Yanzu Yaya Za'ayi ???
Sai Malamin Yaje Yasami Iyayen Yarinyar
Yace Musu Ga Abinda Ke Faruwa Kuma Babu
Kyau a Binne Mutum Da Wani Kayan Ado.
.
Nan Take Aka Amince Akan za'aje a Ciro
Zoben.
.
Zuwansu Keda Wuya Suna Bude Ramin, Sai
Sukaga Wasu Bakaken Kunami Dayawa a
Cikin
Ramin Suna Harbinta.
.
Limamin Daya Dawo Sai Yafadawa Iyayen
yarinyar Abinda yake Faruwa.
.
Don Allah Idan ku Karanta kudinga yin LIKE
da Comment BY: (c) M. Kabiru Muhammad,
ko kuma kuyi Share dinsa domin 'yan
uwanku su amfana..
.
Ya Tambaye Su Shin Akwai Wani Hali Da Take
Dashi Mara Kyau Ne ???
Sai suka Ce A'a.
.
Aka Tambayi Qawayenta Suma Sukace A'a.
Sai Malamin Ya Tambayi Mahaifiyarta, Shin
Tana Sallah Kuwa ???
.
Sai Tace Eh! Tanayi Amma Matsalarta 'Daya
Itace;
Idan Tana KALLO Ko CHATTING Ba Tayin Sallar
Akan Lokaci harsai lokacinta yakusan fita.
.
Sai Malamin Yace:
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN"
.
To Wannan Kunamin Sunayi Mata Azabane
Saboda Rashin Sallar Da takeyi Akan Lokaci.
.
Don ALLAH Mu Qara Kula Da Sallah Domin
Itace Za'a Farayi Mana Screening Ranar
Qiyama.
.
Mudinga yinta Akan Lokaci, kada kallo ko
chatting yadinga yaudararmu.
.
Musami Nutsuwa Yayin Da muke yin ita Sallar
kada mudinga yin gaggawa.
.
Muyi Sallah Kamar Sallar yin Bankwana da
duniya.
A gaskiya kam yanzu muna cikin matsala.
.
ALLAH Ya Yafe Mana Kura-Kurenmu
Manyansu Da Kananunsu.,,
STATUS📱
1●Shin ka na tuna cewa duk abin da ka saka a Status/Story dinka ka na da naka kasafin na lada ko zunubi?? Awanni 24 za su yi, amma suna iya zama maka zunubi mai gudana ko lada mai gudana, ka za6i abin da ka ke son gani cikin littafin ayyukanka.
2●Haram yana nan a matsayinsa na haram ko da a STATUS ne! Kowane status sai ka bude ka kalla, ka kalli tsiraici da sunan status! ka kalli abin da bai halatta gareka ba da hujjan cewa ai status ne kuma su suka saka!! To zunubinsu na nan kai ma na ka yana nan!!!
3●Wasu sun mayar da status gurin tallata kansu da rayuwar da suke ciki, me suka ci, me su ka sha, suturarsu, gidansu, motar da suke hawa, nuna ma duniya irin rayuwa ta alfarma da suke ciki da sauransu ba dare ba rana! lallai kambun baka gaskiya ne idan baka sani ba!!!
4●Wasu kuma sun mayar da status gurin bayyana damuwoyinsu, koke koke da korafe korafe, habaice habaice da yada magana, bakanta ma juna ko kokarin bakanta ma wani ko sanyashi cikin damuwa! shin wannan ita ce kadai hanyar magance matsaloli a gurinka? wannan ai kauyanci ne da wauta!!!
5●Kai ne saka izgilanci ga Addinin Allah da musulmai da sunan ai comedy/
6●Shin abin da za ka saka a Status dinka ABU NE DA ALLAH YA YARDA DASHI? SHIN AKWAI WATA FA'IDA A SAKAWAN? Wani a nan status dinka zai dauka ya a jiye a wayarsa ko kuma ya cigaba da yadawa mai kyau ne ko marar kyau! Ka sani za ka dauki zunubinka da zunubin adadin da suka kalla ko suka yada!
7●Wani ba ya kishin ya daura iyalinsa a status ta ca6a ado, abokanshi su gani kowa ma ya gani! ba ya jin komai bare yayi kishinta! ita ma bakauyar yin hakan shi ta dauka matsayin soyayya! To ga sakon Manzon Allah(SAW) gareka: Allah ba zai yi dubi ga marar kishin iyalinsa ba ranar Alkiyama!!!
SUNNONIN DA AKA MANTA DA SU
*1-Karkabe Shimfida kafin kwanciya barci*
Yana daga cikin sunnar Manzon Allah ﷺ karkabe shimfida da gyarata kafin kwanciya barci,amma mafi yawan mutane mun manta da wannan sunnah bamu aiki da su.
Daga Abi Hurairata رضي الله عنه,Yace;Manzon
*(Idan Dayanku yazo zuwa ga shimfadarsa,to yayi ruku da cikin mafiyansa sai ya
karbabe shimfidarsa,kum
@رواه مسلم.
*2-Idan kun gaisa da mutum kada kayi sauki janye hannunka*
Yana daga cikin Ladabi bayan sallama hada hannuwan dama na juna dan gaiswa.
Yana cikin ladabi karami shi zai farawa babba sallama kuma babba shi zai fara baima karami hannu.
Daga Anas رضي الله عن yana cewa;
*"Manzon Allah ﷺ idan ya gaisa da hannunsa
da wani mutum,baya cire hannunsa,har sai dai mutumin ya fara cire hannunsa)*
@صحَّحه الألباني.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Babu wasu musulmai guda biyu da zasu hadu da junansa,su hada hannuwansu guda
biyu suna gaisawa,face Allah ya gafarta masu kafin su raba hannayansu)*.
@صححه الألباني.
*3-Yawaita addua da rokon Allah a tahiyar karshe kafin sallama*
Akwai gurare guda biyu mafi mahimmanci yin addua acikinsu a cikin sallah,Cikin sujada da bayan Tahiyar karshe.babu wani guri da Manzon Allah yafi yin Addua acikin sallah kamarsu.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Idan Dayanku yayi zaman Tahiya acikin Sallah to yace*
"التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ .... ...............
Har zuwa karshen Tahiya,Sannan ya zabi adduar da yake so ya roki Allah"a
wata riwayar kuma ya zabi adduar da yake so ya roki Allah anan".
@رواه البخاري ومسلم.
*4-Hani akan bada labarin duk abinda kaji ko aka fada maka*
Manzon Allah ﷺ yana cewa-
*(Ya ishi mutum cikar laifi,mutum ya riqa bada labarin dukkan abinda yaji ko
aka bashi labari)*
@رواه مسلم.
*5-Yin adduar sauka wani guri ko gurin zama ko sabon gida da dai sauran guraren bakonta*
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Dukkan wanda ya sauka a wani masauki,Sannan yace*
"أعوذ بكلم
DUK LOKACIN DA ZAKA AIKATA SA'BON ALLAH, ZAI YI KYAU KA TUNO DA ABUBUWAN NAN GUDA BIYAR :
1. Tuno da girman Allahn da zaka sa'ba ma.
2. Tuno cewa yana kallon duk abinda kakeyi.
3.Tuno cewa Mala'iku suna nan tare dakai suna rubuta dukkan abinda kakeyi. (Sune shaidu akanka).
4. Tuno da mutuwarka da kwanciyar Qabarinka.
5. Tuno da ranar hisabi, Ranar da zaka amsa laifukanka agaban Miliyoyin halittu.
*MAFIYA RINJAYEN MASU SHIGA ALJANNAH.*
Annabi (s.a.w) ya ce:
"Mafiya yawa rinjayen masu shiga Aljannah su ne masu tsananin kiyaye
dokokin Allah (S.W.T), sannan kuma masu kyawawan Ɗabi‘u da halaye nagari."
*KIYAYE DOKOKIN ALLAH:*
Allah Madaukakin Sarki Ya fada a cikin suratu Maryam aya ta 63 cewa:
(تِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَنْ كَانَ تَقِيًّا)
Ma'ana:
"Wannan it ace Aljannah wadda muka yi tanadin ta ga bayina amma masu
kiyaye dokokin Allah, masu jin tsoron Allah."
*KYAWAWAN ƊABI‘U:*
Abdullahi bn Amru bn Ass (R.A) ya ce:
Annabin Rahma masoyina (s.a.w) ya ce:
"Mafi ɗaukaka a wajen Allah daga cikin ku (mutane) su ne wadanda suka fi
kowa kyawun hali.
'Ƴan uwa ga *KEYS* din shiga Aljannah amma fa game so, don Aljannah ba ta rago ba ce ko malalaci, don haka mu dage.
Ya Allah Ka tausaya mana Ka gafarta mana zunubanmu da kura-kurenmu baki daya saboda isar Shugaba Annabin Rahama Annabi Muhammadu (s.a.w). Amin.
*SAƘO ZUWA GA IYAYE!*
Haƙiƙa al'amarin tarbiyyar yara musamman ƴaƴa mata, abu ne mai muhimmanci matuƙa, wanda da yawa a wannan lokacin mafi yawan iyaye suka yi sakaci ƙwarai a kan sa.
Za ka samu yarinya ta fara girma ta kai shekara sha biyar 15, amma iyaye ba su damu da ina ta ke zuwa ba, yaushe ta ke dawowa makaranta ; da ƙawayen da ta ke mu'amala da su.
Saboda haka, yana da kyau iyaye sun sanya idanu a kan ƴaƴansu musamman ƴaƴa mata. Akwai wasu shawarwari masu tsada da na tsara zan baiwa iyaye, domin katange ƴaƴansu daga maɓarnata:
1. Sanin waɗanda ƴaƴanku suke mu'amala da su a fili da kuma boƴe?
2. Sanya ido game da suturar da ƴar ku/ɗan ku suke sanyawa musamman lokacin da
za su fita gida.
3. Hanasu kallon wasu tashoshin da ake yaɗa ɓarna da lalata tarbiyya.
4. Dakatar da ita daga fita gun saurayi da sunan soyayya, idan ba aurenta zai
yi ba.
5. Sanya ido da bincike a cikin wayoyinsu, da kuma suwa suke mu'amala da su a
wayar.
6. Lura da lokacin da suke kwanciya barci da daddare.
7. Sanyasu suyi muraji'ar abin da aka musu a makaranta.
8. Ƙoƙarin zama da su domin jin matsalolinsu, da kuma shawarwari.
9. Ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninku da malamansu na boko da Islamiyyah.
10. Bayan kunyi iya bakin ƙoƙarinku sai ku biye da yi musu addu'a, Allah ya
shiryar muku da su hanya madaidaiciya.
MU KOMA GA ALLAH
1. Da zarar ka tashi za ka bude data don ganin sakon duniya. Amma Sallar Asuba cikin jam'i ta gagare ka. Mu koma ga Allah.
2. Kana iya minti 90 cikin kallon ball idan an yi rashin sa'a a tafi karin lokaci. Amma Sallar farilla ta gagare ka cikin Jam'i don kallon ball. Mu koma ga Allah.
3. Kana iya haddace 'handout' don ganin ka ci jarrabawar duniya ta dan Adam, Amma baka iya haddace surah daya ta Alqur'ani don guzurin lahira. Mu koma ga Allah.
4. Kana da halin kyautar mota don neman suna, Amma baka da hannun kyautatawa gajiyayyu da marayu don neman lahirarka. Mu koma ga Allah.
5. Kana da lokacin musu, Amma baka da lokacin yi wa Annabi salati. Mu koma ga Allah.
6. Kana da kudin sayan mota da sutura ta alfarma, Amma sayan tsinsiya ta sharar dakin Allah ta gagare ka. Mu koma ga Allah.
7. Kana da lokacin karanta jarida, Amma baka da lokacin karanta maganar mahaliccinka. Mu koma ga Allah.
8. Kana iya kuka don asarar abun duniya, Amma tuna azabar kabari ya gagare ka. Mu koma ga Allah.
9. Kana da lokacin kallon 'season film', Amma vaka da lokacin sada zumunci tagagare ka, don neman haye siradi. Mu koma ga Allah.
10. Kana da lokacin zuwa ko ina ne don neman abun duniya, Amma neman ilimin sanin mahaliccinka ya gagare ka. Mu koma ga Allah.
11. Kai ne jagora wajen zalunci da cin dukiyar al'umma, Amma kiran sallah (Ladanci) abun kunya ne a gareka. Mu koma ga Allah.
12. Ka zabi rayuwar duniya fiye da ta lahira, bayan ba ka san yaushe za ka mutu ba. Mu koma ga Allah.
HADISI
Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce; {LALLAI MUMINI DA
YAYI HA'KURI AKAN CUTARWAR MUTANE YAFI ALKHAIRI FIYE DA WANDA BAI YI HA'KURI
AKAN CUTARWAR SU BA.}*_
°
[Sahihul Bukhari; 388, Tirmidhi; 2507, Ibn Majah; 4032]
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa mumini mai hakuri bisa cutarwar mutane yafi
wanda ba ya hakuri alkhairi. Allaahu a'alam._
ABUBUWA GUDA 20 NA GYARAN ZUCIYA
1-Yawaita karantun alqurani mai girma,da Kokarin sani ma'anoninsa da kokarin yin zikirai da suka tabbata daga Annabi Muhammad ﷺ.da kuma bin sunnar Manzon Allah ﷺ.
2-Rage cikin abinci da yawa,ka riqa cin abinci iya buqata.
3-Yawan sallah dare da yawaita ibada cikin dare lokacin da mutane suke barci.
4-Rokon Allah ya gyara maka zuciyarka tare da yin adduar alokacin amsa addua da guraren amsa addua.
5-Zama tare da mutanan kirki dan su tunanatar dakai Allah da jin nasiha da wa'azi daga wajansu da kuma yin koyi da kyawawan halayensu.
6-Yawaita hiru idan zakayi magana kuma ka fara yin tunanin matsayin maganar kafin ka furtata.
7-Nisantar sabon Allah da nisantar masu sabon Allah da nisantar zama tare da su.
8-Yin kokarin cin Halal da amfani da dukiyar halalal da nisantar cin haramun da shubuha.
9-Ka nisanci abubuwan kyama da abubuwa masu halakarwa kamar yi da mutane da shirka da sabawa mahaifa da sauran miyagun halaye.
10-Ka yawaita aiyukan nafila bayan ka sauke farilla,da kuma yawaita nafila kala kala.
11-Yawaita Azumin nafila da bibiyar aikin hajji da Umara.
12-Yiwa kanka hisabi lokacin kwanciyar barci akowane rana da yin hisabin rayuwa gaba daya.
13-Ka sani lallai Allah yana sane kuma yana kallonka duk lokacin da zakayi wani aiki.
14-Kyautatawa mahaifa tare da yi masu biyayya.
15-Yawaita zuwa ziyara maqabarta dan tuna lahira.
16-Yin sadaka ga marayu da masu karamin karfin da gajiyayyu,musammman ma alokacin kuncin rayuwa.
17-Ziyarar duba marar lafiya dan yi masa addua da daukar darasi.
18-Kiyaye Salloli akan lokacinsu kuma acikin jam'i.
19-Yin tunani acikin halittun Allah madaukakin sarki.
20-Nisantar zalumci
Allah ne mafi sani.
HADIS
*Manzon Allaah(SAW)* *ya ce; {AN NUNAMIN NASARORIN DA ZA'A BU'DE MA
AL'UMMATA A BAYANA, SAI HAKAN YA SANI MURNA!.}*_
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa muminai zasu rin'ka cin nasara sai dai
jarabawa na iya zuwa musu lokaci zuwa lokaci. Allaahu a'alam.
MANZAN ALLAH TSIRA DA AMINCHIN ALLAH SU QARA TABBATA
AGARESA YACE:
*
Zamani zai Zo Al'ummata zasu zamo Masu tsananin nuna soyuwa ga abubuwa 5 su
kuma manta da abubuwa biyar.
*
¹' Zasu so """Duniya""" sannan su manta da """lahira"""
*
²' Zasu so """Dukiya""" Sannan su manta da
"""Hisabi"""
*
³' Zasu so """Halitta""" Sannan su manta da
"""Mai-halittar"""
*
4' Zasu so """Benaye""" Sannan su Manta da
"""Kabari"""
*
5' Zasu so """Sabo""" Sannan su manta da
"""Tuba"""
*
Ya Allah Kayi mana gafara, Kasa mu zama Masu yawan Tuba a gareka.
*
Kayi kokarin yada wannan tunatarwa ga Yan uwa Musulmi, ta hanyar Share.
*
Allah Ya bamu Ikon yin ameeen
SAMUN GAFARAR ZUNUBAI LOKACIN KWANCIYA BARCI
Shin kana son Allah ya gafarta maka zunubanka baki daya kafin ka kwantabarci??
Idan kana son haka to ka kiyaye abinda Manzon Allah ﷺ yace a fada dan samun hakan lokacin da ka kazo kwanta barci.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Wanda ya fada lokacin da yaje kwanciya barcinsa yace;
"لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير
لا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم سبحان الله والحمد لله ولا إله إلا الله
والله أكبر"
An gafarta masa zunubansa ko kusakuransa,ko da sunkai yawan kumfar teku).
@صححه الألباني.
Yana daga cikin ladubban kwanciya barci a sunnar Annabi ﷺ
-Yin Alwala irin alwala ta sallah
-Gyara shimfida
-Karanta suratul Fatiha
-Karanta Quhuwa da faqai da nasi sau uku uku,sannan ka kofa a hannunka sai ka
shafi abinda ya saukaka ajikinka,zakayi hakan sau ukku
-Karanta suratul kafirun
-Karanta Ayatul Kursiyyu
-Karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul Baqra(wato Amanar Rasul....).
-Yiwa kanka Hisabi da yin gafara da yan uwanka dan kada ka kwanta da fishi ko
haushin wani.
-Yin addu'o'in kwanciya barci
-Fadar SUBHANALLAH sau 33
-Fadar WALHAMDU LILLAH sau 33
-Fadar WALLAHU AKBAR sau 34,bayan ka kwanta barci
-Kwanciya a bangaran jiki na dama
-Kashi wuta da dukkan wani haske
-Rufe mazuban ruwa ko abinda da kofofi tare da fadar BISMILLAH lokacin rufewa
-Sanya niyyar tashi sallar Assuba
-Yin sallar wutiri lokacin kwanciya.
Allah ne mafi sani
Allah ka bamu ikon koyi da Manzon Allah ﷺ a dukkan ibadarmu.
ANA GANE MUMINI NE A WURARE UKU:
Idan ya samu ya gode ma Allah, idan ya rasa ya koka ga Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ga Allah.
🔴 Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani.
🔴 Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah adukkan lamuransa.
🔴 Murna da annashuwa sun tabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun.
🔴 Wadatar zuciya ta tabbata ga mutumin da kullum yake gode ma Allah akan kowacce baiwar da yayi masa komai kankantarta, kuma ba ya kaiwa Qarar Ubangiji awajen halittunsa.
🔴 Cikar buri ya tabbata ga Mutumin da kwadayin gamuwarsa da Allah a Lahira ya hanashi dogon burin Zaman duniya.
🔴 'Dandanon zakin imani ya tabbata ga mutumin da ya fifita Son Allah da Manzonsa akan komai na duniya da lahira.
🔴 Lada mai yawa ya tabbata ga Mutumin da yaji kalmar gaskiya kuma ya isar da ita ga al'umma don su amfana kuma suyi yi aiki da ita.
Allah yasa mu dace, amin
*FALALAR SADA ZUMUNCI*
ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺃَﻳُّﻮﺏَ ﺍﻟْﺄَﻧْﺼَﺎﺭِﻱِّ، ﺃَﻥَّ ﺃﻋﺮﺍﺑﻴﺎ ﻋﺮﺽ ﻟِﻠﻨَّﺒِﻲِّ
ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻓِﻲ ﻣَﺴِﻴﺮِﻩِ، ﻓَﻘَﺎﻝَ : ﺃَﺧْﺒِﺮْﻧِﻲ ﻣَﺎ
ﻳُﻘَﺮِّﺑُﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ، ﻭَﻳُﺒَﺎﻋِﺪُﻧِﻲ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ؟ ﻗَﺎﻝَ : ” ﺗَﻌْﺒُﺪُ
ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺸْﺮِﻙْ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ، ﻭَﺗُﻘِﻴﻢُ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ، ﻭﺗﺆﺗﻲ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ، ﻭﺗﺼﻞ
ﺍﻟﺮﺣﻢ .” ﺁﺩﺍﺏ ﺍﻟﻤﻔﺮﺩ
Ankarbo daga Abu Ayyubal ansary (R.A) wani mutumin qauye y bijirowa manzon
Allah (s.a.w) acikin tafiyarsa sai yace: Kabani labarin abunda zai kusantar
dani Aljannah kuma yanesantar dani daga Wuta ? sai Manzon Allah (s.a.w) yace:
“Kabautawa Allah kar kahada shi da komai , kuma katsaida Sallah , kabada Zakkah
, kuma kasadar da Zumunci ”
ﻋَﻦْ ﺃَﻧَﺲِ ﺑْﻦِ ﻣَﺎﻟِﻚٍ؛ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ ” : ﻣَﻦْ ﺃَﺣَﺐَّ ﺃَﻥْ ﻳُﺒْﺴَﻂَ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺭِﺯْﻗِﻪِ، ﻭَﺃَﻥْ ﻳُﻨْﺴَﺄَ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺃَﺛَﺮِﻩِ ، ﻓَﻠْﻴَﺼِﻞْ ﺭﺣﻤﻪ “.
Daga Anas dan Malik Manzon Allah (s.a.w) yace: “Duk wanda yakeso ayalwata masa Arziqinsa , kuma ajinkirta masa ajalinsa to yasadar da Zumuncinsa”.
ﻋَﻦْ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺑْﻦِ ﻋَﻮْﻑٍ؛ ﺃَﻧَّﻪُ ﺳَﻤِﻊَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻳَﻘُﻮﻝُ : ” ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﺰَّ ﻭَﺟَﻞَّ : ﺃَﻧَﺎ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦُ، ﻭَﺃَﻧَﺎ ﺧَﻠَﻘْﺖُ ﺍﻟﺮَّﺣِﻢَ، ﻭَﺍﺷْﺘَﻘَﻘْﺖُ ﻟَﻬَﺎ ﻣِﻦَ ﺍﺳْﻤِﻲ، ﻓَﻤَﻦْ ﻭَﺻَﻠَﻬَﺎ ﻭَﺻَﻠْﺘُﻪُ، ﻭﻣﻦ ﻗﻄﻌﻬﺎ ﺑﺘَﺘّﻪ “.
Daga Abdurrahman dan Auf, yaji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Allah mai
girma da buwaya yace : ” Nine mai Rahama , kuma ni nahalicci Zumunci , kuma
nacirota daga suna na, duk wanda yasadar da ita zan sadar dashi (zuwa ga
Rahamataa) wanda kuma yayanketa zan yanke shi (daga Rahamata) “.
ILLA DA HATSARIN YANKE ZUMUNCI
ﻋﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﺑﻦ ﻣﻄﻌﻢ؛ ﺃَﻧَّﻪُ ﺳَﻤِﻊَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻳَﻘُﻮﻝُ ” : ﻟَﺎ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻗﺎﻃﻊ ﺭﺣﻢ “.
Daga Jubairu dan Mud’im, yaji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: ” Mai yanke
Zumunci bazai shiga Aljannah ba”.
*Allah shine mafi sani*
Yaa Allah ka sanya mu cikin masu Sada zumunci, kar ka sanya mu cikin masu
yanketa.
Ameen
MUN SANI AMMA BAMA AIKI
قال ابن القيم(رحمه الله)
Yana cewa:
Wata yarinya ta rasu sanadiyyar Annoba,sai Mahaifinta ya ganta a mafarki,sai
yace da ita:Yake ya'ta ki bani labari gamd da lahira.sai tace:
"Hakika anyi mana baiwa akan wani abu mai girma,hakika mun sani amma bama
aiki.....ina rantsuwa da Allah, wallahi yin TASBIHI guda daya ko RAKA'A guda
daya a littafinka aiyukana,ita tafi soyuwa agareni fiye da duniya da abinda
yake cikinta".
Hakika wannan yarinya ta fadi wata magana mai tsada da mafi yawan mutane bamu fahimci abinda take nufi ba.
Tana nufin:-
-Musan fadar;
"سبحان الله وبحمده"
Sau dari yana kankare mana zunubai gaba daya ko da sun wuce yawansa ya akai
kumfan teku,amma sai yini da darare masu yawa su wuce bama fadar wannan zikiri.
-Kuma mun san yin raka'a guda biyu na sallar wallaha,yana daidai da sadaka 360,amma sai mu dauki tsawon lokaci bamayin sallar wallaha.
-Kuma hakika mun san yin azumin yini guda na nafila dan Allah,Allah yana tseratar da shi daga shiga wuta na tsawon tafiyar shekara 70,amma mafi yawan mu bamayin azumin nafila.
-Kuma mun san wanda ya tafi duba marar lafiya,mala'iku guda dubu 70 sukeyi masa rakiya kuma suna nema masa gafara,amma kadaine daga cikin mu suke zuwa duba marar lafiya.
-Kuma mun san cewa yin sallar gawa da rakata har a binneta,mutum yana damun ladar Qiradi guda biyu,kuma kowane Qiradi yana daidai da dutsen uhudu,amma mafi yawan mu bama kwadayin yin hakan da samun ladar.
-Mun san cewa dukkan wanda ya ginawa Allah masallaci,koda masallacin na itaceni shima Allah zai gina masa gida a cikin Aljanna,amma mafi yawan masu dukiyar mu basa aikata hakan.
-Mun san cewa wanda ya taimaki matar da mijinta ya mutu da masu karamin karfi,yana da matsayin mai jihadi wajan daukaka addinin Allah,kamar mai yin azumine acikin yini mai raya dare da ibada,amma mafi yawan mu bamu damu da taimakonsu ba.
-Mun san cewa duk wanda ya karanta harafi guda na alqurani yana da ladar kyakkyawan aiki guda goma,amma baka samun masu karatun alqura
***************
Manzon Allah zai yi ceto, kuma wadanda ya cecesu mu zasuyi ceto. Amma ceton nasa ya rabu ne kashi-kashi.
1. SHAFA'ATUL KUBRA: shine babban ceto. Wato ceton da Manzon Allah (saww) zai fara yi kenan aranar Mahashar.
Alokacin da Ubangiji ya riga yayi fushi irn wanda bai taba yi ba, Kuma dukkan Annabawa da Manzanni sun kasa tunkararsa, Sannan halittu gaba daya suna cikin razana da firgita.
Dukkan mutane zasu tafi wajen Manyan Annabawan nan domin neman ceto. Amma kowanne zai ce ba zai iya ba...
Sai Manzon Allah Muhammadu (saww) shi keda Qasaita awannan ranar. Zai je yayi Sujjada agaban zatin Ubangijinsa. Zai yi ma Allah kirari irin wanda wata halitta bata san irinsa ba.
Ubangiji zai ce masa "DAGA KANKA, ROKI IN BAKA".
Sai Shi kuma yace : "YA UBANGIJI AYI HAKURI ASAURARI HALITTA, AYI MUSU HISABI DON KOWANNE YA TAFI MAZAUNINSA".
Nan take Ubangiji zai saurari lamarin halitta, ya fara hisabi agaresu.
To anan ne dukkan wanda yake wajen sai yayi yabon Manzon Allah (saww). Tun daga kan Manzanni da Annabawa, har zuwa kan waliyyan Allah da sauran Muminai, kai har kafiran ma sai sun yabeshi.
Wannan shine Shafa'atul Kubra, kuma shine Makamul Mahmud.
2. CETO NA BIYU: Akwai mutane guda dubu saba'in sau dubu saba'in daga cikin al'ummarsa wadanda albarkacin Manzon Allah (saww) Allahn zai sanya su shiga aljannah ba tare da hisabi ba, ba tare da wata tambaya ko Uqubah ba.
3. CETO NA UKU: Akwai mutanen da sun samu shiga Aljannar, amma shi zai shiga yayi ceto agaresu ya Qara daukaka darajarsu da wannan ceton da zai musu.
4. CETO NA HUDU: Akwai mutanen da sun chanchanta da shiga Wutar, sai an chafkesu za'a kaisu wutar sai su nemi cetonsa. Shi kuma zai dakatar da Mala'ikun sannan yaje ya nema musu ceto awajen Ubangiji, za'a bashi cetonsu sannan awuce dasu Aljannah.
5. CETO NA BIYAR: Zai nemi izinin Ubangijinsa (SWT) sannan ya shiga har cikin wutar yayita fidda Mutanen cikinta ana kaiwa gidan Aljannah.....
Kai dukkan Qurewar matsayi ya tabbata ga wannan Annabin!!!
Idan ya rika ceto, ya rika ceto, har SHAITAN sai ya sa rai, yana miko kansa ko za'a ceceshi!!
Ita kanta Jahannama sai ta kai Qararsa wajen Ubangijinta tana cewa: "YA RABBI! ZAI KWASHESU FA! ZAI KWASHESU FA!!".
Ya Allah yi salati da tasleemi agareshi da iyalan gidansa, gwargwadon Soyayyar da kake masa. Albarkacin wannan Salatin ka sanyamu acikin sahun farko na 'Yan Aljannah.
Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai:
1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai san anfi qarfinta a gidansu.
2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka.
3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss
4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin.
5. Macen da bata gama yin hankali ba.
Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai. Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan da muka tabbatar zabin zuciyoyinmu ne kuma sun dace damu domin samun ingantacciyar Rayuwar Aure!
#Halayen Boye
Samari da ‘yan mata kowa yana iya qoqarinsa wajen ganin ya nunawa masoyinsa halin kirki a lokacin neman aure. Daga cikin matsalolin da ake samu a cikin Rayuwar Aure musamman a farko-farkonta shine a lokacin da ma’auratan suka fara gane halayen juna na gaskiya, wadanda a lokacin da zumar soyayya take dibarsu basu san dashi ba, hakan yakan kawo canji ga irin girma da mutuncin da ma’auratan zasu dinga bawa junansu, musamman idan akayi rashin sa’a daya daga cikinsu ya zamo yana da wani hali na qyama wanda da yake boyewa.
Shawarar da zan bayar anan shine sai mu dinga kulawa sosai a lokacin neman aure, samun kusanci da mutanen gidan masoyan namu ta hanyar qannenshi/ta da abokanshi/
Gaskiya dokin qarfe, idan ka zamo mai gaskiya da halin qwarai to ba ka da tsoron komai a tare dakai!
#Matsala #3
#Mulkin Gida
A duk inda taro ya kai mutum biyu to ya kamata ace akwai shugaba wanda za’a iya cewa shine babba,
ASSALAMU ALAIKUM.
Lokacin *SANYI* ya shigo. Lokaci ne wanda YINI yakeda Qaramci, shi kuma DARE yake da tsawo.
Irin wannan lokaci ne magabata na Kwarai suke kira *Kakar Ibadah.* Kuma magabata sun kasance sukan taya junansu MURNA idan wannan yanayi ya shigo har suna gayama junansu cewa👇🏽
*مرحبا بالشتاء, يقصر فيه النهار للصيام, ويطول فيه الليل للقيام*
*Fassara* 👇🏽
"Maraba da (yanayin) SANYI. *Yini* yana taqaituwa domin Masu AZUMI, kuma *DARE* yana yin Tsawo domin masu QIYAMULLAILI."
A wannan yanayu masu azumi zasuji sauqin azumi domin awannin yinin basuda tsawo, cikin kankanen lokaci zakaga rana ta fadi. Sa'annan Awannin dare sunada tsayi, masu *Qiyamullaili* zasu samu isasshen lokaci suyi sallar dare har su sake komawa bacci cikin natsuwa kuma su tashi su samu sallar asubah.
Ina kira ga kaina da kuma dukkanin 'yan uwana Musulmi, da muyi kokari mu ribanci wannan garabasa da Allah ya kawo mana, ta hanyar yawaita ayukkan ibada musamman Azumin nafila da kuma Sallar dare.
Ina rokon Allah Ya bamu ikon ribantar wannan lokaci mai tsada kuma Ya bamu *ikhlasi* ga dukkanin ayukkanmu na ibadah.
Ina rokon duk wanda wannan tunatarwa takai gareshi da ya turama sauran jama'ah gwargwadon iko, domin gangamewar fa'ida. Ina kuma neman addu'ah daga gareku. Allah ya shiryar damu zuwaga hanya madaidaiciya. Allah ya jiqan iyayen mu.
*Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Sokoto*
👉596. Idan ka shiga damuwa ka tuna cewa, dubu sun yi tarayya da kai. Ka
rungumi qaddara sai ka yi daraja a wurin Allah wanda ya hukunta maka. Ka kyautata ma Allah zato cewa, bai jarabce ka ba sai don ya daukake ka. Kuma
shi ne ya ce, “Lallai tsanani yana tare da sauqi”.
👉597. Shaidan yana da Uwa da Uba da ‘yan uwa da abokai a cikin mutane.
Matar da ke kyamar zuwan baki a gidanta ita ce uwar Shaidan. Wacce ba ta
lullubi ita ce matarsa. Wanda ba ya zuwa Masallaci shi ne babansa.
Almubazzari shi ne dan uwansa. Wanda ba ya bisimilla wajen cin abinci shi ne abokinsa. Mu guji sa da zumunci da Shaidan.�
👉598. Idan ba ka jin dadin ibada, ba ka jin nauyin saba ma Allah, ba ka iya taimakon mabukata saboda Allah, to ka zo rakiyar mutane ne a duniya amma ba da kai ake cin kasuwarta ba.
👉599. Idan kana fama da talauci ka tuna wani na can zai mutu saboda
yunwa. Idan ba ka da lafiya wani na fama da zafin fitar ransa. Idan ka rasa
wani abinda kake so wani ya rasa komai a duniya ban da ransa. Haka rayuwa take. Duk halin da kake cikin sa ka fi wani, wani kuma ya fi ka.
👉600. Idan wani ya kira ka ta waya za ka yi hanzari ka yanke wani layi don
ka sadu da shi. Wani kuma sai ya kira ka sau dari ba ka amsa ba. Mutane matsayi matsayi ne a nan duniya. Ko a lahira matsayinmu ya bambanta. �
amsar itace
(wanda duk ya dogara ga allah kuma zai isar masa duk wani abimda ya dame shi (a al-amarin addininsa ko na duniyarsa) 🌹 ... من عمل صلحا من ز كر اؤ ل نثى ؤ هؤ مؤ من فلنحيينله حيؤ ة صليبه ؤ لنحر ينهم احر هم با حسن ما كا نؤ ايعملؤ 🌹 amsar itace wanda duk ya yi aiki na gari namiji ne ko mace, matuk'ar dai shi mumini ne , to wallahi lallai zamu raya shi rayuwa mai dad'in gaske,kuma tabbas zamu yi musu sakayya mu basu ladan ya mafi abin da suke aikatawa.🌹 .... ؤ اصبر ؤاان الله مع الصبر سن 🌹amsar itace ma'anar(kuma kuyi hakuri,don hak'ik'a, allah yana tare da masu hak'uri)🌹 . ان تكؤنؤاتا لمؤ ن فا نهم يالمؤن كماتالمؤن ؤترحؤن من الله ما لايرحؤ ن .
🌹 amsar itace (in har ku(muminai ne)kuna jin radad'i to suma(kafirai)su
Wanene Boka??
*A larabci ana kiransa da ALKUHHAAN,boka shine Wanda ikirarin sanin gaibun abinda zai faru nan gaba kuma yake baima mutane labarin abubuwan gaibu wadanda bai faruba sai nan gaba,kamar yace wane zai ci zabe ko wane zai fadi,ko wane zai auri wance ko wani zai saki matarsa*.
Wanene Malamin Duba;
*Da larabci ana kiransa da ARRAF, wato mai duba ko bugon kasa,shine wanda ya baima mutane labarin gurin da wani abu nasu ya bata ko abinda aka sace masu yace yana waje kaza,daga cikin abubuwan mutane da suke bata,yana ikirarin sabin gaibun abun da ya faru*.
Boka da Mai Duba dukkan su kafuraine sun kafirta saboda ikirarinsu akan cewa sunyi tarayya da Allah acikin sanin gaibu bayan Allah yana fadar cewa;
*(Babu wanda ya san ghaibu sai Allah shi kadai)*.
Kuma saboda kayarda Allah cikin abinda Allah ya fadar cewa babu wanda ya san ghaisu sai shi kadai,amma su suna cewa sun sani
Allah yana cewa
*(قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ)*
Ma'ana;
(Kace babu wanda ya san ghaibu cikin sammai ko kassai sai Allah shi kadai....)
@النمل 65]
*HARAMUNNE ZUWA WAJAN BOKA KO MAI YIN DUBA*
Daga Safiyyah bntu Abi Uzaid daga Daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ ورضي الله عنهن daga Manzon Allah ﷺ yace:
*(Wanda yaje wajan malamin duba ko Boka,sannan ya tambayesa wani abu kuma ya gaskatsa akansa,baza'a karbi sallolinsa ba na kwana arba'in)*
@رواه مسلم.
Awata riwayar yana cewa;
*(Duk wanda yaje wajan mai yin duba ko Boka,kuma ya gaskata abinda ya fada masa,hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa da Manzon Allah SAW)*
@وفي مسند الإمام أحمد ،وأبو دَاوُدَ والحاكم والذهبي والألباني والترمذي وابن ماجه وغيرهم :
Daga daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ tace;Manzon Allah ﷺ yace;
*(Wanda yaje wajan malamin duba sai ya tambaye shi wani abu,baza'a karbi sallarsa ba ta kwana arba'in)*
@أخرجه مسلم[2230].
*TA FARA MUSULUNTA* a duk duniya kuma ta yiwa musulunci hidima da dukiyar ta da duk abinda ta mallaka harda GwalaGwalanta
*(NANA KHADIJA) (R.A)*
*🧕MACE CE*
Sanadiyyar samun Taimama a shari'a *(UMMUNA A'ISHA) R.A*
*🧕MACE CE*
Ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi{s.a.w}
*NANA A'ISHA (R.a)*
*🧕MACE CE*
Sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah sanda akai sulhun
*HUDAIBIYYA* Kuma *MACE* ce ta shawo akan *SAHABBAI* har suka tsira daga fushin Allah.
*(UMMU SALAMA) R.A*
*🧕MACE CE*
Ta Kwantarwa Manzon Allah *HANKALI* Lokacin da kiran karya da aka yiwa A'ISHAT, kafin saukar wahayi
*(BARIRA) (R.A)*
*🧕MACE*
Na sanadiyyar shigar mutum Aljannah Wanda Manzon Allah *{S.A.W}* yace idan mutum ya tarbiyyantar da
ita koda bashi ya haife ta ba, zai shiga *ALJANNA* shi da Manzon Allah *{S.A.W}*
*🧕MACE CE*
Ta zamo Ma'auni damai Aure zai gwada kimarsa agun Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yanada sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah.
*🧕MACE CE*
Shari'a ta tanadar *MATA* Ladan Jam'im Salloli guda biyar (5) Da Juma'a da Jana'iza da Jihadi duk basai taje ba amma sanadiyyar ta Kyautatawa *MIJINTA* Allah Zai bata duk *LADAN* wadannan Ibadun.
*🧕MACE CE*
Sanadiyyar warware matsalar Zihari, suratul *(MUJADALA)*
*🧕MACE CE*
Ta fara yin Sa'ayi tsakanin *SAFA da MARWA (HAJARA)*
*🧕MACE CE*
Sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratl *(NAML)*
*BILKISU MAI GADON ZINARI*
*🧕MACE CE*
Sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar *(R.A) (FATIMA)*
*🧕MACE CE*
Ake samun nutsuwa da ita! *LITASKUNU ILAIHA* Namiji bazai taba samun sukuni ba sai yana da mace!
*🧕MACE CE*
Duk mulkin mutum da dukiyar shi sai da ita yake kara kima a idon mutane!
*Mata iyayen mune Mu girmamasu!*
MACE TA GARI
*MACE TA GARI* ADDINI⚙Kasancewar mace mai addini yana da muhimmanci sosai. Kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi, Manzon Allah (SAW) yace “ana auren mace saboda abubuwa hudu: dukiyar ta, da kyawun ta, da dangin ta da addinin ta,....”, amma sai ya bayar da shawarar a zabi mai addinin. Wannan shi zai bata dama ta iya kiyaye abubuwa da yawa da suka shafi zaman aure, saboda tana jin tsoron kar tayi wani abu mai muni ya zawo mata matsala da Allah. Idon an ce mace mai addini ya hada da abubuwa da yawa kamar haka:
Ilimi:
Mace ta gari ya kamata ta kasance mai ilimi na addini da na rayuwa. Kar ki kasance bagidajiya. Dole ne ki yi amfani da ilimin ki na addini da na rayuwa domin nuna kwarewa wajen zaman aure da mu’amala da miji da sauran jama’a.
Tauhidi:
Dole ne mace ta gari ta kasance tana da cikakken tauhidi. Yawancin mata ana samun su da matsala ta wannan bangare ne idon wani abu da zai sosa musu rai ya faru kamar za’a yi mata kishiya, sai ka ji ta shiga yawo wajen bokaye; ko kuma suna zaune da kishiyar sai wani abu ya same ta, misali ta daina haihuwa ko kuma dan ta ya mutu ko kuma hanyoyin samun kudin ta su samu matsala. Sai kaji ta fara danganta wannan jarrabawar da Allah yayi mata da abokiyar zaman ta, ta manta da Allah. 'Yar uwa ta:
ki sani fa babu abin da zai same ki sai abin da Allah ya kaddara miki kamar yadda Allah ya ce: “Kace babu abin da zai same mu sai abin da Allah ya rubuta mana, shine majibincin al’amuran mu, kuma ga Allah ya kamata muminai su dogara”. (S: Taubah: Q 9:51). Haka kuma Manzon Allah (SAW) ya fadawa Abdullahi Dan Abbas cewa: “... kuma ka sani, dukkan al’uma da zata taru a kan ka, domin ta amfanar da kai, bata iya amfanar da kai sai da abin da Allah ya rubuta maka; kuma da zata taru akan ta cutar da kai, bata iya cutar da kai sai da abin da Allah ya rubuta akan ka....”.
Ki sani duk abin da ya same ki, to jarrabawa ne daga Allah, yana so yaga ya zaki yi; shin zaki mayar da al’amuran ki gare shi ko kuwa zaki yi abin da baya so!
No comments:
Post a Comment