Safeeyyah

 

Bismillahir-rahmanir rahim
 إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

TARBIYYAR YARA



TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI. //1
TARBIYYA hakkine da Allah (SWT) ya wajabtawa Iyaye suyi ga 'ya'yansu, kamar yadda ya wajabtawa 'ya'ya yin biyayya ga iyayensu.
Kamar yadda muka sani, 'ya'ya kyautace (Ni'imace) daga Allah da yake bayar da ita ga wanda yaga dama, kuma Amanace da Allah ya dankata a hannun iyaye. Sabida haka Iyayen da suka kyautata wajen tarbiyyantar 'ya'yansu da ladabtar dasu bisa koyarwar Musulunci, to sun sauke wannan amanar, Wadanda kuma suka yi sakaci kuma suka takaita wajen yi musu tarbiyya to sun tozarta wannan Amanar.
Allah Ta'ala yace: " Ya ku wadanda su kayi imani, ku tsare kawunanku da iyalanku daga wuta, wacce mutane da duwatsu ne makamashinta... "
(Tahrim: 6).
Annabi (SAW) yana cewa a wani hadisi:
" Dukkanninku masu kiwone kuma ababan tambayane dangane da kiwon da aka baku, shugaba me kiwone (dangane ga talakawansa) kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi, mutum me kiwone dangane ga iyalinsa kuma abin tambayane dangane da kiwon da aka bashi."
Bukhari da Muslim.
Akwai wasu hanyoyi wadanda idan muka bisu zasu taimaka mana da yardar Allah wajen Tarbiyyar 'yayanmu, daga cikinsu akwai:
1. MU ZABAWA 'YA'YANMU UWA TA GARI.
Auren mace tagari muhimmin lamarine dake taimakawa wajen tarbiyyar 'ya'ya, domin uwa ita ce makaranta ta farko da yaro ke daukar darasi a cikinta, kuma halaye da dabi'un uwa suna tasiri matuka ga 'ya'yanta, sabida hakane shari'a ta kwadaitar damu wajen auren mace tagari ma'abociyar addini.
Annabi (SAW) yana cewa: " Ana auren mace sabida abubuwa guda 4; dukiyarta, da kyawunta, da daukakarta, da addininta. ka zabi ma'abociyar addini, sai hannunka yayi albarka."
Bukhari da Muslim.
Abu ne mai muhimmanci ga wanda yake da niyyar yin aure ya dage da addu'a akan Allah ya azurtashi da samun mace tagari, kuma yayi "istikhara" wato neman shawarar (zabin) Allah kafin auren, ya kuma nemi shawarar bayin Allah mutanen kirki, sannan yayi kokari wajen yin bincike akan nagartar yarinyar da kuma iyayenta, ya kuma fawwala al'amuransa zuwa ga Allah SWT.
Sannan kuma ya zama wajibi abi hanyoyin da Shari'a ta tsara wajen neman aure, kuma a nisanci sabawa Allah da sunan murna ko farinciki a yayin aure, wannan zai sa Allah Ta'ala ya sanya Albarka a cikin auren da kuma zuriyar da za a samu ta dalilin wannan auren.
2. ROKON ALLAH YA BAKA ZURRIYYA TA GARI.
Wannan dabi'ace ta Annabawa da Manzanni da bayin Allah salihai. Kamar yadda Allah ya bamu labari a kissar Annabi Zakariyya (AS), yake cewa: " A yayin nan Annabi Zakariyya ya roki Ubangijinsa, yace: ya Ubangiji ka bani kyauta daga gareka ta zuriyya tsarkakakkiya, hakika kai mai amsar addu'ane."
(Ali-Imran: 38)
A wata ayar kuma Allah ya bamu labarin salihan bayinsa, daga cikin siffofinsu suna addu'ar Allah ya basu mata da 'ya'ya nagari, yake cewa:
" Wadannan da suke cewa ya Ubangijinmu ka bamu kyauta daga matayenmu da zuriyyarmu abinda idanuwanmu za suyi sanyi dasu, kuma ka sanyamu mu zama shugabanni ga masu tsoron Allah."
(Al-furqan: 74)
Wannan ya nuna mana muhimmancin addu'a da rokon Allah wajen samun 'ya'ya nagari kasancewar har Annabawan Allah da Salihai sun yi irin wannan addu'ar.
Allah ya bamu ikon yiwa 'ya'yayenmu tarbiyya da ladabdar dasu bisa koyarwar Kur'ani da Sunnah,

 FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI
*******************************
Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.
Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.
Malamai sun ce ana karanta Fatiha ne da Qul Ya ayyuhal Kafirun, da kuma fatiha da Qul Huwal-Lahu acikinta. KUMA ana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).
Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :
"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".
Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIFIKO (WATO FALALA)".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
Acikin wata ruwayar kuma Abdullahi bn Umar (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa :
"KAR KU BAR YIN RAKA'O'IN NAN GUDA BIYU WADANDA AKEYI KAFIN SALLAR ASUBA. DOMIN ACIKINSU AKWAI ABABEN KWADAYI".
Domin cikar fa'idah ma, ga wani Sahihin hadisin wanda Imamu Muslim ya ruwaito daga Nana A'ishah (ra) ita kuma daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"RAKA'O'I BIYUN ALFIJIR, SUN FI DUNIYA DA ABIN CIKINTA".
Don haka 'yan uwa bai kamata mu rika barin wannan garabasar tana wucemu ba.
Da yawan Matasa Wasu basu yinta. Dama basu kwanciya da wuri, shi yasa suke makara. Kuma da zarar sun tashi sai su sallaci Asubah, ita kuma su kyaleka.
To lallai rashin yin RAKA'ATAYIL FAJRI ba Qaramar Asara bace agareka ya kai Musulmi!
Wannan asarar tafi asarar Biliyoyin Nairori. Domin kuwa Annabi (saww) yace TAFI DUNIYA DA ABIN CIKINTA. Don haka idan baka yita ba, kamar kayi asarar dukiyar dake cikin duniyar nan ne. Ko kuma fiye da haka.
Na san yanzu wani zai ce "Shin zan iya yinta koda bayan Sallar Asubah ne?".
AMSA : A'a. Ana yinta ne kafin sallar Asubah. Domin bai halatta kayi sallar nafila bayan kayi ta Asubahi ba. Har sai bayan fitowar rana.
Hujjah anan ita ce Sahihin hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU SALLAH (NAFILAH) BAYAN SALLAR LA'ASAR HAR SAI RANA TA FADI. KUMA BABU SALLAH BAYAN SALLAR ASUBAH HAR SAI RANA TA BULLO".
Wani Sahabi mai suna Amru bn Abisata (ra) yace "Ya Rasulallahi bani labari mana game da sallah".
Sai yace masa "KA SALLACI ASUBAH SANNAN KA JANYE DAGA YIN SALLAH HAR SAI RANA TA FITO TAYI SAMA.....".
Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Mafiya yawan Jamhurin Malamai suna ganin halaccin yin ramukon sallah akowanne lokaci, koda bayan Sallar Asubah din ne. Amma banda nafila.
Saboda hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA DA WATA SALLAH (TA FARILLAH KENAN) TO YA SALLACETA IDAN YA TUNA".
Amma yin nafila bayan Sallar Asubah, mafiya yawan Sahabbai duk sun karhanta yin haka. Kamar Irin su Sayyiduna Aliyu Bn Abi Talib. Da Ibnu Mas'ud da Zaidu bn Thabit da Abu Hurairah da Ibnu Umara (Allah shi yarda dasu baki dayansu).
Sayyiduna Umar kuwa, ya kasance yakan bugi mutum idan ya ganshi yana yin nafila a irin wadannan lokutan.
Hakanan Sayyiduna Khalid bn Waleed (ra) Shima yakan bugi masu yin hakan. (Wato masu yin nafila alokutan da aka hana).
Duk da cewa akwai Maluman da suka halatta yinta bayan an sallaci Asubah, wai saboda Hadisin wani mutum wanda ya tashi bayan Sallar Asubah yana yinta amma Annabi (saww) bai ce masa komai ba. To amma gaskiya hujjarsu bata kai wannan din Qarfi ba. ta kowacce fuska.
Saboda wannan haka Annabi (saww) yake yi, Haka Khalifofinsa gaba daya suke yi. Hakanan duk manyan Sahabbansa wadanda aka riko sunnah daga garesu duk suna yinta ne kafin sallar Asubahi (Ba bayanta ba) Haka kuma, dukkan Maluman Mazahib din nan guda hudu.
Anan zan tsaya, sai wani lokacin kuma in sha Allahu. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka karanta.

FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE
*************************************
Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu
Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan
daga ciki zamu lissafo kamar haka:
1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin
Allah da Manzonsa.
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah
(saww) farin ciki aranar lahira. Yace :
"Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni
zanyi ma sauran al'ummomi alfahari
daku aranar Alkiyamah".
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda
Zai fito ta jikinka, har ya girma yana
Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL
LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI".
4. Ta dalilin aure ne zaka samu
Zuriyar da zasu yi maka addu'a
bayan rasuwarka. Wannan yana daga
cikin ayyukan da ladansu ba zai
yanke ba har abada.
5. Yin aure ya kan zama dalilin
runtsewar idanun mutum daga kalle
kallen Haramun, sannan ya kare masa
al'aurarsa daga Zina.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar taimaka ma 'Yar uwarka
Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta
kenan daga Zina.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar
addininka, da ninkawar ladanka fiye
da wanda bashu da aure.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan
ciyarwa da Matarka, da daukar
nauyinta, da ladan samar mata da
Mazaunin da zata rayu.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Qara yawan Musulman duniya
ta hanyar haihuwar da zaka samu.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu
damar Karkatar da himmarka daga
kan neman biyan bukatarka ta hanyar
haram izuwa ga hanyar halal. Da
kuma samun ladan saduwa da
iyalanka.
11. Zaka samu lada mai girma sosai
idan Har Allah ya azurtaka da 'Ya'ya
mata guda biyu, kumq kayi hakuri
dasu ka kyautata musu, ka kyautata
tarbiyyarsu, Su zasu zama
Garkuwarka daga shiga wuta.
12. Idan ka har 'Ya'yanka guda biyu
suka rasu, kuma kayi hakuri, to Allah
zai shigar dakai Aljannah saboda
wannan.
13. Ta dalilin aure zaka samu
Qaruwar mutuncinka da darajarka
acikin al'ummah. Ka shiga sahun
mutanen da zasu iya jagorantar
lamuran rayuwar al'ummah.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu
Taimakon Allah cikin al'amarinka.
Kamar yadda Manzon Allah (saww)
yake cewa: "
MUTUM UKU, HAKKI NE
AKAN ALLAH YA TAIMAKESU. 1.
WANDA ZAI YU AURE DON NUFIN
KAME MUTUNCINSA. 2. BAWA
WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA
SABODA YA SAMU DAIDAITUWA
(ACIKIN ADDINI) 3. MUJAHIDI (MAI
YAKIN DAUKAKA ADDININ ALLAH

BABBAR MAGANA:
Ranar Lahira Allah yana cewa:
(Ya ku wadanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kowane mai rai ya dubi abin da ya aikata domin gobe (lahira)…) [Al-Hashri, aya ta 18].
1. Mutuwa ba ita ce karshe ba. Mutuwa mafarin wata rayuwa ce mai tsawon gaske, mai ciki da dadi ko wahala, mai kunshe da farin ciki ko bakin ciki. Duk mai kokwanto game da rayuwar lahira mahaukaci ne ba mai hankali ba.
2. Rayuwarmu a nan duniya tana cike da zalunci da ta'addanci da rashin gaskiya da miyagun ayyuka. An mayar da karya ita ce mafita, yaudara kuma ita ce wayo munafurci kuma ya zamawayewa.
3. A rayuwarmu a yau muna ganin ana hukunta marar laifi a kyale masu laifuka, ana kuma wulakanta mai mutunci sannan a karrama fitsararre. Don haka idan har mun yarda da cewa Allah adalin Sarki ne, to babu makawa dole ne mu yi imani da samuwar wata rayuwa bayan wannan ta duniya da muke ciki, watau rayuwa wadda a cikinta ne Allah zai mayar wa kowane mai hakki hakkinsa, ya hukunta duk wani mai laifi gwargwadon laifinsa. Duk wani mai hankali da ya san ya kamata dole ne ya yarda da haka.
4. Yarda da lahira da imani da sakamakon cikinta ne kadai zai hana wa dan'adam zaluntar dan'uwansa, zai kuma kara wa mutumin kirki kwarin gwiwar aikata ayyukan alheri,domin yana da tabbacin cewa zai ga kyakkyawan sakamakon aikinsa.
5. Ashe bai kyautu mu ci gaba da tunatar da junanmu wannan babbar magana ba

MACE MAI WUYAR SAMU A YAU
_______________

___________________
Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyar samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita. Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma ka sani, mace daya ce kawai, ta ke yin tasiri a rayuwa, wacce ranka kullum zai kasance a kanta.
Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, Ita ce wadda ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda).
Haka kuma ita ce wadda kowace mace take fata ta zama.
Ga siffofinta guda goma, kamar.
haka:
1. Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
2. Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da
zai haddasa matsala a tsakaninsu.
3. Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.
4. Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.
5. Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.
6. Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da.
riritawa.
7. Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da
fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.
8. Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.
9. Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.
10. Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.
Fatanmu ubangiji yasa mudace da mata na Kwarai.

 IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA
Idan duniya tazo Qarshe za'ayi wani dare mai tsawo wanda saboda tsananin duhunsa tsoro zai kama mutane sai su fita zuwa Masallatai suna ta addu'a suna rokon afuwa awajen Allah..
Chan za suga alamar ketowar alfijir, rana zata fito amma ta mafa'darta (wato ta yamma).
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!.
Wannan chanjin yanayin da aka samu shine babbar alamar dake bambanta tsakanin Qarewar rayuwar duniya da kuma ainahin tsayuwar nan ta tashin Alqiyamah.
Da zarar rana ta fito daga mafa'darta (wato yamma) nan take za'a ji kira daga wata murya mai Qarfi..
Tana sabar da mutane cewa "AN RUFE QOFAR TUBA!". Daga lokcin nedukkan wata sha'awa zata fiche daga dukkan zukata, Kuma nadama zata yawaita..
Domin kuwa tuba ba zatayi amfani ga masu yinta ba.. Imani ba zai yi amfani ba, sai ga wadanda suke dashi tuntuni..
Abubuwan dake rike da duniyar dama su hudu ne : - ALQUR'ANI. - KA'ABAH. - MUSULUNCI. - MUMINAI. -
Za'a wayi gari aga Alqur'anai baki daya sun zama farar takarda babu rubutu ko daya.. -
Wani Babban Kafiri zai zo ya rushe Ka'abah (ZUS SAWEEQATAINI) Kuma zai wawashe kayan alatun dake cikinta.. (SUBHANALLAH).
Haka Annabi (saww) ya fa'di sunansa. - Za'a yi wata iska mai dadi wacce zata zama dalilin ficewar rayukan dukkan Muminai..
Su koma zuwa ga rahamar Ubangijinsu. - Za'a wayi gari babu sauran Musulmi ko Muminai aduniya baki daya.
Babu sauran mai cewa "ALLAH! ALLAH!!". - Za'a yi Qarni guda (100 yrs) wanda acikinta babu sauran 'dan halal.. Duk sai Mazinata da 'Ya'yan Zina. Zasu rika yin zina akan layi da bakin tituna.. .
Cikinsu babu wanda yasan Allah balle ya bauta masa.
Sune mafiya sharrin halittu abayan Qasa. Kuma akansu ne Alqiyamah zata tashi.. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL!!
Ya Allah ka kyautata Qarshenmu kasa mu cika da imani Ameen

No comments:

Post a Comment