{ HADISI NA 4 }***
.
An karbo daga abu Abdurrahaman Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yabamu labari shi mai gaskiya ne abin gasgatawa yace:
.
Lallai kowanne dayanku ana tara halittars aacikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba’in yana maniyyi sannan , ya canja yazama gudan jinni kwatankwacin wannan (kwana 40) sannan ya juya yazama tsoka kwatankwacin wannan (kwana 40) sannan, ya juya yazama tsoka kwatankwain haka, (kwana 40) sai a aiko mala’ika yabusa masa rai a umarce shi da rubuta kalmomi guda hudu:
.
A rubuta arzikinsa da ajalinsa dad a ayyukansa da kuma dan wuta ne ko dan aljannah ?
.
Manzon Allah (s.a.w) yace:
.
Na rantse da wanda babu wani abin bautawa da gaskiya saishi, lallai dayanku zaiyi aiki irin na ‘yan Aljanna harya zamanto ba abin dake tsakaninsa da Aljanna sai zira’I daya sai rubutun can ya rigashi yayi aiki irin na ‘yan wuta, saiya shige ta lallai dayannku zaiyi aiki irin na ‘yan wuta har abin dake tsakaninsa da ita bai zira’I daya ba sai littafi ya rigayeshi sai yayi aiki irin aikin yan aljanna sai ya shigeta.''
. Bukhari ( 3208) Muslim (2643).
.
Ya Allah kashigar damu aljannah firdausi madaukakiya.
***{HADISI NA 5}***
.
An karbo daga Ummul Mu’uminina Ummu Abdullahi Aishatu (R.A) tace:
.
Manzon Allah (SAW)
.
“yace wanda ya kirkiro wani abu {da babu shi a da) acikin lamarinmu wannan {Addini} wanda baya daga gare mu {Baya Daga Allah da Manzonsa} shi Abin juyarwa ne
.
Kuduba Sahihul Bukhari (2695).
Ko Sahihu Muslim (1718).
,
Aruwayar Muslim yace duk Wanda ya aikata wani aiki wanda baya daga umurnin mu shi Abin juyarwa ne''
..
Allah (s.w.t) ya kiyaye zukatanmu daga aikata kuskure.
***{HADISI NA 7}***
.
An karbo daga Abu Rukayya (wato) tamimdan Ausid Dari (R.A) yace:
.
Annabi (S.A.W) yace;-
,
'' Addini nasiha ne!
Sai mukace, gawa ?
Sai yace, ( Nasihane ) ga Allah, da littaffansa da Manzonninsa, da shugabannin musulmi da dukkan mutane,
.
Muslim ne rawaito (55).
***{HADISI NA 8}***
.
An karbo daga Abdullahi BN Umar (R.A) yace:
Hakika Annabi (S.A.W) yace:
.
“An umarce ni in yaki mutane, harsai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma har sai (sun yarda Annabi )Muhammad manzon Allah ne, su tsayar da Sallah, kuma su bayar da zakka idan sun aikata haka, jininsu ya ku6uta daga gareni da dukiyoyinsu , sai dai da hakkin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah madaukakin sarki''
..
Sahihul Bukhari (25).
Sahihu Muslim (22).
.
Allah kabamu ikon kiyaye dokokin manzon Allah (s.a.w).
***{HADISI NA 9}***
.
An karbo daga Abu Huraira Abdur-rahman dan Sakhirin (R.A) yace:
Naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
''Duk abin dana haneku da shi toku nisance shi (ku bari) abin dana umarceku to kuzo dashi dai-dai gwargwado .
Hakika yana daga abin daya hallakar da mutanen dake gabaninku shine yawan tambayoyinsu da sabawarsu ga Annabawansu''.
.
sahihul Bukhari 7288) da Muslim 1337).
.
Ma'ana:-
.
Annabi yahana sahabbansa yawan tambayoyi domin kada su takurawa kansu, akan abin da Allah bai dora musuba.
.
Ya Allah kaqara mana biyayya ga annabi Muhammad (s.a.w).
***{HADISI NA 10}***
An karbo daga Abu hurairata (R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Lallai Allah tsarkakke ne kuma baya kar6ar abu, sai mai tsarki.
Allah ya umarci muminai da irin abin daya umarci manzanni dashi yace:
Yaku manzanni kuci daga dadddan abubuwa kuma kuyi aiki nagari kuma (Allah) yafada lokacin da yake umartar muminai cewa:
Yaku wadanda sukayi imani kuci daga dadadan abububawan da muka azurtaku dashi sannan Annabi (S.A.W) ya ambaci wani mutum dayake tsawaita tafiya gashin kansa yayi gizo yayi kura yana mika hannayensa zuwa sama yana cewa:
Ya rabbi ya rabbi amma kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne an ciyar dashi da haram tayaya za amsa masa (Addu’arsa).
sahihu Muslim (1015).
Ya Allah ka katange zukatanmu daga aikata HARAM.
***{HADISI NA 12}***
An karbo daga Abu Hurairata yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:
"yana daga kyawun musulunci mutum yabar abinda baya da mahimmanci, a gareshi. (Abinda ba xe amfane shi ba)
Tirmizi da Ibnu Majah ( 2318) ( 3976).
Allah ka kiyaye mana imaninmu.
***{HADISI NA 13}***
An karbo daga Abu Hamza, anas Dan malika (R.A) yaron gidan Annabi (S.A.W) yace:
Manzon allah (s.a.w) yace:
"Imanin dayanku baya cika harsai yasowa dan uwansa abin da yake sowa kansa."
Bukhari (13) muslim (45).
Allah yabamu ikon kamantawa.
***{HADISI 14}***
An karbo daga Abdullahi dan mas’ud(R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:
"jinin mutum musulmi baya halatta sai yayi daya daga cikin laifuka guda uku:
1. Magidanci (me Aure) mazinaci.
2. Da wanda ya kashe rai.
3. Da wanda yabar addininsa yarabu da jama’a.
Bukhari (6878) da Muslim (1676).
Wannan hadisin ba dashi ake aiki a kasata nigeria ba.
Sun mayar da rayukanmu sai kace na kiyashi.
Ya Allah kashirya mana shugabannin kasata nigeria
***{HADISI NA 15}***
An karbo daga Abu Huraira (R.A) yace:
Lallai Annabi (S.A.W) yace:
"wanda ya kasance yayi imani da Allah da kuma ranar lahira, yafadi alheri ko yayi shiru.
Wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar lahira toya girmama makocinsa
wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar lahira toya girmama bakonsa."
sahihul Bukhari da Muslim ( 6918), (48).
Allah yabamu ikon kamantawa.
***{HADISI NA 16 }***
An karbo daga Abu hurairata {R.A} yace:
"Wata rana wani mutum yazo, yace da Annabi kayi mini wasiyya.
Sai Annabi (s.a.w) yace dashi
"kada kayi fushi kada kayi fushi
Kada kayi fushi
saida yayi ta maimaitawa.
Sahihul Bukhari (6116).
Allah kasa mufi Qarfin zukatanmu.
***{HADISI NA 17}***
An karbo daga Abu ‘ya’ala shaddadu abin Ausi {R.A} daga Annabi {s.a.w} yace:
"Allah ta’ala ya wajabta kyautatawa ga kowanne irin abu da mutum zaiyi a duniya).
Idan za kuyi kisa ku kyautata kisan
Idan, za ku yanka dabba ku kyautatawa yankan,
kowanne dayanku idan zaiyi yankan ya wasa wukarsa domin yahutar da abin dazai yanka.
(Muslim 1955.)
ma'ana;-
Ubangiji (s.w.t) ya wajabta kyautatawa ga kowanne irin abu da mutum zai a duniya ya zamanto ya kyautatashi, kowanne irin abu dan Adam ne babba ne yana bukatar Ihsaninka don haka sai Annabi (s.a.w) zai kawo misali daya wanda yashafi dan Adam.
2. Na biyu kuma wanda yashafi dabba, yace:
Idan kuka yi nufin kisa toku kyautata kisan, wato mutum ne yayi laifin kisa kukazo zaku kasheshi wannan kisan ku kyautatashi.
Abin nufi, kuyi amfani da abin dazai zare ransa nan take, bawai ku daureshi da igiya ku rataye ba, ya dade bai mutu ba.
Wannan idan kukayi haka, kun sabawa wannan hadisin.
Ba a rataya a musulunci, saidai a fille kai, ko ayi amfani da dukkan wani abu wanda nan danan zai dauke numfashi cikin kankanin lokaci.
Cikn second ko abin da baikai second ba, nan da nan ya dauke ran mutm ya huta.
Amma ba mutum ya jigata kafin ya mutu ba, wannan bai halatta ba.
Sannan kuma baya halatta ku kacancana gawa mutum koda kafirine kukazo kasheshi indai kun sare masa rai to yariga ya gabata, basai kun fille kai, kun yanke hannu kun yanka kafa, kun ja a kasaba.
wannan duk ta’addanci ne wanda sharia’ tace
Kada kuyi ta’adanci hakika Allah bay a son ‘yan ta’adda)
(Suratul-bakara)
Amma malamai sunce in mutun ya kashe dan uwansa musulmi kisa na ganganci, akazo ayi masa kisasi yayin to shima in anzo kasheshi babu laifi a kacancana gawar don ya zamnto kisasi ya tabbata, kamar yadda Allah ya fada.
.
Allah ka kashemu da imani.
WALLAHU A'ALAM.
***{HADISI NA 18}***
An karbo daga Abu Zarri, Jundubu Bin Junada, da Abu Abdurrahman mu’azu dan Jabal {R.A} yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Kaji tsoran Allah, aduk inda kake, sannan kabi mummunan aikin da kayi da kyakykyawan aiki,) zai shafe mummunan.
Sannan ka dabi’anci mutane da kyakykywar dabi’a"
Tirmizi 1987 shine ya rawaito yace:
hadisi ne hasanun a wani bugun yace, hasanun sahihun.
Allah ya gafarta mana baki daya.
***{HADISI NA 19}***
An karbo daga Abdullahi dan Abas(R.A) yace:
"Wata rana Nakasance abayan manzon Allah (SAW) sai yace dani.
"Yakai yaro! Zan sanar dakai wasu jumloli kamar haka:
♣Ka kiyaye dokar Allah, sai kaima Allah ya kiya yeka.
♣ka kiytaye dokar Allah zaka same shi yana yanayi maka jagoranci.
♣ Idan zakai roko to ka roki Allah.
♣ Idan zaka nemi temako ka nemi temakon Allah.
♣ Kasani cewa da al’umma zasu taru domin su amfaneka da wani abu, bazasu iya amfanar dakai komaiba , sai da abin da Allah yarubuta maka (cewa naka ne).
♠ Idan da al’umma zasu taru A kan su cutar da kai da wani abu, basu isa su cuce kaba, saidai abin da Allah ya riga ya rubuta maka.
An riga ancire alkalami, takardu sun bushe.
tirmizi (2516) ya rawaito, yace hadisine mai kyau ingantacce.
Allah kasa Al-jannah itace kaddarar da Allah ya rubuta mana.
***{HADISI NA 20}***
An karbo daga Abu Mas’ud Ukbatu dan Amaru Al’ansari Albadariy (R.A) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Yana daga cikin abin da mutane suka riska daga zancen Annabawan farko idan har ba kajin kunya to ka aikata duk abinda kakeso.
(Bukhari 3483).
Allah kasanya mana jin kunyarka.
***{HADISI NA 21}***
An karbo daga Abu amrin ko abi Amrata, sufyan dan Abdullahi (R.A) yace:
"Na tambayi Manzon Allah (s.a.w) cewa fada mini wata magana a cikin addinin musuluncis wacce bazan sake tambayar waninkaba game da ita.
Sai yace;-
", kace nayi imani da Allah sannan kuma ka daidaita."
Muslim ya rawaito
***{HADISI NA 22}***
An karbo daga abu Abdullahi Jabir dan Abdullahi Al’ansari (R.A) yace:
"Wani mutum ya tambayi Annabi (s.a.w) yace dashi:
"Ya Rasulullahi bani labari idan na sallaci salloli na wajibi, na azumci watan Ramadan, na halatta halal, na kuma haramta haram.
Ban kara komai akan haka ba, shin kuwa zan iya shiga Aljanna ?
sai Annabi (s.a.w) yace;
" eh.! Zaka shiga aljanna."
(Muslim. 15).
Ma'ana;-
Wannan hadisi yana nuna mana cewa duk yawan nafilar daza kayi idan farilarka bata cikaba akwai gyara atare dakai.
Ya UBANGIJI kabamu ikon gyarawa.
***{HADISI NA 23}***
An karbo daga Abu Malik haris bin Asim Al-ash’ari yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Tsarki rabin imanine.
Fadin subhanallahi tana cika mizani.
Fadin subhanallahi da Alhamdulillah suna cika kowacce daya daga cikinsu) tana cika abin dake tsakanin sama da kasa.
Sallah haskece, sadaka hujja ce.
hakuri kuma haskene.
Al-qur’ani hujjane gare ka, ko akanka
Dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa sayar da kansa, kodai ya ‘yantar da kansa ko kuma ya halakar kansa.
Muslim (223).
Ubangiji kabamu ikon aikatawa.
***{HADISI NA 24}***
An karbo daga Abu zarri Al’gifari (R.A) yace:
Cikin abin da Annabi (s.a.w) ya rawaitowa daga wajen Ubangijinsa, (s.w.a) lallai Allah madaukakin Sarki yace:
"Yaku bayina na haramtawa kaina zalunci kuma na sanya zalunci yazama abin haramtawa a tsakaninku.
Yaku bayina dukkaniku batattune, sai wanda na shiryar dashi.
kunemi shiriyata ni kuma in shiryar daku.
Yaku bayina dukkaniku mayunwatane sai wanda na ciyar dashi.
Don haka ku nemi ciyarwata, ni kuma zan ciyar daku.
Yaku bayina, kowanenku matsiraita ne .
kunemi suturtawata, zan suturta ku.
Yaku bayina!
ku masu yin laifi ne dare da rana ni kuma Ina gafarta zunubai gaba dayansu.
kunemi gafarata ni kuma zanyi muku gafara.
Yaku bayina baku isa ku cutar daniba ballantana kuce zaku cutar dani.
Baku isa ku amfanar dani ba.
Ballantana kuce zaku amfanar dani.
Yaku bayina da ace na farkonku dana karshenku da mutanenku da aljannunku ku kasance abisa ga zuciyar wani mutum daya cikinsu mafi jin tsoran Allah
hakan bazai kara komai a cikin mulkina ba.
Yaku bayina da ace na farkon ku dana karshenku da mutanenku da aljannuku ku kasance abisa zuciyar daya mafi fajirci.
Hakan bazai rage komai dangane da mulkina ba.
Yaku bayina da ace na farkonku dana karshen ku da mutanenku da aljanunku su cure a waje daya, kowanne ya rokeni kuma kowanne daya daga cikinku nabashi abin daya roka
hakan bazai rage komai daga cikin abin dake wajenaba saidai gwargwadon abin da allura tarage idan an tsomata cikin ruwan teku.
Yaku bayina ayyukanku na kididdige wasu agareku sannan ina cika muku ladanku.
Wanda yasami alheri, ya gode a Allah.
Wanda yasami wanin haka, kar yayi zargin kowa sai kansa.
Muslim ne ya rawaito shi.
Allah ka gafarta mana zunubanmu
***{HADISI NA 26}***
An karbo daga Abu zarril gifari (R.A) daya daga cikin sahabban Annabi (s.a.w) yace dashi
.
Ya manzon Allah (s.a.w) ma’abota dukiya sun tafi da lada suna yin sallahr farillah kamar yadda mukeyi.
Sunayin azumin farillah kamar yadda mukeyi.
kuma suna sadaka da sauran dukiyarsu.
Sai Annabi yace shin Allah bai sanya muku abin da zakuyi sadaka ba ?
Abin da zakuyi sadaka dashi shine:
*Dukkan wani tasbihi sadaka ne.
*Dukkan wata hailala sadaka ce.
*Dukkan umarni da kyakykyawan aikin sadaka ne.
*Hana mummunan aiki sadaka ne, a gabar kowanne daga cikin akwai sadaka.
Sai sahababai sukace:
Ya manzon Allah yanzu mutum zaibiya bukatarsa kuma yazama yana da lada ?
Sai Annabi (s.a.w) yace:
Kubani labari da ace ya sanya gabar tasa acikin haram shin yanada zunubi ?
To haka nan inya sanya a halal anan zai zama yanada lada.
Muslim (1006).
Allah ka gafarta mana zunubanmu.
***{HADISI NA 28}***
An karbo daga Abu Najih, irbadu dan sariya (R.A) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yayi mana wa’azi mai isarwa zukata su tsorata, idanu suka zubar da hawaye.
Sai mukace dashi, ya manzon Allah (s.a.w) kamar wa’azin bankwana to kayi mana wasiyya.
Sai yace,
" ina muku wasiyya dajin tsoran Allah da kuma ji dabi, koda bawa ne yazama shugaba a gareku lallai wanda yarayu a cikinku da sannu zaiga sabani mai yawa.
Yakuma cewa:
"Na umarce ku kurike sunnata, da sunnonin halifofina shiryayyu.
Ku rike tada hakoranku (Fika), ku kiyaye fararrun ala’mura domin kowacce, bidi’a 6atace."
Abu dawud 4607 da Timizi yace wannan hadisi ne mai kyau ingantacce.
Ya Allah ka shiryar damu abisa sunnar Annabi (s.a.w).
***{HADISI NA 29}***
An karbo daga Mu’azu dan Jabal (R.A) yace:
Nace ya Manzon Allah bani labarin wani aiki dazai shigar dani aljannah ya kuma nisantar dani daga wuta.
Sai Manzo (s.a.w) yace:
Hakika kayi tambaya gameda abin da yake mai girma, saidai abune mai sauki ga wanda Allah ya saukake shi a gershi.
Ka bauta wa Allah batare daka hadashi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka kuma ka azimci Ramadan sanan ka ziyarci dakin Allah.
Sannan sai Annabi yasake cewa:
Shin kanaso na shiryar dakai kofofin alheri ba ?
Azumi garkuwane sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa yake kasha wuta haka sallar mutum a cikin yankin dare.
Sannan ya karanta (fadin Allah)
ayarnan dake cewa:
Gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu har yakai inda allah yake cewa ‘ya‘amaluun
sannan sai Annabi (s.a.w) yace:
kanaso nabaka labari kan Al’amari ba, da ginshikansa da kololuwar samansa ?
Sai nace eh ya Rasulullah.
Sai yace, kan al’amarin shine musulunci, ginshikinsa kuwa shine sallah, kololuwar samansa kuwa jihadi.
Sai Annabi (s.a.w) yace:
Kanaso nabaka labairn abin da yake mallakesu gaba daya ?
Sai nace Eh ya Rasulullah bani labari.
Sai yakama harshensa mai albarka yace karike wannan.
Sai nace shin yanzu za'a kamamu da Maganar da mukeyi ?
Sai Annabi yace kaiconka, akwai wani abin dayake kifar da mutane a wuta kan fuskokinsu, samada girbe-girben harsunansu.
Tirmizi ya rawaito hadisi (2616) yace hadisi ne mai kyau ingantacce.
Ya Allah ka kiyaye mana harshenmu
***{HADISI NA 30}***
An karbo daga Abu Sa’alaba Jursumu dan Nasihib (R.A). yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
“Hakiqa Allah Ta’ala ya farlanta farilla, kada ku wulakanta su.
Sannan ya sanya iyakoki, karku ketaresu.
Ya haramta wadansu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu.
Kuma yakyale wadansu al’amura don rahama a gareku, ba don mantuwa ba, karku bincike su.
Darukuduni littafinsa sunan (j 4/shafi na 184 da waninsa).
Ya Allah ka lullu6emu da rahamarka
***{HADISI NA 31}***
An karbo daga Abu Abbas Sahlu dan sa’ad Assa’idi (R.A) yace:
“Wata rana wani mutum yazo wajen Annabi (S.A.W) yace:
“Ya Manzon Allah!
Nuna min aikin da idan na aikata shi, Allah zai soni, mutane ma zasu soni.
”Sai (Annabi (S.A.W) yace:
”Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya kaunace ka, kuma ka nisanci abin dayake hunnun mutane, sai mutane su soka.
Ibnu Majah ne ya rawaito shi (4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.
Ma'ana:-
“Kayi zuhudu cikin lamarin duniya.
”Shine ya kasance mutum ya dauki duniya ba komai ba, abin da kawai zai bukata a cikin duniya, shine duk abin da yake wajibi, larurar rayuwa, abinda rayuwa take bukata kafin ta gudana a gidan duniya, wanda zai zamar maka dole a rayuwa shine ake bukata
***{HADISI NA 32}***
An karbo daga Abu Sa’id, Sa’ad dan Malid dan Sinan Al-Khudiry (R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:
“Babu cuta babu cutarwa.
Ibnu Majah ne ya rawaito shi, (2341) da kuma Darakuduni (228) da waninsu Musnadan.
Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwadda (Juzu'i na 2/shafi na 746).
Sharhi:-
Abin da ake nufi da “Babu cuta” Shine:
kada ka cuci wani, don ka mafana da wannan cutar tasa.
“Babu cutarwa” Kuma tana nufin kada ka cuce shi, koda bazaka amfana da wannan abin ba.
Misali mutum yanada kudi, sai kaje ka sace masa, kazo kayi amfani dasu.
Wannan shine ka cutar da wani don ka amfana.
Ko kuma, mutum ne yanada dukiya ko kadara, sai kaje ka konata, ka rabashi da ita, badon ka amfana da itaba.
Allah kabamu ikon kiyayewa.
***(HADISI NA33)***
An karbo daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce,
Manzon Allah Annabi (S.A.W). ya ce,
“Da za’a bai wa mutune dukkan da’awarsu, da wadansu sun yi da’awar dukiyar wadansu da jininsu’ sai dai hujja tana kan mai da’awa, rantsuwa kuma a kan wanda ya yi musu.”
Baihaki ne ya rawito shi a cikin litaffinsa sunan (J 10/sh 252). Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.
***{HADISI NA 34}***
An karbo daga Abu Sa’id Al-Khuduriy (R.A) yace:
“Naji Manzon Allah Annabi (S.A.W) yana cewa:
“Duk wanda yaga abin ki, to ya gusar dashi da hannunsa, idan bashi da iko, ya gusar dashi da harshensa, idan bashi da iko, to yaki abin a zuciyarsa, wannan shine mafi raunin imani.
(Muslim 49).
Allah kabamu ikon aikatawa
***(HADUSU NA 35)***
An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace.
Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace
“Kada ku rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin Allah ‘yan uwan juna. Muslim dan uwan muslim ne, kada ya zalunce shi, kada ya kuntatar da shi, kada ka yi masa karya, kada ya wulakantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku).!! Yana nuna kirjinsa,” Ya ishi mutum sharri, ya rika tozartar dad an uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi.
Muslim ne ya rawaito shi (#2564).
MA'ANA;-
Abin da ake nufi da hassada shi ne ka rika burin ina ma ni’imar da wane yake cikinta taho ta barshi ina ma dukiyar wane ta ragu jarinsa ya lalace ka rinka jin ina ma mukamin da ka baiwa wane yazo ya rasa to wannan itace hassad kuma siffa ce ta yahudu sun fi kowa sanin Annabi da siffofinsa amma hassada ta hana su yin imani dashi don haka, kayi kokarin ka wanke zuciyarka daga yi wa dan’uwanka musulmi hassada. Ko da mutum yana kokarin yin takara da kai kan wasu al’amura na duniya kai kar kayi takara dashi lallai mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa da haka.
Dangane da cewa,''....kada ku yi cinikin zure ....''kai ne kana da rumfa a kasuwa kana sayar da jakunkuna sai nazo zan sayi jaka muna ciki ciniki kace naira dari biyu ni kuma inacewa naira tamanin kawai sai wani dan kore yazo ya dauki irin wannan jakar yace don Allah ka sayar min da wannan jakar dari da hamsin, “ Shi wanda yazo yayi hakan din yayi ne fa don saboda ni yace Dari da hamsin ka sayar ? yace ‘aa’ to dari da sittin da biyar wai dole sai ya zurma ni na shiga a yi dakyar a sayar masa dari da saba’in bayan kuwa ciniki ne na bogi na karya ba gaskiya bane, don kawai ni in kai dari da saba’in, farashinta kuwa naira tamanin towannan shi ne kore, kuma duk malamai sunyi ittifakin haramcinsa dangane da yiwuwar cinikin kuwa, wadansu suka ce yayiwu wadansu kuma suka ce bai yiwu ba sai dai mafi ingancin magana, cinikin ya yiwu don shi wanda yazo wanna tayi ai ba da shi muka yi ciniki ba
wannan shi ne abin da imamu Malik Bin Anas yace.
Amma idan daga baya ka gane cewa wancan dan kore ne to kana da dama ka fiot ka mayar kace baka so a baka kudinka kuma dole ne a baka. In kuma ka ce shi kenan kai ka hakura kana son abin haka, ba komai ya halatta.
Abu na uku Annabi yace, kada ku zamanto masu kiyayya da juna kaje kana fushi da wani shi ma yana fushi da kai, wannan ma ba’a so abin fushi idan ya faru, to ayi hakuri a rarrashi zuiciya s ta hakura da manzon Allah yace kada ku juya wa juna bayanku yana nufin kar ku kaurace wa junanaku, ku yanke mu’amala da juna in dai an fara mu’amala kar ayanke ta a ci gaba sai in an riga an cuce ka ne to idan akazo za sake zaunawa sai kace a\a ai rannan ka cuce ni ba zan yarda ba. Sallah dai muyi tare, da Azumi komai ma muyi tare sai kuma Manzon Allah yace kada sashenku yayi ciniki acikin dan uwansa abin nufi idan mu biyu muna da haja ta kasuwani da muke sayarwa idan kwastoma ya shigo rumfata muna tsaye munacinikayya na sa masa suna yana tayi, to bai halatta ba kazo ka juye kwastoma nan kace, zo mana in sayar maka kasa da yadda ya baka. Bangare na biyu idan ni saye nake a wani wuri, nazo ina sayen kaya, an sami suna ina yin tayi bai halatta ba wani shi ma ya shigo yace shi ma zai sayi wannan kayan sai har ni na bari ba’a daidaita ba
Daga kashe manzon Allah yace, ku kasance bayin Allah ‘yan uwan juna musulmi dan uwam musulmi ne kada ya zalunce shi kada yayi masa karya kada ya kunyatar dashi ko kaki taimakonsa in ya nemi taimakon ka ka taimaka masa, kada ka wulakantar da shi wai don talaka ne ka bashi matsayinsa da ya dace dashi Aisha (R.A) tana cewa an umarce mu sauke kowanne mutum a matsayinsa. Manzon Allah ya karasa cewa “ ya ishi mutum sharrin ya rinka tozarta da dan uwanka musulmi don talaucinsa ko don karamin ma’aikaci ne ko don dan makaranta ne kauda nba ko komai bane. Snnan sai yace,''....Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne a kan musulmi.'' ma'ana, kowne musulmi game da musulmi dan uwansa, haramunne ya zubar da jininsa, ko ya cinye dukiyarsa, ko ya zubar da mutuncinsa. Shi ne, ko ka zge shi ko ka la'anceshi ko ka jefe shi da laifin da bai yi ba ka yi gini bisa ga zato haka kawai. To wannan duk dai bai haltta ba.
***{HADISI NA 36}***
An karbo daga Abu hurairata (R.A) daga Annabi yace:
Duk wanda kwantarwa mumini wani bakin ciki daga bakin cikin duniya to Allah zai kwantar masa da wani bakin ciki daga bakin cikin irin na kiyama.
Duk wanda ya kawo sauki ga wanda yake cikin tsanani, to Allah zai kawo masa sauki a duniya da lahira.
Duk wanda ya suturce musulmi to Allah zaiyi masa sutura a duniya da lahira.
Lallai Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawan ya kasance mai taimakon dan uwansa musulmi.
Duk wanda ya bi wata hanya tana neman ilmi a wannan tafarkin Allah zai saukaka masa hanyar shiga aljannah.
Babu wasu mutane da zasu taru acikin wani daki cikin dakunan
Allah suna karanta littafin Allah, suna darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai nutsuwa ta sauka kansu, rahama ta lullube su, (mala’iku sun kewaye su).
Sai kuma Allah ya ambace su a fadarsa.
Duk wanda aikinsa yayi sanda dashi, to dangatakarsa baza tayi gaggawa dashi ba.
(Muslim 2699) da wanan lafazi.
Allah ya datar damu ga babban rabo
***HADISI NA 37***
An kar6o daga Ibn Abbas (R.A) daga manzon Allah (s.a.w) daga abida ya rawaito daga ubangijin sa mai girma da daukaka yace;
"Hakika Allah ya rubuta kyawawa da munana sannan ya bayyana haka wanda yayi nufi da kyakykyawa be aikata ta ba Allah ze rubuta masa kyakykyawa cikakkiya guda daya
Idan kuma yayi nufi da ita (kyakykyawa) kuma ya aikatata Allah ze rubutamasa kyakykyawa guda goma 10, izuwa ninki dari bakwai 700, i zuwa ninki mai yawa,
Idan kuma yayi nufi da mummuna be aikatata ba Allah ze rubta masa kyakykyawa cikakkiya guda daya 1,
Idan kuma ya aikatata (mummuna) Allah ze rubutamasa mummuna guda daya 1"
(Bukhari 6491), (Muslim 131)
ma'ana=
wannan hadisin yana nuna irin rangwame da qaunar da Allah (s.w.a) yake yi ga bayin sa da kuma afuwarsa da rahamar sa
sannan ma'anar kyakykyawa shine:- kayi aikin al-khairi sannam da ladan da xa a baka
ma'anar mummuna shine;- kayi aikin sa6o da kuma xunubin da xa'a baka
Ya Allah ka bamu ikon aikata kyakykyawa
***Hadisi na 38.***
An karbo daga Abu Hurairata, (R.A) yace:
Manzon Allah yace:
Allah ta’ala yace duk wanda yayi gaba da waliyyina to na bashi sanarwa yazo yayi yaki dani.
Bawana bazai kusance niba, da wani abu da nafi kauna, sama da abin dana wajabta masa.
Bawana bazai gusheba yana kusanta ta da nafiloli har sai na zamanto ina kaunarsa, idan na kaunacee shi, sai na kasance jinsa, da yakeji dashi, da ganinsa da yake gani dashi da hannunsa da yake damka dahsi da kafarsa da yake tafiya da ita.
Wallahi idan ya rokeni zan bashi abin daya roka kuma wallahi idan ya nemi tsarina zan tsareshi.
Bukhari (6502).
Ma'ana =
Allah yana magana A wannan hadisin aka waliyan Allah (masoyan Allah) ba waliyan shedan ba
Ya UBANGIJI ka 'yantamu.
***{HADISI NA 39}***
An karbo daga dan Abbas (R.A) yace:
“Manzon Allah (s.a.w) yace:
Allah ya yi rangwame ga al’ummata abinda tayi bisa kuskure ko mantuwa da abinda aka tilastata akanta.
Hadisin ne mai kyau Ibnu majah ne ya rawaito shi (2045) da baihaki a
.
Ma'ana=
Wadannan abubuwa guda uku an yi rangwame ga Alummar Annabi (s.a.w) kuma wannan dayane daga cikin abin da yake Nuna falalarmu akan sauran al’umma da ba a basu wannan damar ba.
Mu kadaine muke da irin wannan damar, don yace a hadisin, Allah ya yi rangwame ga al’ummata wanan yana nuna sauran al’ummar da suka gabata basu sami wannan falalar ba
***{HADISI NA 40}***
An karbo daga Abdullahi dan Umar (R.A) yace:
Manzon Allah yadafa kafadata yace:
Ka kasance a duniya tamkar bako ko kuma wanda yake kan hanya.
Dan Umar (R.A) yana cewa:
Idan kakai yamma araye kar kayi tsammanin zaka kai safiya.
Idan kuma kawayi gari to kar kayi tsammanin zakakai yamma.
Kariki aikin alheri lokacin lafiyarka, saboda lokacin rashin lafiyarka.
Kariki aiki alhei lokacin rayuwarka, saboda ka amfana dashi a lokacin mutuwarka.
Bukhari (6416).
Allah yabamu ikon kiyayewa
***{HADISI NA 41}***
An karbo daga Abu Muhammad Abudullahi dan Amru dan As (R.A) yace:
Manzon Allah yace:
Imanin dayan ku baya cika harsai son zuciyarsa tayi biyayya ga abin da nazo dashi.
(Hakim 164) (khadib 368)
Hadisin ne ingatacce, mai kyau ingantacce.
Allah kaqara mana biyayya ga Annabi (s.a.w)
***{HADISI NA 42}***
An karbo daga Anas dan malik (R.A) yace:
Naji manzon Allah yana cewa:
Allah madaukakin sarki yana cewa:
Yakai dan Adam!
Lallai bazaka bauta min ba, kuma ka sa rai game da rahamata face saina gafarta maka ban damu ba.
Ya kai dan Adam da ace zunubanka zasu cika sashen sama gaba daya, sannan kanemi gafarata saina gafarta maka.
Yakai dan Adam da ace zakazo min da cikin kasa gaba daya zunubi ne sannan ka gamu dani, ba tare da ka hadani da kowa ba, nikuma zan kawo maka gafara, cikin kasa.
Tirmizi ne rawaitoshi (3540) yace hadisine mai kyau ingantacce.
Allahu Akbar , irin soyayyar da Allah (s.w.t).
Ya Allah ka gafarta mana zunubanmu baki daya.
***HADISI NA 43***
Ankar6o daga ibn Abbas (R.A) yace;
Annabi(s.a.w) yace;
"ku sadar da wajibai ga Ahlinta Abinda ya rage na daga wajibai to yana ga mutum namiji"
(Bukhari 6732) (Muslim 1615)
***{HADISI NA 44}***
An karbo daga nana Aisha (uwar muminai bada muna fukai yan shi'a) (R.A) tace:
Manzon Allah yace:
"shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa."
Bukhari da Muslim (2656) (1444) suka rawaito shi.
ma’ana
idan mace ta haife ka tana da matsayin mahaifiyarka bazaka aure taba, a shari’ance bazaka auri duk ‘yayan data haifaba, bazaka auri kannenta ba, domin sun zama kannen mahaifiyarka.
'Yayan data haifa sun zama kannenka.
To shine abinda hadisin yake nufi.
***{HADISI NA 45}***
An karbo daga Jabir dan Abdullahi (R.a) yace:
Naji manzon Allah (s.a.w) yace:
A shekarar bude makka a lokacin manzon Allah yana makka yana cewa:
"Lallai Allah da manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade, da gunki sai akace:
Ya manzon Allah bamu labari gameda kitsen mushe ana shafawa a jikin jirgin ruwa ana shafawa a fata ana kunna fitilu da shi.
Shin ya halatta ko bai halatta ba, ?
Sai Annabi yace a’a wannan ma haramun ne.
sannan sai manzon Allah yace:
Allah (s.w.t) yace:
Na la’anci yahudawa Allah ya haramta musu kitse sai suka kawata shi sannan suka sayar dashi, suka cinye kudinsa
Bukhari (2236) musleem (1581) sune suka rawaito shi .
Ma'ana=
Bai halatta ka sayar da giyaba, kar kace banasha, shi kenan sayarwa ma zunubi ne.
Haka kuma mushe, misali ragonka ya mutu yanzu yanzu nan sai wani arne kusa dakai yace kasayar masa sai kace tunda arne ne bari in sayar masa wannan bai halatta ba.
Sai dai kaje kajefar wani wuri in yaje ya dauka wanna bada yawunka ba.
Kun fahimci abinda hadisin yake nufi ko ?
***{HADISI NA 46}***
An karbo daga dan Abu Burda daga babansa.
Daga Musal Ash’ariy (R.A) yace:
Annabi ya turashi kasar Yemen saiya tambaye shi dangane da wani abin sha da ake yi acan sai yace menene abin?
Sai yace
“Albit’u da Almizru “sai akace da Abu burda menene Albit’u sai yace, wani tsimine da akeyi da zuma, almizru kuwa wani tsimi ne da akeyi da alkama.
Sai Annabi yace:
"Duk abu maisa maye haramun ne.
Bukhari ne rawaito shi (4343) .
Ma'ana.
Duk abinda zakasha yasaka tangal-tangal da nishadi haramunne,
Amma banda kamar irinsu Allurar bacci da akeyi a asibiti idan za'ayiwa mutum aiki. Saboda wannan larura ce,
Allah kashiryar damu akan tafarki madaidaici.
***{HADISI NA 47}***
An karbo daga Mikdamu dan Ma’adi Yakrib (R.A) yace:
Naji Manzn Allah (S.A.W) yana cewa:
"Dan Adam bai taba cika wani bokiti ko wani koko mafi sharri, sama da cikinsa ba.
Ya ishi dan Adam yaci wadansu yan lomomi wadanda zasu tsayar masa da gadon bayansa."
Ma'ana (Yunwa bazata galabaita shiba).
Idan dole sai yaci abinci dayawa sai ya kasa cikinsa kashi uku.
1. Kashi daya abinci.
2. Kashi biyu ruwa.
3. Kashi dayan ya barwa numfashi.
Ahmad 9 juzu'i na 4/shafi 132) da kuma Tirmizi 9 2380) da Ibnu majah (3349).
Tirmizi yace, Hadisi ne mai kyau.
ME AKE NUFI DA WANNAN HADISIN ?
Abinda yake nufi wannan shine ladabn cin abinci da Annabi ya koyar da mutane.
Annabi yace ka kasa cikin ka gida uku don haka sai wasu malamai sukace wannan abin da Annabi ya bayar shin umarnine na wajibi idan anqi binsa anyi sabo ko kuma shiryarwa ne ?
AMSA
Idan ka kama wannan abu ka kasa cikinka uku zaifi dacewa.
Amma idan ka kama wannan na biyun bakayi wani zunubi ba.
Allah ka tabbatar damu akan sunnar Annabi (S.A.W).
***{HADISI NA 48}***
An karbo daga Abdullahi dan Amru (R.A) daga Annabi yace:
“Abubuwa guda hudu wanda ya kasance tare dasu, toya kasance munafiki.
1. Idan yayi magana sai yayi karya.
2. Idn yayi alkwari sai ya saba.
3. Idan anyi rigima dashi, sai ya ketare dokar Allah.
4. Idan kuma aka bashi amana sai ya yaudareka yaci.
(Bukhari da Muslim) (34) ( 58) suka rawaito shi.
Allah kasa bama cikin wadannan siffofi.
***{HADISI NA 49}***
An karbo daga Umar dan Khaddab (R.A) daga Annabi yace:
"Da ace kun dogara ga Allah hakikanin dogaro, daya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye.
Suna sammako da yunwa amma suna dawowa da yamma cikinsu akoshe."
Imam Ahmad da Tirmizi da nasa’I da Ibnu Majah, da Ibnu Hibban da Imam Ahmad da Tirmizi da nasa’I da Ibnu Majah da Ibnu Hibban da Ahmad (2344) da Nasa’I a cikin sunan Alubra (Juz'i na 8/shafi na 79) Da hakim (418) Tirmizi yace, hadisin ne ingantacce.
Kuduba kugani 'yan uwa kullum tsuntsu da yunwa yake tashi, amma saboda dogaro da Allah daya tashi
Duk inda yanufa bazai dawo ba, saiya cika cikinsa da abinci.
(wamay ya ta wakkal alal lahi fahuwa hasbuh)
Ya Allah kaqara mana tawakkali gareka.
{HADISI NA 50}
An karbo daga Abdullahi dan Busur, (R.A) yace:
Wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi (s.a.w) yace:
Ya Manzon Allah shari’oi sunyi mana yawa a bamu wani babi cikakke da zamu rike.
“Sai Annabi yace:
kada harshenka yabushe wajen Ambaton Allah.
Ahmad ne ya rawaito shi (188, 190).

No comments:
Post a Comment