50 Hadith

Bismillahir-rahmanir-rahim


***HADISIN MU NA YAU***
.
.
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Wanda yayi karya a gareni. to ya tanadi mazaunin sa a wuta'
.
(Muslim).
.
Allah ya kiya shemu.
.
***HADISIN MU NA YAU***

An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Ku laqqantawa mamatanku 'LA ILA HA ILLALLAH'
.
(muslim).

Note:
Ma'ana: daga sanda kuka fahimci dan uwanki yazo gar-gara to ku laqanta ma sa kalmar shahada.

***HADISIN MU NA YAU***
. An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Idan mutum ya mutu Ayyukan sa sun yanke sai dai guda uku (3).
1.Sadaqatu Jariya (sadaka mai gudana).
2.Ilmi da ake amfanuwa da shi.
3.'Da na gari da zai dinga yi masa Addu'a.
.
(Muslim)
Allah ka sa muma mubar irin wadannan baya domin dinga samun Incom a lahira.

***HADISIN MU NA YAU***
.
.
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Wanda ya tuba kafin Rana ta bullo da ga Mafitarta Allah ya kar6i tuban sa'
.
(Muslim)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Salloli biyar da Jumu'a Izuwa Jumu'a. Da Ramadhana Izuwa Ramadhana Ana kankare zunuban da suke tsakanin su. Idan (mutum) ya nisanci manyan zunubai'
.
(Muslim)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Ba zaku shiga Al'jannah ba Har sai kunyi Imani. Baza kuyi Imani ba Har sai kunyi soyayya.
Shin bana shiryar daku a bisa wani Abu ba! Wanda Idan kuka aikata shi zakuyi soyayya!
'KU YADA SALLAMA A TSAKANIN KU'
(Muslim)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:
' Alamomin munafiki guda uku (3) ne:
1.Idan yayi zance se yayi karya.
2.Idan yayi Al'qawari se ya sa6a.
3.Idan aka amince masa se yayi Ha'in ci.
.
(Bukhari & Muslim).
Allah ka karemu daga fadawa daya daga wadannan munanan Hali.

***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''An qawata wuta da Abubuwan sha'awa, Sannan an qawata Al'jannah da abubuwan Ki''
.
(Bukhari & Muslim)
.
Note:
Ma'ana : Ita wuta an ka wata ta da abubuwan da zuciya take so take sha'awa Irin su kida da sauran kayan shaidan ci. Ita kuma Al'jannah An qawata ta da Abubuwa na Al'khairi wanda Ita zuciya take qin su.
.
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace: Hakika Annabi (s.a.w) yace:
.
''Wanda ya halarci Jana'iza yana da Kiradun guda (1) Wanda kuma ya halarce ta Har aka binne ta dashi (ya raka ta) yana da Kiradani guda (2) '
.
Sai Aka ce da Annabi (S.a.w) Menene Qiradaaa ni??
.
Sai Annabi (s.a.w) yace:- 'Misalin duwatsu biyu masu girma'
.
(Bukhari & Muslim).
.
Wannan gara6asa ce da kuma Falala ta zuwa Jana'iza ya Yan uwa se mu daura Himma domin samun wannan gara6asa.

***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace:
.
''Hakkin musulmi akan (dan uwansa) musulmi guda biyar ne:
.
1.Mayar masa da Sallama.
2.Duba shi Idan bashi da lafiya.
3.Zuwa masa Jana'iza.
4.Ka amsa masa gayyatar sa.
5.Kayi masa Addu'a Idan yayi Atishawa.
.
(Bukhari & Muslim).
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
' Na haneku da yin zato domin Hakika zato shine mafi karyar zance'
.
(Bukhari & Muslim)
.
.
Wannan Wasiyya ce da Annabin mu yayi mana fatan zamu kiyaye.
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace:-
''Wani mutum yazo wajen Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Ya Ma'aikin Allah!
.
Wane mutum ne yafi Can-Canta da na Kyautata masa???
.
Sa Annabi (s.a.w) yace:-
.
'Mahaifiyarka'
.
Sai mutumin yace Sannan wa??
.
Sai Annabi (s.a.w) yace: 'Mahaifiyarka'
.
Sai mutumin yace: Sannan wa??
.
Sai Annabi (s,a.w) yace: 'Mahaifiyarka'
.
Sai mutumin yace sannan wa??
.
Sai Annabi (s.a.w) yace: ' Sannan Mahaifin ka'
.
.
(Bukhari & Muslim)
.
Wannan Hadisin yana nuna mana yin biyayya ga Iyaye da kuma daraja Irin ta Mahaifiya wadda Annabi (s.a.w) ya mai-maita sau uku akan mahaifiya wannan ta sanya mu Yan Izala muka fi kowa biyayya ga Iyayen mu domin muna kwadaitar da su ga bin Allah Amman bama durqusa musu domin bama son su sa6awa Allah. A'a mu se dai Sunnah Sak babu sakin layi.

Note:-
Ba zan Tsawaita ba:
' Masu durquso sukan ce ai iyaye ne girma masu ake yi. Wannan gaskiya ne Amman fa ku tuna Allah ya fada a cikin suratun Nisa'i:- WA'IZA HUYYITUM BI TAHIYYATUN FA HAYYU BI'AH SANA MINHA AU RUDDUHA'
.
Ma'ana:
'Idan An gaisheku da gaisuwa to ku mayar da mafi kyawunta ko kuyi makamanciyarta'
.
To Idan ka durqusawa mahaifinka don gai suwa shi kuma yaya zeyi tunda an ce in anyi gaisuwa a maida Fiye da ita ko dai-dai da ita??
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Kalmomi Guda Biyu masu sauqi a bisa Harshe. Masu nauyi a ma'auni Masu Soyuwa ga mai rahama (Ubangiji) ' Kalmomin Sune:-

'SUBHANALLAHI WA BIHAMDIHI .
'SUBHANALLAHIL AZIM'

(Bukhari & Muslim)
Kunji Anbaton Allah bisa koyarwar Annabin sa ba bisa koyar war.....
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Hurairah (r.) yace: Annabi (s.a.w) yace:-
,
''Idan dayan ku ya farka daga baccin sa , ya face Hancinsa sau uku 3 Domin Hakika Shaidan yana yawo abisa Hancin''
(Bukhariy 23295, Muslim 238),
Wannan Hadisin Annabi (s.a.w) yana koya mana riga kafi da kuma tsafta,
Ya Allah don son da muke wa Annabin ka Da Iyalan Gidan sa ka bamu iko cikin biyayya ga Annabinka,
.
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Hurairah (r.a) Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Da badan kada na matsawa Al'ummata ba da na umarce su da yin asuwaki a kowance Al'wala''
.
(Ahmad 2460, Nasa'i 1/68, Ibn Khuzaimah 140,)
.
.
Ya Allah ka bamu Ikon riko da sunnar Annabin mu,
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abiy Hurairah (r.a) yace:- Annabi (s.a.w) yace:-
''Idan Kuda ya fada cikin abin shanku Ku dimiya shi sannan ku ciro shi, Hakika A cikin daya daga fuka-fukan sa akwai Cuta A dayan (Fika-fikin kuma akwai Waraka)''
A riwayar Abu Dawud ya kara da cewa ''Hakika Shi yana Fadawa ne da Fika-fikin da yake da cuta a cikin sa''
.
(Bukhari 3320,)
Annabin mu Likitan likitoci Ya Allah ka bamu Ikon koyi Da Annabin mu,
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi katada (r.a) Hakika Annabi (s.a.w) ya fada game da mage:-
.
''Hakika Ita ba najasa bace HAKIKA ita tana daga masu Kekkewayawa A gareku''
.
(Abu Dawud 75, Tirmidhiy 92, Nasa'iy 1/55, Ibn majah 367, ibn khuzaimah 104,)
.
Wannan a takaice yana nufin mage ba najasa bace ita,

***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Hurairah (r.a) yace : Annabi (s.a.w) yace:-
''Tsarkin Kwaryar (Abin al'wla) dayan ku Idan kare yayi lallage a cikin sa shine ya wanke shi sau ba kwai na Farkon su da kasa''
.
(Muslim 636)
.
A wata riwayar ta Tirmidhiy '' Na Farkon su dana Karshen su '' (Za'a wanke da kasa),
.
(Tirmidhiy 91),
.
Wannan ka'ida haka take har yau Amman wadan su maluman suna ganin amadadin kasa ka iya saka sabulu ko Omo da sauransu,
.
Amman abinda yafi don kariya shine kasa Kasar Domin ko da a yanxu binciken Likitoci na wannan Zamani sun tabbatar da Idan kare yasa baki To babu abinda ke iya kawar da kwayar cutarsa se kasar nan da Annabi (s.a.w),
.
Allahu Akbar kaji likitan likitoci, su se yanxu suka fahimta amman mu musulmai tuni Mun ringa munji kuma munyi Imani daga Annabin mu, Ya Allah kai salatin ga Annabin ka,
.
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace :- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Me abin hawa yayi sallama ga me tafiya a kafa me tafiya a kafa yayi sallama ga na tsaye (wadanda ba tafiya suke ba) marasa yawa su yiwa masu yawa ''
A wata riwayar ta Bukhari kuma:-
''Karami yayi ga babba'' (6231)
(Bukhari 216, Muslim 6232)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace:- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
''Idan kunji kukan zakara! Ku roki Allah daga falalar sa. Domin hakika mala'ika ya gani,
Idan kukaji kukan jaki! Ku nemi tsarin Ubangiji daga shaidan domin hakika shaidan ya gani''
(Bukhari 3303, Muslim 2729)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace :- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
''A cikin ranar jumu'a akwai wani lokaci musulim ba zai dace da ita ba shi yana tsaye yana sallah , Ya tambayi Allah Al-khairi Har sai Allah ya Kar6a masa''
.
(Bukhari 6300, Muslim 852)
Ya Allah ka bamu dacen wannan lokaci,
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi Huraira (r.a) yace:- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
''Hakika Allah yayi rangwame (Afuwa) ga Al-ummata Abinda ta zantar a cikin ranta ma tukar bata aikata ba ko ta zantar da shi''
.
.
(Bukhari 127, Muslim 5269)
Tunasarwa;
''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
Wannan hadisi yana nuna Allah yayi Afuwa / Yafiya ga mutane a dangane da Abinda suka raya a zuciyar su ba tare da sun aikata wannan Abinba ko sun xantar da shi to Allah baxe kama su da laifin sa ba,
''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
Ya Allah muna rokon ka kada ka kama mu da kura-kuran mu Allah ka gafarta mana laifukanmu don son mu da Annabinka na Hakika.
***HADISIN NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace:- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Allah (s.w.a) yace:- Dan Adam yana cutar dani yana zagin zamani Nine zamani Al-Amari yana hannuna Ina jujjuya dare da yini''
(Bukhari 7491, Muslim 2246)
***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace:- Hakika manzon Allah (s.a.w) yace:-
''Ubangijina mai girma da daukaka yana sakkowa izuwa saman duniya ko wane dare yana cewa:-
'Wa ze rokeni na Amsa masa??
'Wa ze tambayeni na bashi??
'Wa ze nemi gafarata na gafarta masa??''

(Bukhari 1145, Muslim 758,)
.
Yan uwa kunji gara6asa da bonus daga ubangijin mu ya Allah kabamu ikon neman gafarar ka da rokonka a koda yaushe.

***HADISIN MU NA YAU***
An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace :- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Wanda yayi Imani da Allah da ranar lahira kada ya cutar da da makocin sa ,
Wanda ya kasance yayi Imani da Allah da ranar lahira ya girmama bakonsa.
Wanda ya kasance yayi Imani da Allah da Ranar lahira Ya fadi Al-khairi ko yayo shiru''
(Bukhari 6136, Muslim 47)
Ya Allah kabamu ikon Aiki da sunnar Annabin mu,
***HADISIN MU NA YAU***

AN kar6o daga Abi huraira (r.a) yace:- ''An tambayi manzon Allah (s.a.w) 'Wane Aikine mafifi ci ?? Sa Annabi (s.a.w) yace:-
.
''Imani da Allah da manzon sa''
Sai Akace Sannan me? Sai yace:-
''Yin Jihadi saboda Allah''
Sai Akace sannan me? Sai yace:-
''Aikin hajji kar6a66e''
.
(Bukhari 26, Muslim 83)
•••HADISIN MU NA YAU•••
Ankar6o Daga Abi huraira (r.a) yace:
''Idan Dayan ku yayi Tahiyya ya nemi tsari da Abu hudu yace:
''ALLAHUMMA INNAI A UZU BIKA MIN AZABI JAHANNAM WAMIN AZABIL KABR WAMIN FITNATIL MAHYA WAL MAMATI WAMIN SHARRI FITNATIL MASIHID DAJJAL''
(musulim 577)
Allah ka tabbatar damu kan sunnar Annabin ka da yin riko da ita takalmin kaza

•••HADISIN MU NA YAU•••
Ankar6o Daga Abi huraira (r.a) yace:
''Mafi Al-khairin ranar da rana take 6ullowa ranar jumu'a , Acikinta aka Halicci Annabi Adam Acikinta aka shigar dashi Al-jannah A cikinta ya fita daga cikinta''
(Muslim 854)
•••HADISIN MU NA YAU•••
Ankar6o Daga Abi huraira (r.a) yace:
''Wanda ya tuba kafin rana ta fito daga mafadarta , Allah ze kar6i tubansa''
(Muslim 2703)
Ya Allah ka kar6i tubanmu ka gafartama kura-kuran mu


•••HADISIN MU NA YAU•••
.
Ankar6 Daga Abi huraira (r.a) yace:
.
''Hakika Annabi (s.a.w) yace:
.
''Allah s.w.a yace: Dukkan Ayyukan dan Adam na gare shi Sai dai azumi hakika shi nawane ni xan bada ladanshi Warin bakin me azumi yafi dadi awajen Allah fiye da kanshin Al-miski''
.
(Bukhari 5927. Muslim 1101)
***HADISIN MU NA YAU***
.
Ankar6o Daga Abi huraira (r.a) yace:
.
''Hakika Annabi (s.a.w) yace:
.
''Allah yace: Ka ciyar ya dan Adam Zan ciyar agareka''
.
(Bukhari 5352. Muslim 993)
.
Allah kabamu iko da damar ciyarwa domin mu samu ciyarwar Allah madaukakin sarki

***HADISIN MU NA YAU***
Ankar6o Daga Abi huraira (r.a) yace:
.
''Hakika Annabi (s.a.w) yace:
.
''Allah ba ze dube shi ba ranar Al-kiyama wanda ya take tufafin sa da girman kai''
.
(Bukhari 2087, Muslim 5788)
Allah ya karemu daga wuce iayaka irin na yan bidi'a
An kar6o daga Abi Huraira (r,a) Hakika manzon Allah (s.a.w) yace;-
''Idan dayanku ya kyautata musuluncinsa dukkan kyakykyawan aikin da ya aikata xa'a rubuta masa kwatankwacinta guda goma Izuwa ninki Dari bakwai dukkan mummunan aikin daya aikata xa'a rubuta masa misalinta guda daya''
(Bukhari 129, Muslim 42)
Y'an uwa kunji yadda Allah yake son mu da rahamar sa se mu dage da bauta masa ba tare da miss ba
.
Ya Allah muna rokon ka ninninka mana Hasanat din mu



An kar6o daga Abi Huraira (r.a) Hakika manzon Allah (s.a.w) yace:-
.
''Shaidan yana zuwa ga dayan ku se yace : Waye ya halicci kaza! Waye ya halicci kaza!! (har sai yace) waye ya halicci ubangijin ka!!! Idan kaji haka Ka nemi tsari daga ubangiji''
.
(Muslim3276, Muslim 134)
.
.
Ya Allah ka karemu daga sharrin shaidan da mabiyansa



***{HADISIN MU NA YAU}***
.
An karbo daga Abu Huraira Abdur-rahman dan Sakhrin (R.A) yace:
.
Naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
.
"Duk abin dana haneku toku nisance (ku bar aikatashi) abin dana umarceku dashi to kuzo dashi gwargwadon iko.
Hakika yana daga abinda ya hallakar da mutanen dake gabanku shine yawan tambayoyinsu da sabawarsu ga
Annabawansu.
.
(Bukhari 7288) da (Muslim 1337).
------------------------------
Annabi (s,a,w) yahana sahabbansa yawan tambayoyi domin kada su takurawa kansu, akan abin da Allah bai dora musuba.
.
Ya Allah kaqara mana biyayya ga annabi Muhammad (s.a.w)



•••HADISIN MU NA YAU•••
.
An kar6o daga salim daga mahaifin sa (r.a) yace
.
"Haqiqa manzon ‪#Allah(s.a.w) yace"
.
""Babu hassada se ga abu guda 2 mutumin da #Allah ya bashi Al-qur ani yana bitarsa dare da rana
mutumin da #Allah ya bawa dukiya yake ciyar da ita (ta hanyar Allah) dare da rana""
.
(Bukhari da muslim)
¤¤¤ {HADISIN MU NA YAU} ¤¤¤
.
¤¤An kar6o daga Abi huraira (R.A) Hakika manzon ‪#‎ Allah(s.a.w) yace'
.
¤" Kada dayan ku yayi burin mutuwa im ma dai me kyautatawa (me aikin al-khairi) ne tana yiwuwa yaqara (aikin al-khairin)"¤
.
¤¤{Bukhari 7235, Muslim 2682,}¤¤
.
¤A wata riwaya ta Bukhari ya qara da cewa'
.
¤"Idan me sa6o ne tana yiwuwa ya daina"¤



{HADISIN MU NA YAU}
.
an kar6o daga Abi hurairah (R.A) yace
.
"Hakika manzon ‪#Allah(s.a.w) yace"
.
Wani mutum yana tafiya akan hanya se yaga wata kaya (me cutarwa) se ya kawar da ita (ya dauketa daga kan hanya) se Allah ya gode masa kuma ya gafar ta masa
.
(bukhari 654) & (muslim 1914)
.
A wani hadisin me Alaqa da wannan manzon rahama (s.a.w) yace kawar da qazanta daga kan hanya sada qa ce
---------------------------------------
Ya #Allah ka sanya mu cikin masu samun rahamar ka a wannan wata me Al-barka



••• ¤{HADISIN MU NA YAU}¤ •••
.
An kar6o daga Abi musa (r.a) yace;
.
Annabi (s.a.w) yace:
.
••• "Hakika ‪#Allah mai girma da daukaka yana shimfida hannunsa da daddare (na qudura) domin kar6ar tuban masu sa6o da rana sannan yana shimfida hannunsa da rana domin kar6ar tuban masu sa6o da daddare har sai rana ta fito daga mahudarta" •••
.
••(muslim 2759)••
••A wata ayar kuma Allah (s.w.a) yace"
.
••"ku nemu gafarar ubangijin ku haqiqa shi me gafara ne"••
.
(suratu nuh 10)
.
Haqiqa #Allah yana qaunar bayinsa ya #Allah ka gafartamana zunuban mu



(HADISIN MU NA YAU)
.
An kar6o daga Anas dan malik (R.A) yace:
.
  :manzon Allah (s.a.w) yace:
.
"Kuyi sahoor domin cewa acikin sahoor akwai Al-barka"
.
(Bukhari & Muslim)
.
A wani hadisin kuma daga Anas dan malik da zaid bin sabit (R.A) sukace:
.
:Munyi sahoor da manzon Allah (s.a.w) sannan muka tashi izuwa sallah.
.
Anas yace" sai nace wa zaidu :
.
'Nawane tsakanin kiran sallah da sahoor??
.
Sai zaidu yace" gwargwadon karanta aya 50
.
(Bukhari & Muslim)
.
saboda haka anso jinkirta sahoor sannan a gaggauta buda baki
.
Ya ‪#Allahmuna roqon ka kasamu daga cikin bayinka da kake yan tawa a cikin wannan wata mai al-barka



¤{HADISIN MU NA YAU}¤
.
An kar6o daga Mu'awiyya (R.A} yace;
.
Annabi(s.a.w) yace;
.
"WANDA allah yake son shi da Al-khairi se ya sanar dashi Addini"
.
(Bukhari, 7312; Muslim, 1037)
.
Ya Allah ka sanar damu Addinin ka kuma bamu ikon aiki dashi­



{HADISIN MU NA YAU}
An kar6o daga Uqbatu bin Amir yace;
'Annabi (s.a.w) yace:
.
" Wanda yayi Al-wala sannan yace:
.
" Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya sannan ya shaida Annabi muhammad (s.a.w) bawan (Allah) ne kuma manzon sane,
.
Za'a bude kofofin Al-jannah guda 7 a gareshi ya shiga ta inda yaga dama"
¤[Muslim, 234]¤
.
Fadin wannan kalma ba wai ta tsaya ne ga furuci kawai ba se ka qudurce a zuci kuma kai biyayya ga Allah da manzon sa,
.
Allah ka kar6i ibadun mu a wannan watan


*** ¤{HADISIN MU NA YAU}¤ ***
.
¤An kar6o daga Abi sa'eedul khudri (R.A) yace:
.
Annabi(s.a.w) yace:
.
¤" Wanda ya yarda da Allah shine ubangiji ya yarda da Addinin musulunci Da kuma Annabi muhammad (s.a.w) Al-jannah ta wajaba a gare shi"¤
.
(Abu dawud 1529)
.
¤"An kar6o daga Anas (r.a) yace :
.
Annabi (s.a.w) yace:
.
¤" Babu dayan ku da ze shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi muhammad (s.a.w) manzonsa ne yana mai gasgatawa a cikin zuciyarsa face sai Allah ya haramta wuta a gareshi"¤
.
(Bukhari 128, Muslim 32)
.
Imani da Allah da manxon sa baya taqaita ga furici kawai face se kayi aiki da shi don haka ba wai kace a baki ka yarda da Allah ba kuma kana yin Abinda ya sa6a da koyarwarsa dole se kabi abinda yaxo da shi shine kai imani dashi,
.
Allah yasa mu dace



{HADISIN MU NA YAU}
.
An kar6o daga Abi Hurairah (r.a) yace
.
"Hakika manzon Allah (s.a.w) yace"
.
"" A cikin rana jumu@ a kwai wani lokaci mu sulmi ba ze dace da shi ba yana mai addu'a face idan ya roqi ‪#Allah Al-khairi ze bashi (za'a amsa addu arsa)
.
(bukhari 6400) & (muslim 802)
.
***An kar6o daga Abi hurara {r.a} yace:-
.
Annabi {s.a.w} yace:-
.
''Bawa {mutum} ba ze suturta bawa ba har sai Allah ya suturtashi a ranar lahira''
.
{muslim}
.
Allah ka samu cikin wadanda Allah ze suturta
.
A wani hadisin na Abu huraira yace:- Annabi {s.a.w} yace:-
.
''Duniya kurkukun mumini ce kuma Al-jannar kafiri''
.
{muslim}
.
A wani hadisin na Abi hurairah yace:-
.
'Badade na {yana nufin Annabi s.a.w} yayi min wasiyya da Abu guda uku
.
1.Azumin kwana uku a kowane wata
.
2.Sallah duha {walaha}
.
3. Nayi wuturi kafin nai barci
.
{Bukhari & muslim}
.
Ya ‪#‎ Allahka bamu ikon riko da sunnar Annabin mu garam gam

 


1 comment: