Islamic





Bismillahir-rahmanir rahim
 إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

MATA 10 WADANDA ALLAH YA TSINE MUSU:
1-Mata masu tsaga fuskokinsu
2-Mata masu aske gashin ido
3-Mata masu kankare hakori (hushirya)
4-Mai karin gashi da wadda ake karamata
gashin
5-Matar da mijinta yayi fushi da ita
6-Mata masu shigar maza
7-Mata masu yawan ziyartar kabur-bura
(makabarta)
8-Mata masu kururuwa akan mamaci
9-Mata masu auren kashe wuta
10-Mata masu bayyana tsiraicinsu.
Manzon Allah saw yace: 'Yaku taron mata!!
kuyi
sadaqa, kuma ku yawaita neman gafara
؛
(istigfari)

ALJANIN BANDAKI
================
_Nau'in Aljanu masu zama a bandaki_
Wato *Khadimul Hammam*

 

*_Khadimul Hammam_* wasu nau'in Alajanu ne masu zama a bandaki ko bola ko kuma dukkan wani wajen kazanta da dauda.
Bandaki shi ne inda suka fi zama da iyalansu domin a nan ne suka fi samun abinda suke bukata.
Wadannan Aljanu masu zama a bandaki galibinsu ko kuma dukkanninsu Arna ne kuma Mugwaye masu hadari sosai.
Suna zama a bandaki suna kallon tsaraicin mutane kuma tanan ne suke samu su shiga jikin 'yan-Adam har su saka musu wannan cutar da ake kira sanyi ko sabara ko kuma toilet infection a turance, wato cututtukan da ake dauka a bandaki.
Khadimul Hammam sune Aljanun da Bokaye suke amfani da su wajen sanyawa mutane Warin_Jiki ko Warin_Ja6a kamar yadda wasu suke kiran cutar. Wato idan akay wa mace irin wannan Asiri to duk wanda ya zo da nufin aurenta sai ya ji tana wani irin wari ko doyi mara dadi, haka ma in matar aure ce sai mijinta ya dinga ji tanay masa doyi amma ita ba ta jin doyin kuma ba wanda zai ji sai me neman auren na ta ko kuma mijin na ta.
Sai ka ga mace duk wanda ya zo zance wajenta ba ya dawowa kuma ta rasa dalili.
Irin wadannan Aljanu mazauna bandaki sune suke sa Bokaye su binne layoyi a masai ko a bandaki. Sukan sa mutum ma ya karanta Alqur'ani a bandaki ko ya karanta wasu dalasimai na sihirin bokanci don ya samu kusanci izuwa gare su.
Ba sa yadda su zauna tare da mutum sai ya zama cikakken kazami me yawo da dauda da janaba kuma mara son ibada mara imani.
*ABUBUWAN DA KE SAWA ALJANIN BANDAKI YA SHIGA JIKIN MUTUM*
_Wadannan wasu abubuwa ne da suke sawa Aljanun bandaki su shiga jikin Dan-Adam su zauna har su dinga cutar da shi_.
_1- Rashin tsaftace bandaki._ Idan ana barin bayi yana doyi da wari ba a kula da shi ana tsaftace shi, to Aljanu za su zauna aciki kuma za adauki cututtuka.
_2- Yin fitsari ko bayan gida tsirara._ Idan mutum yana cire kayansa tsaf ya ajjiye a gefe lokacin da zai yi fitsari ko bayan gida, yana sawa Aljanu suy sha'awarsa su shiga jikinsa.
_3- Kallon gabas ko juya mata baya yayin bayan-gida ko bawali._ Ba a so mutum ya kalli sashin Ka'abah ko ya juya mata baya lokacin da yake bayan gida, hakan yana sa Aljanu su ga tsiraicin mutum.
_4- Yin tsarki da kashin dabba ko qashin dabba_ domin abincin Aljanu ne.
_5- Yin surutu ko maganganu marasa amfani a bandaki._ Ko yin waya ko jin kida da dai sauransu, yana sa su shiga jikin mutum.
_6- Rashin wanka da zama da kazanta ko janaba._ Yana sawa su shiga jikin mutum domin sun ga dan'uwa.
_7- Zama_ a kofar bandaki ko a bola ko juji ko dukkan gurare masu kazanta.
_8- Sihiri._ Koda ba ka yin wani daga abubuwan da muka ambata to da akwai sharrin masihirta 'yan bid'a da suke tura wa mutane Aljanu jikinsu.
Ana iya siyen irin wannan Aljani a tura shi jikin mutum don ya mayar da shi kazami kuma mai baqin jinj acikin al'umma.
*ABINCIN KHADIMUL HAMMAM.*
_Abinda Aljanin bandaki yake ci ya rayu._
1- Yana lasar tsummokaran jini da mata suka ajjiye a bandaki basu wanke ba.
2- Suna cin bayan_gidan me shiga bandaki ba ya addu'a.
3- In bandaki yana da kazanta to suna tarewa a ciki.
_YADDA ZA KA GANE ALJANIN BANDAKI YA SHAFE KA_
_Idan har wannan Aljani ya shafeka, ko kuma an tura maka shi ta hanyar sihiri, to ga wasu alamomi da za ka fuskanci hakan a jikinka._
1- Mutum zai dinga _dadewa a bandaki_, ay ta jiransa ya ki fitowa kuma ba abinda yake aciki sai tunani.
2- Yawan ganin wani mutum ko wata mata a bandaki ko kuma ganin abin tsoro a ciki.
3- Mutum zai zama me zama da kazanta da kuma rashin son yin tsafta. Za ka iya samun budurwa ba ta wanka sai an mata duka. Ko kuma magidanci yay sati bai wanka ba.
4- Za ka dinga yawan jin _warin kashi_a jikinka ko a kusa da kai. Har dinga tunanin ko a bandaki ka shafo kashin amma ba zaka ganshi ba.
5- Mutane za su dinga gudun mai lalurar basa son zama da shi. Domin suna jin yana wari, shi kuma ba ya ji. Saidai kawai ya fuskanvi mutane suna kyamarsa amma bai san dalili ba.
6- Rashin son yin Sallah da karatun Alqur'ani da sauran ibadu.
7- Mai lalurar zai dinga ganin kimar bandaki da muhimmancinsa fiye da ko ina. Don haka yana da son kasancewa a bandaki.
8- In mutum ya shiga bandaki sai ya ji ya fi nutsuwa da samun nishadi. Wani ko kudi zai kirga ya fi so ya shiga bandaki.
9- Yin surutai haka kawai a bandaki. Ka ji mutum yana magana shi haka, saidai hakan ya fi faruwa ga yara.
10- Za ka dinga jin kamar motsi ko kuma anay maka magana in ka shiga bandaki.
11- Yawan shiga bandaki ba tare da wani dalili ba.
12- Jin kamar an caka maka allura ko kibiya a tsaraicinka lokacinda kake biyan bukata a bandaki.
13- Kaikayin-gaba mara jin magani.
14- Kurajen_gaba marasa jin agani.
15- Fitar farin_ruwa_mai wari musamman ga mata.
16- Yawan ganin kashi a inda kake zaune ko kuma jikin tufafinka.
17- Warin jiki ko warin qashi mara jin magani.
18- Mace zata dinga jin kamar wani abu zai fito daga gabanta kuma sai ya ki fitowa. Kullum yanay mata amma in ta je asibiti za ace ba a ga komai ba.
18- Rashin sha'awa da jin zafi lokacin saduwa.
19- Fitar ruwa mai wari da kuma yin al'ada bakikkirin mai doyi.
20- Yawan kasala musamman lokutan sallah.
Da dai sauran alamomi makamantan wadannan.
*NEMAN TSARI DAGA SHARRIN ALJANIN BANDAKI.*
_In kana kula da wadannan insha Allahu wadannan Aljanu ba za su samu damar ra6arka ba._
1- Cire zobe idan za ka shiga bandaki.
2- Karanta addu'ar shiga bandaki.
* ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ ﻭﺍﻟﺨﺒﺎﺋﺚ *
wato *_"Allahumma inniy a'uwzu bika minal khubuthi wal khaba'ithi"._*
3- Shiga bandaki da kafar hagu.
4- Fitowa daga bandaki da kafar dama.
5- Fadar *_ ﻏﻔﺮﺍﻧﻚ _*
wato *_"Gufra nak"_* bayan fitowa daga bandaki.
6- Yawan tsafatace bandaki.
7- Ka lazumci zama da tsarki da kuma zama da alwala.
8- Yawan karatun Alqur'ani da Azkar.

*MENENE DANNAU?*
Dannau shi ne lokacinda mutum ya kwanta yana bacci, sai ya ji kamar an zo an danne shi, an shake masa hanci da baki, ba ya iya motsi ko numfashi ko magana kuma yana ihu amma ba a ji. Mutum ya kan cika da tsoro da tunanin mutuwa lokacinda abun yake faruwa da shi.
Kashi uku zuwa shida bisa dari (3-6%) na mutanen duniya suna fama da matsalar Dannau. Yayinda kashi talatin bisa dari (30%) na matasa kuma suna fama da wannan matsala, aqalla kowanne acikinsu ya ta6a fuskantar matsalar Dannau ko da sau daya ne a shekara.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ .
A gargajiyar Bahaushe, Dannau wani Aljani ne da yake zuwa ya hau kan mutum lokacin da yake bacci, ya shaqe shi, ya hana shi sukuni.
A binciken da Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah ta gudanar, ta gano wadansu abubuwa da suke kawowa `yan Adam matsalar Dannau wadanda suke da alaqa da Aljanu da kuma masu nasaba da abubuwa na zahiri wadanda ba na Aljanu ba.
Menene Dannau?
Akan samu wasu na'in Aljanu da suke zuwa su hau kan ruwan cikin mutum, su daddanne shi, su shaqe shi, sannan su toshe masa kafofin fitar iska kuma su daure masa jijiyoyi. Sukan zauna akan mutum daga `yan mintuna zuwa `yan awoyi, har sai sun gama yi masa abinda ya kawo su.
ALAMAR ALJANI YANA SO YA DANNEKA.
Tun kafin bacci ya dauke ka, Aljanin zai iya zuwa ya tsaya akanka, yana jira kay bacci, ya danneka.
Ga alamomin da zak gane.
1- Kafin abin ya faru, za ka fara jin ciwon kai ta qeyarka, kafin bacci ya dauke ka.
2- Faduwar gaba, lokacin da ka dan fara gyangyadi.
3- Jin nauyi a kafadarka, kamar ana daddanna maka.
4- Mutuwar jiki gaba daya, musamman in kana so ka tashi kay alwala kafin bacci. Karshe dai saidai ka kwanta haka.
5- Mutum zai ji ya kasa yin addu'a kafin bacci, ko kuma ya ce sai an jima zai yi.
6- Idan ka fara yin bacci sai ka ji kamar an zungureka ka farka.
7- Jin tsigar jikinka tana tashi kafin bacci.
8- Wani zai ga kamar ana giftawa ko ya dinga jin motsi a wajen kwanciyarsa.
9- Za ka ji kamar ka zama dan mitsitsi ko kuma ka zama gingimeme, ka cika daki.
10- Mutum zai ji kamar ana yin sama da shi, ko kuma kamar ana gudu da shi a mota.
Dadai sauran alamomi.
Wadannan alamomin da muka ambata, suna nuna cewa Aljani ya zo kusa da kai, yana jira kay bacci ya danneka.
ALAMOMIN DANNAU, LOAKCIN DA YA DANNEKA.
1- Farkawa daga bacci cikin mugun firgici da bugawar zuciya mai karfi.
2- Toshewar kofofin iska ta yadda mutum zai kasa magana da numfashi. Za ka ji kana so kay ihu ko addu'a amma ka kasa ko kuma kana ihun amma ba ya fita.
3- Daurewar jijiyoyin jiki. Wato mutum ya kasa motsa kowace ga6a ta jikinsa, kamar hannu ko kafa da dai sauransu.
4- Jin alamun hannuwan mutane ko wasu halittu suna daddanneka ko suna shaqeka. Wani lokacin ma mutum yana kallon Aljanun da suka danne shi ido da ido.
5- Ganin wani mutum ko wasu mutane sun shaqeka, suna dura maka wani abu a bakinka.
6- A lokacin da abun yake faruwa da kai, zaka ji kana jin dukkan abubuwan da mutanen gidanku suke yi. Kana jin maganganunsu kuma kana fahimta. Ma'ana hankalinka bai gushe ba, saidai kamar matacce kake jinka, don ba abinda kake iyawa.
Amma fa wannan yana faruwa ne a tsakanin bacci da ido biyu, ba mafarki ake ba. A zahiri yake faruwa da mutum.
ME YASA ALJANU SUKE DANNE MUTANE?
Ba kowanne Aljani ne Dannau ba, sai dai akwai irin Aljanun da suke danne mutane da kuma dalilai mabambanta da suke sawa suyi hakan.
Nau'in Aljanun da suka fi danne mutane su ne Jinnul Ashiq, Jinnut tayyar, Jinnul Qariyn, Jinnul Katfa, da kuma Jinnus sihr. Wadannan nau'in Aljanu duk mun yi bayani akansu tun a baya, amma dai mai bukatar karin bayani akansu zai iya tuntu6ar shafin bashir.halilu@yahoo.com
Daga cikin abubuwan da suke sa wa Aljanu su danne mutane.
1- Wasu Aljanun, musamman Jinnul Ashiq, suna danne mace ne in tana bacci don su samu damar saduwar jima'i da ita. A irin wannan hali ne mace zata ga gardi ya danneta, ya shaqe mata baki, yana saduwa da ita. Kuma in ya gama ya tafi, sai taga jikinta ya 6aci da maniyyi.
Haka ma idan namiji ne, zai ji ko yaga wata mace ta danne shi, tana wasa da gabansa, kuma in ya farka zai ga ya 6ata jikinsa.
2- Aljani yakan danne mutum ne don ya samu damar zuba masa guba ajikinsa. Aljanu, musamman Jinnus Sihr, suna zuwa su zubawa mutum guba a bakinsa ko a al'aurarsa, to amma ba za su iya ba sai in mutum yana bacci sannan su zo, su dura masa ta karfin tsiya.
3- Akwai Aljanu masu danne mutum don su cire masa wani abu daga jikinsa. Ya fi faruwa da mata masu ciki. Sai mace taga wadansu sun danneta, sun caka hannu a gabanta ko a cikinta, sun ciro wani abu. Daga nan sai taga jin ya 6alle mata, ko ta tashi da ciwon mara mai tsanani, in kuma tana da ciki sai ya zube. Haka ma Aljanu mashaya jini. Suan danna mutum su tsotsi jininsa ko ruwan jikinsa.
4- Wani Aljanin tsananin rashin lafiya ce take damunsa amma wannan ya fi faruwa lokacin sanyi. Wani Aljanin in tsananin rashin lafiya ta dame shi, ya san yadda zai yi ya juyewa dan-Adan ita, don shi ya samu sauki. Don haka sai ya danneka, yay maka aman guba, yay tafiyarsa.
5- Haka kuma idan Aljaninka ba ya so ka tashi da wuri don aikata wani aiki, to zai zo, ya danneka, ya shaqeka.
6- Wasu Aljanun, kamar Jinnul Katfah, ba su da kwarin kafafuwa. Don haka duk sa'adda suka ra6i mutum saidai su danne shi su abokance shi, don in suka bari ya tashi ya tafi ba za su iya binsa ba, kuma ba su da kwarin kafafuwa sannan ba sa jurewa tsayuwa.
Wannan a takaice kenan.
YADDA ZA KA GANE AL-JANI NE YA DANNEKA, BAYAN KA WATSTSAKE.
1- Za ka tashi kaga Azzakinka a miqe, ma'ana Aljana ta biya bukatarta da kai, ta tafi.
2- Ko mace ko namiji, zaka tashi, kaga ka 6ata jikinka da maniyyi.
3- Idan gari ya waye, za ka ji wajenda suka danne maka yanay maka ciwo. Sawa'un ciki ne ko kirji ko mara ko kuma akanka suka zauna.
4-Tashi da ciwon kai, musamman ta keya da kuma jin alamar baccin bai isheka ba.
5- Galibi mutum ya kan wuni gabansa yana faduwa.
Da dai sauransu.
YADDA ZAKA GANE AL-JANI YA DANNE WANDA YAKE KUSA DA KAI.
1- Akwainwani Bawan Allah da ya ta6a gaya min cewa, sha'awar matarsa ta dauke, kwata-kwata ba ta sha'awar mijinta ko gamsuwa da yayin jima'i. To amma in tana bacci sai yaga tana wasu abubuwa kamar ana saduwa da ita. In ya tasheta daga baccin ya tambayeta meke faruwa?!, sai ta ce masa ai wani ne yake saduwa da ita, kuma tana jin dadi.
Don haka daga cikin alamomin da zaka gane Aljani ya danne na kusa da kai, akwai ganin yana wasu abubuwa kamar mai yin jima'i, a yayin da yake bacci.
2- Ganin idon mutum yana jujjuyawa lokacin da yake bacci. Wannan dai ita kadai ce babbar alama, domin ba wata ga6a ta jikin mutum da take iya motsi. Saidai a wasu lokutan wani har bige-bige yana iya yi, tare da ihu
BAMBANCIN MAFARKI DA DANNAU.
Shi mafarki kwata-kwata mutum bai san abinda yake faruwa a kusa da shi ba kuma mutum zai iya ganin an dauke shi zuwa wani waje daban. Mafarki acikin bacci ake yinsa, ba a ido biyu ba.
Yayinda shi kuma Dannau hankalin mutum ba ya gushewa, saidai ya kasa sarrafa ga6o6in jikinsa, kuma mutum ba zai ga an kai shi wani waje daban ba.
Don haka Dannau a hakika yake faruwa, ba tunani bane kuma ba mafarki bane.
ME YAKE JANYOWA MUTANE MATSALAR DANNAU?
Kamar yadda mukay bayani a farko, mafi yawan masu fama da matsalar Dannau matasa ne, domin kashi talatin bisa dari 30% na matasan duniya suna fama da wannan matsala.
Yanzu ga wasu dalilan da suke janyowa Aljani ya zo ya danne mutum.
1- Rashin kwanciya da tsarki ko alwala.
2- Rashin yin addu'ar kwanciya bacci.
3-Kwanciya Rub-da-ciki, ko rigingine ko kwanciya a 6arin hagu.
4- Kasancewar mutum dama can yana da matsalar Aljanu.
5- Asiri. Idan aka aiko Aljani don ya zuba maka wani abu ajiki.
6- Bude tsaraici yayin kwanciya bacci, na iya sawa Aljani ko Aljana suyi sha'awar kwanciya da mutum.
7- Shaye-shayen kayan maye. In mutum yana shaye-shaye, hakan yana janyo Aljanu `yan shaye-shaye `yan uwansa su dinga zuwa suyi maye akansa.
8- Kaiwa tsakar dare ana yin abinda Aljanu suke so. Wato mutum ya raba dare yana jin kida da waka, ko kallon bidiyo da makamantansu.
19- Kwanciya a mazaunin Aljanu ko kwanciya akan `ya`yan Aljanu. Mun yi bayani akan Guraren zaman Aljanu tun da dadewa.
Da dai sauransu.
ME MATSALAR DANNAU ZATA IYA JANYOWA MUTUM?
Idan mutum yana yawan samun matsalar Dannau, za ta iya kai shi ga:
1- Rashin samun bacci. Wanda shi kuma zai haifar masa da matsaloli masu yawa.
2- Yawan ciwon kai.
3- Yawan bugawar zuciya, wanda shi ma zai iya janyo masa matsaloli da yawa.
4- Makuwa. Abinda ake nufi da makuwa shi ne, lokacin da mutum yake cikin tafiya, sai kwai yaga ya daina gane hanya, koda kuwa a unguwarsu ne ko wajen da ya sani. Mutum zai ga kamar bai san wajen ba, saidai ya tambaya ko kuma a kai shi gida. Saidai wannan ta fi faruwa da tsofaffi da yara.
5- Matsalar Dannau tana shafar kwakwalwa kai tsaye. Wanda hakan zai iya haifar da matsaloli masu yawan gaske.
YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR DANNAU.
1- Yin tsarki da alwala kafin kwanciya bacci.
2- Tsaftace wajen kwanciya da nisantar guraren zaman Aljanu, wadanda mukay bayaninsu a wannan shafi tuntuni.
3- Yin addu'a kafin kwanciya bacci.
4- Fara kwanciya a 6arin dama da kuma rufe kunne da hannun hagu. Wato in mutum ya kwanta, sai yasa hannunsa ya rufe kunnensa.
5- Inda hali, ka dena kwanciya a daki kai kadai. Sai da wani a kusa da kai.
Duk wanda yake samun matsalar Dannau har sau biyu a shekara daya, to yana cikin wadanda matsalarsu tay min, saboda bai fiye faruwa akai-akai ba, sai da wata babbar matsala.
Yana da kyau ka ziyarci mai Riqiyyah, ya bincika kanka, don gano wadanne irin Aljanu ne suke danneka da kuma abinda suke yi da jikinka ko kuma abinda suke zuba maka.
*Sai Bashir Halilu ya ce*
Wasu suna yi min korafin cewa rubutuna yana yin yawa, ba sa iya karantawa, duka, amma dai gaskiya akwai ilimai da yawa da ya kamata ace `yan uwa suna amfana da su a wannan fanni.
Insha Allah.


 

AMFANIN ZOGALE GOMA SHA
TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM
==========================

Ana Bukatar Jama'a su yada wannan Post
zuwaga Sauran Al'umma domin Qaruwa da
Juna.
.
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a
sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
.
2- Ana shafa danyen ganyen zogale
akan goshi
domin maganin ciwon kai.
.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen
ganyen zogale
inshaAllah jinin zai tsaya.
.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya
hada garin
zogale da man zaitun ya shafa.
.
5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko
gembo domin saurin warkewa.
.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci
yana
maganin hawan-jini da kuma karama mutum
kuzari.
.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa 'yar
kadan domin maganin ciwon
shawara.
.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga
ruwan
danyen zogale, haka ma mai fama da
ciwon
kunne.
.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale
da
zuma dan karin nono.
.
10-Wanda ke fama da yawan fitsari
wato cutar
Diyabetis ya rinka shan furen zogale
da citta kamar shayi.
.
11-Idan aka tafasa furen zogale da
albasa aka
sha kamar shayi yana maganin
sanyi.
.
12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin
tsutsar ciki ga yara.
.
13-Ana daka ganyen zogale da
'ya'yan baure a
sha da nono ko kunu yana maganin
ciwon hanta.
.
14-Ga mai fama da sanyin kashi ko
wani kumburi
zai soya 'ya'yan zogale a daka su
sannan a hada
da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
.
15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke
ciki tare da karanfani, citta, masoro
da kuma
kimba domin karin karfin da namiji
da sa masa
kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
.
16-A daka saiwar zogale da 'ya'yan
kankana a
sha da nono yana maganin tsakuwar
ciki
(Apendis).
.
17-Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon
Aids zogale kan radadinshi ta hanyar
shan ruwan
dafaffen zogale.
.
18-Haka kuma mai fama da Typhoid da
malaria
da kuma ciwon basir ko shawara, zai
iya yawaita
shan ruwan dafaffen zogalen domin
samun sauki.

MAGANIN DA NAMIJIN GORO YAKEYI AJIKIN DAN ADAM
Namijin goro dai goro ne da mafi akasarin kowane yanki na Nijeriya dama fadin Africa ana amfani dashi.
Malaman lafiya na Africa sunyi bayanin cewa wanna goron yana maganin cututtuka da dama ajikin dan adam,kamar haka;-
1.Namijin goro; Yana maganin tari da ciwon sanyi
2.Namijin goro; Yana maganin ciwon ido da kara hasken idanu.
3.Namijin goro; Yana maganin ciwon jiki da gabobin jiki.
4.Namijin goro; Yana maganin malaria zazzafin cizon sauro
5.Namijin goro; Yana maganin maza da kara lafiyar mazakuta,da wankin mara.
masu buqatar maganinmufa munanan muna jiran kuyi magana kuma cikin iyawar Allah mutane da dama suna siya ana dacewa da iznin Allah .

ALAMOMIN CIWON KODA
Alamomin Ciwon koda:
Idan saman tantanin mara na fitsari ciwon yake, akan samu ciwon kwi6in ciki, daga lokaci zuwa lokaci, wani zubin har da yunkurin amai, ko ma aman. Irin wannan tsakuwa ce ta fi kawo shi kuma ciwon kwi6in yafi tsanani, don har kwantar da mutum zai iya yi, mutum ya kasa katabus. Idan kuma daga mara ne zuwa kasa ciwon yake, za a ji ciwon mara maimakon na kwi6in ciki, ko a rika fitsarin jini da jin zafi da wahalar fitar fitsari, ko a ga fitsari na rabuwa biyu (a maza).
HANYOYIN KARIYA!!!
Hanyoyin kariya daga wannan ciwo
1-Duk wanda aka taba samun a danginsa an cire wa wani tsakuwa a kodarsa ko a matsarmama, to shi ma yana cikin hadarin samun tsakuwa a koda, domin abin akwai gado. Akwai abinci kuma irin su alayyahu da jan nama, wadanda sukan jawo saurin samun tsakuwa a koda, don haka wadannan mutane ya kamata su nisance su amma da hujjar zasu maye gurbin abincin da wani irinsa, kamar latas da kifi.
Akwai kuma yanayi na zafi da kan iya sa taruwar ita wannan tsakuwa, duka dai a irin wadannan mutane da kan iya samu. Don haka yawan shan ruwa lokutan zafi yakan kiyaye taruwar dattin da za su hadu su ba da tsakuwa.
2-Ga masu noman rani na fadama, ko na damina a gonar da ruwa kan taru, ba tare da sun sa takalmin ruwa ba, da masu wanka a ruwa maras tsabta kamar kududdufi duk ya kamata su san cewa akwai kwayayen ciwon tsargiya da kan iya shiga jikinsu su kawo kari a tantanin fitsari.
Saka takalman roba
(takalmin ruwa) ga manoma don kariya daga kwayayen schistosoma zai iya kiyaye su. Su kuma masu wankan rafi ko
kududdufi, sai dai su guji hakan, don kuwa su ma suna cikin hadarin kamuwa da wannan tsuro.
3-Duk wanda ya taba noman fadama inda ruwa kan kwanta, ba
tare da takalmin ruwa ba, ko kuma ya taba yin wankan rafi, musamman idan mutum ya taba yin tsargiya ko fitsarin jini
amma bai sha magani ba, to yana da kyau yaje asibiti mafi kusa a gwada fitsarinsa a kuma ba shi maganin kashe wadannan tsutsotsi masu kawo tsuro a mafitsara.

ILLOLIN RUWAN SANYI GUDA TAKWAS!
.
1. TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- bugun zuciya shike gyara dumin jiki da daidaita numfashi to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kunsan yawancin yan film na kasar indiya da yan ball da boxing da wrestling tsayawar bugun zuciya ke ajalinsu kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi yayin da suke aikine yake jawo musu...
2. LALATA TSARIN KAYAN CIKI:- shan ruwa mai sanyi yana tattare hanji guri daya sai ya sanya abinci yaki narkewa da wuri hakan kan jawo matsalar hanji ulcer kenan ko kuma tashin zuciya. Yawancin masu shan ruwan sanyi suna yawan zubda yawu ko tashin zuciya ko saurin kullewar ciki.
3. DAUKE KARFIN JIKI:- Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum yaji dadi amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon cewa yayinda ruwan mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai naurorin jikin sunyi kokarinsu na ganin sun maida wannan ruwan ya daidaita da dumin jikin hakan yanasa suyi rauni sakamakon kokarin da suke yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kunji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazxabi a hankali kuma sai kuji ya daina.?
4. CIWON MAKOGWARO DA DAKUSHEWAR MURYA:-
Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har sukai ga basa amfaninsu mai kyau a mai sha yakai shekaru arbain sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ko muryar ta fashe kwatankwacin mashayin taba.
5. CIWON HANTA DA KODA:- dukansu suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayinda bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa in haka ta samu mutum ya shiga matsala.
6. BUSAR DA RUWAN JIKI:- akwai naurori a jikin dan Adam da aikinsu shine sadar da ruwa ko ina a jikin mutum ta yanda ko ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan naurorin sukan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su zama so weak.
7. MATSALAR MAAURATA:- Wannan abune tabbatacce harga likitocin zamani cewa shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar da mace in mahaifarta nada rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin inzali ko kuma ya rage masa kuzari. Yana dauke niimar jiki su zamo basa gamsuwa da juna.
8. BASIR DA CIWON KAI NA GEFE MIGRAINE:-
shan ruwan sanyi yanda nace muku yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir.
Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa migraine. Shi kuma migraine yana kashe jijiyoyin ido a daina gani sosai in yayi nisa har hauka yana sawa.
Ubangiji Allah shikara mu Allahumma amen.

MAGANIN FITSARIN KWANCHE BABBA DA YARO.
Ita wannan matsalar ana iya shawo kanta ne ta hanyoyi guda biyu kamar haka :
MAGANI : A nemi kwayoyin habbatus sauda, a rika yiwa yaro hayaki dasu. Kuma yana dan tsugunawa akan hayakin. Sannan kuma a rika gauraya masa habbatus sauda din yana shan cokali guda tare da zuma. Ko kuma ya shafe jikinsa da man Habbatus sauda din wanda akayi tofi acikinsa. In sha Allahu zai dena.
2. ADDU’A : Arika tofa masa wannan addu’ar, ko kuma akoya masa ya rika yinta da kansa, ko kuma a rubuta masa ajikin takarda ya sanya ajikinsa yayin da zai kwanta.
Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bn Amru bn Al-As Sahabin Manzon Allah (saww) yana rataya ma ‘ya’yansa Qanana wannan addu’ar. Gata nan kamar haka :
ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻜﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﺎﻣﺎﺕ ﻣﻦ ﻏﻀﺒﻪ ﻭﻋﻘﺎﺑﻪ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﻣﻦ ﻫﻤﺰﺍﺕ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﺃﻥ ﻳﺤﻀﺮﻭﻥ ”.
‘A’udhu bi kalimatil Laahit tammati min ghadhabihee wa ‘iqabihee wa min sharri ibadihee wa min hamazatish shayateen wa an yahdhurooni.
FASSARA : Ina neman tsari da cikakkun kalmomin nan na Allah daga fushinsa da Uqubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin fizge-fizgen shaitanu, kuma (ina neman tsarinsa) kada su halartoni.
In sha Allahu koda babban mutum ne yake fama da matsalar fitsarin kwance, in dai ya lazimci wadannan abubuwan tare da gaskatawa zai ga biyan bukatarsa.
Wallahu aalam.

MAGANIN H.I.V (AIDS).
Cutar H.I.V ko AIDS cutace da take addabar Al'ummar mu ta
yau. Babu shakka wannan maganin zai taimakawa masu fama
da wannan matsalar sosai da sosai
Kada masu wannan Cuta Su dauki Wannan
Fa'idar da Wasa.
Wannan fa'idar Mujarraba Ce Babu haufi a kanta. Domin
akwai wata Asibitin Hijama dake Qatar sun kasance suna
bawa masu wannan Cuta wannan Fa'ida kuma ana dacewa da
Iznin Allah.
Za'a Nemi Garin Si'itir Cokali 20 Garin Habbatus sauda Cokali
25 Plasko Cokali 10 Garin Citta Cokali 10 Garin Zogale Cokali
10 Garin Ruman
Cokali 10 Garin Kurfat Cokali 5 a samu Zuma Mai Kyau Lita 3
a Hade su a chakuda a cikin Zumar sosai.
A Rika Shan Cokali 3 Sau 3 a Yini Tsawon Wata Biyu. Bayan
watan Biyu a je a sake Auna Jinin Mutum.

AMFANIN MAN ZAITUN``` ✪✪
⁝⁞⁝⁞ •••GUDA 50 ••• ⁝⁞⁝⁝
GA DAN ADAM
◍◍◍◍◍◍◍◍◍◍◍◍◍◍
Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu, Annabi Muhammed (S.A.W) da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.
⁝⁞⁝⁝ ZAITUN DA MAN ZAITUN ⁝⁞⁝⁞
Shidai zaitun itac
iyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin
ALKUR'ANI MAI GIRMA
haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka.
(
) tirmizi ne ya ruwaito
■ DAGA CIKIN AIKIN ■ ZAITUN■
́
```KARFIN MAZAKUTA```
Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai
Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah
```CIWON CIKI```
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.
Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah
```CIWON KAI```
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya.
```CIWON HAKORI```
duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.
```CIWON HANTA```
duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.
```CIWON DADASHI```
Duk mutumin da yake ciwon dasashi saibya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.
o
```CIWON SUKARI``` o
duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah
```CIWON ASMA```
duk mutu
min da wannan ciwon ya kamashi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko ya'yan sa ya dinga turara wa.
```CIWON KODA```
duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana insha Allah.
```CIWON BAYA```
duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa abayan insha Allah.
´```CIWON RAMA````
duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zaiyi kiba.
□ ```ZAZZABI MAI ZAFI``` □
duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah.
```KYAWUN FUSKA```
Duk mutumin da yake
so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda bazai cutaddashi ba, to yadinga shafa man zaitun Dana habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai mamakin yadda fuskarsa data koma.
ZUBEWAR GASHI.
duk mutumin da gashint
a baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube , to saita samu ruwan zafi ta wanne kanta dashi sannan bayan ya dan bushe saita zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kannata dashi gaba daya kullum.
□ KARANCIN JINI
duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana.
BAYAN GIDA MAI KAURI
ロ゚BASUR duk mutumin da yake shan wahala in yazo zaiyi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya turashi acikin duburarsa.
•CIWON MARA GA MATA•
duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon ,saita samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da zatayi haila bazai Mata ciwo ba.
◉◞SANYIN KASHI◟◉
duk mutumin da kashinsa yayi sanyi baya iya motsashi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan insha Allah .
KYAWUN FATA DA LAUSHINTA
Duk mutumin da yake so fatarsa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa dashi bayan Yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa zata koma insha Allah
•••♪ KURAJEN KARZUWA
duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa awajan har ya warke.
♪. •••••∆ CIWON KUNNE
duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun Dana habbatussauda yana digawa a kunnensa insha Allah.
♪. ••••••¶ CUTAR KYASFI
duk mutumin da yake da KYASFI ajikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe ,ya dakashi yayi laushi sai ya Jada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.sai ya wanke
(^_^;) SHAFAR ALJANU•••√
duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa sonshi, shida habbatussauda
Da haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su akowane hali, in da hali ma ya mai dasu mansa na shafawa amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu'a.
¶•••CIWON KARKARE•••¶
Duk mutumin da ciwon karkare yasa meshi, to sai ya samu man zaitun, sannan asamu lalle a kwaba, sai azuba man zaitun din acikin lalle a gauraya, sannan a karanta (AYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa ajikin wannan karkare insha Allah
CIWAN NONO
Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar, to Ana hada man zaitun da garinsa, abarbada akan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.
● ´MOTSA SHA'AWA ●
Ma
n zaitun yana motsa sha'awa in an shafashi lokacin da ake yi wasa.
(
(CIWAN SAIFA))
duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma farar saka ya sha, insha Allah.
TSUTSAR CIKIσ
duk mutumin da yake da tsutsar ciki
, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su yasha, wannan tsutsar zata mutu.
=^CIWAN HANJI (ULCER)^=
Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi yaji kasu ya dinga sha har sai ya warke.
ó
ò FITSARIN KWANCE óò
Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Dana habbatussauda a zuba a nono a dinga bashi yana sha zai dai na. Insha Allah
MUTUWAR JIKI(KASALA)
Duk mut
umin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zaiji karfin jikinsa.
. √••••YAWAN ZABBABI•••••√
duk mutumin da yake yawan yin zazzabi , to saiya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma maras hadi ya dinga sha insha Allah
CUWON GABOBI
Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo to saiya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a GABOBI.
∩KWARKWATA∩
duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta Bari sai Rana ta take sai ta zubar wannan man a kannata ta barshi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke insha Allah zata ban kwana da kwarkwata.
CIWAN TARI
duk mutumin da ya kamu da kowanne irin Tari to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da yar'citta da tsamiya da zuma, sai ya hadasu guri daya ya cakuda ya dinga ci insha Allah.
/✪ MAJINAR KIRJI ✪\
duk mutumin da yake yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma.
^▽^TARIN HUKA^▽^
Duk Wanda yake tarin huka to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya kullum.

MATSALOLIN YARA
Matsaloli nayara.
__________________________________
Dangane damatsalar yaro maiyawan kuka shawara da malaman muslunci suka bada zaayi yaro yasami natsuwa yadaina yawan kuka, kuma yarika samun yin barci sosai.
Hanyoyin dazaabi sune kamar haka:
1.zaa iya samo wani magani daake cemasa kamun, idan ansamo shi sai adinga tafasa shi kamar shayi anatacewa anabawa yaro kadan kadan yanasha.
2.Ko asamo Albabunaj sai arika tafasa shi bayan yahuce sai amasa wanka dashi,koko kokuma asanya shi tururin yabugi jikinsa kaman yadda ake surace, mai littafin (Attadawi bill aashab)haka yakawo yace hakika wannan yanada amfani matuka ga yaro wajan samun nishadi da walwala dasamun barci sosai.
3.Idan kuma yarone maiyawan kuka yahama uwa sakat, to hajiya ga hanya amuslunci, malaman muslunci sunbaki, yadda kau zaayi shine Zaasamo gari na (Shanmmar) wasu sunace masa sammar,wasu sunace masa shamri, kada aje saya aga bambamcin suna ace bashi bane, idan ansamo shi zaarika tafasawa bayan yahuce sai arika bawa yaro yana sha, amma zaa iya hadamasa shi dazuma, ko suga, mai wannan littafin yace wannan magani yana hana yaro yarika yawan kuka, insha Allah kuma ba zairika sonyin yawan kukaba da iznin Allah.
Bangaran tari nayara ko toshewar majina yaro yarika yin susur-susur numfashi baya fita dakya, ko yawan mura, ko yawan tari nayara to uwargida gamaganin dayafi nazamani awannan fannin, ammafa sai kin jarraba zaki gane hakan, abinda zakiyi shine zaki samo man tafarnuwa, dazuma maikya sai kihada yawan man tafarnuwa yawan zuman sai kizuba maul kal cokali, idan yanada yawa, idan kuma dan kadanne to uwargida karamin cokali yaisa sai ki girgiza sosai, sosai to magani yahadu.
Zaki rika bawa ma yaron naki cokali daidai sau uku ko hudu arana yadangabta yanayin larurar zaki rika bashi yanasha amma duk saada zaki bashi wannan maajun, to sai kin girgiza, zaadce Insha Allah.

ILLOLI GUDA ASHIRIN DA BASIR (DAN KANOMA) KE HADDASA
Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :
1.TSUWAR HANJI (INTESTINAL DISTURBANCE).Zaka rinka jin hanjin cikinka na yawan tsuwa akowane lokaci.
2.KUMBURIN CIKI :Cikinka zai kumbure saboda toshewar hanji a sanadin dattin ciki da yawaitar girman kwayoyin cuta da rashin samun damar abinci ya yi saurin narkewa.
3.YAWAN TUSA (FREQUENT FLATUELENCE) : Zaka rinka yawan fitarda iska akai akai,wani iskan sai ka ce wanda ya ci mosai.
4.ZAFIN JIKI DA CIWON KAI : Jikinka zai rinka zafi ga kuma yawaitar ciwon kai wanda baya jin magani kamarsu analgesic.
5.RASHIN CIN ABINCI KA KOSHI : Basir na haddasa maka kaji baka iya cin komai,kusan komai ka ci sai kaji ba dadi.Take ka koshi.
6.YAWAN ZUWA TOILET: Basir kan sa kayi ta yawon zuwa toilet,idan kaje kuma kayi ta faman yunkur da nisha sai zafin musiba da fitar majina ko jini dan tsirit.
7.RAMEWA : Basir kan sa ka rame kamar mai ciwon qanjamau.
8.CIWON GABOBIN JIKI : Basir kan haddasa ciwon jiki da kowace ga6a ta jiki.
9.TASHIN ZUCIYA : Sai kaji kamar kayi amai,kana ta faman zubarda yawu.
10.FITAR BAYA : Duburarka zata fito waje (basir mai tsiro)
11.CIWO A CIKIN DUBURA : Sai kaji matsanancin ciwo ka kasa tsayawa ko zama.
12. DAUKEWAR SHAWA : Namiji yakasance kamar baima balaga ba,ita kuma mace batama san meye biyan bukata ba,duk tabi ta bushe ba ni'ima ba wata gamsarwa.
13. KAIKAYIN DUBURA : Basir kansa dubura ta tsage ga zafi da fesowar kuraje.
14.KURAJE GA MATSE MATSI : Basir kan haddasa irin haka amma mutane da dama suna tinanin kamar sanyi ne,to na sanyi ya sha banban dana basir.Dan na sanyi akan ga zubar farin ruwa masu yauqi da wari kamar danyen kifi.
15. YANA MURDE HANJI : Ta yanda zai haifarda ru6ewar hanji da sauran cutukan ciki.
16. BAYAN GIDA MAI TAURI : Yana haddasa bayan gida mai tauri kamar duwatsu,kamar kashin dabbobi.
17.Basir na kawo ciwon baya.
18.Basir na haifarda (LIVER ABCESS)
19.Basir na haifarda Brain abcep,sai yakasance kamar ka kuwata.yana ma haukata Dan-adam.
20.Yana hude hanji (intestinal ulceration,ga zafin ciki kamar mai ulcer)

 

LOKUTAN DA ALJANU SUKA FI SHIGA JIKIN MUTANE
Shaitanun Aljanu idan suna so su shiga jikin Bil Adama, sukan
jira wasu lokuta na musamman domin samun cikakkiyar damar
yin hakan.
Wadannan lokutan sun hada da:
1. Lokacin da mutum yake cikin tsananin Fushi ko 'bacin rai.
(Shi fushi daga Shaitan ne. shi kuma shaitan an halicceshi ne
daga Wuta).
2. Lokacin da mutum yake cikin tsakiyar aikata wani abu na
sa'bon Allah.
3. Lokacin da mutum yake cikin tsananin sha'awar aikata zina
ko makamancinta. (Shi yasa mafiya yawan masu aikata
istimna'i suna fama da shafar Aljanu).
4. Lokacin da mutum yake cikin tsananin murna akan abinda
ya shafi sa'bon Allah.
5. Lokacin da mutum yake cikin sauraron wakokin soyayya, ko
kallon wani abu na batsa.
6. Lokacin da Mace tayi shigar nuna tsaraici (indecent
exposure) ko kuma Zane-zanen ado ajikinta. Ko kuma ta fesa
turare mai Qarfi.
7. Lokacin da mutum ya manta da ambaton Allah baki daya, ya
shagaltu cikin abinda Allah ba yaso.
Ya Allah kakaremu dagadukan sharrin aljani kowani mugun
mutum Allah kasa mugamada duniya lafiya
Aameen

 

AMIYRUL BAITI ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﺒﻴﺖ
.
Ko kuma Khadimul Manzil ﺧﺎﺩﻡ ﺍﻟﻤﻨﺰﻝ
.
.
Aljanin gida .
.
Su wadannan wasu nau‘i ne na Aljnu da su ke zaune tare da mutane a cikin gida.
.
Galibin su dama can su na zaune ne iyaye da kakannin su tun wajen yana daji, don haka koda an gina wajen ya zama gida sai su ci gaba da zama tare da mutanen gidan.
.
Su wadanna nau‘in Aljanu su na tasirantuwa ne da irin abinda mutanen gida ke aikatawa. Misali idan mutanen gidan su na sallah to su ma za su yi sallah tare da su ko karatun Alqur‘ani. Idan kuma mutanen suna jin kade-kade da wake-wake to su ma sai ya zama wannan su ke so.
.
.
ABUBUWAN DA KE KAWO ALJANU CIKIN GIDA
.

åBarin gida ba mutane a ciki tsawon shekaru ko watanni.
.
åBarin wani daki a cikin gida ba kowa a ciki, to Aljanu za su tare a ciki.
.
åYawan kunna kade-kade a cikin gida.
.
åAjiye abubuwan Shaidanu a gida, kamar gumaka ko karnuka.
.
åRashin karatun Alqur'ani a cikin gida.
.
åYin shaye-shayen kayan maye a gida.
.
åZuzzubar da abinci ko abin sha a kasa.
.
åBarin gida da kazanta da tarin shara ko bola.
.
åGina gida a kan shuri.
.
Da dai sauransu.
.
.
YADDA ZA A GANE AKWAI MAIYRUL BAITI A CIKIN GIDAN MUTANE :-
.

*yawan jin sallama ko takun kafafu ba tare da an ga kowa ba.
.
*yawan ganin wani mutum ko mace zaune a cikin gida ko bandaki.
.
*yawan 6atan kaya kuma a rasa wanda ya dauka, sai lokacin da ba ka bukatar sa kuma sai ka gan shi.
.
*Yawan ganin an hargitsa ma ka kaya ko an yi ma ka bincike kuma ka rasa kowaye.
.
*yawan 6acin rai ko faduwar gaba idan ka na cikin gida amma in ka fita sai ka daina ji.
.
*yawan tsagewar wata katanga a cikin gida kuma duk gyaran da za a yi sai ta kuma darewa.
.
*Yawan ganin wata dabba ta gifta kamar maciji ko kare dds kuma in an duba sai a rasa inda ya shiga.
.
*yawan jin dudubniya ko kokaye-kokaye a saman daki.
.
.
Yadda ake korar wannan Aljani daga cikin guda:-
.
A dinga karanta Suratul Baqarah duk bayan kwana uku a gidan, ko a dinga kunnawa a kaset.
.
Idan kuma ba su fita ba to sai a nemo mai rukiyya ya yi magana da su,ya sallame su.




Abubuwa Guda Goma Da Mata Basa So Ga Maza
Idan Kana Aikata Daya Daga Ciki To Ka Sani Matarka Na Hakurin Zama Da Kai.
Daga Nana Asmau Abdulkadir.
1. Mai Shan Giya
2. Mai Neman Mata
3. Kazan Wanda Bai Tsaftace Jiki Ko Bakin Shi
4. Raggon Namiji Wanda Ba Ya Iya Gamsar Da Matarsa A Yayin Saduwa
5. Mai Yawan Fada
6. Mai Yawan Kushe Matarshi
7. Matsoraci
8. Mai Hassada Ga Matarshi
9. Mai Yawan Fushi
10. Wanda Baya Da Lokacin Zama Suyi Hira Da Matarshi
Daga Karshe Ina Addu'a Ga 'Yan Uwana Mata Allah Ya Bamu Maza Nagari.
KISHI
Namiji zai kara aure, in anyi magana yace sunna ne, amma idan ya zo sallar farillah ba lalle ya tuna ya yi nafila a matsayin sunna ba.
Mace ta riki kishi in an yi magana yace matan magabata na kwarai ma sunyi, amma in ance kiyi hakuri ta kan manta a wannan fagen tayi koyi da hakuri irin na matan magabata na kwarai.
In zamu yi addini muyi shi ta kowani bangare karmu dauki hukuncin da yayi daidai da son zuciyar mu kawai.
AKWAI HIKIMAR ALLAH DA YACE MAZA MUYI AUREN MATA HAR HUDU HUDU
Da zarar kana so kaji dalilai kala kala, har da wanda zakayi dariya, to kayi maganar karin Aure a cikin Mata wa'yanda Allah ya rufawa asiri suka sami Miji.
Wasu Matan ko me zaka kawo musu ba Ayar Qur'aani ba, zasuyi kokarin yin Tawili da kawo Ra'ayi daban daban don dai su nuna karin Auren dai bai kamata ba.
Daga masu cewa su ba Kishiya suke gudu ba, sai dai wai suna tsoron wasu matan ne da Sharri suke shigowa.
Kai kace kamar dole ne Mijinsu yace masu Sharrin zai karo musu, ko kai kace babu masu Alkhairi a cikin wasu Matan basu ba.
Wasu kuma suce wai ai Mazan ne basu da Adalci, kai kace tsoron Allah ne yasa bata son wata macen tazo ta hadu da rashin Adalcin na Mijin nata, duk dafa ita tana tare da wanda ba Adalin ba.
Wata ma cewa take: "Wallahi gwara Mijinta yaje yayi Dadiro a waje, matukar dai ba kawo mata 'Yar uwar gida za'ayi ba, wai domin Kazantar da baka gani ba ai tsafta ce inji su.
Wasu kuma kawai tsabar son gallazawa Mijin nasu ne, kawai suna tsoron in an kawo wata ne kada ta zama mai sassauci ga Mijin nasu.
Koma dai menene Ra'ayin Mata, kari ya zama dole domin rage yawon ba gaira babu dalili a wajen Mata.
Ko yaya kuke Gani 'Yan uwa Maza da Mata?


•••MACE ABOKIYAR RAYUWA•••
.
Idan mace ta soka tana sonka ne da dukkan zuciyar ta, amma hakan bai hana tayi maka laifi, duk lokacin da mace tayi maka laifi, kai kuma ka mu'amalanceta da hankalinka ka tuna soyayyarta da tama, ka tausayawa raunin ta, kayi mata afwa, ka mu'amalance ta kyakkyawar mu'amala tare da tausasa lafazi da kyautata aiki a gare ta.
.
Acikin Alqur'ani maigirma ALLAH (SWT) Yana cewa:
.
وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا
.
“kuyi musu mu'amala da kayautatawa, Sannan idan kun ki su, to akwai tsammaninku kuki wani abu alhali kuwa ALLAH Ya sanya wani alkhairi mai yawa a cikin sa.” [Suratul Nisa'i: 19]
YA KE 'YAR UWA! KAFIN KI ZA'BI MIJIN AURE,
YA KAMATA KIYI MA KANKI WADANNAN
TAMBAYOYIN :

- Shin wannan saurayin don Allah ka'dai
kike Qaunarsa, ko kuwa saboda wasu dalilai
naki na son duniya?
- Shin zaki so ache wannan shine Uban
'Ya'yanki?. Kuma shin zakiyi alfahari
aduniya da lahira idan kika haifi 'da (yaro)
mai irin halinsa da yanayinsa?.
- Shin wannan saurayin yana da halaye irin
na Tsoron Allah? (Yawan tuna Allah, kiyaye
dokokinsa, Bin umurninsa, yin abu don
neman yardarsa).
- Shin wannan saurayin idan ya zama
Mijinki zaija ki zuwa ga Aljannah ne, ko
kuwa zuwa ga Azabar Allah??.
- Shin yana Mutunta Mahaifansa da 'Yan
uwansa Mata? Idan har yana Mutuntasu to
zai mutunta naki. Idan kuma yana
wulakantasu to kema sai ya Wulakanta naki.
- Shin yana yi miki zancen batsa awajen
hirarku? Ko kuma yana Kokarin ta'ba jikinki?
(Idan yana da wannan halin to Ki Gujeshi
domin shai'dani ne).
- Shin yaya tarbiyyar gidansu take? Idan
gidansu akwai tarbiyyah to zaki ga alamar
hakan daga gareshi da kuma Qannensa
Mata da Maza.
- Wajen za'bin saurayi kada Zaqin bakinsa
ko kyawun adonsa ya rudeki. Mafiya yawan
Samari suna amfani da Zaqin bakinsu ne
wajen yaudara da amfani da 'Ya'yan
Mutane.
Kada ki sa'ba ma Allah don neman yardar
Saurayi. Idan kika bama saurayi damar ta'ba
jikinki, to lallai Kinci amanar Iyayenki bisa
wahalar tarbiyyar da suka baki.
Kin ci amanar 'Yan uwanki da danginki
tunda kin shigo musu da Mummunar
Alfasha atsakaninsu. Kin ci amanar Mijin da
zaki aura nan gaba.. (Koda shima Mazinacin
ne).
Kin ci amanar Zuriyar da zaki haifa nan
gaba. Tunda kika aikata zina kin gurbata
Musu jini da wannan dau'dar Zinar taki.
Mafi girma kuma ita Amanar Allah da kika ci.
Domin dukkan gabobin jikinki ya badasu
amana ne agareki don kiyi amfani dasu
wajsn neman yardarsa.
Manzon Allah (saww) kuwa yace Koda
bayan rasuwarsa ana nuna masa ayyukan
al'ummarsa. Shin ba zaki ji kunya ba, ache
yaga Zina acikin ayyukanki?.
Wannan Nasiha ce daga Zauren Fiqhu
da fatan Allah yasa ta zama
dalilin shiriya ga Masu aikata wannan
Kaba'irah. Wadanda basu yi kuma Allah shi
kiyayemu baki daya. Ameen.
MU KIYAYE HARSUNAN MU
Harshe wata tsokace mai muhimmanci ajikin dan Adam,bayan zuciya babu abinda ya kai harshe amfani da hadari a jikin dan adam.
Harshe ni'imace da Allah yayiwa dan Adam,amma idan dan Adam yayi sakaci wajan kulawa da shi da amfani da shi yanda shari'a ta aminci sai ya kai mutum zuwa ga halaka.
Da harshen dan adam yake ambaton Allah ya zikiri da karatun alquranin da salati ga Manzon Allah SAW,da harshene mutum yake yabon Allah ya rokesa da sunayensa da siffoninsa,sannan da harshene mutum yake fadar kalmar da take janyo masa yardar Allah da rahamarsa har Allah yayi masa gafara ya sanya shi a aljanna sanadiyyar fadar wata kalma da harshensa.
Da harshene kuma mutum zai fadi kalmar da zata janyo masa fishin Allah da azabar Allah har ta dauwamar da shi acikin wutar jahannama har abada.
Manzon Allah SAW yayi Umarni akan kiyaye harshe kamar yanda ya fadawa Babban Sahabinsa Mu'az bn Jabal R.A yace masa;
*(..........Ka kiyaye wannan tsoka)*sai ya kama harshensa.sai Mu'az yace;
"Yanzu ya Manzon Allah ashe za'a kamamu da laifi akan abinda harshenmu yake furtawa,?"sai Manzon Allah SAW yace masa;
*(Mahaifiyarka tayi Asararka,shin akwai abinda yake kai dan Adam acikin wuta akan fuskarsu inbanda abinda da harshensu yake furtawa ba)*
@رواه الترمذي وقال؛حديث حسن صحيح.
¤Kiyaye harshe yana kai mutum zuwa ga aljanna¤
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Wa zai kiyaye min abinda yake tsakanin gemunsa{wato harshensa}da abinda yake tsakanin cinyoyinsa{wato al'aurarsa}ni kuma zai tsaye masa shiga aljanna)*
@صحيح البخاري رقم-(6474)
¤Wanda ya kiyaye sharrin harshensa zai shiga aljanna¤
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Dukkan wanda Allah yayi masa karkuwa daga sharrin harshensa da sharrin al'aurarsa,zai shiga aljanna)*
@حسنه الألباني في صحيح الترغيب رقم:(2413)
A wata riwayar;
*(Dukkan wanda ya kiyaye harshensa da al'aurarsa,ya shiga aljanna)*
@حسنه الألباني في صحيح الترغيب رقم:(2860).
¤Harshe yana daya daga cikin abubuwan da suke saurin kai mutum gida wuta¤
Kuma an Tambayi Manzon Allah SAW akan mafi yawan abinda yake shigar da mutane aljanna sai yace;
*(Kiyaye dokokin Allah da kyawawan haleye)*.
Da aka tambayi mafi yawan abinda yake kai mutane wuta sai yace;
*(Harshe da al'aura)*
@حسن الألباني إسناده في صحيح الترمذي-رقم:(2004)
Dolene sai dan Adam ya tashi yayi yaki da harshensa sannan zai sami damar mallakarsa.
الإمام ابن القيم رحمه الله;
Yana cewa;
"Dan haka yin hakuri akan barin sabon harshe yana cikin mafi girman nau'in hakuri,domin sabon harshe yana saurin halaka dan Adam,kamar gulma da yi da mutane da zagi da giba da karya da qazafi........dukkan wanda ya auka cikin wadan nan laifukana na harshe zasuyi saurin halakasa dan haka dole sai dan Adam ya tashi yayi hakuri ya yaki wadannan cutuka na harshensa....."
@عدة الصابرين : (126-127)
Allah ne mafi sani
Allah ka bamu ikon kiyaye harshenmu baki daya.


WACE CE MACE TA GARI? 01💑
Mace ta gari kalma ce da ko wacce mace ta ke son ta ga ta alaqantu, ko an alaqanta ta da shi. Ko da kuwa ba ta da abubuwan da za a kira ta da ta gari ďin.
Domin kalma ce da take mayar da mummunar mace kyakykyawa. Ta ďaga darajar ta, tare da qimanta ta, da qara mata farin jini a cikin al'ummar da take rayuwa da su.
Zama mace ta gari ya 'kunshi abubuwa da dama, wasu ke za ki yi ma kanki. Wasu mijinki za ki yi ma wa, wasu kuma mutanen da kike rayuwa da su. Kafin ki zama cikakkiyar ta gari. A taqaice dai wannan rubutu zai ta'bo 'bangarori da dama na zama mace ta gari.
Rubutun zai kasance a taqaice ba tare da dogon labari ba. Don haka In da kike kan yi sai ki qara dagewa. Waɗanda baki yi sai ki fara. In da kike da kuskure kuma ki gyara. Yar'uwata daure ki gyara halin ki, daure ki zama ta gari a gidan miji na gari. Domin shine ribar zamanki a duniya. Kuma mabuɗin buďe kofar shigar ki zuwa Jannah. Annabi ya faďe ki ya sake faďi, don haka daure ki shiga cikin jerin waďanda Manzon Rahama ya yaba.
Kina zama ta gari iskan da ke ratsa gidan ki zai canza. Ki ji kin samu wani qarin kwalliyan da baki iya ganinta. Ki ji kin samu qarfin guiwar kusantar Mahaliccin ki.
Tsiya, tashin hankali da wulaqanta miji ba sa kawo komai sai wulaqanci. Da dana sani a duniya da lahirar mace. Kuma babu in da za su sauke ki sai a wuta, in baki yi ma kan ki faďa kin gyara ba. Shin ke baki so a ce ke ta gari ce macen kirki?
Ina roqon Allah Ya ba ni ikon faďin dai-dai

WACE CE MACE TA GARI? 02💑
ITA CE JIN DA'DIN DUNIYA
Ko da musulunci ya fifita maza akan mata, sai kuma ya ďaura musu nauyi da yawa na kula da mu. Su suke fita nema su yi wahala. Sai aka sanya mu zamo nutsuwa da hutu agare su. Wanda rashin dacewa da salihai zai iya jefa su cikin damuwa, da rashin walwalar rayuwa.
Allah (SWT) Yana cewa:
((وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ.))
"Kuma akwai daga cikin ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku nutsu zuwa gare ta (matar) kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle ne wancan akwai ayoyi ga mutane masu tunani." [Q:30:21].
A hadisai da dama Annabi (SAW) Ya yi magana akan mace saliha. Kuma ya nuna muhimmancin ta ga ďa namiji. Ya ce:
((الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَخَيْرُ مَتَاعِ الدُّنْيَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ)). [رواه مسلم].
"Duniya ďan jin dadi ne, kuma mafi alkhairin daďinta shine: "Mace ta gari". [Muslim].
Kuma ya ce:
((عَنْ أَبِي أُمَامَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ: مَا اسْتَفَادَ الْمُؤْمِنُ بَعْدَ تَقْوَى اللَّهِ خَيْرًا لَهُ مِنْ زَوْجَةٍ صَالِحَةٍ، إِنْ أَمَرَهَا أَطَاعَتْهُ، وَإِنْ نَظَرَ إِلَيْهَا سَرَّتْهُ، وَإِنْ أَقْسَمَ عَلَيْهَا أَبَرَّتْهُ، وَإِنْ غَابَ عَنْهَا نَصَحَتْهُ فِي نَفْسِهَا وَمَالِهِ)). [ابن ماجه].
"Mumini bai fa'idanta da wani abu bayan tsoron Allah wanda ya fi alkhairi fiye da Mace ta gari. Idan ya umurce ta sai ta yi masa biyayya, idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai. Idan kuma ya yi rantsuwa a kan ta sai ta ku'butar da shi, in kuma baya tare da ita sai ta kiyaye kanta da dukiyar sa". [Ibn Majah].
A wani hadisin mai kama da wannan Manzon Allah (SAW) ya ce:
((أَلَا أُخْبِرُكَ بِخَيْرِ مَا يَكْنِزُ الْمَرْءُ؟ الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ، إِذَا نَظَرَ إِلَيْهَا سَرَّتْهُ، وَإِذَا أَمَرَهَا أَطَاعَتْهُ، وَإِذَا غَابَ عَنْهَا حَفِظَتْهُ)). [رواه أبو داود].
"Shin ba na baka labarin mafi alherin abun da mutum ya taskance ba? Sai ya ce: "Ita ce mace ta gari, Idan ya kalle ta sai ta faranta masa, in kuma ya umurce ta sai ta yi masa biyayya, idan kuma ba ya wurinta sai ta kiyaye shi" [Abu Dawud].
Sannan ya sake cewa:
((قال عليه الصلاة والسلام: (من رزَقه الله امرأة صالحة، فقد أعانه على شطر دينه، فليتقِ الله في الشطر الثاني)). [رواه الحاكم والطبراني، وسنده صحيح].
"Duk wanda Allah Ya azurta shi da mace saliha to ya bashi rabin addinin sa, sai ya cikashe sauran da tsoron Allah." [Ɗabarani da Hakim].
Duka waďannan hadisan suna nuna irin daraja da muhimmancin kasancewar mace ta gari. Idan ki ka zama ta gari, to kin zama zinariyar da kowa ke son mallaka. Ko da mijin ki ne ya rasu, ko yayi kuskuren rabuwa da ke, to kowa zai ta rububin son auren ki. Saboda kasancewar ki ta gari.
Zaki zama abun kwatance ga qawayen ki da 'yan'uwan ki. Kuma abun buga misali a wurin salihan mutane. Sannan ki mutu kuma ki shiga Aljannah Madaukakiya. Allah dai Ya ba mu ikon zama na gari.
💑 WACE CE MACE TA GARI? 03 💑
ITA CE MUSULMA MU'UMINA
Farkon matakin zama ta gari shine ta kasance musulma. Musulma kuma ita ce wacce ta yi imani da Allah ta kaďaita Sa a matsayin abun bautar ta, kuma ta miqa wuya ga Allah ta hanyar miqa wuya ga umurnin Sa da dokokin Sa. Kuma ta yi imani da Annabi Muhammad ta hanyar yi masa da'a a umurnin sa da gasgata sa a labaransa. Da nisantar haninsa da bautawa Allah kaďai ta hanyar da ya shar'anta. Ta tsaida Sallah da haqqoqin ta. Ta bada Zakka, ta azumci watan Ramadana ta je aikin Hajji in ta samu iko. Wannan ce cikakkiyar musulma.
Sannan ta ďauki matakin zama Mu'mina, shine imani da Allah da Mala'ikun Sa, da Manzannin Sa, da Litattafan Sa, da Ranar qarshe, da imani da Qaddara mai kyau ko mara kyau.
Ba zaki ta'ba zama ta gari ba har sai kin yi imani da waďannan abubuwan, tun daga nan ne zaki fara ginin zama ta gari.
Domin wata a ďabi'un ta da halayen ta sai ka tambayi kanka anya kuwa wannan matar ta yi imani da waďancan abubuwan da na ambata kuwa. Saboda gaba ďaya ta bar imanin ta da rukunan musulunci sun yi rauni. Kuma tana shirka tamkar bata yi imani da Allah a matsayin abun bautar ta ba. Kuma tana qaryata qaddara da faďa da Sunnar Annabi (SAW). Don haka sai ki farfađe kanki domin kin san irin fito na fiton da kika yi da Allah da Manzon Sa (SAW). Kuma ki nemi gafara ki yi ďamarar zama ta gari.

💑WACE CE MACE TA GARI? 04💑
ITA CE MAI IBADA
Bauta dai shine dukkan abun da Allah Ya ke so, kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.
Kuma duk mace ta gari zaka same ta da ibada, wato mai dagewa ce wurin bautar Ubangijinta. Sannan tana tsoron Allah da qanqan da kai gare Sa.
Kuma ta aminta tun daga farkon auren ta cewa aure ibada ne, kuma Sunnah ne mai qarfi zata raya. Kuma duk abun da take yi a cikin gidan ta tana da lada. Idan mace ta sa haka a ranta abubuwa da yawa a rayuwar aure za su zo mata da sauqi.
Ita ce mai dogaro ga Allah a cikin dukkan al'amuran ta. Kuma tana komawa gare shi a lokacin yalwa da lokacin tsanani. Kuma tana godiya gare Shi a cikin ko wane hali.
Mace ta gari sam bata wasa da sallolin ta biyar a gidan ta. Kuma ba a barin ta a baya wato tana tashi cikin dare ta roqi alkhairan duniya da lahira.
Tana qoqarin yin azumin nafila tare da izinin mijin ta.
Tana qoqarin yin kyauta da sadaqa.
Tana dagewa wurin yin addu'a. Duk abun da ya same ta na rayuwa to ta kan tsananta roqo.
Mai yawan ambaton Allah ce da Istigfari. Bakin ta danye yake wurin ambaton Allah. Ba ashar da maganganu marasa amfani ba.
Tana yin biyayya ga mijinta, idan har umurnin sa bai sabawa Mahalicci ba.
Kuma tana dagewa da sauran ibadodi na samun lada.
In ba ku manta ba Annabi (SAW) ya faďa a hadisi:
((إِذَا صَلَّتِ الْمَرْأَةُ خَمْسَهَا، وَصَامَتْ شَهْرَهَا، وَحَفِظَتْ فَرْجَهَا، وَأَطَاعَتْ زَوْجَهَا، قِيلَ لَهَا: ادْخُلِي الْجَنَّةَ مِنْ أَيِّ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ شِئْتِ)). [رواه أحمد].
"Idan mace ta yi sallolin ta biyar, ta yi azumin ramadan, ta kuma kiyaye farjin ta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, sai a ce da ita: "Ki shiga aljannah daga qofar da ki ka gadama daga cikin qofofin Aljannah". [Ahmad].
Babu yanda za a yi a kira ki ta gari, bayan kina tsallake sallah, wato yin sallah yana miki wahala.
Inaa! Mace ta gari ta miki nisa, don ita rige-rige take wajen ganin ta kusanci Mahaliccin ta da ibada.

*ME ALJANNAH TACE BAYAN AN GAMA HALITTAR TA.???*
Ya Inganta a Hadithai masu yawa daga Annabi s.a.w bayan Allah s.w.t Ya gama halittar aljannah Allah ya Umarce ta tayi Magana, To Me tace.???
*"عن أبي سعيد عن النبي صلى الله عليه وسلم قال (خلق الله الجنة لبنة من ذهب ولبنة من فضة وملاطها المسك، فقال لها تكلمي فقالت ''قد أفلح المؤمنون" فدخلتها الملائكة فقالت طوبى لك منزل الملوك. )* الطبرني "11,11439"
Ma'ana *"An karbo daga Abee Sa'eed Daga Annabi Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi Yace (Allah Ya Halicci Aljannah da Bulo na Zinari da Kuma Bulo na Azurfa Sannan Simintin ta Shine na Turaren Almisk, Sai Allah Yace da ita (Aljannah) Yi Magana Sai Tace " Lallai Muminai Sun Rabauta." Sai Mala'iku Suka Shigeta (Yayinda Suka ga Ni'imomin ta da Allah Ya halitta a ciki) Sai Suka ce Lallai Madallah da Wannan Masauki na Masy Matsayi )*
Daga Cikin hadithan da Suka zo akan Maganar da Aljannah tayi Sunzo dayawa da riwaya mabanbanta Kamar yadda yazo a cikin Tafsirin Ibn katheer a farkon Suratul Muminoon, Sannan a hadithan da Suka Zo zamu fahimci.;
1- Allah S.W.T Ya Halicci Aljannah da Hannun sa Masu tsarki da Girma da Bulo na Zinari da Azurfa da Wasu blocks na Yaqutu da Marjani da Zabarjadah Sannan Siminti ta na Turaren Almisk ne, Tanada Kayan ado na Lu'u-Lu'u da Kuma Wani Nau'i na Za'afaran .
2- Aljannah tayi Magana Yayinda taga Irin Ni'imomin da aka Sanya mata a Cikin ta, Kuma Dukan Su na Muminai ne yasa ta yi farin cuki kuma ta Jaddada Cewa;
(قد أفلح المؤمنون) سورة المؤمنون (١)
"Lallai Masu Imani Sun Rabauta."
3- Mala'iku Sun Shiga Aljannah Kuma Sun Duba Sun tabbatar da Ni'imar da Allah yayiwa Aljannah Suna da yawa akan masu imani yasa Suma Sukace.;
طوبى لك منزلا الملوك.
4- Allah S.W.T Ya Halicci abubuwa a aljannah Wanda babu Wanda yasan adadin Su sai Shi, Kamar yadda Abdullahi bn Abbas ya ruwaito daga Annabi s.a.w Yace
(خلق فيها مالا عين رأت ولا أذن سمعت ولا خطر على قلب بشر)
"A cikin ta Allah Ya Halicci abinda ido bai taba gani ba, Kunne bai taba Ji ba, Sannan Zuci
Allah ya Sanyamu chikin aljannah baki daya.
Ki zama tamkar fulawa mai kyawun kallo a idonsa,
mai qamshi a hancinsa, mai kuma amfanarwa idan an murje ta.😉
😍Soyayyar ki gare sa farin cikinsa, ki yi kishinsa ta hanyar ninka kyautatawa, ladabi ta hanyar girmamawa da mutuntawa, ki yi biyayya da jin maganarsa da kiyaye masa, sanya shi nishaďi da kissan tattali, ke ki zama hasken idonsa gaba ďaya idan ya kalle ki uwar 'ya'yan sa.
Ki yi deleting duk wata MACE ta hanyar ninka addu'a a kansa wurin Allah. 😎
Allah Ya bamu kan su mu dafa mu cinye a duniya da lahira
SAKO ZUWA GA MATA-2
KI KYAUTATAWA MIJINKI ZAKI SHIGA ALJANNA.
Ki nemi yardar mijinki ta hanyar kyautata masa da kalamai masu dadi da aiyukan ibadar aure yin hakan zai shigar da ita aljanna insha Allah.
*Aiki dan kadan marar wahala zai janyo maki dauwama acikin aljanna*
Manzon Allah yana cewa;-
*(Shin bazan baku ba labarin Mata yan aljanna ba daga cikin ku?Mata masu yawan haihuwa wadanda suka iya soyayya,wadda idan tayi maka laifi zata dora hannunta akan naka,sannan sai tace ga hannuna nan akan hannunka bazan dauke hannuna ba akan naka ba har Sai ka daina fishi dani har sai ka yafe min)*.
@السلسله الصحيحه 3380.
Manzon Allah yana cewa;-
*(Idan mace ta sallaci sallolin guda biyar na farilla,kuma tayi azuminci azuminta na farillah,kuma ta kiyaye farjinta daga zina,KUMA TAYI BIYAYYA DA KYAUTATAWA MIJINTA,za'ace da ita kishiga aljanna ta dukkan kofar da kikaga dama)*
@صحيح الترغيب 1932.
Manzon Allah yana cewa;-
*(Baya I ga mace da tayi azumin nafila alhalin mijinta yanana har sai da izininsa)*
@صحيح ترغيب 613.
Manzon Allah yana cewa;-
*(Idan mutum ya kirayi matarsa zuwa shimfidarsa sai taki :-*wa,ya kwana yana mai fishi ita,Mala'iku suna la'antarta har zuwa ta wayi gari)*
@صحيح مسلم 1434.
Allah ne mafi Sani.
WAYARKI
A sanda kika siyo wayarki mai daraja kokari kike ki lullubeta da screen guard, ki sanya mata cover ki rufeta rujub, da zaa tambayenki meyasa baki bar ta tsirara ba?
Amsar itace saboda kariya bana so ta fadi ta fashe ta rasa daraja, ko tayi saurin tsufa ko ta kode da wuri.
Tambaya ta anan itace:-
~Keda wayar cikinku wanne yafi daraja?
~Meyasa kika yarda wayarki tafiki daraja kike iya suturta amma ke kike yawo tsirara?
~Shin ke baki da bukatar kariyar ce, ko ko kinfi bukatar saurin tsufar ne da saurin kodewa da wurin akan wayarki?
YADDA ZAKA CI RIBAR ZAMA DA MACE
Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.
Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su
NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna
NA UKU: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku
NA HUDU: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayinka
NA BIYAR: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa
NA SHIDA: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su
NA BAKWAI: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaqo mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana kokarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta kuwa shine sakinta.
To kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin kuskuren, da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina-baina
NA TAKWAS: To kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kadaa wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata masu kyau
NA TARA: Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah mds ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a wadanban lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya dauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka saukaka mata umarnika da hane- hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya saukaka mata farillansa
NA GOMA: Ka sani cewa ita mace ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.
Annabi (SAW) yace" Inai miku wasiyya da mata Ku rike su da alheri, domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tankwararre kuma Mafi tankwarewar kashi shi ne sama , idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan kuma ka barshi haka to zai dawwama a tankware kuma a karkace, to don haka inai muku wasiyya ta gari dangane da mata.
Kum Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina"
Allah ya bamu ikon zama da iyalanmu lafiya


ZAGIN MATACCE....
IKRAMA BIN ABI JAHIL ya nuna qiyayya Mai tsanani ga addinin islama bayan yaqin badar ya na cikin y'an committee da aka kashewa iyayan su a yaqin badar, don HAKA ya cutar da muslunci matuqar cutarwa
HAKA Nan Abu ne bayyananne a tarihin muslunci irin cutarwar da Abu jahil yayi wa Annabi Sallallahu alaihi wasallam
Bayan fatahu makka Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace game da mutanen makka duk Wanda ya shiga ka'aba ko gidan Abu Sufyan ya tsira, Amma yace duk inda IKRAMA BIN ABI JAHIL ya shiga a kamo shi a kashe shi, da IKRAMA yaji labarin ya gudu ya bar garin can ya kusa tsallaka gabar kogi, matar IKRAMA BIN ABI JAHIL ta karbi muslunci taje ta roqi Annabi ya yafewa IKRAMA, Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya yafe Masa,
Sannan matar sa ta bi bayan sa ta sanar dashi cewa Annabi ya yafe masa, ya dawo zuwa garin makka ya muslunta
Kafin ya dawo Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace da sahabban sa
"IKRAMA ZAI ZO MUKU YANA MUMINI MAI HIJRA , KADA KU ZAGI BABAN SA, DOMIN HAQIQA ZAGIN MATACCE YANA CUTAR DA RAYAYYE BA YA ISA GA MAMACI"
TO KAI A MATSAYIN Ka NA MUSULMI MAI IKRARIN BIN KOYARWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM A INA KA SAMO NAKA ILIMIN NA ZAGIN MAMACI?
na tabbata duk irin yadda kake Jin cewa bawan Allahn ya cutar da Kai ( idan ma ya cutar da Kai din) ba najin zai Kai 1/10 na cutarwar da Abu jahil yayi wa Annabi Sallallahu alaihi wasallam, Amma Habibiy abin koyin mu sallallahu alaihi wasallam yace kar a ZAGe shi!!!
Don HAKA idan ka zagi margayi Abba kyari don kana rayawa ya zalunce ka to ZAGIN ka ba zai Isa gare shi ba, sai dai in iyalin sa da masoyan sa sun ji ZAGIN ya cutar dasu Wanda su Kuma Basu mulke ka ba ballantan su zalunce ka, ka ga anan Kai kayi zaluncin
Ya kamata mu zama masu aiki da hankali da Kuma ilimi
Allah ya gafarta Masa yasa aljanna ce makomar sa ya kyautata namu qarshen



SIFFOFI TALATIN (30), NA MAFI SHARRIN MAZA, ABIN KI GA KO WACCE MACE!
-----------------.
Tabbas yana daga abin ki ga 'ya mace auren namiji mai irin wannan halayya:
1. Maqagi mai yawan
alfasha, Mai yawan bayyan tsiraicin matarsa ne ga abokansa da wasu al'umma da ban, tsiraicin matarsa tamkar hoto take ga sauran al'umma.
2. Mai ci shi kadai ya hana kowa, har da wadanda suka ziyarce shi (Marowaci).
3. Mai dukar
matarsa da bawansa, wanda iyalansa ke fakewa
da waninsa, yana maraba da dukkan hadarin da zai auku ga matarsa.
4. Mai sa6awa
iyayensa ne, ba ya saurara musu.
5. Mara kishin matarsa ne: ba ya damuwa wacce irin fita matarsa take yi, ba ya kuma kulawa da inda za ta je ko ina ta fito, shi kuma ba ya tafiya da ita ko ina.
6. Mai yawan cin haram, kullum abincin gidansa da haram yake ciyar da iyalansa.
7. Mara da6i'ah ne, duk lokacin da wani abu ya hada shi da wani sai ya yi zalunci.
8. Mai mummunar hali, ga amanar da aka bashi kuwa mai wulakantarwa ne.
9. Wanda matarsa bata iya katange shi ga wasu mata, duk da kokarinta wajen kyautata masa da tsare haqqoqinsa da take.
10. Shi ne wanda bai san ci da shan matarsa ba, ballantana suturarta.
11. Mai rashin godiya ga Allah ne, ballanta ya yi godiya ga abokin halittarsa.
12. Kullum maganarsa dafi ce, tamkar dafin maciji.
13. Wanda bai san daraja da girman iyayen matarsa ba.
14. Shi ne mai hana matarsa neman ilmi, kuma shi bai koyar da ita ilmin ba.
15. Mara kuzari ne a wajen kwanciyar aure, mai ha'inci ne wanda ba ya biyan bukatar matarsa a gadonta.
16. Kazami ne shi mara tsafta, kucaki ne shi bai iya kwalliya ba.
Kwalliyarsa sai in zai je wajen daurin aure ko bikin (party) wani abokinsa ko dan'uwansa.
17. Tsauna ne shi, mara furucin ko hazanci wajen magana.
18. Mai yawan bincike da kokkofi ne shi, ga rashin amintarsa ga matarsa.
19. Wanda ba ya yaba wa matarsa kan irin kokarinta, yabonsa na fitsararrun mata ne a waje.
20. Mugu ne shi, ba ya tausayawa matarsa da 'ya'yansa, kuma ba ya kar6ar uzurin kowa.
21. Mai yawan mita da surutu ne shi mai fadin sirrin matarsa ga wasu mata, a lokacin da aka 6ata masa rai kuwa hukuncinsa zalunci ne da bakaken magana.
22. Mai yawan zagin iyayen matarsa ne, kuma bai san mutuncin kowa ba, ba ya girmama na gaba da shi.
23. Mai kazafi ne da kage a duk lokacin da wani husuma ya hada shi da matarsa. Zancensa kuma karya ce, baya kusantar ma'abota gaskiya.
24. Mai yawan sabon Allah ne shi, ba ya ganin girman zunubi.
25. Mai yawan zargi ne ga matarsa, kullum ba ya kyautata mata zato.
26. Shi ne wanda ba ya zama ya ji koke-koken iyalinsa, kuma ba ya shawartan matarsa akan lamuransa da nata.
Mai halin ko in kula ne da tarbiyan gidansa.
27. Ba ya tausayin matarsa a lokacin rashin lafiya ko wani lalura na rayuwarta.
28. Mai yawan fushi ne, kullum ransa a 6ace yake, ba ya sakun fuska ga iyalinsa, in ka gansa cikin fara'a to ya zo neman kwanciya da iyalinsa ne.
29. Mai yawan dariya ne, ga kuma kyauta da murmushi ga matan da ba nasa ba.
30. Lallai ne shi mara tsoron Allah ne, kuma lokacinsa kullum a wulakance take, ba ya tsare dokokin Allah akansa.
-
tabbas duk macen da ta sami namiji mai wannan halayya ba ta more ba.
Kuma tana cikin kurkuku mai tsananin zafi da azabtarwa!
-
Allah Ya raba ko wacce mace da irin wannan lusarin namijin da bai san girman darajar mata ba´.
Allah Ka sa kar mu dauki hali guda daga wannan munanan halayya.
FALALAR ZIYARAR YAN UWA DA KUMA SAN JUNA SABODA ALLAH.
Zayara da sadar da zuminci da yn soyayya dan Allah,yana cikin mafi girman aiyukan alkhairi da suke samu soyuwa da matsayi awajan Allah, shiyasa Annabi s.a.w ya kwadaitar damu yinsu agurare masu yawa kuma shima yayi hakan a aikace.
1-Manzon Allah s.a.w yace:
(Lallai Allah zai ce a ranar Alqiyama:Ina masu yin Soyayya dan girmana "ma'ana masu yin soyayya dan Allah dan girman Allah" a yau zan sanya su a inuwata ranar da babu wata Inuwa sai Inuwata).
@صحيح مسلم
2-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Abubuwa guda ukku wanda ya samesu ya sami dandanon zakin Imani,
-Allah da Manzonsa su sukafi soyuwa agare shi fiye da dukkan komai.
-Kuma yana son bawane badan komai ba sai dan Allah.
-Kuma yana kyamata a koma cikin kafirci bayan Allah ya tsamoshi daga cikinsa kamar yadda yake kyamatar a sanya shi wuta).
@صحيح البخاري - رقم: (21)
3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai wani mutum ya tafi ziyarar dan uwansa zuwa wani gari,sai Allah ya tura masa Mala'ika akan hanyarsa,sai Mala'inkan ya tambayesa ina zakaje?? Sai yace: zanje ziyarar dan uwana a wancan gari,sai Mala'ikan yace:Shin zakajene dan kwadayin wani abu da kakeso ya baka?sai yace: A'a babu abinda zai kaini zuwa wajan sai dan ina sonsa dan Allah kadai.sai Mala'ikan yace da shi: Ni dan Sakon Allah ne,hakika Allah yana sanka kamar yadda kake son dan uwanka dashi).
@صحيح مسلم - رقم: (2567)
4- 3-Annabi s.a.w yana cewa:
(Imanin dayanku baya cika har sai ya soma dan uwansa irin abinda yake soma kansa).
@صحيح البخاري - رقم: (13-45)
5-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Duk wanda yaje duba marar lafiya ko ya kaiwa dan uwansa ziyara dan Allah,sai wani mai kira yayi kira yace:
Ka dace ka rabauta kuma an tanada maka mazauni acikin aljanna) حسنه الألباني ف صحيح الترمذی @
6-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Mutumin da ya kai ziyara ga dan uwansa wani gari dan Allah,yana samun aljanna).
@حسنه الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2604)
7-Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Allah madaukakin sarki yana fada:
Soyayyata ta wajaba ga masoya guda biyu da sukeyin soyayya sabodani,da masu jama da junansu sabodani,...... da kuma masu ziyartar junansu sabodani).
@صححه الألباني في
📚 صحيح الجامع - رقم: (4331)
8-Annabi s.a.w yana cewa:
(Lallai mafi cikar samun matsayi a musulinci shine mutum yayi soyayya dan Allah kuma yayi kiyayya saboda Allah).
@الألباني في صحيح الجامع - رقم: (2009)
Allah ka bamu ikon yi soyayya da kuma ziyarar yan uwanmu da abokin arziki da sauran musulmai dan Allah, amin

*AMFANIN MAN ZAITUN A JIKIN MUTUN* {1}
Shidai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin, ALKUR'ANI MAI GIRMA
haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) *yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka.*
() tirmizi ne ya ruwaito
DAGA CIKIN AIKIN ZAITUN
*́KARFIN MAZAKUTA*
Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai
Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah
*CIWON CIKI*
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.
Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah
*CIWON KAI*
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya.
*CIWON HAKORI*
duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.
*CIWON HANTA*
duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.
*CIWON DADASHI*
Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.
*CIWON SUKARI*
duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah
*CIWON ASMA*
duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko ya'yan sa ya dinga turara wa.
*CIWON KODA*
duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana insha Allah.
*CIWON BAYA*
duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa abayan insha Allah.
*CIWON RAMA*
duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zaiyi kiba.
*ZAZZABI MAI ZAFI*
duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah.
*KYAWUN FUSKA*
Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda bazai cutaddashi ba, to yadinga shafa man zaitun Dana habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai mamakin yadda fuskarsa data koma.
*ZUBEWAR GASHI*
Duk mutumin da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube , to saita samu ruwan zafi ta wanne kanta dashi sannan bayan ya dan bushe saita zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kannata dashi gaba daya kullum.
*KARANCIN JINI*
duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana.
*BAYAN GIDA MAI KAURI*
ロ゚BASUR duk mutumin da yake shan wahala in yazo zaiyi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya turashi acikin duburarsa.
*CIWON MARA GA MATA*
duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon ,saita samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da zatayi haila bazai Mata ciwo ba.
*SANYIN KASHI*
duk mutumin da kashinsa yayi sanyi baya iya motsashi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan insha Allah.
*AMFANIN MAN ZAITUN A JIKIN MUTUN* {2}
*KYAWUN FATA DA LAUSHINTA*
Duk mutumin da yake so fatarsa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa dashi bayan Yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa zata koma insha Allah
*KURAJEN KAZUWA*
duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa awajan har ya warke.
*CIWON KUNNE*
duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun Dana habbatussauda yana digawa a kunnensa insha Allah.
*CUTAR KYASBI*
duk mutumin da yake da KYASFI ajikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe ,ya dakashi yayi laushi sai ya Jada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.sai ya wanke
*SHAFAR ALJANU*
duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa sonshi, shida habbatussauda
Da haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su akowane hali, in da hali ma ya mai dasu mansa na shafawa amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu'a.
*CIWON KARKARE*
Duk mutumin da ciwon karkare yasa meshi, to sai ya samu man zaitun, sannan asamu lalle a kwaba, sai azuba man zaitun din acikin lalle a gauraya, sannan a karanta *(AYATUL KURSIYYU)* sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa ajikin wannan karkare insha Allah
*CIWAN NONO*
Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar, to Ana hada man zaitun da garinsa, abarbada akan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.
*MOTSA SHA'AWA*
Man zaitun yana motsa sha'awa in an shafashi lokacin da ake yi wasa.
*CIWON SAIFA*
duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma farar saka ya sha, insha Allah.
*TSUTSAR CIKI*
duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su yasha, wannan tsutsar zata mutu.
*CIWAN HANJI (ULCER)*
Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi yaji kasu ya dinga sha har sai ya warke.
*FITSARIN KWANCE*
Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Dana habbatussauda a zuba a nono a dinga bashi yana sha zai dai na. Insha Allah
*MUTUWAR JIKI* (KASALA)
Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zaiji karfin jikinsa.
*YAWAN ZAZZABI*
duk mutumin da yake yawan yin zazzabi , to saiya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma maras hadi ya dinga sha insha Allah
*CIWON GABOBI*
Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo to saiya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a GABOBI.
*KWARKWATA*
duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta Bari sai Rana ta take sai ta zubar wannan man a kannata ta barshi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke insha Allah zata ban kwana da kwarkwata.
*CIWAN TARI*
duk mutumin da ya kamu da kowanne irin Tari to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da yar'citta da tsamiya da zuma, sai ya hadasu guri daya ya cakuda ya dinga ci insha Allah.
*MAJINAR KIRJI*
duk mutumin da yake yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma.
*TARIN FUKA*
Duk Wanda yake tarin huka to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya kullum.
MATA SUNA DA ALKAHAIRI MAI YAWA
Sune mafiya yawa a gidan aljanna.
Sune mafiya yawan 'yayan Annabi Adam A.S
Kuma sune mafiya yawa acikin gidan Wuta.
DALILI NA FARKO
Manzon Allah SAW yace;
*(Naga gidan wuta,sai naga mafiya yawan cikinta matane)*
A wata riwayar saboda
*(Suna yawan La'anta da kafarcewa mazansu)*
@متفق عليه عن أبي سعيد رضي الله عنه
Manzon Allah SAW sai ya fada masu maganin da zai fitar da su daga wuta da cewa;
*(Mata ku yawaita Sadaka ko da da abin adonku ne domin naga da yawa daga cikin a wuta )*sai mata sukayi tayi sadaka a awannan lokaci.
Babbar hanyar magance shiga wuta ga mace bayan imani da bautarAllah shi kadai to babu kamar
*Yawaita Sadaka*
*Kyautatawa miji*.
DALILIN NA BIYU
Manzon Allah SAW yace;
*(Lallai farkon Tawagar mutanan da zasu shiga aljanna,suna masu siffa kyakkyawa kamar wata daren haske,masu biyo bayansu suna kamar tauraro a sami mai haske sosai,kuma kowane mutum daga cikin yan aljanna yana da mata biyu,sannan babu wani gwauro marar mata acikin aljanna)*.
@رواه مسلم عن أبي هريرة رضي الله عنه.
القاضي عياض رحمه الله:
Yana cewa;
"Abinda wannan Hadisi yake nunawa to shine *Mata sune mafiya yawan yan aljanna,saboda kowane mutum yana da mace biyu a aljanna sannan babu gwauro a aljanna sannan hadisa yazo yana baiyana mutum daya za'a bashi daga yan matan Hurun'in da yawa a aljanna*".
@انتهى من شرح النووي على مسلم.
DALILI NA UKKU
القاضي عياض رحمه الله:
Yana cewa;
*"Idan ka hada wadan nan Hadisai guda biyu,zaka fita da sakamakon cewa MATA SUNE MAFIYA YAWAN 'YAYAN ADAM"*.
@سلسلة الأحاديث الصحيحة
Allah ka kara yiwa mata iyayen mu albarka ya gafarta masu ya sanya su a aljanna baki daya.
SOYAYYA.
Yana daga cikar soyayya yiwa matar ka kyawawan addu'o'i a bayan idonta. Shiyasa masana kuma kwararru a wannan fannin sun tabbatar Duk wanda kake so to, soyayyarka gare shi ba zai yi koda rabin cika ba matukar baka yi masa kyawawan addu'o'i a bayan idonSa, sun kuma tabbatar daga cikin fa'idar da ake samu a Duniya sakamakon yiwa wanda kake so addu'a a boye akwai samun soyayyar wanda kake yiwa addu'ar domin addu'a ga wani a boye yana daga kyawawan ayyuka da shari'a ta kwadaitar akan su.
Ta yiwu sun fahimci hakan ne a Dalilin fadin Allah Madaukaki:
{إن الذين وعملوٱ الصالحات سيجعل لهم الرحمن ودا}
(Lalle wadanda suka yi imani kuma suka aikata kyawawan ayyuka Allah zai sanya so da qaunarSu cikin zukatan BayinSa).

KUZABI MA'ABUCIYA ADDINI MAI KYAWUN HALI
Babu mai morewa rayuwar aure sau wanda ya bi umarni da shawarar Manzon Allah wajan zabar matar aure,wato ka zabi mai hali;-
*Ma'abuciya addini mai halin kwarai mai tarbiya,mai sonka saboda Allah*
Amma dukkan wanda yabi son ransa da kwadayin duniya da son kwawar duniya wajan zabar macen aure yaki bin shawarar Manzon Allah,to yayi asara kuma zai ga sakamakon abinda ya zaba na wulaqanci da nadama.
Hadisi ya Inganta daga Annabi yace: "
*(Ana auren mace ne saboda abubuwa hudu,don dukiyarta ko dangantakarta ko kawonta ko addininta,to ka zabi mai addini,za ka wadatu da ita)*
@Bukhari da muslim suka ruwaitosa daga abu huraira.bukhari: 5090,muslim: 1466)
Awata riwayar abu huraira:-
*(Ba a auren macce sai saboda abubuwa hudu)*
@Mustakhraj abi awanah: 4008)
Haka wannan hadisi ya zo ta hanyar jabir dan abdullahi (muslim: 715) sai dai ba a ambaci dangantaka ba.
Ya kuma zo daga abu sa'idin alkhudriy (musnad abi yaala: 1012) da lafazin: *(Ana auren macce don dayan abubuwa uku:dukiyarta da kyawonta da addininta,na horeka da mai addini da dabiu)*
Makamancin wannan lafazi ya zo a riwayar ummul muminina aisha.
@musnadu ahmad: 25191)
الـلَّهُ :
Yana cewa;-
{فَانْكِـحُوا مَا طَـابَ لَكُـم ْمِـنَ النِّـسَاءِ}
Fassara;
*{...ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã}.
العَلّامَـة السَّـعْدِي -رَحِـمَهُ الله-
Yana cewa;-
*"Ai abinda yafi dacewa wajan zabar mace aure,kazabi mai halin kwarai mutumniyar kirki mai addini da tarbiya,wanda zaka sami kwanciyar hankali sanadiyyarta,wadda ta hada kulawa da addini da hali mai kyau abin yabo,da wasu dhabi'u masu karawa mutum daraja da kima"*.
Acikin wannan ayar mai girma,akwai;-
*"Kwadaitarwa wajan zabar mace wadda ta hada dukkan siffofin kamala da hali mai kyau da tarbiyar addini da kuma halin da mace take da su wanda sune ake kalla wajan zabar macen aure"*.
Domin shi aure ana duba abubuwa kamar haka awajan zaben macen da za'a aura;-
*1-Tarbiya mai kyau da kulawa da addini sannan a sami soyayya saboda Allah tare da tausayi mafi rinjaye wajan soyayyar*
*2-Macece wadda zata iya yin hidima na gida na yau da kullum tare da daukar dukkan buqatan mai gida da kulawa da gida da bada tarbiyya*
*3-Mai kyawawan halaye abin yabo abin koyi ga kowace al'umma*
*4-Mafi girman abinda ake dubawa shine addininta da hankalinta da tarbiyarta*.
@تيـسير اللطـيف المنان صـ (١٩٩) ]
Allah ne mafi sani.
*Allah ka bamu mata na kwarai da zuri'a mai albarka ka sanya mu zama nagari awajan matan mu*.
 
 ZUWA GA AMARYA
1-Ki sani cewa aure ibada ce, don haka za ki iya samun abubuwan da rai ba ya so, domin aikin aljannah ne.
2-Zaman aure hukuri ake yi, domin rayuwan aure ba na wata 1 ko
shekara 1 ko 50 bane, rayuwa ce ta har a bada sai da hakuri.
3-Miji shugabane a gareki, don haka duk abin da yake bukata a kowani
lokaci dole ki aikata mishi.
4-Duk abin mijinki baya so ki nisance shi, domin yawan sabawa miji ya
sa wa ya tsane ki.
5-Ki kula da dukkan abin mijin ki yake so kira ki aikata shi ko da za ki
walaha a aikatawa, domin wannan shine zai sa mijinki ya kyaunace ki.
6-Kada ki yarda wani ya san sirrin da ke tsaninki da mijinki ko da
iyayenki ne.
7-Ki kulada dukkan shawarar da kowace ‘kawa za ta ba ki, ki sanya ‘yar‘wanki na kusa a matsayi a bokiyar shawara.
8-Ki ji tsoran ALLAH a duk yadda ki ke, ALLAH zai sanya miki mafita
akan dukkan al‘amuranki



1 comment:

  1. https://mynovels.com.ng/abubuwan-da-ke-haifar-da-raunin-mazakuta/

    ReplyDelete