Friday, December 21, 2018

ZUWAN TURAWA ZARIA

ZUWAN TURAWA ZARIA
Posted by: Sadiq Tukur Gwarzo
Tun gabannin mamayar turawa ga daular Zazzau, an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da yadda ta kasance a baya sabili da wasu dalilai
Da fari dai, akwai rikicin cikin gida daya mamaye kabilun fulani da suka jagoranci kar
ɓe ikon Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.
Ance tun zamanin Sarki na farko aka soma wannan sa
ɓanin tsakanin Jagora kuma sarkin Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja'e shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai aka bashi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.
Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan rasuwar Sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen shekara ta 1897 kenan.
Hakan ya samu ne ta yadda kabilu hu
ɗu na fulani da aka sani da mulkin zazzau suka nuna bukatarsu ga mulkin, kabilun sune Mallawa, Katsinawa da Barnawa.
A cikin masu neman mulkin akwai
ɗan marigayi Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam Lawan ɗan tsohon Madaki da kuma wani daga cikin 'ya'yan tsohon sarkin zazzau Mallam Sambo.
Babban abinda kuma ya samar da sa
ɓani a lokacin shine yadda Galadima ya tsaya kai da fata cewar wani kurma kuma Makaho mainsuna Mallam Muhammd ya kamata a baiwa sarauta. Mutane sunce hakan nada nasaba da kokarinsa na ɗora wanda ba zai iya kataɓus ba a mulki ta yadda zai rinka juya shi.
Ganin karfin ikonsa yasa wa
ɗancan kabilu na fulani suka dunkule tare da goyawa Madaki kwasau baya domin ya zama sarki. Akan haka suka nemi gudunmuwar Sarkin Kano Aliyu Babba, da kuma rundunar 'yan bindiga da mahaifin Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa, shikuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga Sokoto.
Ana cikin wannan kiki-kaka, sai wazirin sokoto Buhari yazo zazzau da niyyar masalaha. Ya lura da ha
ɗarin dake ciki ainun idan aka ɗora wani ba Kwasau ba akan gadon mulki, tunda yasan yadda Basasa ta kaya a kano, sai kurum ya ɗora Madaki Kwasau sarautar Zazzau.
Yin haka keda wuya sai wasu daga mabiya da garuruwa suka fara yin bore.
Sarki Kwasau ya shirya yaki ya tafi Gwari, da Kataf da Kadara tare da tilasta musu yin biyayya a gareshi.
Abu na biyu kuma da ya sake raunana zazzau shine hare-haren da take samu daga wasu sarakunan hausa misalin Mara
ɗawa da Ningawa.
Idan dai ba'a manta ba, a lokacin Mara
ɗawa na tsaka da kai hare-hare kasar hausa. Bayan sarkin su Dan baskore ya mutu, sai wanda ya gajeshi mai suna Baratiya ya ɗora akan inda ya tsaya.
Baya danan sai Mutanen Ningi, wa
ɗanda akai-akai suke kawo hari ga birnin Zazzau. Shine har akace sun taba yiwa zazzau ɗin ruwan kibiyoyi a lokacin da suka kawo faɗa zazzagawa suka shige cikin ganuwa suka kulle kansu. Kuma har sun kwace ikon wasu garuruwa irinsu Soba, Dutsen Wai da Kubau daga Zazzau.
Kari akan haka shine Sarkin Kwantagora Nagwamutse, shima a lokacin ya addabi zazzagawa da hari.
Duk kuma a wannan lokaci turawa fakare sukai suna kallon zazzau. Saboda ance sun gama lissafa cewar itace cibiyar da zata fi a garesu wajen kafa sansani kafin kaiwa Kano da Sokoto hari.
Kuma kasancewar akwai turawan mishan dake al'amuransu a Zaria sai ya zamana turawa basu da burki gareta, suna shigowa suyi hur
ɗoɗinsu babu tsangwama.
Ana haka sai labari yazowa Sarkin Zazzau Kwasau cewa turawan mishan sun nemi wurin zama a Kano amma sarki Alu ya koresu, sannan rundunar dakarun turawa mai suna 'West African Frontier Force' (WAFF) ta kone garuruwan Remo da Kaje dake karkashin zazzau, kuma da ra
ɗe raɗen zasu kawowa zaria yaki don hana cinikin bayi. Sai kawai sarki Kwasau shima ya kori turawan mishan daga kasar sa suka koma Girku da zama.
Yin wannan keda wuya sai shugaban waccan runduna ta turawa mai suna Kaftin Kambell ya kawo ziyara ga sarki Kwasau, yace yazo kulla abota ne dashi tare da samar da yarjejiniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
Abinda ya kara kwantar wa da Sarki Kwasau hankali a game da turawa shine yadda suka kame kwantagora tare da korar sarkin su abokin hamayyarsa Sarki Ibrahim Nagwamutse a shekarar 1901, sannan kuma suka kame sarkin a wani fa
ɗa da sukayi a Maska suka aike dashi garin Lokoja aka tsare.
Wannan yasa hankalinsa ya kwanta dasu domin sunyi masa maganin abokin hamayyarsa, suka rinka kwararowa cikin zaria suna lamurorinsu.
Sai dai kwatsam babu aune, sai sarkin Zazzau Kwasau yaji turawa Sun ayyana Zaria a matsayin garin da suke iko dashi tare da kawo wani bature mai suna Kaptin Abadie da akafi sani da suna Mai jimina a matsayin Rasdan na garin, wannan yasa sarkin cikin damuwa da
ɓacin rai.
Ya shiga tunanin mafita a wannan lamari, gashi yana da rauni wajen fa
ɗa da turawa, sannan sarkin Bidda ya aiko masa da gargaɗin kada ya kuskura yace zai buga dasu, gashi kuma yana jin kaskancine ya cigaba da zama a kasansu.
Don haka mafitarsa biyu ce, kodai ya hakura ya zauna cikin kaskanci, ko kuma ya nemi taimakon sarkin Kano Alu yayi yaki dasu.
Da tunani yayi zurfi, sai kurum ya za
ɓi shawara ta biyu..
Sarkin Zazzau Kwasau ya gamsar da zuciyarsa cewa ko kaɗan ba zaiyi biyayya ga turawa ba, tunda kasar sace ba tasu ba. Kuma ba addini ɗaya gare suba. Don haka ya soma tunanin mafita.
Akan haka ya aike wa Sarkin Kano Aliyu Babba wasikar neman tallafi, yana mai shaida masa cewar kiristoci sun yawaita a Zazzau, har kuma sun yi kaka gida gareta tare da maisheta mallakinsu, don haka yana neman mafita.
Ana haka sai rikicin kisan Kyaftin Moloney ya bijiro.
Shi Kyaftin Moloney, shine Rasdan na Kyaffi. Ita kuwa Kyaffi tana karkashin daular Zazzau ne a lokacin. Kuma Sunan shugabanta wanda yake a matsayin wakilin sarkin Zazzau a Kyaffi shine Magaji Dan Yamusa.
Akace rannan Kyaftin Moloney ya tara mutane yana musu jawabi, yana karanto turanci garesu, wani bakin mutum kuma yana tafintan abin da duk ya fa
ɗa.
Magaji Dan Yamusa da tarin wasu jama'a duk suna wurin.
Kwatsam sai rashin fahimta ya dabaibaye tafintan kyaftin Moloney sakamakon tsauraran kalmomin turancin da Moloney ke karantawa, shikuma tafinta sai ya rinka yiwa turancin fassarar kalma da kalma..
Akan haka ya fa
ɗawa mutane cewar turawa keda iko dasu, da komai nasu. Har matayensu ma mallakin turawa ne.
Ance kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney akayi yana mirginawa a kasa, Magaji Dan Yamusa ya saro shi.
Daga nan fa
ɗa ya ɓarke tsakanin mutanen Magaji da dakarun Moloney.
Daga karshe dai, Magaji Dan Yamusa ya gudu da tawagarsa zuwa kano. Sarkin Kano Alu Babba yaji da
ɗin abinda Bakonsa yayi, ya karrama shi tare da bashi mafaka.
Duk da cewar akwai sa
ɓanin inda wannan rikici ya auku, shin a Keffi ne ko a Zaria, amma dai turawa sun ɗora alhakin faruwar hakan akan Daular Zazzau, tunda acikin ikon ta abin ya faru.
Sannan kuma sun damu matuka bisa abinda Sarkin Kano yayi, wannan yasa suka sake
ɗaura aniya da kaimin tafiya kano da yaki duk da cewa daman fakonta sukeyi.
Ganin haka sai Sarki Kwasau ya soma shirin guduwa, saboda ya tabbatar abinda zai faru ba mai da
ɗi bane.
Ya sake aikewa da wasika ga Sarki Alu Babba na kano yana sanar masa da cewar lallai ba-suga ta zama ba, ha
ɗari gagarumi na zuwa garesu.
Sukuwa turawa sai suka ji tsoron idan Sarkin Zazzau ya gudu da mutanensa, to fa zaije ya ha
ɗu ne da Sarkin Kano su kara karfi, don haka sai suka baza dakarunsu akan hanyoyin Zaria zuwa kano, zaria zuwa Katsina da Zaria zuwa Bauchi, da niyar hana sarkin gudu ko kuma a kame shi idan ya gudo.
Rannan sai kurum Rasdan na zaria watau kyaftin Abadie, ya aikewa Sarki Kwasau gayyata domin tattaunawa.
Sarki Kwasau ya fusata da haka, yace don me kamar kyaftin Abadie kirista da yake a kasarsa zai kira shi yazo, don haka ba zai jeba.
Daga nan sai turawa suka samu yadda suke so, suka turo dakaru masu
ɗumbin yawa cikin zaria, suka yiwa fadar Sarki kwasau kawanya, sannan suka shiga suka kama shi tare tafiya dashi Wushishi. Acan suka tsare shi har Allah yayi masa rasuwa.
Kuma an samu cewar Sarki Kwasau yayi rubututtuka dangane da yadda aka kamashi da halin daya tsinci kansa. Aciki akwai wata takarda mai suna 'Nuzhatul Asiyr' inda ya rubuta cewar turawa sun kama shine bisa kin yi musu biyayya, a yammacin wata ranar jumua cikin kwanaki goman karshe na watan Jumada Ula. (dai-dai da 19-satumba-1902).
Sannan kuma ya bayyana farin cikinsa bisa yadda suka kamadhi ba tare daya bi umsrninsuba ya zauna akarkadhinsu, hsr ma ya kamanta kansa da mutanen Ashabul Kahfi a wata waka ea aka samu ya rubuta.
Daga karshe, sai turawa suka na
ɗa Galadima Salmanu sarkin Zazzau a farkon shekarar 1903.

No comments:

Post a Comment