TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
SADIQ TUKUR GWARZO
GABATARWAR
Muhammad Sani Umar
Da
John Hunwick
A wani lokaci a shekarar 1902, wani matashi mai suna Abdullahi ya
riski kano daga arewa, ana tsammanin daga Ghadamus yake. Bamu samu
labarin komai dangane da dalilin zuwan saba, da kuma danginsa, amma dai
wannan labarin daya rubuta na daga madogarar mu dangane da labarin nasa.
Domin acikin labarin ne ya bayyana kansa a matsayin ɗalibi, amma
ba'a fuskanci a takamaimen fannin da yake ɗalibtar ba, domin babu wata
alama dake nuna yazo kano ɗaukar karatu a gurin masana, amma mun samu
labari cewa wasu shekaru da suka shuɗe yayi aikin tafinta ga kawunsa na
wajen mahaifi dake zaune a kano, wanda hujjoji sun tabbatar da cewa
balaraben Ghadamus ne da kasuwanci ya kawo shi kano.
Abdullahi Al
Ghadamasi ya riski kano watanni 8 kafin turawan mulkin mallaka su riski
kano, har su cita da yaki a shekarar 1903. Don haka muna iya cewa shi
ganau ne ba jiyau ba akan yadda yakin ya kasance.
Haka kuma, bamu
samu komai dangane da hakan ba sai a wajajen shekarar 1907, zuwa 1908
sanda Abdullahin ya amsa kiran C.L Temple na neman wanda zai taimaka
masa a fannin tafinta masanin Arabi da Hausa. A wannan lokaci C.L Temple
na kokarin tafiya hutu ne burtaniya, watakila bayan ya kammala
ayyukansa a sokoto kenan a watan janairun 1908.
Koda yake, ance
aikin Abdullahi da Temple baiyi tsawo sosai ba sabili da yadda akace an
nusar da Temple cewar akwai rashin gaskiya/cushe a aiyukansa na fassara.
Babu Jimawa ne kuma akace Abdullahi Alghadamasi ya shiga aiki da H.R
Palmer, wanda a lokacin babban aikinsa shine tattara haraji daga loko da
sakunan kasar kano.
Kuma kamar yadda muka fahimta, Palmer yayi
mu'amala dashi saɓanin yadda Temple yayi dashi ta hanya mai kyau harma
yana yawan godiya gareshi. Kai, muna iya cewa ma babu shakka, Abdullahi
ne matashin da Palmer yake nufi da 'matashin balarabe' a farkon
littafinsa na sunayen sarakunan kano mai suna 'Kano chronicle' wanda
yace ya ɗauka aiki, har kuma yana iya fahimtar larabcin Tripoli dana
Ghadamus.
Sannan, Babu takamaimen dalilin daya sanya Abdullahi
Alghadamasi ya rubuta wannan tarihi, amma tana ita yiwuwa Palmer ne ya
karfafe shi yayi. Haka kuma bamu da takamaimen sanin halin da Abdullahi
ya cigaba da kasancewa bayan Palmer ya tafi hutu Burtaniya. Koda yake,
ance Palmer yayi nufin tafiya tare dashi Burtaniya ɗinma, amma yayin da
suka riski Birnin Ikko, Sai Abdullahi ya karaya, har ya yanke shawarar
bazai iya jure doguwar tafiya cikin teku ba.
Don haka, samun
wannn tarihi muna iya cewa abu ne mai kyau a garemu, domin mahangan da
tarihin ya kalla. Da fari dai, Abdullahi yana cikin kwaryar kano turawa
suka zo, don haka ya gani kuma yaji abinda zai iya bada labari akansa.
Sannan kuma tarihin ya kalli kasar hausa daga fuskar turai, tunda
yayi aiki da turawan harma turawan sun gyara masa wasu aiyukan nasa.
Yadda Turawa Suka Riski Kano.
Ali ɗan Abdullahi Alfallati (Aliyu Babba Zaki) ne sarkin kano na
wannan lokaci, kuma yana kan mulki sai labarin yaki ya zowa wannan gari.
Ali, sarkin wannan gari yana sane da labarin yaki. Amma sai yayi shiru bai yayata ga jama'a ba.
A lokacin da tsoro ya cika masa zuciya, sai ya tattara amintattun sa,
sannan yace musu "Kuyi sani yaku jama'a, nayi niyyar yin tafiya zuwa
sokoto. Don haka waɗanda duk sukayi biyayya dani suna iya bina wannan
tafiya"
Daga nan sai ya shiga tattara jagororin yakinsa, da manyan
jarumansa da barori, ya sanar musu da shirinsa na tafiya sokoto domin
ziyartar iyaye da kakanninsa. Don haka a iya watanni biyu suka kammala
shiri.
Da lokacin tafiya yayi, sai sarki Ali ya kira yaronsa mai
lakabin Sarkin Shanu, yace masa "Ya kai sarkin shanu, lokacin tafiya
sokoto ziyartar iyaye da kakanni na yayi. Gashi kuma kai zan dankawa
kasarnan a hannunka ciki da kewayenta da dukkanin hakimanta. Wannan
mukamine dana sanya a hannunka, don haka kayi kokarin rike shi da amana
da kuma gaskiya. Kuma na sanar da Ma'aji Usmanu ya tallafeka wajen tsare
wannan birni, tare da larabawa mazauna mutanen Tripoli da Ghadamus.
Idan wani abu ya faru abirni, ko makiya suka zo daga ko ina, to ina
umartarka kayi aiki da nutsuwa, kuma ka nemi shawarar larabawan nan
wajen yanke hukunci.
Bayan nan kuma, sai ya sake kiran Ma'aji
Usmanu yayi magana dashi da cewa "Kayi sani ina shirin tafiya sokoto
ziyartar iyaye da kakannina. Kuma na sanya kasarnan a hannunka dakai da
Sarkin Shanu. Idan wani abu ya auku a birni, ko ka samu labarin zuwan
makiya daga ko ina, to kuyi aiki da nutsuwa tare da larabawan nan
mazauna birnin nan. Kunga muna da iyali, bayi da tarin dukiya, don haka
ku nemi shawarar su don samun sahihiyar mafita, lalle ne suƴ mutane ne
masu ingantacciyar fahimta.
Saboda haka kada kayi watsi da
ra'ayinsu. Ni yanzu zan tafi. Idan Allah Ubangiji ya tabbatar zan bar
gari ranar 4 ga watan shawwal ( shekarar 1320 kenan, dai-dai da
3-1-1903.)
Ita kuwa kofar kansakali. Kada ku rufeta domin tanan zamu rinka sadar da manzanni a tsakanin mu.
Sarkin kuma ya sake shaidawa Sarkin shanu cewa "Kai wakili nane, don
haka duk abinda ya faru bayan rabuwar mu ka sanar dani ta hanyar
wasika, kuma kada ka bari aike ya tsaya a tsakaninmu daga gareka da
ma'aji. Amma lamurorin sharia, sai kubar su a hannun Alkali, ku kuma
kuji da abubuwan da suka shafi Sarauta.
Don haka, idan Allah ya
dawo damu kano lafiya, muka sameku kunyi aiki da nagarta kun cika
umarninmu, to hakika zan saka muku da abinda zai faranta muku zuciya. Ku
sani Allah Ta'ala yace 'babu abu mafi kamantuwa da sakayya ga alheri
sai alheri' (Q 55:60). Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri amin"
No comments:
Post a Comment