Friday, December 21, 2018

ZUWAN TURAWA 2

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
Kashi na Biyu
SADIQ TUKUR GWARZO
Bayan anyi haka, sai sarki Kano Ali ya bar kano ranar 4 ga ga watan shawwal tare da tawagarsa, wadda ta kunshi dogaransa, dakarunsa da sauran barorinsa.
Kwana 26 bayan sun bar Kano sai labari ya riski kano cewar turawan yamma sun isa zariya harma sun kwaceta da yaki.
Da fari da suka shigo kano, sun riski wani kauye mai suna Bebeji ne. Sai kuwa suka kori mutanen garin suka kashe shugabansu da ake kira sarkin fulanin Bebeji.
Da labari ya riski sarkin shanu, sai nan take ya sanar wa da Ma'aji Usmanu cewar Turawa fa sun shigo kasar kano, harma sun cinye Bebeji da yaki.
Dajin haka, sai Ma'aji Usmanu ya tashi ɗan aike zuwa ga Larabawan nan mazauna kano, yace yana bukatar ganinsu.
Zuwansu keda wuya, sai ya shiga labarta musu halin da ake ciki na zuwan Turawan Yamma, sannan ya rufe da cewar wacce shawara zaku bamu bisa wannan lamari?
Larabawan nan sai suka ce ka sani ya kai Ma'aji, mu baki ne anan kasar, bamu da abin cewa anan. Kurum dai idan har suka rufar mana da yaki da niyyar kashemu tare da kwace dukiyoyin mu, to hakika muma zamu far musu da yaki daboda faɗin Annabi Muhammad S.A.W cewar duk wanda ya mutu yana kokarin kare dukiyarsa, to yayi mutuwar shahada. Haka kuma duk wanda ya mutu yana kokarin kare kansa daga halaka, shima yayi mutuwar shahada. Iya abinda zamu iya cea kenan.
Ma'aji Usmanu yace ku fahimce ni. Sarkin mu ya bar garin nan kuma ya umarcemu da cewa duk binda ya taso, muyi shawara daku, kuma kada mu tsallake ra'ayinku. Don haka kuji zancena, a yanzu muna zaune daku gari ɗaya, muna neman taimakon kune domin kare garinmu daga makiya.
Sai larabawan nan sukace wa Ma'aji Ka barmu muje gidajenmu tukunna.
Sai kuwa Maaji ya barsu suka tafi.
Da yammaci, sai dukkansu suka hallara kamar haɗuwa ta fari. Ma'aji ya kara nanata musu abinda ya faɗa da farko, sukuwa sai suka amsa masa da cewa "mun amince da duk abinda ubangiji yayi hukunci damu."
Sai Ma'aji yace "to idan Allah ya kaimu gobe muna raye lafiya, inason dukkanku da bayinku ku ɗauki makamai ku taru a bakin ganuwa. Nikuwa zaku sameni a bakin ganuwar Bebeji, don haka sai muga abinda Allah zaiyi."
Sai larabawa suka ce "munji abinda ka faɗa, Allah ya bamu nasara akansu amin."
Daga nan sai Ma'aji Usmanu ya tura da wasika izuwa sokoto, yana mai sanar da Sarkin Kano Alu Babba lamurorin da suka auku bayan barinsa birni.
Kashe gari, ranar talata (koda yake lissafin ranar ya nuna 4 ga shawwal + kwana 26, zai baka 1 gawatan zulka'ada na 1320, kuma ranar jumua ta kama) tun da sassafe wasu larabawan sukayi hawa da bayinsu suka tsaya a gefen ganuwa suna masu ɗauke da makamai.
Babu jimawa sai muka ga wasu mutane da suka fita izuwa Bebeji tare da Ma'aji sun shigo birni a sukwane kuma a gigice. Suna gudu kamar ransu zai fita, kowanne ya nufi gidansa suka shige abinsu.
Koda mutane suka ga haka, sai suka bisu a baya. Bayan ɗan lokaci wasu suka fito kofar gida, shine kuma sai mutane ke tambayarsu abinda ya faru. Shine sai suka ce hakika yau munga abinda zai fitar da zomo daga raminsa.
Mutane sukace bamu gane ba, me kuka gani kenan?
Mutanen nan "sukace munga kiristoci turawan yamma waɗanda zasu fitar damu daga garinmu. Suna ɗauke da madafu da ɗakaru masu yawan gaske. Lallai mun shaida waɗannan 'yan ta'adda suna nufowa ganuwar mu."
Kafin kace haka, sai muka fara jiyo kararrakin bindigogi, ana harba wata babbar bindiga da ake kira mai ruwa.
Harbinsu na farko suka karya kofar birni. Da suka harba na biyu kuwa sai da gidan sarkin kofa ya rushe. Harsashin yayi fata-fata dashi kansa sarkin kofar, ya faɗi matacce.
Koda larabawa suka ga haka, sai suka shiga cewa Ya Ubangiji Allah ka tsaremu daga sharrin wannan rana. Madalla da ubangijinmu mai tsarewa.
Daga nan fa sai suka rarrabu, kowannensu ya nufi gidansa ya shige, suka kulle kofofinsu, sannan suka haye bisa saman sorayen gidajen nasu.
Jim kaɗan da faruwar haka, sai turawa suka shigo birnin kano.
Suka shigo dasu da sojojinsu. Sannan kai tsaye suka nufi kofar fada. Suka shiga gidan ta kofar kudu. Jagoransu wani bature ne da ake kira Mai kwagiri.
Da shigarsu sai suka hangi wani mutum a tsaye da takobi zare a hannunsa. Su basu san kowanene ba, amma nan take baturen nan mai kwagiri ya harbeshi da bindigarsa, mutumin ya faɗi matacce. Kai kace tun jiya ya mutu. Ashe kuwa sarkin shanu ne wanda sarki Ali ya baiwa ajiyar gari.
Turawa fa suka rinka kutsawa cikin fadar nan tare da sojojinsu, da alamar akwai abinda suke nema amma basu same shiba. Domin babu abinda suka taras sai yara kananu da mata. A Gidan kuwa babu abinda kakeji sai koke-koke..
A wannan fada, turawa suka kafa dandalinsu.

No comments:

Post a Comment