Saturday, December 8, 2018

SHANYEWAR KAFA (Physio Hausa)

KA SAN DALILIN SHANYEWAR KAFA BAYAN ALLURA A DUWAWU?
"Injection Nerve Palsy" matsala ce da ke faruwa sakamakon raunata jijiyar laka ta 'sciatic nerve' dake kai saƙonni zuwa wasu gungun tsokokin ƙafa.
Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura akan jijiyar yayin yin allura a duwawu, ko idan ruwan allurar ya lalace, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar wanda hakan ka iya danne ko shaƙe jijiyar har aikinta ya kassare.
Waɗanda suke da haɗarin gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:
1) Wanda bai bada haɗin kai yadda ya kamata ba yayin yin allurar, musamman Ƙananan yara.
2) Mai rama sosai.
3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.
4) Da kuma wanda tsautsayi ya faɗawa.
Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukkan rassan jijiyar a ƙafar nan take ko bayan wani ɗan lokaci.
Alamomin sun haɗa da:
1) Matsanancin ciwo
2) Sagewa
3) Rauni ko rashin ƙarfin ƙarfa
4) Rashin ji a fata kamar taɓawa
5) Wahalar tafiya: dingishi, jan kafa, da sauransu.
Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, gaggauta ankarar da jami'in lafiyar da yai allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa kamar ba ayi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti ka iya kawo naƙasu ga ƙafar.
Saboda haka akwai matuƙar buƙatar ganin likitocin jijiya-ƙashi-da-tsoka (Physiotherapists) domin su ke da alhakin dawo da aikin ƙafar da ta sami wannan matsala.
Copy from Physio Hausa
Page
Posted By Adamu Mahadi Adam Gaya


No comments:

Post a Comment