Sunday, December 9, 2018

ABUBUWA GOMA DANGANE DA ZUCIYA

ALLAH GWANI | ABUBUWAN MAMAKI GOMA DANGANE DA ZUCIYA
1] Zuciya tana fara bugawa tun kwanaki 22—23 da halittar ɗan-tayi a mahaifa.
2] Girman zuciyar mutum ta kai girman dunƙulallen hannun mutum.
3] Zuciya tana bugawa sau 60—100 a minti ɗaya yayin hutu — yayin da ba'a aiki.
4] Zuciya tana bugawa kimanin sau dubu ɗari (100,000) a kowacce rana.
5] Zuciya tana buga ko harba jini da yakai yawan galan dubu biyu a rana.
6] Zuciya za ta iya cigaba da bugawa bayan an cire ta daga jiki.
7] Zuciya ta dogara ne da tsarin lantarki domin bugawa.
8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 —190 a minti ɗaya.
9] Zuciya tana harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu yakai mil dubu sittin (60,000 Miles) in da za'a warware su.
10] An fara yin tiyatar zuciya a shekarar 1893, wanda likitan zuciya Daniel Hale Williams baƙar fata ɗan ƙasar Amurka ya gudanar.

1] Ciwo
2] Kumburi
3] Ɗumi idan aka taɓa gaɓar
4] Kasa iya aiki da gaɓar
Abin da ya kamata a yi bayan targaɗe:
1] A kare gaɓar ta yadda ba za'a ƙara yin irin motsin da ya haddasa ciwon ba.
2] A hutar da gaɓar daga aikinta, saboda cigaba da aikinta ka iya ta'azzara raunin.
3] A sanya ƙanƙara a wurin ƙimanin minti ashirin: Za'a sami ƙanƙara sai a faffasata, sannan a ɗaureta a zani ko tawul mai tsabta sai a sanya ta a daidai raunin sai ta yi kimanin minti ashirin.
4] A naɗe ko a ɗaure da bandeji; wannan zai temaka wajen kare gaɓar da rage kumburi.
5] A ɗaga gaɓar da ta yi targaɗen sama; misali, ta hanyar ɗorata a kan fulo yayin da ake kwance.
6) Bayan wannan taimakon gaggawa, a gaggauta tuntuɓar likitan Fisiyo domin cigaba da jinyar gaɓar har ta warke ta dawo aiki yadda ya kamata.
Warkewa ta wannan hanya zai sa tantanan su warke, sannan a magance motsawar raunin ko tashinsa ta hanyoyi da dama kamar; amfani da na'urorin rage raɗaɗi da kuma na'urorin da ke haɓaka tohowar tantani ba tare da dogara akan shan magunguna ba.
Abubuwa da ba'a so a yi bayan targade:
1) Kada a lallanƙwasa ko mimmiƙar da gaɓar da zarar an yi targaɗe da zimmar dawo da aikin gaɓar ko rage raɗaɗin ciwo.
2) Kada a mulmula wurin targaɗen.
3) Kada a yiwa gaɓar ruwan ɗumin har sai bayan kwana uku.
4) Kada a shafa mai ko wani magani me zafin gaske a targaɗen.
#Sprain
#Sport #Injuries
#Athletics
#Ligaments
Copy from Physio Hausa
Posted by Adam m. Adam


No comments:

Post a Comment