Friday, December 21, 2018

TARIHIN KARAYE

TARIHIN KARAYE
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
Littafin 'Ƙaraye Maƙarar Maganar Kano' da Alh Shehu Garba Ƙaraye da kuma Umar Ƙaraye suka wallafa ya kawo manyan muhimman batutuwa na tarihi da suka faru a Ƙaraye.
Daga ciki, sunyi maganar Wanzuwar garin ƙaraye tun kafin soma sarautar Bagauda a Kano, a shekara ta 999 miladiyya.
Littafin ya tafi akan cewa tun da jimawa, akwai maguzawa da suke zaune a garin ƙaraye, waɗanda suke bautawa bishiyoyin kukoki da kuma na Rimaye.
Daga Rimayen da aka samu ana yiwa bauta don samun tagomashi akwai Rimin yaki-yaki, Rimin Kwatankwaro, Rimin tagwaye, da Rimin kofar Zango. Sai dai littafin bai faɗi asalin daga inda waɗannan mutane maguzawa suka zo ba.
Dangane da sunan wannan gari na Ƙaraye kuwa, a wani wuri littafin ya faɗi cewa Sunan shugaban Maguzawan farko a garin shine Ƙaraye, don haka ake kiran garin da sunansa.
Amma kuma a wani wuri na daban, littafin ya sake kawo cewar sunan ƙaraye ya zone daga yawaitar Ƙaro dake wata bishiya a tsakiyar garin.
Garin ya soma kafuwa ne a arewa da inda yake a yanzu, kuma anan ya wanzu tsawon lokaci har bayan jihadin fulani, sannan ya dawo inda yake da zama yanzu. Koda yake, har yanzu ana kiran wancan gari da suna tsohuwar ƙaraye, domin akwai mutane zaune acikinsa. Kuma akwai alamu masu nuni da tsufan gari da kai tsaye akan iya lura da zarar an shiga cikinsa.
Ana ganin Ƙaraye ta girmama, kuma ta shahara a zamanin baya, ta yadda faɗaɗar ta ya tuƙe da ƙasashen Katsina, Zaria da kuma kano, kafin daga bisani a kacaccala ta.
Haka kuma tayi tashen sadaukantaka da ƙarfi wurin yaƙi, tayadda tun sa'ar da ta ƙulla alaƙar zumunta da kano, ba'a taɓa samun wata rundunar mayaƙa data shigo Kano daga yamma don kawo hari ba, domin tun kafin isowarta Ƙaraye zata tarbeta tare da tabbatar da cewar tayi nasara akanta. Wannan shine asalin kiran ƙaraye da suna 'ƙyauren yamma da birni'.
Tsoffin garuruwan yammacin kano da sukayi tarayya da ƙaraye a tsawon zamunna da suka shuɗe sune Baɗari, Goɗiya, Yalwan ɗan ziyal da kuma shanono, sai kuma Getso, da Ƙwanyawa, da Gwarzo daga baya, da wasu makamantansu.
Waɗannan garuruwa na fsrko suna da tambura da ake ƙaɗawa sarakunansu, wanda ke nuna bunƙasar sarautarsu da kuma haɓakar garueuwan nasu.
Garin Ƙwanyawa na can yamma da Ƙaraye, kuma ya haɓaka ta yadda har akwai ganuwa kewaye dashi . An samu cewa awancan zamanin, dukkan garuruwan dake kewayen, basu da wurin fakewa idan an kawo harin yaƙi sama da Ƙwanyawa ko Ƙaraye. Da zarar sun shige birni aka ɓame ƙofa tofa sunsha, sai dai kaga sadaukai na hawa saman ganuwa suna harbo kibbau ga abokan gaba.
Wata rawa gagaruma da ƙaraye ta taka itace lokacin yaƙin Jihadin fulani don tsarkake addinin musulunci a kano. A wannan zamani, ƙaraye ta fafata da dakarun masu jihadi aƙalla sau uku, kuma ta samu nasara akansu sau biyu.
Kashi na farko shine a lokacin da masu jihadi suka yaƙi Goɗiya, sai suka gangaro yamma da nufin barin ƙasar kano izuwa ƙasar Ghana.
Karo na biyu kuwa shine a lokacin da masu jihadi suka dawo kano, sai suka riski dakaru sun haɗu ana saurarensu a ƙaraye, suka fafata dasu amma basu samu nasara ba.
Sai da taimakon Allah masu jihadi suka karya lagon ƙaraye gami da ƙwace garin a karo na ƙarshe da suka buga.
Ance a zamanin Sarkin Kano Sulaimanu ne aka ɗaga darajar Shugabancin ƙaraye izuwa darajar Sarki, saboda kasancewar wanda aka naɗa ya shugabanceta mai suna Mallam Adamu Kwasanlo, bafulani ne basulluɓe, wanda ya taka rawa a yaƙin jihadi. Don haka akace masa darajar sarautarsa ta sarki ce, yadda a gaba ba zaizo ya shiga sahun masu neman sarautar kano ba.
A yanzu haka, karaye ƙaramar hukuma ce a jihar kano. Kuma har yau sarkin yanka gareta, amma dai yana a matsayin Hakimi ne na mai martaba Sarkin Kano.
(Kaɗan daga tarihin ƙaraye kenan. Mai son jin ƙsri sai ya nemi littafin 'Ƙaraye Maƙarar Maganar Kano').

No comments:

Post a Comment