Saturday, December 8, 2018

TARIHIN ANNABI ADAM A.S

TAQAITACCEN TARIHIN ANNABI ADAM (A.S)
Dalilin halittar Adam a.s.
An ruwaito cewa, Kafin halittar
Adam tsira da aminci Allah su
tabbata garesa Duniya ta kasance
cike take da aljannu da dabbobi
masu fada da makamantansu.
Sannan kuma ya kasance Allah
madaukaki yana da wakilai a bayan
kasa wadan da suke umurni da aiki
kyakkyawa kuma suna hani da
mummunan aiki.
Har zuwa lokacin da aljannu
suka kangarewa Allah suka yi
taurin kai, sannan suka saba wa
Allah madaukaki. Suka canza suka
kirkiro bidi'o da ayyukan assha. Sai
Allah ya umurci mala'iku da su
duba zuwa ga halittar kasa wadda
ke cikin fadin Duniya, sanna su kalli
abin da suke aikatawa na daga
ayyukan assha, sai ya umurce da su
canza wadannan halittu su halitta
wadansunsu wadan da zasu zama
wakilan Allah kuma suna bauta
masa. Sannan sai Allah madaukai
ya ce musu :"zan sanya khalifana a
bayan kasa", sa suka ce masa:"
tsarki da daukaka sun tabbata a
gareka ya ubangijinmu, Yanzu ka
sa wanda zai rika barna da zubar
da jini a bayan kasa?" kamar yadda
aljannu suka rika yi, ka sanya mu a
bayan kasa matsayin khalifofinka
ta yadda zamu rika tasbihi da
godiyarka, sannan muna tsarkake
sunanka. Sannan muna yin biyayya
ga abin ka umurce mu da shi. Sai
Allah madaukakin sarki ya ce
musu:" Ni nasan abin da ba ku sani
ba".
Sai Allah ya tayar da Mala'ika
Jabra'il, ya aika sa ya debo kasa ya
mayar da ita yumbu sai ya halitta
Adam daga wannan yumbu ya dai-
daita halittarsa ya hura masa rai.
Halittar Hauwa'u Matar Adam
A.s.
Allah madaukaki ya sa wa
sabuwar halittarsa suna Adam,
sannan sai Allah ya halicci Hauwa'u
matarsa daga sauran yumbun da
ya yi saura daga halittar Adam a.s.
Sai Adam a.s ya kalli hauwa'u
ya ganta halitta makamanciyarsa,
sai dai kawai ita mace ce. Sai ya yi
mata magana kuma ta ba shi amsa
da harshensa. Sai Adam ya
tambaye ta wace ce ita? sai ta ce
masa: Ni halitta ce da Allah ya
halitta ni.
Sai Allah ya sanar da Adam
dukkan sunayen abubuwa kuma ya
sanya tausayi da kauna a
tsakaninsa da Hauwa'u. Don haka
sai ya yi kwadayin kallonta da
magana da ita sai ya je kusa da ita,
sannan sai ya tambayi Allah cewa
wace ce wannan halitta mai kyau
haka wadda nake kwadayin
kallonta da kuma kusanci zuwa
gareta? Sai jawabi ya zo masa da
cewa: ya Adam wannan Hauwa'u ce
kana so ta kasance tare da kai da
kauna, kuma kuna masu Magana
tare? Sai Adam ya ce: E ya Ubangiji
godiya ta tabbata gareka.Sai Allah
ya ce masa to baiwata ce ka neme
ta daga gare ni, sai ya ce to ina
nema ya ubangiji ka yarda? Sai
Allah madaukaki ya ce yardata ita
ce ka koyar da ita ilimin addinina.
Sai Adam ya ce wannan yana
gareka ya ubangiji idan ka so zai
yiwu.sai Allah ya ce lallai na so
hakan kuma na aura maka ita. Sai
Adam ya yarda kuma Hauwa'u ta
zama matarsa.
Girmama Adam da kin sujjar
iblis ga Adam
Allah madaukaki ya yi nufi a
bauta masa ta hanyar sabuwar
halittarsa Adam, don haka sai ya
umurci mala'iku da su yi masa
sujjada don girmamasa, sai dukkan
mala'iku suka fadi suka yi gaisuwa
ga Adam a.s.
Amma Iblis ya kasance daga
aljannu ya kansa ce tare da
mala'iku lokacin da Allah ya umurce
su da su yi wa Adam sujjada a
matsayin girmamawa, Iblis ya
kasance an halitta shi ne daga wuta
kuma mai tsananin biyayya ga
ubangijinsa don haka ne ya samu
damar kusantar Ubangiji, sannan ya
san shi cikin sahun mala'iku. Amma
sai Iblis ya sabawa ubangiji a
wannan karo ya ki yin sujjada ga
Adam a.s. ya kasance mai girman
kai yana neman uzri akan umurnin
Allah na yin sujjada ga Adam.Don
haka ne ya kasance duk ibadar da
ya yi ta tafi a banza, duk da cewa
babu wanda ya yi ibada kamarsa a
cikin mala'iku ko Annabawa. Sai ya
cigaba da neman uzri akan cewa
wai Allah ya halicce shi da wuta al
halin Allah ya halicci Adam da
yumbu, domin yana ganin cewa
lallai ai wuta tafi yumbu, ya za'a yi
ya girmama wanda aka yi da
yumbu alhalin ya fi shi.
Allah madaukakin sarki yana so
ne a bauta masa kamar yadda yake
so ba yadda shaidan yake bukata
ba, don haka ne Allah ya la'ance shi
kuma ya kore shi daga
rahamarsa.sannan Allah ya haramta
masa wasu karamomi da yake da
su kamar yadda mala'iku suke da
su, ya kasance tababbe har zuwa
ranar kiyama kuma zai kasance
tare da wadan da suka bi shi a
cikin matsananciyar azaba.
Lokacin da Iblis ya ga hushin
Ubangiji ya tabbata gare shi ya sai
nemi ladar ibadar da ya yi a sheka
da shekaru a wajen Ubangiji, abin
da ya nema kuwa shi ne Allah ya ba
shi damar ya rayu har zuwa ranar
kiyama. Sai kuwa Allah ya ba shi
wannan dama. Ya nemi wannan
dama ne kuwa domin ya yi
ramuwar gayya ga Adam wanda ya
sa aka nesantar da shi daga
rahamar Allah. Sannan kuma ya
nemi damar ya samu dama akan
Adam da 'ya'yansa wato dukkan
mutane. Don haka sai shaidan ya
cigaba da girman kai yana da'awar
cewa wai ya fi karfin Adam da
zuriyarsa. Don haka ne ya ke cewa
ai sai ya batar da duk zuriyar Adam
sai kawai yan kadan daga cikinsu.
Adam na neman taimako daga
Allah
Kamar yadda muka fada a baya
Allah ya ba Iblis damar rayuwa har
zuwa ranar tashin kiyama, sannan
ya samu dama akan mutanen da
suka bi shi, sai kawai salihan bayi
wadan da suka yi ayyukan kwarai,
wadannan ba ya da iko akansu.
Adam A.s. da ya fahimci haka,
shi ne yake cewa Allah kai ne kawai
kake da iko akan bayinka, kai ne ka
ba Iblis wannan dama kuma kai ne
kake da iko akan komi, Ya Allah ina
neman tsarinka. Sai Allah ya ce wa
Adam ka je duk wanda ya aikata
mummuna daga zuriyarka yana da
zunubi guda, idan kuma ya aikata
mai kyau yana da lada goma. Sai
Annabi Adam ya cigaba da cewa ya
Ubangiji a kara. Sai Allah
madaukaki ya ce to zan gafara ga
bayinka ba tareda kulawa ba. Sai
Adam a.s ya ce ya yi ya uabangiji.
Mantuwar Adam da kuskurensu.
Allah madaukaki ya zaunar da
Adam da Hauwa'u a gidan
Aljanna,sannan ya yi musu kashedi
da Iblis cewa lallai su yi hankali da
shi kuma abokin gabarsu ne kada
ya fitar da su daga gidan
Aljanna.Sannan Alllah ya hane su da
kada su ci wata itaciya a gidan
Aljanna amma suna iya cin kowace
ban da ita. Amma sai Iblis ya zo
musu da sura ta yaudara ya ce
musu ai idan suka ci wannan
itaciya to lallai zasu dawwama a
gidan Aljanna. Adam da matarsa
sun manta da kashedi da Allah ya yi
musu na kada su yi kusa ma da
itaciyar nan, kuma lallai kada su
yarda da yaudarar shedan domin,
makiyinsu ne, don haka suka bi
yaudarar Shaidan suka ci wannan
itaciya. Sakamakon yadda Shaidan
ya bayyana matsayin maikaunarsu
kuma maitausaya musu.Domin ya
nuna musu cewa idan suka ci
wannan itaciya ai zasu iya komawa
ma Mala'iku ko kuma su dawwama
a rayuwa ba zasu mutu ba.
Bayan kuwa Adam da Hauwa'u
sun ci wannan Itaciya sai Allah
madaukaki ya fitar da su daga
gidan Aljanna, inda Adam ya sauka
a wani wuri cikin India ita kuwa
Ahuwa'u a jidda kamar yadda aka
nuna cikin tarihi da ruwayoyi.
Annabi Adam da Hauwa'u da
sauran Mal'iku sun yi bakin ciki da
fitar Adam daga Aljanna.
Gafarar ubangiji ga Adam da
Hauwa'u:
Bayan saukar Adam da
Ahauwa'u daga gidan Aljanna sai
Allah ya aika mala'ika zuwa ga gare
su cewa ya gafarta musu, sannan
ya aika musu da hemar gidan
Aljanna domin su samu inda zasu
zauna a cikin duniya.
Bayan nan Allah ya umurci
Annabi Adam Adam da da'a zuwa
gare shi sannan kada su yi shirka
da shi, sannan Allah ya yi musu
albishir da cewa duk wanda ya bi
Allah daga cikin bayinsa zasu koma
wancan gidan Aljanna mai ni'ima.
Haka Dai Ada da Hauwa'u suka
cigaba da rayuwa a cikin duniya
suna haihuwa har duniya ta cika da
bil Adam.
Ya 'yan uwa musulmi wannan
kissa tana cike da abubuwan lura a
ckin rayuwa ta yadda take nuna
mana cewa mu yi la'akari sosai a
rayuwarmu, mu kaucewa sabon
Allah, domin sakamakonsa ba mu
san yadda zai kasance ba. Muna ga
dai yadda shaidan ya kasance mai
girma da daukaka amma laifi daya
ya yi, ya fitar da shi daga rahmar
Ubangiji har abada. Don haka dole
ne mu yi hankali mu guji sabon
Allah domin ba mu sani ba kada ya
zama sakamakon tabewarmu wa
'iyazu billah. Alla ya kiyashe mu
Amin.
.

1 comment: