Friday, December 21, 2018

FANISAU

TARIHIN DAKE YANKIN 'TSAUNIN FANISAU'
Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Tarihin garin Fanisau na komawa ne shekaru sama da dubu kwatankwacin shekarun kafuwar Kano.
Wani tsoho mai suna Usman Abdul'aziz Jikan wakilin Shawara, ya sanar mana da cewa tarihin Fanisau da tarihin Kano abubuwa biyu ne da suke a matsayin ɗaya.
Babu wanda ya san ainihin lokacin da mutane suka soma zama a gefan wannan tsauni na Fanisau tun kafin ma wurin ya zama gari kenan amma dai an gamsu da cewa kusan duk shigen al'adun da suka wakana akan dutsen Dala an samu kwatankwacinsu akan tsaunin Fanisau.
Wani Bamaguje da ake kira Gwambari Jade ne ya fara dawowa saman tsaunin Fanisau da zama daga kano sama da shekaru dubu ɗaya da suka gabata, shikuwa ya kasance Waziri ne ga Barbushe a wajen bautar gunkin Tsumburbura dake saman dutsen Dala tun a zamanin Maguzanci.
Ance da mazauna Dala, da Magwan, da Gwauron Dutse gami da Fanisau duk maguzawa ne masu ƙabila iri ɗaya. Sai dai sanin tushen su gami da yarensu zuwa yanzu yana da matuƙar wahala.
Irin waɗancan mutane ne suka soma zama a kewayen tsaunin Fanisau tun wurin yana ƙurgurmin daji.
Tana iya yiwuwa albarkar namun daji dake wurin da kuma neman tallafin Aljanar dake saman dutsen ce ta sanya mutane suka rinƙa komawa yankin da zama, sannu a hankali har ya zama gari.
Tabbas, akwai wata aljana dake saman wannan tsauni na Fanisau wadda ake kira da suna 'Aljanar Kan Dutse', wadda akace ita ƙawa ce ga Aljanna Tsumburbura. Wadda kuma aka samu cewa asalin maguzawan da suka soma zama a wurin suna mu'amala da ita na tsawon lokaci.
Ance tun a wancan zamani, takan taimaki garin wajen samun nasarar duk wani yaƙi daya taso. Sannan da zarar an tura mayaƙan Fanisau yaƙi zuwa wani yanki, har kuma sukaci nasara, sai aji garin fanisau ya kaure da guɗa. Don haka tanan mutanen garin kan gane nasarar yaƙin mayaƙansu tun gabanin su komo gida.
Sannan duk tawagar data nufo garin Fanisau da yaƙi zata ganshi yayi duhu, hayaƙi na tashi daga gare shi.
A tsawon zamani, garin Fanisau ya kasance kamar wata unguwa ce dake nesa da birnin kano wanda sai an shige wani surƙuƙin daji ake kaiwa gareshi. Ance sai a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa yasa aka zagaye garin da ganuwa, sannan aka fitar masa da kofofin shiga ta yadda da zarar yaƙi ya matso, sai mutanen dake zaune a kewayen garin su rugo su shige don meman mafaka.
Ance Sheikh Abdulƙadir Al Magili daya riski Kano a wuraren ƙarni na goma sha biyar zamanin Mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya sauka ne a Fanisau, sarki yana aika masa da abinci gami da sauran ababen buƙata. Amma daga baya aka tasoshi ya dawo Zauren Tudu, dake Ƙofar Wambai ta birnin Kano.
Asalin sunan Fanisau ya fito ne daga wani shahararren malami daya soma zama a garin bayan gushewar mulkin Maguzanci, ana kiransa da suna Mallam Nisau.
Shaharar Mallam Nisau ta sanya har daga wurare ake zuwa ɗaukar darasu wurinsa. Don haka mutane kan ce 'Na tafi Fan Nisau'. Har daga bisani ake kiran garin baki ɗaya da suna Fanisau.
Garin Fanisau na cike da Mayaƙa waɗanda suka taka matuƙar rawar gani wajen kare martabar Kano. Shiyasa ake ganin akwai kyakkyawar alaƙa mai tsawo tsakanin mazauna Fanisau da kuma mutanen birnin Kano, saboda tun tale-tale, duk yaƙin da Kano zata buga sai ta tafi da mayaƙan Fanisau.
Amma sai a zamanin mulkin Fulani aka soma yunƙurin ginawa garin babban Masallaci tare da gidan Sarki. Kuma ana ganin koda sheik Abdullahi Gwandu, ƙani ga Mujaddadi Usmanu ɗan Fodio yazo kano, sai daya riski Fanisau.
An sanar mana cewa Sarki Ibrahim Dabo ne ya soma wannan aiki na gina masallaci, sai kuma babban ɗansa daya gajeshi watau Sarki Usmanu ya Kammala.
Daga nan kuma aka soma yin hawan Fanisau, inda Sarki ke ware rana dashi da tawagarsa su tafi Fanisau, ya zauna a gidansa tsawon yini ɗaya sannan ya komo birni, al'adar da har zuwa yau ba'a daina yinta ba.
Akwai labarun fitattun mayaƙa da yawa da aka taɓa samu a garin Fanisau, misalin su Samagi, Sha'aike, Ɗan Toro, Bashar, da wani mai suna Sa'adu Kuzo ku duka..
Sa'adu kuzo ku duka shine wanda akace a zamaninsa saboda tsabar jarumtaka, duk yawan dakaru zai afka musu har kuma yayi galaba akansu. Don haka jama'a ke matuƙar tsoronsa har takai ko Dagacin garin baya iya shigewa ta gabansa face ya cire takalmi.
Sannan ance ko ɓarawo aka kamo daga wani gari za'a kai shi Kano don yin hukunci, sai an kawo ɓarawon gabansa ya buge shi sannan ayi gaba..

No comments:

Post a Comment