Friday, December 7, 2018

MAGANA TA KARE







MAGANA TA KARE: CIWO NE YA DAME KA A BAYAN CINYA?
Aikin gungun tsokoki a kowacce gaɓa na kishiyantar juna ne. A yayin da gungun tsokokin da ke gaban cinya suke aikin miƙar da gwiwa, su kuwa na baya suna aikin laƙwashe gwiwa ne.
Saboda waɗanna gungun tsokoki suna aiki ne a kishiyance, a yayin da gungun tsokokin gaba sukai rauni (ƙarfinsu ya ragu) sai su kuma na baya su ɗaure. Idan tsoka ta ɗaure kuma wannan zai sai tsayin tsokar ya ragu.
Abin da ke biyo bayan ɗaurewar shi ne ciwo a gungun tsokokin, musamman a lokacin tafiya, gudu ko kuma yayin da aka durƙusa daga tsaye, misali, lokacin yin ruku'i yayin sallah.
Za ka iya ganewa ko kana fama da ɗaurewar gungun tsokokin ta hanyar kwatanta yanayin da aka nuna a kwance a hotunan ƙasa. A yayin da kayi hakan kuma ka fuskanci ciwo a tsokokin kafin ƙafar ta miƙe sosai, to akwai wannan matsala.
Da zarar ka fara jin wannan ciwo, tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin warware wannan matsala cikin sauƙi.
#HamstringTightness
#Reciprocal #Inhibition
#SportInjuries
Copied from Physio Hausa
Posted by Adam Mohd Adam

No comments:

Post a Comment