ANNABI NUHU
Sa'ad Da madaukakin sarki Allah ya aiko annabi Nuhu duniya ba ga dukan
kabila na duniya ya aiko shi ba. Ya aiko shi ne ga mutanen da ya fito a
cikinsu. ALLAH ya hore shi ya zo ya qira su ga bin Allah ya gaya musu abubawa
marasa kyau, ya hore su da bari, ya gaya musu masu kyau, ya hore su da
aikatawa, aka haife shi kamar yadda ake haihuwar kowane d'a, ya girma, kana aka
nufe shi da kawo saqo. ya zo ya yi qira a jama'arsa subi ALLAH su aikata abin
da ya umarce su da aikatawa su guji abinda ya hore su da gujewa. Amma ina, sai akad'an
daga cikin mutanen nasa suka bi maganarsa. ya yi ta qoqarin bayyana musu
masifar da za ta fad'a musu in sun sa6i saqon Allah, da nasihar da za ta same
su in sun bi. Amma ina? da yawa ba su kar6a qiran ba.
Da Annabi Nuhu ya yi, yay, ya ga dai abin ya faskara har Ubangiji Allah ya
bayyana masa babu sauran wanda zai ba da gaskiya gare shi daga cikin mutanensa.
sai ya roqi Ubangiji Allah da ya hori da jama'ar nan tasa da azaba Ubangiji ya
kar6i roqonsa, zancigaba ubangiji ya kar6i rokonsa ya sanar da shi cewa zai
cika qasa da ruwa yadda duk jama'ar za ta nitse ciki. ubangiji ya umarce shi,
shi Annabin da ya sassaqa jirgi, wanda zai shiga shi da wadanda suka ba da
gaskiya da shi. Annabi Nuhu ya shiga sassaqar jirgi. mutanen da ba su ba da
gaskiya da shi ba, da suka ji dalilin sassaqa jirgin, sai suka riqa zawa suna
yi masa dariya. suna cewa, Annabci ya qiya ne kuma aka koma sassaqa?"
Allahu Akbar ! yana gama sassaqa jirgi wa'adin Allah ya cika sai kawai aka ga
sama da qasa duk sun kece da kawo ruwa. Tun jama'a na gudu daga wannan tudu su
hau wannan har abin ya buwayi tudu. Ruwa ya shafe qasa, ya shafe tudu, bai rage
kan wani abu ba a waje. A sa'an nan sai Annabi Nuhu kawai, amincin Allah ya
tabbata a gare shi, shi kadai ke yawo cikin jirginsa, shi da wadanda suka bada
gaskiya a gare shi, da dabbobi, da dai duk wadanda Ubangiji ya nufe shi da
dauka. amma kafirai duk sun halaka ! Da suka qare Allah ya umarci sama da qasa
da daina ruwa Wannan shiNE.
ALLAH YA SAKA
ReplyDeleteAllahu akbar
ReplyDeleteMungode sosai fa Allah ya qara basira
ReplyDelete