(Tsakure daga Muk'alar Nazarin Tarihin Hausa)
Sadiq Tukur Gwarzo
Hakika, sanin inda kalmar hausa ta samo asali abin bukata ne a garemu, duba da yadda muke da kauna gami da soyuwar son jin tarihi mafi gaskiya na wannan harshe namu.
Idan wasu sunce asalin kalmar 'Bahaushe' wadda ake lakabawa wanda duk ya fito daga masu yara harshen Hausa, ta zone daga kalmar 'Baushe', ma'anarta kuma mafarauci, to sai muce ita kalmar hausa kuma daga ina ta samo tushiya?
Kalmar Hausa ance bakuwa ce, wai daga baya tazo. Ance ma masanin tarihi Leo Africanus ya tabbatar da cewa a zuwansa Katsina da Kano a karni na sha biyar, baiji ana faɗin sunan hausa ba, kuma da yaren gobiranci yaji ana magana.
Haka kuma manazartan littafin nan mai ɗauke da tarihin kano mai suna 'Kano chronicle' sun tabbatar da cewa tun daga zamanin Bagauda har zuwa kan Abdullahi Burja, ba'a amfani da kalmar hausa. Sai a wuraren karni na sha biyar, lokacin ɗansa Yakubu aka soma jinta
Tabbas, hakan na iya zama gaskiya, sai dai akwai-ja a maganar yaren gobiranci da akace Leo Africanus ya tarar ana yarawa a kadar hausa.
Domin masu bada tarihin Gobirawa sunce asali daga misira suke, yaki ya korosu, suka rinka sauka da tashi a wurare mabanbanta, sai a karni na sha biyar suka riski birnin Lalle da Gwararramu. Kunga kenan a wancan lokacin (karni na shabiyar) basu iso inda kasar hausa take ba a yanzu.
Sannan kuma a wancan lokacin, wasu littattafai sun bada tabbacin wanzuwar wasu kabilu a wannan yanki namu. Misali, kabilun Maguzawa, Katukawa, Gazargawa, Tokarawa, Damarguzawa da sauransu.
Hakan na iya nufin Kabilar hausa mai yara yaren hausa itama ta wanzu amma dai bada Hausa ake kiranta ba, kuma sai daga bisani ta bunkasa tare da haɗiye ɗaukacin kabilun dake makwabtaka da ita.
Amma dai ga binda wasu masana suka faɗa dangane da asalin kalmar hausa:-
- Mr C.R Niven (1971) cewa yayi: Hausa daga buzaye ta fito, domin sunan da ake kiran mutanen dake zaune a arewacin kogin kwara kenan.
- Farfesa Skinner (1968) cewa yayi :Hausa daga kalmar Aussa ne na mutanen songhai wadda ke nufin Arewa. Kuma yace akwai daɗaɗɗiyar alaka tsakaninsu ta yadda har hausawa sun aro kalmomi a wurinsu. A cewarsa ma kalmomin Bene da Soro duk nasu ne.
Marigayi Mal Aminu kano cewa yayi hausa daga Kalmar Habsha ne. Domin shi yana ɗaya daga masu cewa asalin hausawa mutanen habasha ne tun lokacin daya riski habashan yagano akwai kamance-ceniyar
Sarkin Ningi Marigayi Alhaji Haruna cewa yayi an samo kalmar Hausa ne daga labarin Bayajidda sa'ar daya kashe macijiya shine sai tsohuwa Ayyana ta rinka ceea 'ai wani mutum ne ya kasheta wanda ya HAU-SA' maimakon tace yahau doki...
Shin menene Ra'ayinku game da Asalin Kalmar ta Hausa???
No comments:
Post a Comment