Saturday, December 8, 2018

SHANYEWAR TSINTSIYAR HANNU (Physio Hausa)

SHANYEWAR TSINTSIYAR HANNU
Shanyewar tsintsiyar hannu da ake cewa "wrist drop" a turance matsala ce da ke faruwa sakamakon raunata jijiyar laka ta "radial nerve" da take aiki a kan tsokokin da ke da alhakin ɗago tafin hannu sama.
Yayin da jijiyar lakar ta samu rauni tsokokin ba za su iya gudanar da aikinsu na ɗaga tsintsiyar ko tafin hannun sama ba yayin da tafin hannun yake a kife yana kallon ƙasa.
Abubuwan da suke haddasa raunin jijiyar sun haɗa da:
1] Rauni sakamakon sara, suka ko yanka a wuya ko dantsen hannu.
2] Kuskurewar allura a dantse.
3] Shaƙewar jijiyar sakamakon ɗaurin karaya fiye da ƙima.
4] Raunata tushen jijiyar daga wuya sakamakon haɗarin abun hawa ko biyo bayan tangarɗar fitowar kan jariri yayin haihuwa.
5] Haka nan masu larurar shanyewar ɓarin jiki kan samu wannan matsalar sai dai a wannan yanayin ba jijiyar ce ke samun matsala ba face matsala daga ƙwaƙwalwa.
Wannan matsala ka iya naƙasa hannu musamman idan ba a ɗauki matakin ganin likitan Fisiyo a kan lokaci ba.
Tuntuɓi likitan Fisiyo a yau domin shawo kan matsalar.
#WristDrop
#RadialNervePalsy
#BrachialPlexusInjuries
#ObstetricErbPalsy


1 comment: