Annbi musa, amincin Allah ya tabbata a gare shi, yana cikin qabilar bani isra'ila ne. A masar aka haife shi, a zamanin wani fir'auna da ake qira Alwalidu ibn musab-ibnal-ray
Ana nan haka, sai wata mace, a cikin yahudawa watau matar imrana ta haifi d'a, aka sa masa suna Musa.shine kuma annabi musa da zamu baku labarinsa a yanzu. Da uwarsa ta haife shi, sai tsoro ya cika ta, ga shi ya fito namiji. ba mace ba, watau fir'una zai sa ke nan a zo a kama shi a yanka, kamar yadda ake yanka sauran "ya "yansu maza. tana cikin wannan zulumi, mai baqanta rai sai madaukakin sarki Allah ya aiko mata da ilhami aka ce mata ta sami akwati, ta saka jinjirin a ciki ta rufe, ta dauka ta je ta jefa shi cikin kogin nilu.
shi ke nan sai ta zabura ta bi umarnin mahaliccinta da ta jefa shi a kogi ta dawo gida sai ruwa ya yi ta tafiya da shi, Ubangiji ya yi mata alqawarin zai mayar mata da shi, ya kuma sanya shi cikin Manzanni, bisa ga nufin Madaukakin Sarki Allah.
ya kuma sanya shi cikin manzanni, bisa ga nufin Madaukaki sarki Allah, har ruwan ya kai akwatin kusa da birnin Fir'auna, sai akwati ya sarqafe a gefen kogi. shi ke nan, wadansu jama'ar fir'auna sun zo diban ruwa sai ga akwati, suka dauka suka kai wa matar fir'auna. Daga aka fasa akwati sai ga jariri ciki, da ransa kuwa, ba matacce ba. Daga nan sai matar fir'auna ta dube shi tayi mamaki, ta ce kada a kashe shi, qila in ya girma ya zama mai amfani a gare mu, ko kuwa ma mu riqe shi kamar mu muka haife shi: Shi ke nan, Annabi Musa yayi ta girma a cikin birnin fir'auna. Mun gaya muku kuwa tun baya, irin zaman da jama'ar su Annabi Musa, wato bani isra'ila suke yi a qarqashin daular fir'auna. Hasali ma dai yahudawa alokacin sune kamar bayi na mutanen masar. Ana nan a haka, da Annabi Musa fa ya kawo qarfi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaki yahudawa, har ya cire musu wannan qangi na bauta, da qasqanci da azaba, wadanda suke samu daga fir'aunya kuma sanya shi cikin manzanni, bisa ga nufin Madaukaki sarki Allah, har ruwan ya kai akwatin kusa da birnin Fir'auna, sai akwati ya sarqafe a gefen kogi. shi ke nan, wadansu jama'ar fir'auna sun zo diban ruwa sai ga akwati, suka dauka suka kai wa matar fir'auna. Daga aka fasa akwati sai ga jariri ciki, da ransa kuwa, ba matacce ba. Daga nan sai matar fir'auna ta dube shi tayi mamaki, ta ce kada a kashe shi, qila in ya girma ya zama mai amfani a gare mu, ko kuwa ma mu riqe shi kamar mu muka haife shi: Shi ke nan, Annabi Musa yayi ta girma a cikin birnin fir'auna. Mun gaya muku kuwa tun baya, irin zaman da jama'ar su Annabi Musa, wato bani isra'ila suke yi a qarqashin daular fir'auna. Hasali ma dai yahudawa alokacin sune kamar bayi na mutanen masar. Ana nan a haka, da Annabi Musa fa ya kawo qarfi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaki yahudawa, har ya cire musu wannan qangi na bauta, da qasqanci da azaba, wadanda suke samu daga fir'auna.
wannan tausayi na Annabi Musa zuwa ga jama'arsu ta bani Israil
ANNABI MUSA
ya keta jama'a ya samo musu ya shayar da dabbobinsu suka ta fi.
shi kuwa ya koma gindin wata itaciya ya zauna yana cewa, ya ubangiji, ni mabuqaci ne ga abin da ka sauqar mini daga alherinka, to da "yammatan nan suka koma gida sai ubansu ya tambaye su, yau lafiya kuka komo da wuri haka? sai suka ba shi labarin taimakon da wani mutum baqo yayi musu. sai tsohon ya aiki daya daga cikinsu ya ce ta je ta qira masa baqon nan don ya saka masa. Da shi Annabi Musa ya zo masa, ya tambaye shi daga inda yake, da ya ba shi labari, sai dan tsohon nan ya ce kada kaji tsoro ka ku6uta daga mutane azzalumai!
A nan tsohon nan yace masa ina so in aurar maka daya daga cikin "ya"yan nan nawa biyu. sadaki kuwa ka zauna tare dani kana yi mini hidima, shekara takwas. in ko ka cika suka kai goma, wannan ganinka ne ni ba na nufin tsananta a gare ka. za ka same ni cikin bayin Allah masu salaha, in sha Allahu!
Annabi Musa ya karbi wannan aure, bisa wannan sadaki yace Allah shine shaida ga abinda muke fad'a;
Aka yi aure.
Jazakumullahu khairan
ReplyDeleteJazakumullahu
ReplyDelete