ME
YE ABIN YI BAYAN TARGADE?
Targaɗe na daga cikin raunikan da ke ci wa mutane tuwo a ƙwarya, musamman
matasa 'yan wasannin ƙwallo, da sauran wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Har
da ma tsofi ko waɗanda shekarunsu suka miƙa da ke da ƙarin haɗarin faɗuwa.
Targaɗe rauni ne ga tantani ko tantanai da ke riƙe da ƙashi da ƙashi a gaɓa.
Wannan rauni kan kasance sakamakon faɗuwa, tintiɓe, tsalle, bugu, murɗewar ko
ɗamewar gaɓa fiye da ƙima, da sauransu. Haka nan targaɗe yana faruwa ne a kan
gaɓa kawai.
Matakan targaɗe: An kasa matakin targaɗe zuwa matakai uku kamar haka:
1] Matakin farko: Tantanin zai sami rauni saboda ɗamewa.
2] Mataki na biyu: Tantanin zai sami rauni saboda 'yar yagewa ko tsagewa.
3] Mataki na uku: Tantanin zai tsinke ne gaɓa daya.
Alamun targaɗe sun haɗa da faruwar waɗannan abubuwa a gaɓar:
No comments:
Post a Comment