Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
Ance Sarki sibana wani shahararren sarki ne kuma qasaitacce daga cikin rukunin sarakunan da suka mulki Birnin Andaluz, dadaddiyar masarautar da a wani zamani can daya gabata mulkinta ya kusan game ko ina a sassan duniya.
Shidai wannan sarki, tarihi ya nuna asalinsa baiyi gadon sarauta ba, ba kuma wani Kakkarfan jarumi bane, wannan ne babban abin mamaki alokacin jahiliyya har ace wani wanda bai hada wadancan biyun ba ya zamo sarki, alhali lokacin rayuwa ce kwatankwacin ta dabbobi, mai qarfi shine a sama, sarauta da shugabanci ko wanne iri ne gida ko ace zuriya yake bi, wato idan akace wane shine shugaba kaza, tofa shekaru aru-aru masu zuwa zaka samu cewar zuriyarsa ce ke riqe wannan kambun.
Sibana dai kafin zamowarsa Sarki, ance masani ne amma fa matalauci naqin qarawa tun alokacin da sani bai wadata ba kuma arziki bai zamo ruwan dare ba, masanin dalasumai ne; wasu kalmomi da ake ta'allaqa su da wasu halittu wadanda ido baya iya gani, masanin hukunci ne, mai kamanta adalci ne, kuma gwanin tsara magana ne. Sannan kuma an haqqaqe cewar yana cikin sahun wasu mutane da akewa kallon gida-dawa a wancan lokacin, wadanda suke neman buqatunsu a wurin Allah. Idan zasuyi alqawari, bada shaida ko tawassali don samun wata buqata, sunayi ne da Allah wanda sukayi imanin al'arshinsa yana sama, duk da cewa a lokacin akwai qarancin ilimin wanene Allah.
Wata rana sibana yayi mafarki ana masa magana da wata sassanyar murya, ana cewa "ya kai wannan mutum, haqiqa Allah yayi maka baiwar ilimi da hikima, abinda tsiraru acikin bayinsa ne suke dashi. Allah ya fifita taka fiye da yawa-yawan mutanen wannan alqarya. Don haka lokaci ya gabato wanda Allah zai daukaka ka da ilimin ka, ba bisa ga abinda kayi gado ba, ba kuma bisa ga wata bajinta da kayiwa al'umma ba, sannan zai qasqantar da jahilai bisa ga abinda suka dade suna aikatawa na munanci ga Allah.
Ya kai wannan mutum, kayi shiga irin ta qasqantattun mutane kanufi Fada gobe, kasanar da sarki cewar zaka bashi amsar tambayar sa, zaka sanar dashi aikin da Allah yake aiwatarwa da hannunsa tare da qwararan hujjoji matsawar ya yarda da sharadin zai baka kayansa na sarauta, zai sanya naka, zaka hau kan karagarsa kuma dole kowa yayi maka biyayya sannan zaka fadi amsar.
Ya kai wannan mutum, kayi sani cewa daga nan mulki ya dawo gareka. Ka sanar da mutane hukuncin Allah da ikonsa wajen daukaka qasqantacce da qasqantar da daukakakke yafi ga haka, kayi mulki kuma da gaskiya da adalci. Haqiqa zaka dauwama acikib mulki, zaka samu duk cikar burikanka matsawar baka fara gaggawar yanke hukunci acikin lamurorin kaba, sannan matsawar fushi bai zamo yana tunkudaka aikata munanan aiyuka ba.." Yana zuwa nan ne ya farga afujajan.
Farkawar sa keda wuya ya samu kansa yana maimaita maganganun da aka sanar dashi. Babu abinda ya mance kai kace gar-da-gar aka sanar dashi wadannan zantuka. Tunani ya mamaye shi, ya rasa abinyi. Anan ne ma yake fahimtar ashe gari ya waye, rana ta take.
Yana cikin wannan hali ne kuma ya jiyo San kira yana shela a gari yana cewa "yaku mutanen wannan alqarya, Sarki Alkandaruz yana sanya muku albarka, yace asanar daku, bai daukewa kowa ba halartar taron daurin aurensa gobe a fada da gimbiya Sulbaniya ba, sannan yace asanar daku ya tanaji babban muqami da tarin dukiya ga duk wanda yazo masa da amsar da daddiyar tambayarsa gagara amso. Abinda kawai akeso shine, kafadi aikin da Allah yake aikatawa da hannunsa, ka kuma kawo hujjoji qwarara tare da inda ka same su."
Wannan abu ya qara dagawa sibana hankali, wato dai lamarin mafarkin sa akwai wani sirri acikinsa. Sai dai abin da ke bashi tsoro shine tayaya zai iya gaskata mafarkin? Idan dai sibana bai manta ba, a shekarar data gabata, sarki ya hallaka kimanin mutane talatin wadanda suka zo da zummar amsa wannan hatsabibiyar tambaya tashi. Daman shardin tambayar kenan, duk wanda baiciba, ajalinsa yazo kenan. Idan mutum yazo da amsa, sarki zai amsa, sai kuma yace kawo hujjoji da kuma inda kasamo wannan amsa. Tofa ana ake yinta. Saboda mafiyawan mutane shaci fadi kurum sukeyi, tunda alokacin kan mutane bai waye da ilimin saukakkun littattafai ba, Allah dinma da yawa wai-wai dinsa kurum akeji.
( #Sadiq Tukur Gwarzo)
A zahiri, Sibana baiyi niyyar tunkarar Sarki Andaruz da wannan kasada ba. Sarki Andaruz fa jarumin gaske ne, yana da girman jiki, da kwarjini, gashi da qarfin fada aji. Sarakuna ma shakkar sa yake ji, don haka duk abinda yake so ko basa so, ala tilas akeyi masa. Amma kasancewar tunanika da qunci sun yiwa Sibana yawa, sai ya tsinci kansa yana mai cire son rayuwar duniya a ransa, yayi niyyar magance quncin dake ransa ta hanyar kai kansa ga halaka, wataqila zai samu sukuni idan aka hallakashi. Mafitar daya daukarwa kansa itace, zaibi umarnin da aka bashi a mafarki, in yaso sarki ya kashe shi ya huta da zullumi gami da quncin rayuwar daya ke fama dashi.
Kamar yadda aka buqata kuwa, fadar Sarki Alkandaruz tayi cikar kwari. Daman qasaitacciyar fada ce mai cike da gine-gine dogaye. Sarki yana can saman wata husumiya akan karagarsa. A qasan sa kuma manyan waziransa ne da wasu sarakuna wadanda aka gayyato domin shaida daurin auren Sarki da Gimbiya. Kasancewar Sarki yana matuqar qaunar gimbiya sulbaniya yasanya shi cikin annushuwa a wannan rana da zai aureta. Dariya kawai yakeyi, kyauta yakeyiwa bayi sai kace ruwan sama, gashi can akaraga yasha fararen tufafi masu tsada masu dauke da ado na jan jauhari da lu'u-lu'u.
(#Sadiq Tukur Gwarzo)
Kamar yadda aka tsara, za'ayi shela ne har sau uku. Idan an samu wanda yazo ya baiwa sarki amsar tambayarsa, to sai a gabatar dashi a gaban sarki. Idan kuwa ba'a samu ba, shikenan sai a daura auren sarki da gimbiya daga nan kuma ashiga sahun shagulgulan biki. Don haka mai shela ya fara shela. Yayi kira da murya kakkarfa, yayi kirari ga sarki, ya yabi gimbiya, sannan ya nemi duk wanda yazo da amsar tambaya ya matso, yana mai koda kyaututtukan da sarki yayiwa duk wanda ya dace tanaji.. Sarki zai baka babban wazirinsa, zai baka damar tattara harajin duk masarautun dake qarqashin ikon sa, zai aura masa aure da mata dari, zai bashi katafaren gida.. Dadai sauransu.
Mai shela ya qara yin shela akaro na biyu, amma wurin nan tsit kakeji. Talakawa duk sun shiga taitayinsu, kunsan ance wargi wuri yaka samu. Qwaqqwaran motsi ma bakaji, kai kace cewa akayi duk wanda ya motsa abakacin rayuwarsa ne. A karo na uku ma mai shela ya qara yin shela wanda bai rufe baki ba sai ga Sibana kwaram-kwaram yana sanye da tufafi yagaggu, ga kayan hauka nan rakwacan sanye ajikin sa. Ya nufi husumiyar Sarki kai tsaye, kwachachaf-kwac
Dakarun sarki sukayi kansa asukwane saboda ko ina sune dauke da takubba gayawa jini na wuce, wasu kuma riqe da kibau, harda masu majaujawa. Suka sha gabansa, babban su ya daka masa tsawa yace kai mahaukaci, a fadar Sarkin sarakuna kake ka natsu. Sibana ya daga kansa yana mai dubansa ba tare da tsoro a tare dashi ba yace "Ni ba mahaukaci bane, kuma amsa nazo nabaiwa sarki. Kayi sani cewa Karshen tababa da zubda jinin jahilai yazo, kuma lokacin da gaskiya zatayi halinta ya tabbata. Don haka ka sanar da Sarki cewa duk abinda yakeso ya sani lokacin sa yazo, zan bashi amsa ba kuma naneman abiya da da wata kyauta amma fa sai idan har zai iya cika sharuddai na guda uku dazan ambata".
Sarki ya qyaqyace da dariya, ya buga qafa qasa cikin annushuwa da qeta da yaji abinda wannan mahaukaci yazo dashi. Yace "ku matso dashi gabana, yazo ya fadi wadannan sharudda, mu kuma munyi alqawarin zamu cika su. Amma fa idan har ya kasa bada amsa, to da sannu zansa ayi gunduwa-gunduwa
(#Sadiq Tukur Gwarzo)
Ko kadan Sarki bai dauki wadannan sharudda abisa wasu abubuwa masu sharadi ba, don haka nan take ya amince. Abinda yake hangowa kawai shine zai taya bera bari ne, wato zai qure qaryar wannan mahaukaci inyaso sai ya gallaza maza da azaba mafi muni, tayadda al'ummarsa zata qara jin tsoronsa. Da yake kuma Sarki ne wanda yake sa gabansa aduk inda yakeso, sai ya kasance babu daga cikin wazirinsa wanda yace maza kanzil akan cika wadannan sharudda.
Sibana ya zauna akan karagar sarki. A halin yanzu shine Sarki, domin kuwa duk dakarun sarki umarninsa suke jira ba umarnin Sarki Ankaldaruz ba. Sibana ya dubi taron jama'a yace "yaku jama'ar Andaluz dame nayi kama yanzu??? Mutane suka dauka gaba daya da cewa "da sarkiiiii". Ya qara cewa "wannan fa damai yayi kama?" Yana mai nuni da sarki Alkandaruz? Mutane suka qara cewa "da mahaukaci". Sai ya kalli Sarki Alkandaruz yace " wannan shine aikin da Allah mai iko ya aiwatar da hannunsa yanzu-yanzu. Sarki ya zamo mahaukaci, mahaukaci ya zamo Sabon Sarki." (#Sadiq Tukur Gwarzo)
Sarki Alkandaruz yayi tsaki, ransa ya baci saboda abin kamar yazo masa da qasqanci. Sannan ya dubi Sibana yace "to yi sauri ka cire kayannan ka dawo nan, wadannan kayan sun. Isheni da tsami. Sannan kuma idan ka kasa bani hujjar maganar ka da inda ka samo amsar na rantse sai na lahira ya fika jin dadi". Da fadin haka sai yayi kan karagar da nufin ya hankade sibana da qarfin tsiya. Ai kuwa nan take sibana ya dakawa dakaru tsawa, yace ku kama shi kuyi maza ku kai mini shi kurkuku. Ai duk wanda yake son zurfafa bincike acikin lamarin Allah hauka da qasqanci ne makomar sa" Aikuwa ala dole, suka amshi umarnin sabon sarki, tsohon sarki tun yana ashariya, har ya dawo yana magiya, amma ina, bakin alqalami ya bushe. Anan take ya fara fahimtar kuskurensa. (#Sadiq Tukur Gwarzo)
Sabon Sarki yayi jawabi mai ratsa jiki ga al'umma, yayi musu nasiha da gaskiya, adalci gami da zama lafiya. Daga nan kuma aka dauka aurensu da gimbiya Sulbaniya..
Wannan shine matashiyar wannan labari..
Darussan dake shirin GASKIYA DACI GARETA na wannan lokaci sune;
*Ya kamata mutane mu qara jin tsoron Allah, haqiqa ikon da Allah yake dashi yafi gaban a misalta.
* Hakika Allah shine mai yadda yaso, kuma ina aywatar da ikon sa cikin hikima a kowanne lokaci.
* duk baiwar da Allah yayi maka, kada kayi izgila. Kada kabari karfin iko ya yaudare ka har ka shiga hurumin Allah Ta'ala, domin haqiqa Allah bazai kyale ba.
* Duk kuncin da kake ciki, ka miqa lamuranka ga Allah Ta'ala. Idan lokacin da hukuncinsa yayi, babu makawa sai ya auku.
* ya 'yanuwa, haqiqa muna zaluntar kawunanmu a wannan zamani ya yadda muke qasqanta darajar ilimi da ma'abota ilimi, muke kuma ganin dukiya da muqami sune qololuwa a rayuwa. To dai dayake ance Gaskiya daci gareta, ya kamata mu sanar da kanmu cewa wannan tunani na halaka ne. Ya kamata mu sanar da kawunan mu gaskiya tun kafin wani ya sanart mana.. Shi Ilimi ai yafi dukiya, Manyan malamai duk sun sanar da haka, don haka shi yafi buqatuwa mu nema sama da duk wata daukaka ko matsayi.
Ku tuna dai, wani masani yana cewa a waqe "Duk daukakar da ba'a sameta ta hanyar ilimi ba, qarshenta qasqanci ne. Idan shugaba ya zamo mai ilimi, ilimin na zamar masa riga qasaitatta da kuma fitila mai jagoranci."
Zamuci gaba da yardar Allah.
LABARIN SARKI SIBANA DA GIMBIYARSA SULBANIYA
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
Da yake Allah shine mai yadda yaso a lokacin da yaso, a dare daya Sibana ya zamo sarki mai cikakken iko kuma qasaitacce. Shikuma azzalumin sarki ya zamo mazaunin gidan Jarun. Abinka da mai Ilimi, sarautar Sarki Sibana sai ta sauya. Ya kawo tsare-tsare masu kyau na adalci, ya haramta cin hanci da almundahna, ya kuma yi umarni da rage dumbin harajin da talakawa ke biya don sauqaqewa gare su. Wannan yasa nan da nan ya samu farin jini. Lungu da saqo sai waqoqi ake raira masa na yabo, gami da zambo ga tsohon sarki.
A daren farko da Sarki sibana ya shiga dakin amarya gimbiya subaniya, sai yake ganin abubuwan kamar a mafarki. Shi kansa yana mamakin wannan juyi da Allah yayi masa. Dakin nata an qawata shi da ado na alatu, ga fitilu masu kyawun gaske reras. Kamshi kuwa sai tashi yake yi, ga sautin wasu yammata kuyangi masu rera waqoqi yana tashi kadan-kadan, yabonsa kurum sukeyi tare da amaryasa, nan fa wani farin ciki ya qara cika masa zuciya, tuni ya fara mancewa da wahalar duniya, domin a yanzu jinsa yakeyi kamar tunda aka halicce shi shine Sarkin duniya.
Duk inda yasanya kafarsa, laushi yakeji kamar zai nutse. Ya hangota zaune bisa wata darduma, tana sanye da jajayen kaya masu ado da zinare, walwali da sheqi kawai takeyi.
Gimbiya Sulbaniya ta yaye mayafin daya rufe mata fuska, gami da dago kanta sama kadan. Ta dubi Sarki sibana, shima ya kalle ta, sannan ta duqar da kanta qasa tana mai cewa " Marhaban dakai Sarki daya tamkar da dubu,
sarkin da adalcinsa zai game duniya, sunan sa zai ratsa samaniya,
izzar sa zata wanzu har qarshen duniya,
An halicce ni don zamowa baiwa a gareka.
Maraba dakai haske maganin duhu.
Ina da buqata a gurin ka ya kai jarumin maza.."
( #SadiqTukurGwarz
Sarki sibana ya zura mata ido. Ganinta yake kamar aljana. Kyawun ta ya wuce a misalta, kallon kwayar idanunta kadai ya isa ya mantar da mutum wahalhalun duniya. Haka ma kallon daukacin fuskar tata . Kalmominta sun dauke shi daga wannan duniyar. A halin yanzu jinsa yake kamar anyi masa hisabi yana cikin aljanna. Sarki sibana ya nisa daga yanayin da yake ciki, dakyar ya samu kansa. Sannan yace "nayi miki alqari kome kike nema agurina zan miki matuqar ina iyawa"
Daga nan gimbiya sulbaniya ta fara bashi labarin ta kamar haka. "Ya kai wannan sarki mafi karimci daga sarakunan duniya, kayi sani cewa Sunana sulbaniya, mahaifina sarki Rama shike sarautar masarautar Ramayana dake kasar hindu. Ya kasance yana da fada aji, da karfin mulki. A yanzu haka ma, mutanen kasarmu na ganinsa kamar wani mahalicci, tunda har bauta masa akeyi. A lokacin da mahaifiyata ta dauki cikina, sai aka nemeta aka rasa. Nan fa hankalin mahaifina ya tashi. Da yake shima masanin tsafi ne, sai ya dugunzuma a cikin tsatuben sa, har saida ya gano inda take.
Ashe wani hatsabibin boka ne mai suna sundusur ya dauketa izuwa wani tsibiri mai suna Laaka, waje ne da ake kallo a matsayin mafi hatsari a duniya. Dalilinsa nayin hakan kuwa shine, yayi bincike a fagen tsafinsa sai yaga cewa za'a haifeni, zan kuma zamo mace kyakkyawa mai annuri, sannan kuma wani sirri zai kasance dani cewa dukkakan wanda ya aure ni, matuqar yana faranta min rai, babu wani abu dazai tunkara ba tare da yayi galaba akansa ba. Ya fahimci tauraruwa ta kakkarfa ce, hadimai na kuma suna da matuqar tasiri anan duniya.
Wannan lamari ya tayar da hankalin mahaifina matuqa gaya. Har ya rasa sukuni. Duniya tayi masa kunchi. Ya rasa menene mafita. Ana haka sai ya tara hakimansa da sarakunan yaqinsa, ya nemi shawararsu abisa zuwa tsibirin laakha domin dauko matarsa. A haqiqa, kasancewar kowannen su yasan hatsarin dake kunshe cikin wannan tafiya, babu wanda ya goyi bayan sa. Har mutane na ganin bai kamata ace akan rai guda daya tilo ba ayi asarar rayuka marasa adadi.
Daga nanfa kunchi ya qara tasarwa mahaifina. Kullum cikin hawaye yake da bege, kawai sai wata basira ta fado masa. Yace aransa, tunda ina da karfi a tasirin tsafi, kuma ta hanyar tsafi aka sace matata, to kuwa tilas nabi ta hanyar siddabaru na kwato ta, koda kuwa hakan zaisa nayi asarar rayuwa tane ma baki daya. Daga nan ya kira wazirinsa ya mallaka masa jiran gari, sannan ya nufi daji abinsa.
(#SadiqTukurGwa
Koda isar sa kungurmin daji, sai ya sami kan wani dutse ya hau, ya zauna yana mai harde kafafuwansa, ya janyo wani kuben tsafi qarami irin na yaqi, ya fara busawa. Ai kuwa nan take dabbobin daji suka fara amsa kira. A wannan lokaci, namun daji kala-kala sun samu halarta, birai da karnukan dawa sune manya 'yan gaba dai-gaba dai. Bayan runduna ta hadu, kawai sai ya nausa cikin daji yayin da sukuma dabbobi suke biye dashi. Duk inda suka ratsa sai dai kaga bishiyoyi na zubewa aqas, qura na turnuqewa sama, iska kuma qaqqarfa na kadawa. A haka har suka isa wawakeken ramin da za'a tsallake a isa tsibirin Laakha.
Shi daman wannan tsibiri, ana kallon cewa babu mutum ko dabba dake rayuwa acikin sa, sai dai gagarumai kuma hatsabiban maridan aljannu. Don haka ne Boka sundusur ya zabi ya gina gidansa anan, saboda yasan babu mai iya kai masa chaffa. Dadin dadawa, tsibirin yana kewaye ne da wani wawakeken rami, babu wanda yasan zurfin sa, kuma wuta ce ke fitowa daga qasan sa izuwa sama. Saboda haka ya zamo cewar koda tsuntsaye basa kai kawo a saman ramin, domin babu zato wutar ke fitowa, duk kuwa abinda ta samu ko ta shafa, take zaka ganshi yayi qurmus.
Mahaifina ya zurawa wannan rami ido yana nazari akan hanyar qetare shi. Daga bisani dai sai yayi shawarar cewa gada zai hada ta tsafi wadda zata rinqa tafiya a saman ramin har taje daya gavar, kuma zata rinqa gociya da zamiya ga wannan wuta. Wannan shine kadai mafita. Nan take ya umarci dabbobi dasu karyo itatuwa.
Haka kuwa akayi, yasa aka daddatsa wasu, aka nemo ganyayen da ake igiyoyi dasu, dashi da birrai suka shiga aikin gada. Sai da suka gama tsaf, sannan suka hau kanta suna mai fuskan tar ramin. Gada ta tashi sama, ta fara tafiya sannu a hankali akan wannan rami.
Basu jima da fara tafiya ba sai ga wani katafaren tsuntsu, ashe shima aman wutar yake yi, nan take suka fara gumurzu. Tsuntsu na kwararo wuta daga sama, rami na watso tashi daga qasa, ita kuma gadar tsafi nata faman zuzzullewa. Idan ta zulle, shashin wuta ya shafi wasu daga dabbobin nan sai dai kawai aga sun kama ci da wuta, kafin a jima sun zama toka. Wannan abu yayi matuqar dagawa magaifina rai. Har saida yayi nadamar fitowar sa, sai ma da ya gamsu cewa tilas rayuwar sa zata salwanta a saman ramin nan, sannan akayi sa'a wuta ta fito ta qasa, shikuma tsuntsun nan na sama yayo qasa-qasa gami da saito gadar da nufin qone gadar baki daya qurmus, kawai sai gadar da waske, ai kuwa nan take wutar ta chafki tsuntsun. Yayi wata qara gagaruma, kafin ajima ya qone qurmus.
(#SadiqTukurGwa
Wannan yasa suka sami raguwar bala'in da suke ciki. Amma kuma saukar su kan tsibirin keda wuya wani sabon bala'in ya dawo. Domin irin wadannan tsuntsayen n sunfi dubu ke dakon su. Da hango saukar su kuwa sai suka tashi sama, suka shiga aman wuta babu qaqqautawa. Nan fa rundunar mahaifina ta tarwatse, gashi basu da wasu makamai na mayar da martani, dole dabbobi suka shiga gudun neman mafaka, wasu suka nufi qarqashin duwatsu, wasu kuma suka koma da baya kan gada.
Da dai mahaifina ya rasa abinyi, sai shima ya quduri niyyar jarraba irin nashi tsafin, amma ga mamakinsa, duk abinda ya qudurci yi sai yaqi yiwuwa, sai da dabarunsa suka qare qar-qaf, yayi gudu kamar zai halaka wajen tsira daga sharrin tsuntsayen nan, wasu dabbobin kuwa duk sun qone, sai da suka dawo 'yan qalilan. Kwatsam sai mahaifina yayi wata shawara. Yaga cewa tunda tsuntsayen nan wuta suke fesowa, to bari shima ya koma wutar, wataqila zai kubuta daga sharrin su. Ai kuwa sai kawai ya rikide izuwa curin wuta, sannan ya nufi kofar shiga fadar da gudu.
Nan fa tsuntsayen nan suka ce dawa aka gama mu ba da kai ba? Suka tashi haiqan akansa, wuta kurum suke fesowa, shi dai bai canza siffa ba a haka har ya shiga fadar boka sundusur, duk inda ya wuce sai dai kaga wuta naci ganga-ganga a fadar, suma kuma tsuntsayen suka himmatu a mayar da wuta, kafin jimawa sai ga sassan fadar yana ci da wuta.
***
Darussan mu na wannan lokaci sune:
1. Kayi imani da Allah a kowanne lokaci, kada kuma duniya ta rudeka. Allah na iya canza duniyar ka akoda yaushe.
2. Shugabanci yana da wuya. Dole sai ka rinqa bin maslahar al'umma. Kada don kana shugaba ka dora buqatar ka fiye data mabiyanka.
3. A kowanne lokaci ka fadawa kanka gaskiya. Duk lamarin da zaka shiga, ka lura da wahalhalunsa, kada ka bari dadi ko bakin ciki ya rudeka kayi abin ba tare da kasan rikicin da zai iya aukuwa ba.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
No comments:
Post a Comment