Saturday, December 8, 2018

TARIHIN ANNABI YAQUB A.S

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI YA'AQUB.
***** RAYUWAR ANNABI YA'AKUB
A.S *****
Kamar yadda bayani ya gabata
cewa, an haifi Annabi Ya'akub AS a
zamanin Annabi Ibrahim AS, kuma
an aiko shi a zamaninsa. An ce a
tsakanin wadannan ya'yaye guda
biyu na Annabi Ishak wato Isa AS
da Ya'akub AS, a dabi'a irin ta
zuciyar dan adam sai Annabi Ishak
yafi son babban dansa Isa.
Sai wata rana Annabi Ishak yacewa
Isa kaje ka farauto min nama zan yi
maka wata addu-a. Sai Annabi
Ya'akub AS yaji, sai yayi sauri yaje
ya farauto masa naman nan ya
kawo. Sai Annabi Ishak ya karba
yayi masa addu'a yana zaton Isa
ne. To tun daga nan Isa yake fakon
Ya'akub yana so ya kashe shi. Da
dai Ya'akub yaga babu dama, sai ya
bar garin ya gudu wajen kawunsa.
Laban ya zauna a can. Shi ne yayi
masa aure, ya aura masa yarsa da
ake kira Layya. Ita ce ta haifa masa
Rabilu da Sham'unu da Lawi da
Yash'habu da Zabahunu/Zaihunu.
Bayan rasuwarta, sai ya auri yar
uwarta Rahilu ita ce ta haifi Yusif
da Binyaminu, wanda rasu a
lokacin haihuwarsa. Sai kuma wasu
ya'ya hudu da wata mata daban
wadda ake kira Balha ta haifa masa
shine ya bada adadin ya'yansa
goma sha biyu (12)
Annabi ya'akub AS ya kasn ce a
cikin ya'yan nan nasa duk yafi son
Annabi Yusif AS.
yahudawa suna cewa, dukkanninsu
Annabawa ne. An ce Rabilu shi ne
babbansu a shekaru sannan
Sham'unu sai Yahuza shi kuwa duk
yafisu ra'ayi mai kyau. Domin a
lokacin da suke shawarar kashe
Annabi Yusif AS shi ne wanda ya
bada shawarar jefa shi a rijiya a
maimakon kisan, kuma Annabi
Dawud AS da Annabi Sulaiman AS
suna cikin jikokin Yahuza. Sannan
sai Lawi shi kuma Annabi Musa AS
da Annabi Harun AS jikokinsa ne.
Sai kuma Yusakkiru sai Zailun. Sai
kuma Jadiru. Sai Ushaizu sai
waddanu. Sai Nafsali sai kuma
Binyaminu da Yusuf.

1 comment:

  1. sometime it becomes very hard to find out a well written and nicely mounted lavatory which provide you correct and useful facts concerning tests and syllabus. but, i discovered this weblog and have been given a few relevant facts which is probably clearly beneficial for me. Work Injury Treatment

    ReplyDelete