TARIHIN SARAKUNAN KANO A TAƘAICE
KASHI NA ƊAYA
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
Mazaunan Kano na Farko
Marigayi Alhaji Abubakar Dokaji ya faɗa a littafinsa mai suna 'Kano ta
dabo cigari' cewar tun a ƙarni na tara waɗansu maharba da babu
takamaimen inda suka fito suka zauna akan duwatsun dake sararin da ake
kira Kano ayau, watau misalin dutsen Dala, Gwauron dutse, Magwan, da
Fanisau.
Sai dai, wasu na ganin faruwar hakan ya auku ne tun a wajajen ƙarni na bakwai
Farauta shine mafi akasarin abinda waɗannan mutane suka fiyi, amma daga bisani suka soma taɓa noma.
Sarkin Kano na ɗaya: Bagauda.
Masu haɗa tarihin Kano dana Bayajidda, sunce yawaitar rashin zama
lafiya daga mahara masu zuwa kamen bayi ne yasa mazauna kano suka rinƙa
kai ƙorafi ga sarauniyar Daura Daurama. A lokacin Sarkin Daura Bawo kuwa
sai ya turo ɗansa Bagauda Kano don yayi mulki.
Akace Bagauda yayi
zamani da wani bafaden Barbushe shugaban masu bautar tsunburbura mai
suna Jankare, kuma daya ƙi bashi goyon baya sai yasa aka kama shi aka
yanka.
Bagauda ya iske alƙaryun Gazargawa, Zadawa, Fangon, Zaura,
Dundunzuru, Shiriya, Sheme, Gande, Tokarawa, da wasunsu waɗanda ke
zazzaune a sassan ƙasar kano irinsu Wasai, Sontolo, Barkum Watari,
Jakara, Shike, karmami, Ringim da wasunsu.
Bagauda ya sauka a
Dinari ya shekara biyu, sannan ya koma Barka ya gina Talotawa, sannan ya
koma Sheme inda ya tarar da waɗansu manyan matsafa waɗanda ya mallake
su, misalin Galosami, Barmi, Gazawari, Dabgege, Fasataro da Bakin Bunu.
Ance sa'ar da Bagauda zai baro Daura ya taho ne da mutanensa irinsu Kududdufi, Buram, Isa, Baba, Akasan, Darman, da Goriba.
Sai dai, Maje Ahmad Gwangwazo ya ruwaito shigen haka a littafinsa
'Tarihin Kano kafin Jihaɗi littafi' na ɗaya, amma akwai saɓani a wasu
wuraren, musamman dalilin zuwan Bagauda daga Daura da kuma hawan
Sarautarsa.
A nashi ɓangaren, yace Bagauda ɗan Bawo tun yana yaro
yake jin labarin yadda yankin Kano ke haɓaka daga mahaifiyarsa
Sarauniya, don haka daya girma sai ya kwashi abokansa ya sulale zuwa
kano. Kuma sai daya shafe shekaru biyu yana koyon yaren Hausa, domin shi
Bamange ne. Sannan yace mutanen kano da kansu suka ga dacewar ayi masa
sarauta saboda halayensa na kirki wajen yiwa jama'a Hukunci da kuma
jarumtakarsa.
Waƙar Bagauda kuwa da Mal. Abdullahi Kabuga ya rera
mai bayar da tarihin Kano, ta nuna cewar Kafin Bagauda yazo kano, anyi
wata gagarumar yunwa a wannan yanki daya zama ƙasar Hausa ayau, don haka
mutane suka rinƙa barin garuruwansu suna tafiya neman abinci. A haka
Bagauda yazo kano ya sauka a Maɗatai, kuma ya soma taɓa noma tare da
ganin albarkarsa. Daga nan ya aika gida iyalansa, ƴanuwansa da abokansa
suka taho gare shi. Daga cikinsu akwai irinsu Shehe, Gwale,
A wata
mahangar kuma musamman wadda ta fito daga wasu Maguzawan Kano, sun faɗa
cewar Bagauda Bamaguje ne Bahaushe, wanda ya riski Kano daga yamma. Kuma
asali ya baro gida ne da ɗan Uwansa mai suna Bugau. Bagauda ya rabu da
yayansa Bugau a garin Baɗari yazo wurin wani ɗan kabilarsa mai suna
Goɗiya ya zauna, daga bisani ya wuce zuwa kano.
Bagauda dai yayi
shekaru 66 a mafi inganci yana mulkin kano, kuma a zamaninsa ance an
samu matuƙar tsaro da zaman lafiya a kano, duk da wasu na ganin har ya
mutu akwai ɓurɓushin mabiya Barbushe da basa yi masa biyayya.
Sarkin Kano na biyu: Warisi
Ance shi ɗa ne ga Bagauda, sunan Mahaifiyarsa Saju. Alhaji Ahmad Bahago
ya kawo waɗannan sunaye a matsayin manyan fadawan Warisi a littafinsa
Kano ta Dabo Tumbin Giwa: Galadima Mele, Barwa,Buram, Sarkin Gija
Koramayi, Maidalla Zakar, Makama Gargi, Jarmai Goshin wuta, Jarmai
Baƙoshi da waɗansu.
Ance ya shekara 33 kan karagar kano, a
zamaninsa aka soma naɗa sarautar gado a kano, watsu ƴaƴayen abokan
mahaifinsa suka rinƙa samun sarautar iyayensu bayan rasuwarsu kamsr
yadda ta auku gareshi. Kuma an samu zaman lafiya a mulkinsa, saidai ba
kamar zamanin Bagauda ba.
Sarkin Kano na uku: Gijimasu
Ance shi
ɗane ga Warisi, sunan mahaifiyarsa Yanusa, ya zauna a Garazawa da mulki
tsawon lokaci, sannan shine ya soma bada shawarar yiwa kano ganuwa don
kangeta daga mahara.
A zamanin nasa ne kuwa aka soma ginin
ganuwa, ya haɗa kusan kafatanin mazauna kano aka soma aikin ginin
ganuwa. Bayan an gama, sai akayi mata kofofi takwas. Ance shanu ɗari
sarki ya yankawa ma'aikata a ranar farko ta soma wannan aiki. Wasu sunce
ya kasance mai yawan kyauta don haka ya samu nasarar haɗa kan jama'ar
Kano a zamanin sa.
Akwai masu cewa ya gina fadarsa ne a Madabo, amma wasu sunce a Gwammaja yayi ta.
Sarakunan kano na huɗu: Nawata da Gawata
Ance su tagwaye ne sunyi mulki tsawon shekara ɗaya kuma a tare, idan
yau ɗaya na bisa mulki, ɗayan zai kasance a gida sai kashegari yazo
yahau karagar mulki.
Kuma tagwayen masu da ake gani har yanzu a hannun Sarkin Kano nasu ne aka haɗe wuri ɗaya tsawon lokaci.
No comments:
Post a Comment