Friday, December 21, 2018

ZUWAN TURAWA 4

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
Kashi na Huɗu
Sadiq Tukur Gwarzo
Bayan yaki ya kare, sai Turawa suka mika da tafiyarsu izuwa Sokoto.
Ragowar dakarun can kuwa da suka tsere, sai suka nufo kano da gudu don neman mafaka.
Sai dai tun kafin su iso, tuni har labari yazo ga turawan da suka rage a kano, waɗanda aka barsu a gari da zimmar su tsare garin tunda sun karɓe iko dashi.
Ai kuwa tun kafin dakarun su iso, sai turawan suka haɗa tawaga suka nufi wajen ganuwa, suka jejjeru suna sauraren su.
Bayan misalin awa guda suna jira, sai ga dakarun sun karaso. Wanda ya karɓi shugabancin tawagar shine Wamban Kano Abbas, tunda idan ba'a manta ba, da fari Sarki Alu ne ke shugabancin dakarun, amma bayan ya sulale sai Waziri Amadu ya maye gurbinsa, yanzu kuwa da waziri Amadu baya nan, shine Wambai Abbas ya zama jagora.
Turawan nan suka tsaida waɗannan dakaru, sannan suka karɓe dukkanin makaman dake jikkunan su.
Daga nan aka basu damar shiga garin kano bisa sharaɗin kowa gidansa kurum zai nufa, banda kuma yinkurin tada tarzoma.
Anyi haka a lokacin tsakiyar sanyi na wannan shekarar.
Daga nan kuma, sai Turawa bayan sun koma gida suka shiga neman shawarwari daga gurin Larabawa mazauna kano akan wanda ya kamata a naɗa sarki a kano musamman wanda ya fito daga zuriyar Abdullahi.
Sai larabawan nan sukace ai kuwa Wambai Abbas ne yafi dacewa, tunda babban su waziri Amadu ya rasu.
Sai turawa suka amsa da cewar haka nan ne.
Sai dai fa duk da haka, turawa sun shiga tambayar Manyan kano na wancan lokacin dake zaune a birni, cewar wa ya dace ayiwa sarki, sai suma ɗin kuwa suka ce abaiwa Wambai Abbas sarauta.
To kunji yadda sarki Abbas ya zama sarki na farko a kano a zamanin turawa.
Yanzu kuwa, bari mubi sawun turawa izuwa sokoto, karkashin jagorancin Bature mai kwagiri domin muji yadda ta kasance.
Koda turawa suka shiga kasar sokoto, sai suka game da wasu dakarun turawa dake zaune a wani gari mai suna Argungu, suka nufi sokoto baki ɗayansu.
A yammacin ranar wata lahadi Turawa suka isa garin sokoto, a wannan yammacin kuma yaki ya kaure a tsakanin Dakarun sarkin musulmi kuma sarkin sakkwato Attahiru da turawa.
Ance a wannan rana sai da aka shafe dare babu bacci ana gwabza yaki, ba tare da wani ya samu galaba akan ɗanuwansa ba.
Da garin Allah ya waye, sai aka sake komawa fagen fama. Aka shiga gwabzawa.
Amma a wannan karon, cikin kankanin lokaci aka soma rinjayar dakarun sakkwato da yaki, saboda salon faɗa da turawa suka sauya.
Da sakkwatawa suka ga ba dama, sai runduna ta yage..
Sarkinsu Attahiru Abdu yaja tawaga yayi gabas da gudu.
Wazirinsa mai suna Muhammadul Bhukari kuma yaja tasa tawagar yayi arewa da gudu.
Shikenan, sai turawa suka shiga cikin garin sokoto cikin salama.
Suka shiga tara mutane wuri ɗaya, sannan sukayi musu jawabi cikin girma da arziki.
Sukace "kada wanda ya tsorata, domin mu ba zamu cutar da kowa ba."
Harma sun kasance suna cewa mutane "Ku zauna a gidardajinku, yakin ya kare, a yanzu kuna cikin kariya da tsaro, don haka kada wani abu ya firgita ku "
Sai dai kuma wani abin haushi ga turawa shine, har yanzu basu kama Sarkin Kano Ali da Abokinsa Magaji ɗan Yamusa ba, don haka. Wannan karon ma, ba tare da jimawa ba sai suka sake yin shiri suka fita daga sokoto izuwa neman ababen harinsu..

No comments:

Post a Comment