Saturday, December 8, 2018

DAGA YARA SAMA (Physio Hausa)

KA SAN HAƊARIN DA KE TATTARE DA DAGA YARA DA HANNU ƊAYA?
Daga cikin raunukan da iyaye ko masu raino kan yiwa ƙananan yara ba tare da an sani ba akwai raunin nan na gwiwar hannu da ake cewa "Pulled elbow" ko kuma "Nursemaid elbow" a turancin likita.
Raunin na "Pulled elbow" 'yar ƙaramar gocewar ƙashi ce a gaɓar gwiwar hannu da tafi samun ƙananan yara 'yan ƙasa da shekaru shida. Raunin yana faruwa ne sakamakon saɓulewar ko yagewar tantanin "annular ligament" da yake riƙe da kan ƙashin "radius" a gaɓar gwiwar hannu.
Me yake kawo wannan rauni?
Sakamakon gaɓoɓin yara 'yan ƙasa da shekaru shida ba su gama yin ƙwari sosai ba, saboda haka tantanin da ke riƙe da kan ƙashin na "radius" bai gama ɗaure ƙashin yadda ya kamata ba. Wannan yasa ƙananan yara aka fi jefawa cikin haɗarin gamuwa da wannan rauni yayin ɗaukansu.
Saboda haka wannan rauni yana da alaƙa da rashin lura ko ganganci yayin ɗaukar ƙananan yara kamar:
a) Kama tsintsiyar hannun yaro da ɗagawa da hannu ɗaya yayin goyawa a baya.
b) Kama tsintsiyar hannun yaro da ɗagawa domin yi masa lilo da hannu yayin yiwa yara wasa.
c) Kama hannu ko tsintsiyar hannun yaro da ɗagawa domin ɗorawa ko saukewa daga abun-hawa, ko kuma tsallakar da su rami ko tudu.
d) Fisgo hannun yaro yayin wasanni, da dai sauransu.
Alamomin wannan rauni:
1) Yaron da ya sami irin wannan rauni kan yi ƙorafin ciwo daga gwiwar hannu zuwa tsintsiyar hannu musamman idan akai yunƙurin motsa hannun.
2) Haka nan yaro zai maƙale hannun a jikinsa, sannan ya miƙar da gwiwar hannun tare da juya tafin hannun zuwa jijkinsa.
Sai dai irin wannan rauni ba kasafai yake zuwa da kumburi a gwiwar hannun ba.
Saboda da haka ake kira ga iyaye da su guji ɗaga ko ɗaukar yara musamman 'yan ƙasa da shekaru shida da hannu ɗaya, sannan su nusar da masu rainon yaransu domin kiyaye afkuwar wannan rauni.
Garzaya da yaro asibiti da zarar an lura da yaro ya kasa amfani da hannunsa, kuma yana ƙorafin ciwo a gwiwar hannu zuwa tsintsiyar hannunsa, bayan zargin faruwar ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo raunin da aka ambata a sama.
Likitocin Fisiyo (Physiotherapists) ne ke taka muhimmiyar rawa wajen gyra ko mayar da tantanin da ya saɓule da jinyar raunin har a warke.
 Copy from Physio Hausa
facebook page
Posted: Adam M Adam Gaya


No comments:

Post a Comment