Friday, December 21, 2018

GIMBIYA HARIBAI

HIKAYAR GIMBIYA HARIBAI, ƊIYAR SARKIN DAULAR PITUGAR DAKE HINDU
SADIQ TUKUR GWARZO
A wani lokaci mai tsayi daya gabata a Hindu, anyi wani sarki a daular Pitugar mai jiji-da-kai. Sunansa Dheema.
Sarkin yana da ƴaƴaye ƴammata guda biyu, dukkansu kyawawa ne. Ɗaya ta faye yawan surutu, gata da halin ko-in-kula, sunanta Kalimbai. Ɗayar kuwa sunan ta Haribai, kuma ita mai shiru-shiru ce da natsuwa.
Da lokacin aurensu yayi, sai wani hamshaƙin attajiri ya fito neman auren babbar cikinsu watau Kalimbai, ai kuwa sarki ya bashi aurenta. Akayi gagarumin biki na ƙawa, duk gari kowa sai labari yake saboda kece raini da akayi a wannan biki.
Bayan biki ya ƙare, sai Sarki Dheema ya lura da kaɗaicin da ɗiyarsa Haribai take fama dashi tun bayan auren yayarta Kalimbai, don haka sai yakan ware lokaci yana zuwa ɗakinta suna firar duniya da ita.
Rannan sarki ya shiga ɗakin Haribai suna taɗi kamar yadda suka saba, sai idanuwansa yakai ga wani fai-fai a ɗakin mai ɗauke da rubutu kamar haka: "Duk gidan da mace mai hikima take a cikinsa, a koda yaushe zai rinƙa bunƙasa"
"Wanene ya sanar dake wannan zance?" Sarki Dheema ya faɗa yana mai nuni da rubutun dake jikin fai-fan.
"Babu wanda ya sanar dani, amma da kaina nayi imani da hakan" Haribai ta bashi amsa.
Sarki Dheema yayi murmushin yaƙe saboda yadda zuciyarsa ta sosu daga wannan magana.
Yace "kinga, ni Sarki ne, kuma kasancewata a gidan nan shine yasa komai da komai yake bunƙasa acikinsa. Don me zakice sai gida na ɗauke da mace mai hikima zai bunƙasa?"
Haribai tace "Baba, magana ta fa haka take. Bunƙasar gidan nan ta dogara ne ga Hikimar mahaifiyar mu"
Sarki ya fusata, ya daka mata tsawa yana muzurai, yace sam ba haka wannan zance yake ba. Amma Haribai ta dage kai-da-fata cewar hikimar mahaifiyarsu a wannan gida ne sanadin haɓaka da albarkar gidan baki ɗaya.
A ƙarshe Sarki ya tashi ya fice daga ɗakin, yana tunanin hanyar da zai ladabtar da wannan ɗiya tasa, har ta gane cewa tayi laifi babba.
Akan haka ya ƙudurce cewa shine zai lalubo mata ƙasƙantaccen mutum ya haɗata aure dashi.
Cikin wannan mako Sarki Dheema ya lalubo wani mutum mai sana'ar saran itatuwa da faskarawa mai suna Nandu, yace masa "Kai Nandu! Zan aura maka ɗiyata Haribai"
Nandu yace "Ranka ya daɗe ni talaka ne, sam-sam ba zan iya ɗaukar ɗawainiyar rayuwar jindaɗin da ɗiyarka zata iya buƙata daga gareni ba. Don haka bani iyawa".
Sarki Dheema yace "aikuwa zaɓi biyu gareka, kodai ka auri Haribai ko kuma nasa a datse min kanka"
Ba shiri Nandu yace ya yarda da wannan aure.
Duk da irin dagewar da waziran Sarki gami da iyalansa sukayi akan hana wannan aure, amma ya kafe sai da akayi.
Haribai kuwa bata taɓa ɗaga kanta akan lamarin ba.
Akayi biki babu armashi, ta tafi tarewa a wani ruɓaɓɓen gida da mijinta Nandu ke rayuwa aciki nesa da gari.
A kullum da garin Allah ya waye, Nandu zai ɗauki gatarinsa ya tafi daji sana'arsa ta saran itace. Acan ne zai wuni aiki, sai da marece zai siyo kayan abinci da ɗan abinda ya samo, sannan ya kaɗo kansa gida abinsa, ita kuwa matarsa ta sarrafa abinda ya kawo ɗin zuwa abinci.
Sai Haribai ta lura da cewa tana wuni bata aikin komai a gida har sai mijinta ya kawo kayan abinci da yamma take aiki. Don haka rannan sai ta shaida masa cewar "ina ganin, daga yau, ka rinƙa raba ƙuɗin da kake samowa zuwa gida uku, kashi biyu ka siyo mana abinci wanda zamuci sau biyu a rana, kashi ɗayan kuwa mu rinƙa tara shi, idan yayi yawa sai mu ƙaro sabon gatari.. Inaso na rinƙa binka daji aiki."
Abinda ya faru kenan, babu jimawa kuɗin siyan gatari ya taru. Suka siya suna zuwa daji saro itace tare. Ya zamana ƙuɗin da suke samu a wannan aiki da wanda suke ajiyewa tari duk sun ƙaru.
Jimawa kaɗan kuma sai Harimbai ta sake samun wata dabarar. Ta sanar da mijinta cewar ta lura da cewar maƙwabciyarsu nada dutsen tishi da ake niƙa alkama izuwa fulawa, don haka tana ganin ya kamata su siyo shi domin ƙara haɓaka hanyar samar da kuɗinsu.
Nandu yayi murna matuka da haka, yace "duk yadda kikace haka za'ayi". Ya ɗauki kuɗin da suka tara ya nufi kasuwa. Bai dawo ba sai da ƙaramin dutsen tishi na dai-dai kuɗinsu.
Sannu a hankali ya zamana suna iya samar da kuɗin da zasu iya warware matsalolin gabansu.
Ita Haribai a iya niƙan data keyi tana samar da abinda zasuci a kullum. Don haka duk kuɗin da Nandu zai kawo gida ajiyewa kurum akeyi.
Daga baya sai Nandu ya ware fili a gidan, ya zamana a kullum itacen yake kawowa ya ajiye ba tare daya siyar ba.
Rannan akayi sa'a, lokacin ana fama da muku-mukun sanyi, sai wani Sarki yazo shigewa ta wannan ƙasa da jama'ar sa.
Ya sauka a wani daji nesa da gari, sannan ya umarci barorinsa su bazama nemo itacen da za'a hura wuta don jin ɗumi.
Koda isowar barorin cikin gari, sai sukayi kiciɓus da gidan Nandu mai ɗauke da tarin itace. Sai kuwa suka nuna buƙatuwarsu ga wannan itace. Nandu ya siyar dashi baki ɗaya garesu. Ai kuwa ya samu riba mai yawa daga wannan ciniki.
A wannan lokaci, Kar kaso kaga murna wurin Harimbai da Nandu.
Rannan kuma, Nandu yana saran itace, sai yazo kan wata bishiya mai kyau. Ganyayenta yala-yala, itacen jikinta kuwa sala-sala ne.
Daya komo gida sai yake nunawa matarsa kalar itacen daya samo a wannan ranar. Sai ta cika da murna, tace "Maigida, wannan ai itacen Sandal ne mai daraja. Aikuwa ya kamata ka ƙoƙarta samo irinsu da yawa ka girke a gidan nan".
Kasancewar Haribai daga gidan sarauta take, ta san darajar wannan itace. Domin sarakuna sunfi son ayi amfani dashi wajen ƙone gawarsu idan sun mutu ko kuma wajen shagalin bukuwan Havan da Pujan.
Kashe gari Nandu ya tafi daji, ya lalubi wannan itaciya ta sandal tare da soma saran ressan ta a hankali ta yadda zata ƙara tohowa. Haka ya rinkayi a kullum, daga wannan zuwa waccan, har sai daya tara wannan itace da yawan gaske.
Akwai wata alƙarya a kusa da birnin Pitugar wadda aka wayi gari Sarkinta ya rasu. Kafin rasuwarsa kuwa attajirin gaske ne. Har kuma yayi wasicci da a ƙone gawarsa da itacen Sandal bayan rasuwarsa.
Sai dai kuma akaf garin, an rasa wanda keda wadataccen itacen sandal da zai isa shagalin wannan biki. Akan haka ɗan sarki mai mutuwa ya bada cigiya zuwa maƙwabtan birane, har kuma akazo masa da labarin cewa akwai wani mai suna Nandu yana dashi.
Sai yace aje wajensa a siyo masa itacen akan ko nawa ya yanka.
Barorin ɗan sarkin sukayi murna da suka tarar da cewa Nandu nada kalar itacen da uban gidansu keso kamar yadda labari yaje gareshi. Suka siyi itacensa da darajar gaske.
Daga nan fa Nandu da mai ɗakinsa suka fita daga kangin talauci. Tunda sun samu tarin dukiya.
Nandu yasa aka gina musu ƙatan gida na sarauta mai cike da manyan zauruka, kai kace gidan sarkin garin ne.
Bayan tsawon lokaci da auren Nandu da Haribai, sai mahaifinta Sarki Dheema ya cika da tausayin ƴartasa, har ya soma da-na-sanin hukuncin daya ɗauka akanta.
Rannan sai ya yanke shawarar ya kai ziyara a garesu duka domin ganin halin da suke ciki.
Bayan ya gama shirya kyaututtukan dazai kai musu, sai ya tashi tare da da barorinsa, kai tsaye ya nufi gidan babbar ɗiyarsa Kalimbai. Yana ɗokin ganinta, a zuciyarsa yana rayawa cewar tabbas tana cikin farin ciki.
"Ɗiya ta Kamli, yaya kike?" Sarki Dheema ya faɗa yayin haɗuwar su da Kalimbai.
Kalimbai ta rugo da murna, ta gaishe da mahaifinta. Sannan ta gabatar masa da ƴaƴayenta waɗanda tace ƙiriniya tayi musu yawa, ko makaranta ma basa zuwa.
Sarki Dheema ya kaɗu da yadda yaga wannan gida duk a hargitse. Ga yara duk babu natsuwa. Sannan Barori biyu ne kaɗai suka rage a gidan, yayin da a farkon aurensu gidan cike yake da masu hidimta musu. Tabbas da alamu karayar arziƙi ta gitta a wannan gida.
Ai kuwa da Sarki ya zanta da ɗiyar tasa sai ya gane cewar itace silar durƙushewar maigidan nata, domin kullum cikin buƙatar kashe kuɗaɗe take, ta gaza sauya rayuwa daga wadda ta saba a gidan sarauta zuwa gidan aure data samu kanta.
Ran Sarki Dheema a ɓace ya fito gidan, yace gida zai koma domin shawarta abinyi.
Yana isa kuma sai akazo masa da katin gayyata, akace masa wani attajiri ne yayi sabon gida yake gayyatarsa bikin tarewa domin neman albarkarsa.
Da sarki ya isa gidan, sai yake ta mamakin girma da kasaitar sa. Mai gidan ya fito ya tarbeshi. Sarki yayi mamakin yadda wannan baƙon attajiri yazo garinsa ya bunƙasa ba tare da saninsa ba.
Ana haka sai ga ƴarsa Hambai ta fito cikin kayan ƙawa, tana ɗauke da murmushi a fuskarta, tana mai marhaba lale ga mahaifinta.
"Sannu da zuwa mai martaba mahaifina".
Sarki Dheema ya cika da mamaki, "ɗiya ta, gidan kine wannan!!!?"
Ta amsa masa da cewa "kwarrai kuwa"
"Tayaya haka ta faru?" inji Sarki Dheema.
Hambai tace "Ranka ya daɗe, ka tuna da abinda ka taɓa karantawa a ɗaki na?.." Daga nan cikin ladabi ta zayyana masa duk hanyoyin da suka bi har rayuwarsu ta zamo haka.
Sarki Dheema ya gyaɗa kansa sama cikin mamaki. Ya raya a zuciyarsa cewa hakika ƴarsa tayi gaskiya.. Duk gidan dake ɗauke da Mace mai hikima, wannan gida sai ya bunƙasa.."

No comments:

Post a Comment